Showing 54001 words to 57000 words out of 231169 words

Chapter 19 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9674

sake yi masa musu ba...hakan ne kuwa ya faru dan kasa cewa uffan tayi..tayi kasa da kai cikin ranta tana mamakin tasirin da eyes dinshi suke dashi a kanta...kofa ya nuna mata yana kallonta alaman she should enter...ba musu balle gardama ta shigo ciki a hankali kaman mara lafia...changing room ya nuna mata ba tareda yace komai ba haka ta shiga ciki tanajin kaman ta dora hannu a kai tace wayyo Allah...bayan ta shiga shima ya shiga doctors changing room yayi changing zuwa theater outfit dinsu snn ya fito zuwa main theatre...matar tana kwance masu anaesthesia sun fara aikinsu a kanta sai doctor faith da doc gabriel da zasuyi aikin tare...ganin har zasu fara bata fito ba ya fita zuwa dressing room din...a tsaye ya sameta ta gama sa kayan sai kallon kanta take tana ganin yanda kayan sukayi mata yawa...tana turo baki tace"kayan ma over size n..."bata karasa idanunta ya sauka cikin nashi sai tayi saurin daidaita kanta da sauri tana cewa"am sir..d..dama yanxun..zan fito"...kallonta yayi from head to toe snn ya tsayar da idon nashi kan gashinta datayi parking a tsakiyar kai ta saki jelar yanata yawo tsakanin wuya da shoulders dinta...da sauri ta dauki hijab dinta ta rufe kan nata dashi baki a tunzure tana fadin"to babu hula fa"...baice mata komai ba ya karasa cikin dakin ya bude wani drawer ya zaro mata one of huluna da suke ciki snn ya wurga mata...saida ta daure fuskanta tsaf snn ta dau hulan ta saka cikin ranta tana zaginshi sbd cilla mata hulan da yayi...hanya ya nuna mata ba musu ta shige gaba yabita a baya...a bakin main theater suka tsaya ta zura wnn gunduma gunduman takalman snn suka shiga ciki...itadai a tsorace take dan bata ta6a shiga theatre ba..tsananin tsoronta ma bazai bari ta shigaba dan ko Allah ya san batason ganin ana yanka mutum sam...amma yau wnn inyamurin ya sanyata dole ta shiga dukda rashin son nata...saida suka gama shirya komai tsaf snn kowa yasa nose mask dinshi suka fara aikinsu...Aysha dai na tsaye tana faman runste ido don bazata iya gani ba wlh...Bobby dayaga yanda take runtse ido sai yayi mata alama da ta matso kusa...ta shiga yarfa hannu har ta fara hawaye shi kuma ya tsareta da ido yanda baza tayi mishi gardama ba...haka ta matsa inda ya nuna mata tana cigaba da hawaye har doc Gabriel nayi mata daria...kafin ta sake kulle idon yace mata"if u dare close those eyes again zakiga yanda zanyi dake wlh..and i mean it"...bata rufe din ba kuwa ta zuba idanu kawai tana kallon abunda sukeyi...kirjinta har sama da kasa yakeyi bata ta6a sanin tanada tsoro har haka ba sai yanxu...hankalinta bai sake tashi ba saida taga sun fara yanka matar...taga yanda suke cutting skin dinta layer by layer kawai sai taji wani hadadden jiri ya fara daukanta...kokari tayi ta rike gefen gadon gam still kuma taki kulle idon sbd kar yayi mata masifa...tun tana iya bakin kokarinta wajen ganin jirin baiyi tasiri a kanta ba har yakai limit din da bazata iya controlling dinshi ba kawai sai gani tayi dakin yana juyawa da ita...ta saki gadon da sauri tareda kai hannu ta dafe head dinta dashi idanunta a rufe still bata dena ganin jirin ba daga karshe ma sai ji tayi ta tafi luuu kaman zata fadi Allah ya taimaka akwai wani gado a bayanta kawai saita fada kanshi ji kake timm...a tare gaba daya doctors din suka dago suna kallonta don sunyi nisa a aikinsu that ba wanda ya lura da abunda ke faruwa da ita sai faduwan nata sukaji...dukda ta fadin kuma jirin bai dena daukanta ba har yanxun tana dafe da kanta hawaye na fitowa idanunta murya can kasa take fadin"wayyo Ammina..wayyo dadyna..wayyo Allahna"...gaba daya doctors din saida sukayi daria banda Bobby da baiga anything funny a nan ba...basubi ta kanta ba suka cigaba da aikinsu that last for 40 to 45 mins kafin suka gama...doc faith ce tayi resuscitating baby su kuma suka karasa duk wani necessary abu da zaa yima matar snn wanda zasu fita da ita sukazo suka dorata kan trolley sukayi waje da ita babynta kuma already an mikashi wa relatives dinta...sauran doctors din suma duk fita sukayi shi kuma Bobby bayan yayi sanitizing hannunshi ya nufi kan gadon da take thinking ko bacci take mishi a theatre and to his biggest surprise sai yaga ashe sumewa tayi...mamaki ne ya kamashi hade da daria at the same time...wato duk iskancin dan iska akwai abunda yake tsorata shi har ya sashi suman dole...shi tunda yake bai ta6a ganin Midwife irinta ba...wai matar dake dealing da kar6an haihuwa itace zata suma sbd Caesarean section "what a shame!.."ya fada trying to control his laugher cox he still can't believe sumewa tayi...wato duk rashin jin nan nata she has this phobia of blood ne ko of the operation din ne gaba daya ma bai sani ba...saida ya gama dariyarshi snn yasa aka kawo ruwa ya watsa mata...ta mike a gigice idanunta kulle take fadin" dan Allah no...i don't want to see it plss i beg u...wayyo Allah besty,Billy,baby come help me plssss"...ta karasa mgn new tears na rolling kan fuskanta...Dr.Bobby still can't believe this...knn da gaske suma tayi sbd abunda ta gani...lallai kuwa tanada aiki a gabanta...a very huge one ma kuwa...a hankali ta bude idonta sai taci karo da smiling face dinshi aikuwa ta wara idanun da kyau tana kallonshi to make sure she is not dreaming...tadai san idan ba mafarki ba ba yanda za'ayi inyamurin nan yayi daria for it's something she never seen..shi kuma ganin kallon da take masa sai ya dinke fuskanshi tsaf tareda matsawa daga inda yake yace"C'mon get dawn before i slap u lazy girl kawai...a haka zaki zama midwife kina painting sbd caesarean?..u are deceiving ur self"...goge tears dinta tayi ta sauko daga gadon tana fadin"ai ni ba ta6a gani bane shiyasa"...harara ya watsa mata yace"shiyasa nace u are deceiving ur self...now ki wuce ki jirani office and if u like kije wani wurin kiga idan na dawo banyi maganinki ba"...wucewa tayi tana sake turo baki sai kuma ta juyo zatayi mishi mgn yace"i said leave"...ba gardama ta sake juyawa ta fice daga wurin...duk jikinta ma wani iri take jinshi kaman na mara lafia...shiko Bobby bayan yayi changing zuwa normal outfit dinshi ya fita zuwa office...zaune ya sameta kan one of sofas dake nan ciki tayi wani dai dai kaman tana office dinta yana shigowa ta mike da sauri tana rarraba ido kamar munafuka...baice mata komai ba ya karasa gaban table dinshi ya dauki stethoscope ya rataya a wuya snn ya juya zai fita ya sake ce mata"Follow me"...banza tayi dashi tana binshi da harara har ya fita snn ta mike itama ta fita tana kwaikwayon mgnrshi" wani wai follow me...sai kace ajiyeni yayi in dinga yi masa bauta...mugu kawai"...ta karasa mgnr da guntun hawaye a idonta...ita dai zataga ranar da zatazo asibitin nan ta tafi bai sa tayi kuka ba...kullum burinshi ya sata yin abunda bataso ko ya wahalar da ita kawai sbd small mistake data aikata bayan ba kanta aka fara ba...Post natal ward suka je ya fara ward round ita kuma tana biye dashi a baya...data gaji da tsaiwa sai ta faki idonshi ta samu wuri zata zauna taji yace mata"zo kimin taking vital signs din wnn"...kamar ta kwada masa mari haka taji amma ba yanda ta iya haka ta mike ta fara taking vital signs din...a takaice ita ta dauki vital signs din duk patients din dake ward din shi kuma yana dubasu...kafin su gama kuwa jikinta yayi laushi liss kaman an nakada mata shegen duka...yau ma kamar jiya da kuka ta fita daga office dinshi bayan ya sallameta.

Haka kwanaki sukayita tafiya kullum Aysha na shan baqar wahala a wajenshi dan ba ranan da zatazo ta wuce bai sata kuka ba...gashi ita kuma ta kasa sabawa da wahalar da yake bata kullum idan ta gani bata ma sanin yaushe kukan ke zuwa...a haka suka kwashe two weeks suna abu daya har suka shiga sati na uku wich is their final week daga shi zakuyi resuming school...if u see how she is happy zakayi zaton graduation ne zatayi gaba daya...nan kuwa murna take sbd Allah ya kawo karshen wahalar da takesha hannunshi dan ko makiyinta bazata yi mishi fatan ya shiga hannun dr bobby ba dan bashda kyau ko kadan...cikakken mara mutunchi ne na gidan gaba shiyasa take addu'a idam sun rabu a nan Allah yasa rabuwarsu knn dan ko a College bata fatan ko hanya su sake hadawa dashi...laf cikinsu ita kadai ce batayi rotating wards ba sbd yanda ya makaleta a office dinshi amma su sauran kusan wards uku kowacce taje...ita Billy daga ANC ta koma Family Planning Unit daga nan kuma taje Ante Natal Ward duk tayi two two weeks a wurin amma ita duk yabi ya takureta a wuri daya ya hanata gaba ya hanata baya sbd baqin hali irin nashi...ita har yanxu tana mamaki idan akace mata musulmi ne dan har ga Allah wnn baqin halin nashi ba idabi'an musulman kwarai bane..ko da yake shima kilan musulmin ne kawai amma bana kwarai ba...shiyasa dole ma tayi murna Allah zai rabata dashi ta huta da ja'iba.














Rano✨






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitar min dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
19
Yau Thursday Aysha na zaune office dinshi ita kadai as shi tunda ya fita sallah bai dawoba dan haka ta bararraje abunta tana ta faman waya da Babynta da har yanxun bai dawo daga tafiyar da yayi ba...bayan sun kammala wayan tayi dialing number Ammi dan da gaske so take taje gida weekend amma Hamma yace wai ta bari ba yanxu ba...ringing biyu Husna ta daga wayan tana cewa"Addah.."tace"na'am ina Ammi?.."Husna ta dan turo baki tace"ke Adda bakida kirki wlh..daga daga wayan zaki wani ce ina Ammi ko gaisawa bazaki bari muyi ba?.."dan murmushi ta saki tana gyara zamanta tace"to sannu Husna ina yini..ya gida ya studies?.."daria Husna tasa jin yanda take gaisheta tace"kai Addah"...itama tana cigaba da smiling tace"to ai naga ba'a iya maki ne shiyasa na gaisheki"...Husna tace"umh to ina nan lafia ya posting?.."da sauri kaman wadda aka tsikara tace"posting dai yazo karshe ki tayani murna wlh..gobe Allah zai rabani da inyamuri in huta da azaba"...daria Husna ta sakeyi tace"nifa Adda har yanxu daria kike bani idan kika kirashi inyamuri..ina laifin ma kice dr bobby"...ta6e baki Aysha tayi tace"ki zauna saina kirashi dr bobby...mutuminda kowa yasan inyamuri ne shi..ranar bakiji wayan da naji yanayi da wani ba kilan dan uwanshi ne sukata inyamurancinsu abunsu"...sauke ajiyar zuciya Husna tayi tace"to congratulations Allah zai rabaki dashi gobe..amma zaku iya haduwa a cikin college fa"...tun kafin ta rufe baki Aysha tace"bakinki ya sari danyen kashi..nidai kiba Ammi waya inyi mgn da ita..where is my habibty?.."tace"yanxun nan suka fita da Hamma...Ammi kuma tana daki tace bacci zatayi kar in tasheta"...Aysha tace"karya kikeyi dan Allah ki kai mata it's urgent plss pls plss..kinji 'yar kanwata"...kafin Husna tayi mgn ta jiyo voice din Ammi tana cewa"Husna daukan min waya kikay kou?.."da sauri ta mika mata wayan tace"dama Adda ce ta kira gashi"...batayi mgn ba tasa hannu ta amsa wayan...Aysha ta wani narke kamar tana gaban Ammin tace"my Ammi"..tsaki Ammi taja tace"zakiyi mgn ko bazakiyi ba?.."ta sake narkewa tace"Ammi zanyi...amma fa nayi missing dinki sosai wlh...wai yanxu Ammi ni ko dan pampering dina sbd bana gida bazakiyi ba kuma fa nice fisrt love dinki tunda ni kika fara haif..."bata karasa ba Ammi tace"Aysha zakici ubanki wlh...abokiyar wasanki ne ni da zakina fadamin such maganganu..wato sbd kinga kwana biyu kinata zuba rashin mutuncinka na kyaleki kou?..to zaki dawo gidan nan ki sameni zany maganinki"...da sauri tace"Ammi am sorry dan Allah...kiyi hakuri ban karawa"...wani tsaki Ammi ta kuma ja tace"naji...yanxun zaki fadi ur reason for calling ko kuma iskancin naki zaki cigaba dayi?.."ta wani marairaice kaman abun tausayi tace"zan fada...Ammi dama fa so nake nazo gida weekend shine hamma wai ba yanxu ba...dan Allah Ammi kice yazo ya daukoni kinji..wlh ina missing dinku"...kai tsaye Ammi tace"saidai kuwa kiyi hakuri dan gobe muma zamu wuce Abuja nasan shiyasa yace ki hakura..amma idan muka dawo ai zakizo so stop worrying urself"...da sauri tace"Ammi me zakuyi a Abuja kuma?.."tace"wani taro ne nasu daddynku akayi inviting dinmu and daga ni sai Najeeb zamu tafi banda su Husna dan nasan yanxun xaki ce an tafi dasu baa tafi dake ba...nasan sbd irin wnn halin naki dadyn ma yace a kyalesu a gida"...ba kunya har wani ajiyar zuciya ta sauke dan wlh da zaaje dasu itama daga hankali zatayi sai an biyo an tafi da ita...yanxu kuwa da taji babu su sai taji hankalinta ya kwanta..zuwa weekend dinma ta hakura idan suka dawo din sai taje...a hankali tace"to shikenan Ammi sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya"...Ammi ta amsa da"Ameen"snn sukayi sallama...tana ajiye wayan idonta ya sauka kan Bobby dake zaune yayi relaxing kan seat dinshi yana kallonta...ta zare idanu sosai hade da dora hannu a kirji cikin tsananin tsoron ko yaji abubuwanda ta fada a kanshi tace"Na shiga uku"...saura kiris daria ya su6uce mishi amma ya fuske...instead sai ya daure fuskanshi yace"so abunda kikeyi min a office knn idan bana nan kou?..yayi miki kyau"...hadiye wani yawu tayi da kyar cikin karfin hali tace"Sir..dan Allah am sorry...kaji"...ko kallonta baiyi ba ya mika mata hannunshi yace"bani wayan"..a razane tace"wich one?.."yace"ur phone"...nan take ta sake tsurewa duk a tunaninta yaji gulmanshi da sukayi tace"Sir dan darajan su Mummy kayi hakuri"...kallonta kawai yayi hade da girgiza kai yacigaba da aikinshi bai sake cewa komai ba...ita kuwa daukan wayan tayi ta turashi cikin jaka tana addu'an Allah yasa baiji wayan da sukayi da Husna ba...karfe uku ya sallameta as usual tana fitowa suka hadu da Billy da sauran 'yan hostel suka karasa inda bus dinsu yake duk suka shiga sai Hostel dinsu.

The following day duk da wuri suka shigo sbd friday gajeren rana ce and kowa tanaso a sallameta da wuri sbd su samu su wuce...lokacinda ta isa office dinshi yanata attending patients sai ta nemi wuri ta zauna kamar yanda ta saba tana sauraron discussion dinsu..wasa wasa tayi learning abubuwa da dama zaman da tayi office dinshi don sata gaba yake idan yana interacting da patient yace idan sun gama zaiyi mata tambayoyi dan haka take bude brain dinta da kyau tana kwashe duk abunda yake fadi..haka duk prescription din da yayi saiya nuna mata nan ma idan sun gama ya shiga mata tambayoyi iri iri so he've learned alot and ko ba komai ta wnn fannin dai zatace yayi abun kirki...da yake patients din ba masu yawa bane around 12 ya gama dasu snn ya fara shirin tafia sallahn jumu'a...before ya fita ya bata log book dinta da yayi signing already snn ya nuna mata kofa yace"A sauka lafia"...wani kayataccen smile ta saki da har both dimples dinta suka bayyana cikin tsantsan farin cikin zata rabu dashi tace"nagode sir"..daga haka ta fice daga office din bobby ya bita da kallo irin na mamaki...tunda yake da ita bai ta6a ganin such smile kan face dinta ba...yanxun duk wnn excitement daya gani kan face dinta na rabuwa dashi ne ko kuwa there is more to it?..kai ai daga gani ma wnn na rabuwa dashi ne...haka nan kuma sai yaji baiji dadin yanda tayi ba.."am i this bad?.."ya fada a fili kaman he's asking someone...ganin yana wasting time dinshi a banza kawai ya fita zuwa parking lot driver na ganoshi ya bude mishi mota ya shiga suka fita daga asibitin.

Ita kuwa Aysha office din da aka fara posting dinsu taje nan ta samu sauran colleagues dinta a wurin kowacce an sallameta an kuma yi mata signing... daga nan aka basu certificate shknn aka sallamesu kowa ta kama gabanta...ita da Billy tare suka fito zuwa parking lot amma basuga motan Sa'eed da yace zaizo daukansu ba...suna kokarin zama sai gashi nan ya karaso dan haka suka karasa inda yayi parking...ko a hanya Aysha kasa 6oye excitement dinta tayi Billy sai tsokanarta take wai daga yanxu tanayi mata laifi zata hadata da proprietor tunda shine maganinta...ita kuwa sai hakilo take bestynta na tayata...yana ajiyesu a hostel suka shiga ciki shima ya wuce.

Around 5 pm suna zaune room 3a gaba daya sai labari suke suke darawa...they are all happy sun gama Clinical Posting dinsu lafia...wayan Aysha data bari cikin dakinsu nata ringing bata ji ba sbd hayaniyan da sukeyi...wata da tazo wucewa taji ringing din shine ta dauka ta kai mata dakin da suke...tana duba screen taga Baby boo jiki sai ta mike da sauri ta fita daga dakin tana fadin"my husband is calling"...Rahma tabita da kallo tana daria tace"Billy wai ina mgnr Sir Abdool ya kwana ne naga Lamido har tayi mishi kishiya sbd wulakanci"...Billy tace"ki bari kawai wlh tunda nake ban ta6a ganin mace kaman Lamido ba...she is indirectly rejecting him for that sugar daddy"...gaba daya daria suka saka kafin wata tace"nima dai ina mamakinta wlh..ta samu mutum kmr sir abdool da yake bala'in sonta wai ta kyaleshi for someone else..she is kind of different"...nan kuma akalar hiran nasu ya koma kan Lamido and her love for sugar daddies kowa yana fadan albarkacin bakinshi...tana fita ta fada room dinsu hadda rufe kofa snn tayi picking...before she says anything yace"My baby am back"...wani ihu data saka saida ya janye wayan daga kunnenshi...lokaci daya kuma ta toshe bakinta tana zaro ido feeling so ashamed of herself for behaving like this...sam batasan sanda ihun yayi escaping bakinta ba wlh..she is just super excited he's back dama ga farin ciki rabuwa da inyamuri ga kuma another good news...shi kuwa Prof daria ya saki sosai jin tayi diff kaman ruwa ya cinyeta yace"baby girl why are u quite?."kamae zatasa kuka tace"sorry...ban san yaushe ya fito ba wlh..am just happy u are back"...murmushi ya kara saki yace" don't worry yanxun dai ki samu ki fito waje in ganki"...idanu ta sake budewa tace"wait..u mean kana hostel dinmu?.."yace"komai bazan iya yi ba har sai na ganki"...ai bata jira ya karasa ba ta kashe wayan da sauri ta rarumi hijab

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login