Showing 180001 words to 183000 words out of 231169 words

Chapter 61 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9718

beautiful face dinta da yasha light make up ya bayyana..Bobby lumshe ido yayi ya furzar da iska kafin ya sake bude idanun a kanta..hannunshi yakai ya kamo nata da yasha red and black henna ya shiga shafa lallen a hankali yana kallonta..dagowa itama tayi tana kallonshi sai kuma ta kasa cigaba da kallon nashi sbd faduwar da gabanta yayi..idonshi taga yayi wani iri shiyasa bazata iya juran kallonsu a haka ba...hannun nata yakai bakinshi ya manna mishi peck a hankali kuma yana cigaba da kallonta yace"u look..."kasa karasawa yayi ya dago fuskan nata yana kallon eyeballs dinta yace"u look.. extraordinary..beautiful..kishi nakeji wasu su kalleki a haka"..hannunta takai itama tayi cupping nashi fuskan tana binshi da kallon da tasan bazai iya resisting ba tace"kayan hakuri it's just for today"..kai ya shiga gyada mata yana murmushi yace"yes.. it's only for today..daga gobe ana daura mana aure shknn u have become mine"..kai itama ta sake gyada mishi tana murmushi alaman yes..kasa hakura yayi saida ya janyota ya hadata da jikinshi sbd yanda yaji kmr fizgarshi akeyi zuwa gareta..hannu takai itama ta zagaye bayanshi dasu a tare suka sauke ajiyar zucia..voice dinshi na breaking yace mata"I..love..you"..lumshe ido tayi itama a hankali tace"I love u too"..dagota yayi daga jikinta yana sake kallon face dinta da har yanxu baiji zai iya gajiya da kallonta ba..itama kallonshi tayi sai taga ya kara haske yayi wani irin kyau da tunda take dashi bata ta6a ganin yayi mata kyau haka ba..shadda ne a jikinshi getzner sai sheqi yake milk colour da aikin coffee a jiki..hula da shoes dinshi suma duk coffee hatta links dinshi coffee colour ne..kallonshi kawai take tana sakin murmushi cikin ranta tana godia wa Allah daya mallaka mata such a handsome man as her hubby..he's looks so cute da har ta kasa dauke idanu a kanshi saida Nur yayi knocking musu kofa duk suka dawo hayyacinsu...bude kofar tayi da sauri ta fita don wani kunya da taji ya rufeta..shima ya bude side dinshi ya fito yana sakin murmushi dake sake fito da annurin face dinshi...su Billy da abokan ango ne sukayi arranging kansu suka sanya bride and groom a tsakiya snn aka sakar musu sauti suka fara shiga ciki...wajen ya cika ya tumbatsa da mutane ba daga brides family ba ba kuma groom's family ba dan suma sunzo da yawansu ne tamkar dama a Gomben suke da zama...tun da suka shigo idanun kowa ya dawo kansu kmr dai yanda ya saba kasancewa a every gidan biki amarya da ango na shigowa all attention yake komawa kansu..duk Wanda ya kallesu sai ya sake sbd tsabar haduwan da sukayi..hannunta na rike cikin nashi suke takawa a hankali ita kanta a kasa yayinda nashi kan ke daidai sai sakin murmushi yake..sunyi matukar dacewa da juna ne sosai ba kadan ba..hatta Mummy da Ammi da kowa take zaune inda aka tanadar mata tareda jama'arta kallon 'ya'yan nasu sukeyi full of love..they look so perfect together..they look takeaway kaman a daukesu a gudu..Lamido dai sake nutsuwa tayi na musamman sbd warning da Ammi ta kora mata wai idan ta kuskura tazo tayi mata rawar kai sai taci ubanta..wnn dalilin yasa ta sake nutsuwa tana takawa daidai har suka karasa inda aka tanada dominsu..bayan sun zauna bridesmaids dinta suma suka zauna a side din da aka tanadar musu likewise abokan ango..bayan sun zauna mc ya fara gabatar da surutanshi kmr dai yanda aka saba..aka bukaci bride and groom da su fito kan stage..tasowa sukayi a hankali Bobby na rike da hannunta suka fito stage din..maman amarya da ango aka bukaci da su fito su nunawa 'ya'yansu so..nan take Mummy da Ammi suka fito kowacce cikin shiganta na alfarma..yanda Ammi tayi kyau mutane da yawa sai sukayi mamakin wai ita ta haifi Aysha yayinda itama Mummy mutane da dama sunyi mamakin ganinta matsayin mahaifiyar Bobby sbd kyawun da tayi...Mummy tana zuwa batasan sanda ta rungume Aysha ba sbd farin ciki aikam wurin ya kaure da tafi da surutun mc..bayan nan sukayi musu watsin kudi snn suka koma..daya bayan daya ake Kiran mutane suna zuwa su watsa kudi su koma su Hajia Aunty Sumy da Aunty Munubiya dama sauran aunties dinshi na both familyn Mummy dana daddy duk sunyi ankonsu iri daya kuma sun taka rawar gani sosai...qawayen amarya su Billy suma ba'a barsu a baya ba sun taka rawar gani sosai sunsha liki suma tareda besty da bai dade da sauka ba...lokacin da aka fara rawa Aysha jikinta har rawa ya farayi sbd so take tayi amma idanun Ammi dake kanta sun hanata kata6us..ga kuma shi kanshi Bobbyn daya kama hannunta ya rike gam sbd gudun kada tace zata shiga tayi rawar don yasan halin kayanshi amma duk hakan bai yiwu ba don aunty Fiddausi da kanta tazo ta dauketa tace a ware musu fili zasuyi rawa aikam duk aka basu wuri dj ya saka musu waqa amma sbd kunya Aysha sai taji ta kasayin rawar kasancewar su biyu ne a wurin..kunyan su Mummy taji ya kamata don haka ta kasa zagewa tayi kaman yanda tayi jiya sai da su Billy suka shigo snn ta dan samu tayi tunda tasan ba ganinta za'ayi sosai ba..can su Aunty Sumy suma suka shigo sai kuma ga su Husna da Miemie da batasan yaushe suka zama qawaye ba..Yusra da Ilham suma duk inda sukayi suna tare don sosai suma suka rakashe a bikin Addah da Uncle Bobby..Ammi dai na zaune tana kallonsu tana daria wato ita dai Fiddausi har gobe bazata gane cewa ta girma ba knn...a fannin su Nur abokan ango suma ba'a barsu a baya ba dan sosai suka taka rawar gani a wurin mutane sai jinjina Kara irin nasu suke...lokacinda aka bukaci su fito suyi rawa Bobby yasha kallon rawa hadda na hauka wajen Friends din nashi especially Nur daya dage sosai yana dilliqar rawa shi ko kunyar students dinsu dake wurin ma baiyi..shi kuwa duk yanda akayi dashi kan yayi rawar kinyi yayi wai shi bai iya rawa ba saida aunty sumy tazo da kanta ta kama hannunshi ta shiga juyawa dashi kuma dukda hakan baiyi rawan da sukeso yayin ba...in summary dai taro yayi kyau Kuma yayi tsari sosai mutane sunci sunsha sun Kuma yi rawa yanda ya kamata..(kunsan dai duk bikin da ba'aci abinci anyi rawa ba bai amsa sunanshi biki ba).
Sai kusan karfe karfe goma na dare aka tashi daga taron mutane kowa ya nemi motar da yazo ya shige ciki aka fara maidasu gida..su Mummy da ahalinta suma duk motocinsu suka shiga suka wuce gida yayinda Ilham da Miemie suka dage kan su saidai a barsu a nan tunda gobe daurin aure..Aunty Sumy batayi musu musu ba ta kyalesu tunda taga yanda jininsu ya hadu dasu Husna don haka ta wuce tareda alqawarin zata aiko Sab ya kawo musu kayansu na gobe.

Nur na gama parking a kofar gidan uncle dinta ya juya yana kallon Bobby dake zaune baya yace"5 mins na baka kayi round up don na gaji so nake na huta"..harara Bobby ya watsa mashi kafin yace"ba dole ka gaji ba kaje ka dirki rawa kaman ba namiji ba"..banza Nur yayi dashi ya bude motar ya fita ya rage daga shi sai amaryarshi a ciki..a hankali ta dago tana kallonshi shima kallon nata yakeyi suna hada ido ya sakar mata smile dinshi mai kyau yace"I love you"..kai kawai take gyada mishi tana murmushi tama kasa cewa wani abu..kallonshi take kmr yanda yake kallonta..murya can kasa ta kira sunanshi"Partner"..ba tareda ya dauke idonshi a kanta ba yace"yes my partner"..hannu takai ta kama nashi hannayen tana kallon eyeballs dinshi tace"kayi kyau"..murmushi ya saki kafin yace"not as u baby..na tabbata ban kaiki kyau ba"..kallonshi kawai take ta kasa dena murmushi sbd farin ciki..Bobby ya lumshe Ido ya bude kafin ya sake matsawa kusada ita yana cewa"love gobe iyanxu kin zama matata na zama mijinki"..Kai ta sake gyadawa cikeda farin ciki..shi Kuma ya sake lumshe idonshi ya bude tareda daukan hands dinta ya dora chest dinshi har yanxun idanunshi a kanta yace"shknn daga gobe duk abunda naga dama zanyi maki and nobody will asked why?.."gyada kai ta sakeyi babu bakin mgn..shi kuma a hankali ya hada fuskanshi da nata before yacigaba da fadin"i can hold u to my arms..i can hug and kiss u baby..i can even..."bata bari ya karasa ba ta toshe bakin da hannayenta..kmr zatasa kuka tace"partner ba saika karasa ba plss..kunya nakeji"..murmushi ya saki yana girgiza kanshi yace"then kinada babban aiki a gabanki..a very huge one"..janye jikinta tayi daga nashi tana turo baki tace"kuma ni fasawa zanyi"..daria sosai Bobby ya saki tareda janyota ya rungume a jikinshi..soyayyarta yakeji na karuwa cikin heart dinshi fiye da yanda yakeji a baya..Allah kadai yasan yanda yakejin kmr ya janyo gobe sbd a daura mashi aure da ita ta zama property dinshi ko hankalinshi zai kwanta..itama lamo tayi a jikinshi ta lumshe tana shaqan daddadan qamshin da yake fitarwa..lokaci mai tsaho suka dauka a haka gaba daya sun manta da kowa da komai burinsu bai wuce su dawwama a haka ba har mahdi ya bayyana..gaba daya sabon son juna ke sake ratsa zukatansu abun kmr hadin baki..Nur da ya gaji da zaman jiransu a waje daddagewa yayi yayi knocking glass din window aikuwa firgigit suka dawo hayyacinsu Bobby ya raba jikinshi da nata a hankali yana kallon face dinta da tayi kasa dashi tana murmushi...bude kofa Nur yayi tareda lekowa tana kallonsu kmr zaisa musu kuka yace"Lamido a sakar mana shi haka mu wuce dan Allah..wlh na gaji so nake in samu in huta"..kai kawai ta iya gyada mishi tana kokarin kwace kanta a hannunshi amma yaki sakinta..daga Ido tayi tana kallonshi shi kuma ya lumshe Ido tareda pecking forehead dinta snn ya saketa yana cigaba da kallonta with a bright smile yace"good night wife"..juyawa tayi ta fita daga motar da sauri har tana hadawa da gudu.

Wedding Fatiha...

Tun safe both bangarori suka fara shirin daurin aure da za'ayi 11 na safe a nan cikin Lamido's Palace..Bobby har nafilah saida yayi na nuna godia wa Allah for witnessing wnn ranar in his life and for praying Allah ya basu zaman lafia da zuri'a nagari..ya roki Allah ya bashi ikon riketa Amana ya kuma bashi damar kulawa da ita iyakar karfinshi..addu'a yayi musu sosai yana idarwa kuma ya fada bathroom yayi wanka snn yazo ya fara shiryawa..some of abokanshi da suke tare dashi sai tsokanarshi wai ya cika zumudi shikam saidai yayi murmushi kawai sbd yasan bazasu ta6a ganewa ba..bazasu fahimci abunda yakeji gameda yarinyar ba shiyasa duk suke wnn surutan.
A gidan Waziri ma sun gama shiryawa tsaf Waziri da kaf yayanshi maza da 'ya'yan 'yan uwanshi da abokanshi dana yaran nashi kai har ma da jikoki duk sun hallara a gidanshi lokaci kawai suke jira su tafi inda za'ayi daurin auren.
Su Mummy ma suna gida suna nasu shirin don a yau zasu wuce da amarya kano zuwa da yamma suma zasuyi igbo day dinsu a can.

A can gidansu Aysha ma shiri sukeyi sosai tun daga kan daddy da sauran 'yan uwa da abokan arziki har zuwa kan Lamido da nashi mutanen shima sai kuma Hajia Ammi da familynta..sosai suke shiri don tun yanxu Estate din nasu ya fara cika da mutane from different angles na Nigeria..manya manyan mutane suna nan da yawa wasu jama'ar daddy ne wasu kuma jama'ar Lamido.














Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
56
Karfe Sha daya da 'yan mintina dubban mutane suka shaida daurin auren Attahir Attahir Waziri(Bobby)da kuma Aysha Ahmad Lamido akan mafi karancin sadaki kaman yanda addinin musulunchi ya tanadar...jama'a sosai ta ko ina Estate din ya cika fal tun daga gidan Lamido har zuwa ciki wajen gidan su Aysha mutane ne keta 6ullowa ta ko ina...ango Bobby tunda yaji anyi sanarwar aure ya dauru tsakaninsu shaidu sun shaida kuma an shafa fatiha sai yaji wani irin nustuwa mai hade da kwanciyar hankali sun sauka a zuciarshi..wani irin feeling yakeji irin na wanda ya samu cikar burinshi bayan yasha wahala...mutane sai zuwa suke suna congratulating dinshi dukda hayaniya dake tashi a wurin ga masu algaita suma da suketa faman busa tun kafin a fara daurin auren...a nan cikin Estate din sukayi reception daga nan kuma suka shiga cikin gida don gaisawa da iyaye..har suka gama gaisuwan suka bar gidan Bobby baiga matarshi ba duk sai yaji hankalinshi ya tafi wurinta burinshi kawai ya sanyata a Idonshi..har sun shiga mota zasu koma can gidan dasu Mummy suke don suna can suna jiran dawowarsu wai za'ayi pictures kasa hakura yayi ya shiga Kiran wayanta amma bata dauka ba dan haka kai tsaye yace ma Nur ya kaishi gidan uncle dinta tunda yasan a can take kwana..kallonshi Nur yayi da mamaki yace"seriously..su Mummy na gida suna jiranmu fa snn ga abokanmu da suka fara wucewa can me kakeso muce musu idan suka rigamu zuwa?.."kama hannunshi Bobby yayi suka dan koma gefe ya wani marairaice kmr ba ango ba yace"Nur try and understand mana..zuwa fa kawai zamuyi mu ganta da gaske ba dadewa zamuyi ba"..ajiyar zucia Nur ya sauke tareda komawa ya sallami wasu daga friends dinsu dake jiransu snn ya dawo tareda wasu suka shishshiga mota zuwa gidan uncle din nata gaba dayansu...a kofar gida yayi parking snn ya sake kiran wayanta ganin bata dauka ba ya kira na Billy..sukayi sa'a kuma ta dauka nan yake fada mata sunzo suna kofar gida..wani irin ihu da yaji sun saki ya tabbatar mishi a hands free ta sakashi knn...walida ce ta fito tayi musu iso har cikin parlor..Lamido na zaune sun wani sanyata tsakiya fuskanta a rufe kmr wanda take yin kuka..hankalinshi yaji ya tashi badai yarinyar nan kuka take ba..ganin ya nufo inda take direct duk sauran mutanen da suka zagayeta suka mike daga wurin Bobby na isa ya mikar da ita tsaye kawai ya rungumeta tareda lumshe ido hawaye farin ciki na ciko idanunshi..he can't believe yau shi aka daurama aure da Lamido..rungumeshi tayi itama sosai tana hawaye sosai kmr Wanda akama auren dole..tunda taji an daura aure jikinta yayi wani irin sanyi data tuna shknn fa yanxu gidansu zata bari gaba daya..tafia zatayi ta bar su Ammi da daddy da Husna da Yusra?..oh Allah ashe haka auren yake?..dukda ta saba tafia ta barsu idan zataje makaranta amma wnn tafian yana da bambanci da Wanda ta sabayi a baya...tafi ta sowar da occupants din wurin suke shi ya dawo dasu hayyacinsu..a hankali ya dagota daga jikinshi yana share mata hawaye gamida girgiza mata kai alamar she should stop..sake 6are baki tayi zata dora daga inda ta tsaya kawai ya hade fuskanshi da nata yana mgn a hankali yace"baby stop..crying..mana"..lumshe ido tayi tana kokarin maida hawayen da suka kasa tsaiwa idanunta..hotuna da videos dai sun shasu a wurin jama'ar dake wurin kowa kokari takeyi ta samu na sawa a status..a takaice dai haka akayi pictures din da za'ayi musu Aysha bata dena kuka ba shi kuma angon nata bai dena aikin lallashi ba..kasa ma tafia yayi wai bata dena kuka ba saida Nur yayi da gaske snn ya samu ya wuce suka tafi..gidan Waziri suka fara zuwa nan ma sukasha hotuna tareda Waziri da uncles dinshi daga nan kuma sukayi can gida inda su Mummy suma suka dora daga inda suka tsaya..karfe biyu da wani abu suka fara shirin tafia kano Wanda zasu dauko amarya already dama sun tafi tun daxun don haka wucewa kawai zasuyi daga nan.

Wata qanwar daddy ce tazo har gidan da suke ta shiga da ita bathroom bayan ta hada mata ruwan wanka full of turaruka tace tayi maza tayi wanka ta fito...tana kuka sosai ta shiga tayo wankan ta fito daidai lokacin kuma Aunty Fiddausi ta kawo mata kayan da zata saka suma bayan an gama turarasu..har zuwa lokacin bata bar kuka ba haka suka hada kai suka gama shiryawa tsaf qanwar daddy mai suna Aunty Amina ta nada mata farin laffaya daya amshi jikinta sosai..daga nan kuma suka kama hannunta suka fita tareda some of friends da cousins dinta da za'a tafi kai amaryan dasu...gidansu aka fara kaita daddy da Ammi sukayi mata nasiha sosai tareda yi mata fatan samun dawwamammen farin ciki a gidan aurenta..daga haka daddy yace su kaita wajen Lamido..Aysha dake kuka wiwi zuwa tayi ta rungume Ammi tana Kara sakin wani kukan kmr dai mutuwa zatayi ta barsu..duk karfin hali irin na Ammi saida ta zubda hawaye itama..ko Allah yasan ba karamin kewar 'yarta zatayi ba amma ya zasuyi?..haka gadonmu yake domin kowacce mace saita dandani wnn zafin na rabuwa da iyaye yayin da zata tafi dakin miji..har su Husna da Yusra kuka suke sosai Billy na tayasu..abun sai ya zama kmr a gidan mutuwa ba gidan biki ba..Saida daddy yayi da gaske snn suka iya 6an6areta daga jikin Ammi sukayi gidan Lamido da ita..ko cikin mota bata dena kuka ba har suka isa gidan Lamido..nan ma cike yake da uncles dinta haka suka dangana da ita har kusa da Lamido snn suma suka zauna..nasiha ya shiga mata shima sosai duk kan zaman aure da rayuwar gidan miji..bayan ya gama wasu daga cikin uncles dinta suma sukayi nasu daga nan kuma aka sake daukanta zuwa wajen wadanda sukazo daukanta suke..tana kuka sosai aka bude back seat ta shiga ciki tareda aunty Fiddausi da Aunty Amina da suka sanyata a tsakiya Billy kuma na front seat driver ya tada motar suka tafi..da akwai wasu motocin guda biyu daya na cousins dinta da wasu daga friends dinta dayan kuma duk yan uwan daddy da Ammi ne zasuje sbd event din da za'ayi a can Kano.

Gidan Waziri aka fara kaita nan ma Waziri ya hadasu tareda Bobbyn yayi musu nasiha sosai daga nan kuma kai tsaye suka wuce Kano don su Mummy already sun dauki hanya tun daxun..shima Bobby daga nan gidan suka shiga motocinsu suka tafi tareda zugar abokai da coworkers dinshi..ko a hanya duk tunaninshi ya koma kanta ne..yanda yaga take kuka daxun abun ba karamin daga hankalinshi yayi ba..wai shi wnn kukan dole ne sai anyishi ko kuwa nata ne dai ya wuce gona da iri?..duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login