Showing 36001 words to 39000 words out of 231169 words

Chapter 13 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9667

tears dinta snn ta shiga office din kai a kasa kaman munafuka...kanshi na sunkuye yana signing wasu papers so bai ga wanda ya shigo ba...ta karasa gaban table dinshi ta tsaya gabanta sai aikin faduwa yake...batasan why take tsoron bawan Allahn nan ba dan duk yanda takai da son ta bude baki tayi mgn kasawa tayi...kawai imagining take ta koma gida daddy ya samu labarin an hanata exam sbd tayi lalle...duk wnn abun da take baisan tana tsaye kanshi ba saida ya gama signing papers din ya dago...mamaki ya kamashi sosai dan baisan itace bakuwar ba...idanunta rufe suna fitar da hawaye sai bakinta daketa motsi kaman tanaso tace wani abu...kallonta ya tsaya yayi da kyau irin kallon da bai ta6a yima wata mace a dunian nan ba...tun daga kan idonta da suke rufe har zuwa kan lips dinta dake shinning as a result of hawaye daya wankesu har yanxun kuma basu dena motsi ba...haka nan yaji wani irin sanyi na rufe mishi jikinshi...irin internal sanyi da mutum keji idan yana fever...ya dauke kanshi da sauri sai kuma yaji hadadden zafi yana maye gurbin sanyin daya faraji...ranshi ya 6aci sosai jin yanda temperature dinshi ke raina mishi hankali...yanxun nn yakejin sanyi after a minute kuma ya farajin zafi...ita kuma har yanxu taki bude ido tana tsaye tana karanta mishi Yaseen cikin zuciyarta wai ko Allah zai dorata a kanshi ya janye abunda ya fada...ganin bayan sauyin temperature har mood dinshi ma ya fara sauyawa gata kuma ta wani yi mishi tsaye a kai kaman wata soldier ya sake dinke fuskanshi tsaf snn yace mata"keh.."a hankali ta bude idonta ta dora kanshi sai kuma ta sauke da sauri tana kwa6e fuskanta irin yanda babies keyi idan zasuyi kuka ganin wnn kallon data tsana yakeyi mata...kirjinta har bugawa yakeyi dan tsoro ta rasa wane irin magic mutumin nn keyi dake sanya mata tsoronshi haka...shidai Bobby baki da hanci ya saki yana kallon ta6ara iya ta6ara...yanda tayi da face dinta dama kana gani zakasan sanrgatacciya ce ta ajin farko ma kuwa...ranshi yaji ya sake 6aci dan a dunia ya tsani shagwa6abbun yara wlh...ya tsani yaga an zubama yaro ido yana zuba iskanci son ranshi baza ayi mishi fada ba sunan wai ana sonshi...can kasan makoshi yace"spoiled brat"...a fili kuma komawa yayi yayi relaxing kan kujeranshi still yana kallonta yace"leave my office if u don't have anything to say"...da sauri ta shiga girgiza kai cikin stammering tace"Sir...am...sorry"...wani kallo yake binta dashi before yace"what did u said?.."ta dan turo baki tace"i said am sorry"...tana rufe baki yace"sorry for yourself..now leave"...shima yana rufe bakin ta hade hannayenta alaman roko tace"Sir dan Allah...dan annabi..dan darajar Mummy da Daddy kayi hakuri"...shiru yayi yana kallonta totally speechless as ta fadi biggest weakness dinshi...in his entire life bashida weakness daya wuce parent dinshi likewise his strength especially Mummy that is still alive...ko ba'a fada ba kuma yasan aikin Nur ne wnn and he will definitely have to deal with him...ganin yanda yayi shiru ya kurama spot daya ido ta sake karya muryanta tace"Sir Please!.."wnn kallon dai data tsana ya watsa mata kafin ya nunata da finger dinshi strictly "but this should be your last...i promise duk na sake ganinki dashi you'll face the consequences"... tun bai rufe baki ba tace" nagode Sir..thank you so much"...bai sake cewa komai ba sai kofa daya nuna mata...ta dan ta6e baki tana goge tears dinta snn ta juya ta fita cikin ranta tace"inyamurin banza".

Taci sa'a tana zuwa aka fara raba question papers ta karasa seat dinta da sauri ta zauna...Billy daketa baza ido taga shigowanta tun daxu ta saki ajiyar zuciya dan sam hankalinta bai jikinta ganin har za'a fara bata shigo ba.

11 daidai suka fito daga exam hall...already Hamma Najeeb na zaune cikin mota yana jiransu dan haka suna fitowa suka nufi inda suka hango motanshi...shima yana hangosu ya bude motan ya fito...suna karasowa ta wani kwa6e fuska kaman zatasa kuka snn ta kama hannunshi ta rike idonta na cikowa da hawaye...hankali a dan tashe yace"what happened again?.."ganin taki mgn ya juya yana duban Billy yace"me akai mata?.."Billy ta buda hannu alaman bata saniba...shi kuma ya kama hannunta suka kan wasu cement chairs dake gefe still hannunta cikin nashi yace"Maama plss talk mana..waya ta6amin Mamana?.."tana turo baki tace"Hamma i don't want to come back to this college kayi mgn da daddy plss"..yace"but Maama why?..did something happen again?.."tace"Proprietor ne...Hamma wlh ya tsaneni..kawai daxu yayita min wulakanci hadda cewa bazanyi exam ba sbd nayi lalle..nidai i don't want to come back plss"...kamo dayan hannunta yayi yana dubanta da kyau yace"Maama kinsan daddy bazai ta6a yadda ba tunda ke kika dage sai an kawoki nan...but i think i have to talk to Proprietor din naku ya bar takura maki kawai"...tana goge hawayenta tace"there is no need..idan kaje ma wulakanci zai maka na sani...Hamma inyamuri ne fa..ko cikakken hausa bai iyaba"...yace"to indai bakiso inje in sameshi ki bar kukan nan haka..yanxun ku debo kayanku mu wuce amarya nata kirana wai inyi sauri in kaiku da wuri"..da sauri ta karasa goge hawayen nan da nan kuma saiga murmushi a fuskanta tace"laaa Hamma kasan har na manta wlh...Billy taso mu tafi nasan yanxu ana can ana shirye shiryen kamu"...girgiza kai kawai Billy tayi tana mamakin halin Lamido da shegen son biki..yanxun nan fa take kuka sha6e sha6e amma daga jin mgnr biki ta wartsake...kayansu kawai suka dakko daga wani class don dama basu fito da shirin komawa hostel ba..suka zuba su cikin booth snn suma suka shiga motan Hamma yaja suka tafi...basu samu yin sallama da Sa'eed ba as har time din yana exam hall bai fito ba..dama ba lokaci daya suka shiga ba so sun rigashi fitowa.

Saida suka fara tsayawa Bauchi suka ajiye Billy snn suka wuce Gombe bayan tayima Lamido alqawarin zata zo gobe ayi bikin da ita yau dai tanaso ta huta gajiya...suna shiga cikin Gombe murnanta ya kasa 6oyuwa dan ba karamin missing gida tayi ba...kai tsaye GRA suka nufa inda a nan Estate dinsu yake...Estate ne babba inda ciki duk wani wanda ke amsa sunan Lamido yake.. a nan ciki gidansu yake tun daga kan 'ya'ya da jikokin Lamido maza baya bari suyi nesa dashi mata ne kadai suke fita shiyasa ake yima Estate din laqabi da LAMIDO'S PALACE...horn yayi jikin tangamemen gate din shiga Estate din wanda daga can samanshi aka rubuta THE LAMIDO'S in capital letters..masu gadi sukazo suka bude mishi yasa kan motar ciki...tsayawa fadan haduwan ciki ma bata baki ne kawai dai is one of the biggest and beautiful Estate i have ever seen...ya tsaru ne iya tsaruwa snn yana daukeda gidajen da ni kaina bazance ga adadinsu ba don sunada yawa sosai...layi na uku ya shiga by his right side snn yayi parking motan a daidai kofan gidan daya kasance shine na uku layin...tun kafin ya kashe motar ta bude kofa ta fita da gudunta ta fada cikin gidan...bata ga kowa a parlor ba dan haka ta wuce zuwa dakin Ammi...a gaban madubi ta isketa zaune tana daura dankwali ta karasa da saurinta tayo hugging nata ta baya tana fadin"Ammi nayi missing diki wlh"...a hankali ta juyo ta zame hannunta daga jikinta snn ta daure fuska tana kallonta tace"bakida hankali kou?..wnn shine sallaman?.."rungume hannu tayi tana turo baki tace"Ammi nayi kewarki nefa sosai shiyasa amma kiyi hakuri"...juyawa Ammi tayi tacigaba da daurinta tace"zakici ubaki ne"...sake turo baki tayi tace"yanxu Ammi ko gaisawa fa bamuyi ba"...Ammi data gama daura dankwali tana kokarin sa wayanta cikin hand bag dake hannunta tace"ni kike jira in gaisheki ai tunda ke kika haifeni"...kaman bata son mgn tace"Ammi ina yini..ya gida"...tace"lafia lau ki wuce kije kiyi wanka ana gama ma su Husna make up kema ayi miki ku taho..tun daxun ake tafiya sbd ke nace su jira ku wuce tare"...tace"to bari inje Ammi..amma Aunty Fiddausi bata zo bane?.."tace"bazata samu zuwa ba Mufid ne ba lafia wai...yanxun mu fara zuwa ku gaisa da daddy sai kije kiyi wankan"...tare suka fita daga dakin bayan Ammi ta yafa mayafinta...tayi kyau sosai cikin coffee lace daya amshi skin clour dinta sosai snn kallo daya zaka mata kaga tsananin kamar da Lamido takeyi da ita...a zahiri kuma bazaka ta6a cewa ta haifeta ba dan yanda suka jero sai sukayi kaman kawaye...a palor suka samu daddy zaune yana yin waya...suka karasa ciki Ammi ta zauna kusa dashi ita kuma malama A'ee ta zauna a kasa tana wani irn nutsuwa kaman mutumiyar kirki...bayan ya gama wayar ya dubi Ammi da tayi mishi kyau kwarai yace"har kin gama?.."tace"na gama daddy zuwa zanyi Najeeb ya ajiyeni a hall din kafin ya fita..su kuma idan sun kammala sai Idris ya kawosu"..gyada kai yayi yana fadin"ohk"..snn ya maida kallonshi ga Aysha da take zaune tsumu a kasa kaman ba ita ba..cikin sabuwar nutsuwar data aro ta yafawa kanta tace"daddy barka da yamma"..yace"yauwa Aysha an dawo?.."tace"mun dawo daddy"...yace"Maa sha Allah ya exams?.."tace"daddy Alhamdulillah"...yace"to Alhamdulillah ya ban ganku tareda Bilkisu ba?.."tace"sai gobe zatazo daddy"..ya gyada kai yace"Allah ya kaimu..sai kije ki fara shiryawa kar suzo suna jiranki"..a hankali ta amsa da"toh.."snn ta mike ta bar parlon...itama Ammi mikewa tayi da bag dinta a hannu tace"nima bari in wuce daddy lokaci na kara tafiya"..kama hannunta yayi ya zaunar da ita yace"ki bari in kaiki da kaina mana...irin kyau da kikayi ya kamata ace sai na gama gani zaki tafi"..murmushi ta saki tana girgiza kai tace"daddy bakada dama wlh...inaga sai kaga mun aurar da Aysha snn zaka gane girma ya fara zuwan mana"...yaja dogon hancinta yace"ke girma ya fara zuwan ma bani ba..kuma ko mun aurar da Aysha ni babu abinda zai canxaki cikin zuciyata"..daria ta saki tana jin kaunar mijinta ta ko ina a jikinta snn ta sake mikewa tace"to nidai ayimin uzuri in wuce ba don ni ba..nasan yanxu ana can ana menana wlh"...bai sake yunkurin hanata ba yace"sai kin dawo Allah ya kiyaye"..ta amsa da"Ameen"..with a smile snn ta fita daga parlon...a main parlor ta samu Najeeb na jiranta dan haka yana ganinta ya mike suka fita tare..dukda cewa hall din da suke bikin cikin Estate din yake yanada nisa sosai da baza'a iya zuwa a kafa ba.

Aysha kuwa tana shiga dakinsu ta iske Husna zaune ana mata make up din Yusra kuma na kwance kan gado...saida suka gama rungume rungumesu itada Yusra as usual Husna nata faman ta6e baki tana binsu da harara snn ta fada bathroom tayo wanka sharp sharp ta fito...lokacin am gamawa Husna an farama Yusra...ita kuma ta tayar da sallah bayan ta idar ta dauki kayanta da yake iri daya dasu Husna har dinki ta saka snn ta zauna zaman jira.

Karfe biyar da wani abu suka shigo cikin hall din...dukkaninsu suna sanye cikin atampan ankonsu dark blue da adon sky blue a jikinta...kaman yanda na fada dazu hatta dinkinsu iri daya ne haka daurin dankwali da akai musu shima iri daya ne..takalmi da jakansu ne ya bambamta amma duk color daya ne...hall din ya cika makil da mutane banda sautin waka ba abunda ke tashi a ciki...amarya na zaune high table tareda angonta...Aysha na hangota ta fara zuwa inda take kawai suka rungume juna cikin rada tace"adda ruky kinga kyan da kikayi kuwa?.."amarya data kasance cousin dinta domin diyar yayan daddy ce tace"duk kyauna ban kaiki ba Lamido"..ta matsa daga jikinta tana dan turo baki tace"kema Lamidon zakice?.."itama amarya komawa tayi ta zauna snn tace"yes koba sunanki bane?.."tace"sunana ne kaman yanda kema yake sunanki..so daga yanxu duk kika kirani da Lamido kema da Lamidon zan kiraki"..murmushi kawai tayi mata ita kuma ta juya ta tafi..can inda ta hango da yawa daga cousins dinta ta nufa wanda duk yawancinsu age mates dinta ne suma duk suna sanye da anko...nan suka hau rungume rungume suna farin cikin ganinta.



Daga wnn page na kawo karshen Free pages dina sbd haka inayina kowa fatan alkhairi...wayanda sukayi patronizing a big thank u to all Allah ya saka da khairan🙏🏻

Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment ta 07063800556.












Rano✨






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344...sai a tura evidence via 07063800556.
13
Basu suka baro hall din nan ba sai after seven...lokacin duk an gaji su hajia Aysha a gajiye aka dawo gida sbd rawa da aka tika wajen...kai tsaye ta fada bayi ta watsa ruwa a jikinta snn ta fito tasa kayan bacci tareda hayewa gado ta nade kaman wanda zatayi bacci...sai yanxu ta tunada wayanta data bari a school bag din daxun...shaf ta mance data dawo bata fito dashi ba ta mike da sauri zuwa inda ta ajiye jakan ta zaro wayan snn ta sake komawa gado...missed calls ta tarar guda 46 aikuwa ta wara ido sosai tana kallonsu..biyu daga ciki na Billy ne sai guda hudu na Besty sai kuma wata bakuwar Number mai sauran 40 din...ta danyi shiru tana nazarin number lokaci daya kuma sai ta wara ido tana sakin murmushi data tuna mai number...wnn sugar daddyn ne da suka hadu a Chicken Republic ranan...Allah sarki bawan Allah shine yayita jera mata missed calls haka?..tayi mamaki ma da bai ta6a kiranta ba sai yanxu...har ta danna zatayi dialing number dinshi sai kuma taga bari ta fara kiran Billy da bsty tukun dan kar ta fara kiranshi ya cinye mata time bata kirasu ba...Billy ta fara kira suka gaisa tareda yima juna ban gajia snn Billy ta jaddada mata tana nan zuwa gobe inshaAllah...suna gamawa ta kura bsty shi kuma korafi yaketa yi wai basu tsaya sunyi sallama dashi ba suka wuce ita kuma tayita aikin bada hakuri har ya hakura...bayan sun gama ta wani sake lafewa kan pillown da take kwance tana lumshe idanu tayi dialing number dinshi da yanxun nn tayi saving as Prof...yana shiga kaman jira yake ya dauka sai ya sauke wani wawan ajiyan zuciya before saying"baiwar Allah laifin me nayi ake ignoring calls dina haka?.."tana smiling tace"sorry bana tareda wayan ne"..yace"hankalina duk ya tashi na fara tunanin kodai ban samu kar6uwa bane"..murmushin ta kara saki tace"sam ba haka bane..bikin cousin dina akeyi shine na manta ban tafi da wayan ba"...yace"to shiknn hope ban takura maki ba?.."tace"not at all"..tana jiyo sautin smile dinshi kafin yace"to yanxu ya zakiyi dani?..inaso in ganki gaskia"..tace"bana Kano yanxu..na dawo gida"..yace"ohh ba kano kikeba?.."tace"yea Gombe"..ya wara idanunshi da kyau kafin yace"no wonder kikeda kyau..dama an fadamin gaba daya 'yan Gombe kyawawa ne"..tayi murmushi kawai..shi kuma ya sake yin kasa da murya yace"to nidai inason ganinki and if kin bani dama har Gomben zan iya zuwa"..tace"haba da akwai nisa fa"...yace"bakiji ance garin masoyi bai nisa ba?..nifa da gaske nake sonki Aysha bada wasa ba..ban ta6a tunanin zan iya auren karamar yarinya ba sai a kanki..so please inaso a bani dama"...shiru tayi tana tunanin me zatace mishi...tadai san ko ta fara shaye shaye bazata fara kawoshi gidansu ba dan Lamido najin labari zaice ta fito da miji a nata aure tunda tara samari take..besides shi kanshi daddy won't take it likely idan yaji ta kawo saurayi gida ba tareda ya nemi izini ba snn Ammi ma ba rufa mata asiri zatayi ba dan bakinsu daya itada daddyn..amma yanxu ya zatayi da wnn bawan Allah data farajin itama kaman tana sonshi...idea ne ya fado mata dan haka da sauri tace"to ka bari mu gama biki zuwa Sunday sai mu hadu a Bauchi"...yace"but why Bauchi?..ba kince Gombe ne garinku ba?.."tace"nan ne garinmu amma bazan iya kawoka gidaba sbd mahaifina zaiyi fada"..yace"zan iya turowa a nemi permission dinshi if kin amince cox banso da girmana in hadu da yarinha baa gidan iyayenta ba..it's not proper ko 'yata aka yima haka bazanji dadi ba"...ta dan shagwabe muryanta tace"nidai banaso kazo yanxu plss and Bauchin fa ba gidan wani zamu hadu ba gidan small mom dita ne..qanwar mamana"...shiru taji yayi for a while da alama yana tunanin yiwuwar hakan ne...kafin yayi mgn ta sake narke murya kaman wadda ke shirin fashewa da kuka tace"shikenan dama nasan ba damuwa kayi dani ba"...da sauri yace"subhanallah baby why zakice haka?.."tace"gashi nan sbd nace mu hadu a Bauchi kanaso kace ka fasa zuwa"..yace"alright ok don't cry plss...kawai ina ganin rashin dacewar hakan ne a matsayina na babba bai kamata na biye miki ba amma zanzo kinji?..zanzo inshaAllah"...lokaci daya ta saki smile tanajin dadin yanda yake mata tace"shknn Allah ya kaimu...ranan sunday inshaAllah"..yace"no problem Allah ya kaimu i can't wait to see you"..tayi daria tana feeling kanta kaman a sararin samaniya..wnn shine exactly dalinda yasa take son sugar daddies...tayi shagwa6arta son ranta babu wanda zaice don me..dan Allah ya sani tana son taga ana pampering dinta ita dai sai kuma Allah bai bata irin wann parents din ba don daga Ammi har daddy ba masu sangarta yara bane..itama din da takeyi kawai don abun yana jininta ne amma ba shagwa6ata suke ba shiyasa wani lokaci Ammi takan ce"wnn yarinya da shagwa6aki muke Allah kadai yasan iskancin sa zaki mana a cikin gidan nan"...sun dauki lokaci mai tsayi suna waya tanata zuba shagwa6arta yana biye mata aikam farin ciki kaman ta zuba ruwa kasa tasha to dama abun nema ne ya samu wai matar driver ta haifi mota😂.

Washegari around 11 Billy ta karaso gidan...if u see yanda suka rungume juna sunata murna zakayi tunanin dadewa sukayi basu hadu ba nan kuwa jiya jiyan nn suka rabu...bayan sun gama hoge hogensu suka je ta gaisa da daddy da Ammi snn suka shiga daki...Billy take bala labarin yanda sukai da Sir Abdool wai ya kai karanta ta dena daukan wayanshi...Aysha ta wani cunno baki tace"wai bama fada miki abunda yayimin ba?.."Billy tace"and so what dan yayi pecking hannunki?..Lamido nifa banga wani abu a nan ba kawai kina nema kiyi complicating abubuwa"...da mamaki tace"seriously?..yanxu ke a wurinki ba komai bane namiji ya kama hannunki yayi kissing?.."Billy tace"of course ba wani abu bane mana indai da soyayya...kema fa da kina sonshi nasan wlh bazaki damu da hakan ba kawai dan bakya sonshi ne"...tace"Alhamdulillah da kika gane bana sonshi...ke ban fada miki ba jiya bakiga wayan da mukasha da wnn mutumin ba wlh..Billy he is so romantic nima harna fara sonshi wlh..gobe ma zaizo mu a hadu gidan Aunty fiddausi"...harara Billy ta buga mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login