Showing 129001 words to 132000 words out of 145898 words
bata jin zata ji sauqin abun.
Sai da tayi mai isar snn ta tashi jikin duk a sanyaye kmr wata mara lafiya,ta rage kayan jikin ta ta fad'a bathroom tayi wanka,tana fitowa tayi shirin bacci cikin wata er farar riga me kmr vest da wandon ta fari d'an guntu iya rabin cinya.
Sai a snn saif ya dawo har ma tana shirin kwanciya,ya nufe ta da saurin sa ya rungume ta jikin sa cikin sauke numfashi yake fad'in"kin tsorata ni cutie meyasa kika dawo bayan nace ki jirani"
Bata ce masa komai ba se janye jikinta tayi a hankali daga nashi ta kwanta cikin juya masa baya taja blanket ta rufe jikinta.
Nan saif ya ajiye ledar da ke hannun shi jiki sa6ule ya zauna gefen kan bed d'in kusa da ita tare da kai lallausan hannun sa yana shafa sumar kanta dake tufke da ribbon muryar sa a natse yace"am sorry cutie kiyi haquri nasan ban kyauta ba da na barki kina ta faman jirana wlh ta kasa fahimta ta ne da wuri sai da qyar snn na samu,shine koda nazo ban kangi ba duk hankali na ya tashi se neman ki nake tayi ina kiranki a waya amma baki d'aga ba,dawowar da ma nayi waya ta zan nemo in kunna dmn na samu in duba direction d'in inda kk,but am sorry kinji i didn't mean to hurt u"
Zarah da ta bashi baya jin maganar tashi take yana qara 6ata mata rai ne kawai,wacce cike da takaici ta share hawayen da suka zubo mata,snn ta tashi taje ta d'auko wayarta ta 6alle ta cire sim card,ta kuma cire zoben diamond d'inda ke hannun ta da ya bata ta had'a da wayar ta ajiye mishi tace"ga kayanka nn bana so kar ka sake sakani a cikin harakar ku kaje can kuci gaba da yin abu iri d'aya kaida ita,idan ma kun iya qauna tasa ku had'iye juna ku kuka sani bai damen ba,dama can ba qaunar junan mu muke yi ba har zuwa yanzu da jikina kawai kake so ba wani abu ba,to wlh ka sani daga yau bazan qara baka jikina ba,kaje can ita taci gaba da baka dama ae kun saba.
Nan kawai ta kwashi blanket da pillow taje can kan sofa ta kwanta.
Sosai cikin damuwa Saif ya bita da kallo kafin yake maida duban sa kan wayarta da ta ajiye masa da zobe,yasan of course wayar su iri d'aya ce da Sophie amma zoben kam musamman ya siyawa zarah shi asalima duk soyayyar su da sophie bai ta6a siya mata zobe ba,wanda yasan duk 6acin rai ne kawai yasa ta had'a harda zoben ta jiye masa ba dan ta ga irin shi a yatsar Sophie ba se irin wayar su kawai da ta gani a hannun ta.
4/23, 10:19 PM] Billy giro😊: _Monday 23/04/2018_
*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»page«» 62*
Nan ya tashi a hankali ya qarasa gurinta cike da son ya rarrashe ta amma fir taqi saurarrar shi,dolen shi ya barta yaje ya shirya musu kayan su sbd sammako zasuyi gobe,yana kammalawa yaje yayi wanka yayi shirin bacci snn ya sake komawa gun zarah wacce tuni tayi bacci ya gurfana a hankali gab da ita yana kallon fuskar ta ya d'aura lallausan hannun sa yana shafa sumar kanta muryar sa a hankali yace"i swear cutie ke nake so ba jikin ki kad'ai ba,kiyi haquri ki daina fushi dani kinji bazan iya jurewa ba.
Nan ya rankwafa dai dai goshin ta ya d'aura mata kiss snn ya qara gyara mata blanket ya miqe tsaye sai kallonta yake tayi kafin yake barin gurin yaje ya kwanta.
Washe gari tunda ya tashe ta sallah daga can kawai tayi wankan ta tana ida sallah ta hau shiri ba tare da tayi mishi ina kwana ba kmr yanda take mishi kullum idan ta ida sallah,saif da bai riga ya tashi daga kan darduma ba kallonta kawai yake bai ce mata komai ba,ya tashi yaje yayi wanka ya hau shiri shima.
Yana gama shiri er qaramar wayar sa ta hau ringing ya d'aga kiran yana mai kallon zarah da ta fitar da kayan tsarabar da yasa mata a cikin kayanta da zata bawa mutanen ta duk ta watsar bata so.
Ya qarasa gurin ta a natse ya kama ta zai tafi da ita jikinsa tayi saurin qwacewa ya bata waya yace"ungo to ga umma tana son kuyi magana"
Ba musu ta kar6i wayar ta hau yin magana da ita cikin harshen fulatanci,yayinda saif ya duqa se kwashe kayan yake da ta watsar zai maida a cikin akwatin ta,dai dai ta gama wayar tayi saurin janye akwatin shaye da toka tana kallon shi,yayinda shi kuma ya d'anyi murmushi cikin rarrashi yace"haba my cutie yi haquri kinji,in kin fitar da kayan nn ya kk so nayi dasu kinsan banda inda zan sa miki su.
Tace"ni ina ruwana ai sai ka barsu a nn ni ba abunda zanyi dasu bana son duk wani abu da ya fito daga gare ka,har kai d'in ma ka tafi can gurinta ita da ta damu dakai,har abadah kuwa ni bazan damu dan ba kai ba.
Kallonta kawai saif yayi da alama mgnr bata masa dad'i ba amma baice mata komai ba se kayan ya zuba a kwatin ta zai rufe,bata barshi ba se qoqarin fidda kayan take.
Fuskar sa a d'aure yace"cutie bana son raini fa kika fitar da kayan nn wlh ranki zai 6aci"
Idanun ta tap da qwallah ta kalle shi tace"to nace maka bana so dole ne"
Cikin zaro mata ido yace"eh dole ne sai kin kar6a kin kuma ba duk wanda aka siyo domin shi.
Nan kawai ya rufe akwatin.
Ita kuma ta miqe cikin kuka mai kmr na shaga6a tana fad'in"ni wlh bana so kuma ba wanda zan ba ko munje sai dai na zuba su a shara.......wayyo! Tayi ihu sbd qafar ta da ya tad'e zata fad'i ya kama hannun ta ta fad'o kan jikin sa ya kwantar da ita tare da yi mata rumfa yaja karan hancinta cikin murmushi yace"fushi baya miki kyau cutie is enuf ki yafewa mijin naki haka bazai sake ba kinji,ya qarashe mgnr cikin kama kunnen sa snn ya janye tare da d'aura mata kiss yace"kuma ki sani ni ke nake so ba jikin ki ba.
Zarah da ke kallon sa cikin ta6e baki tace"hm wanda yake sona da gaske ae kafi kowa sanin shi yana can rashin samu na har yasa sai faman ciwo yake tayi,dan haka kama daina wahalar da kanka kana fad'ar abunda bashi bane a ranka jikin nawa ne kakeyiwa ba kuma zaka sake samun sa ba na gaya ma.
Nan kawai ta tashi saif ya bita da kallo d'auke da idanun sa da har sun sauya kala kan mgnr ta da ta masa ciwo yana kuma mamakin a ina taji jamil na sonta shi dai bai gaya mata ba ya kuma san jamil bazai ta6a gaya mata ba bare shi Abban kd da su kad'ai ne suka san da mgnr.
Bai ce mata komai ba dai se tashi yayi yaje ya bud'e qofa sbd knocking d'in da aka musu,koda ya bud'e d'aya daga cikin ma'aikatan hotel d'in ne ya kawo musu breakfast,da saif d'in ne ya kira a d'azun dmn a kawo musu ya kar6a ya shigo dashi ya ajiye kawai.
Wanda dashi har zarah ba wanda ya kula breakfast d'in har suka gama shirye shiryen su suka fita,suka had'u da su Abba da duk hotel d'in suke,suna gama gaisawa ba 6ata lokaci suka wuce gabad'ayan su zuwa airport.
6angaren su umma kuma baki baya rufuwa har umman kd tazo nn garin sai shiryen shiryen tarbon su Abba suke abinci kala kala kmr masu shirin yin kasaitacciyar walima.
Wa enda koda suka gama jera liyafar a kan dining,su Abba har sun kusa isowa,se shiryawa sukayi suka je airport dmn tarbon su,su duka gabad'ayan su har su Nusaiba.
Inda umma ce ta tuqa mota da kanta,sbd drivern da ke kai zarah school da yanzu ya zamo kmr drivern su na gida,shi kuma Hjy zai kai,da itama ke son taje ta tarbo d'an nata da ta matsu tasa shi a ido,haka shima jamil wanda Alhmdlh yanzu jikin sa sosai ya masa sauqi,bai zauna ba sai da yaje tarbon Abba.
Da gabad'ayan su basu jima da isa ba se ga jirgin su Abba yayi landing,aka tarbi juna cikin murna da farin ciki,yayinda en jarida keta tururuwar ganin Abba sbd tuni sunji labarin cewa ya farfad'o dama rnr da zai dawo shine suka kasa suka tsare kowa yana son yaji wani abu daga gare shi a buga wasu jaridun kuma.
Police ne suka hana su suka bar su Abba suka wuce,da su kuma dmn kare lafiyar shi kad'ai suka zo gurin.
Bayan sun isa gida ana zaune gabad'aya kowa kan dining se cin abinci suke tayi cike da nishad'i.
Saif da still yana nn a cikin yanayin sa na kafin su baro England,ya kasa cin abincin yanda ya kamata se yi yake yana kallon zarah wacce ke zaune a kusa da gefen shi ta maida hankalin ta se cin abinci take,da take jin kmr bata ci sbd yunwar da take jin na qara taso mata,sbd da ita har saif throughout fushi bai bar sunci komai ba sei yanzu,da har ma ta kusa cinye abincin amma yunwar bata daina ci gaba da azalzalar ta ba,awa ma bata sa komai a cikin nata ba take ji,da lokaci d'aya taji wani irin tashin zuciya har ma amai na qoqarin qwace mata,nn tayi saurin rufe bakinta had'e ta miqewa tsaye cikin hanzari zata kwasa aguje,kawai da miqewar ta wani irin jiri ya d'ibe ta da lokaci guda ta zube qasa a gurin.
Ba shiri saif ya ture kujerar da yake zaune akai,ya nufe ta da sauri ya kamata ya tafi da ita jikin sa yana kiran sunanta a rud'e cikin girgiza ta.
Yayinda tuni kowa yayo kansu se kiran zarah d'in suke tayi suma duk a rud'e,jamil ya d'auko ruwa da sauri ya bawa saif ya shiga yayyafa mata still ba alamar zata farfad'o,nn kawai da saurin sa ya tallabe ta ya haura sama da ita se d'akin su Nusaiba ya kwantar da ita kan bed,su umma da ke biye dashi bai iya ce musu komai ba duk ya rud'e se fita yayi yaje d'akin Abba ya d'auko briefcase d'in Abba ta zuwa asibiti ya hau duba ta.
Bayan ya gama dube duben sa kawai yaja blanket ya rufa mata jikinta kansa qasa ya kasa kallon su se fita da yake qoqarin yi,hankalin su a tashe suka ce lafiya wae me yake faruwa ne saifudeen ka dubata kuma se qoqarin fita kake baka ce mana komai ba.
Still bai iya kallon su ba se murmushi yayi cikin sosa bayan kansa irin na jin kunya d'in nn ya kuma fita abun shi ba tare da ya iya ce musu komai ba.
Hakan yasa dukkan su sukayi murmushi dan yanayin sa kad'ai ya fahimtar da su abunda knn,nn Hjy taje da murnar ta ta gwale idanun zarah a hankali tana dubawa har ma da en yatsun ta duk ta duba,kafin take kallon su baki washe ta d'aga hannayen ta sama tana fad'in"kae Alhmdlh murna kan murna ina en jaridun suke suzo yanzu kam bakina sake zan gaya musu jikana ya kusa haifa min wani mijin,su buga jaridu duniya kowa yaji a tayani farin ciki,abun baqin ciki shine ba dad'in fad'a.
Nan ta miqe cikin yin rawar su ta tsofaffi idan suna yin murna.
Su Abba dake kallonta se murmushi suke tayi,a nn Abba ya kalli umma dake kusa dashi wacce bakinta baya ko rufuwa yace"hala dai Hjy ta manta da dama zarah ciki ne da ita inaga kmr na gaya mata fa"
Umma tace"Alhj kafa san dama can zargi mukeyi bamu tabbatar ba wanda a lokacin da mukeyin zargin babu cikin se yanzun ne aka same shi...."Au haba"
Abba ya fad'a bakin sa murna fal ya d'aga hannun sa sama yace".
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي بِنَعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَات.
_(Godiya ta tabbata ga Allah wanda saboda ni'imar sa ce kyawawan ayukka suke cika)_
*Wato addu'ar da Annabin mu yake yi idan abun farin ciki ya same shi.*
Bayan Abba ya ida addu'ar snn ya qarasa gurin zarah ya dafa kanta yace"Allah ya baki lafiya zarah,yasa dukkanin mu nn muna raye koda zaki haifo mana abunda kike tare dashi rayayye mai albarka.
"Amin"
dukkan su suka fad'a.
Saif kuwa yana sauka downstairs jamil yazo da saurin sa yana fad'in"yadai hope ta farfad'o?
D'auke da murmushi yace"eh a'a is...
Ya d'an sosa bayan kanshi kmr yana jin kunyar gaya mishi amma kuma farin ciki bazai barshi ya kasa fad'a mishi ba,nn kawai ya rungume shi yana fad'in"congratulation u are going to be a father"
Jamil da duk ciwon da yayi har ma yana qoqarin manta inda yake ba abunda ya duqufa akai irin addu'ar Allah ya yaye masa son zarah cikin ikon Allah kuwa koda yaji sauqi se yaji kmr an zare masa son nata gabad'aya,se ma qaunar zainab da ta d'arsu a cikin ranshi kan irin hidimar da tayi tayi dashi da baya da lfy.
Ya d'ago saif da sauri yana kallon sa cikin murna yace"kae haba dai!
"Allah kuwa"
Saif ya fad'a d'auke da murnar da yake tare da ita.
Snn a sanyaye cikin jin tausayin jamil ya kama hannyen sa yace"ina mai qara baka....jamil dake murmushi yayi saurin katse shi cikin dalla mae harara yace"4 what zaka qara bani haquri dan Allah ka daina karma wani yaji mu,yanzu lokaci ne da zamuyi farin cikin qaruwar da zamu samu ba wata magana can da ta riga ta wuce ba,and idan mun natsu ma da akwai labari.
Cikin murmushi saif yace"to shikenan yanzu muje ka rakani da akwai magungunan da nake son siyowa kafin zarah ta farka.
Nan suka fita se murna suke tayi musamman saif da farin cikin nasa ma bansan ya zan misalta muku shi ba.
Wanda koda ya dawo ya samu Hjy ta wuce,haka ma su umman kd.
Nusaiba kawai ya samu a d'akin ita da umma,yusra na can tare da Abba a d'akin shi.
Da shigar sa d'akin kawai yaje yayi tsaye a kusa da zarah d'auke da murmushi yana ta kallon ta da still tana kwance bata farka ba.
Umma dake kallon sa tayi murmushi tace"ya akayi ne saif magunguna ne ka siyo?
Sai da ya sadda kansa qasa snn ya d'an sosa bayan kanshi yace"eh umma ina so ne idan ta farka se tasha magungunan"
Nan ya ajiye ledar magungunan kan bedside drawer yace"ni zanje masallaci nayi sallah "
Tace"to shikenan jamil fa ko ya wuce?
Eh yanzun ya sauke ni ya wuce,suma su Abban kd da Hjy sun wuce ne naga ban gansu ba?
Tace"eh sun wuce yanzu yanzu nn kasan yaya ba son tafiyar dare take ba duk da dai daren ya riga ya musu.
Nan saif ya kalli agogon bangon d'akin 9pm yace"haka ne kam to Allah ya kaisu lafiya"
Amin umma ta fad'a kafin yake fita daga d'akin.
Bai jima da fita ba zarah ta farka wacce ba shiri ta zame daga kan gadon se kwara amai take abun ba sauqi har duk jikinta ya lallace wacce cikin jirin da ke d'ibar ta ta tafi suuu tana qoqarin lemewa a cikin aman kuma,Umma tayi saurin kamata ta wuce da ita bathroom dmn ta wanke mata jikinta.
Nusaiba kuwa fita tayi ta d'auko tsumma ta hau goge d'akin wacce tana jin yanda zarah keta yin wani amman kuma a bathroom se duk gabad'aya taji tausayin ta amma kuma har ranta wani irin dad'i take ji da samuwar cikin.
Koda saif ya dawo ya samu ta gama goge d'akin sai qamshi yake.
Ganin gadon wayam ba zarah bai kuma ga umma ba ya tambaye ta ina suke?
Kafin Nusaiba tace komai sai gasu sun fito daga bathroom,Zarah na manne a jikin umma ta riqo ta sbd gabad'aya jikin nata ba qarfi ko tsayuwa ma bata iya yi da kyau.
Saif ya qarasa gurin su ya kama ma umma ita yana tambayar me kuma ya faru umma naga jikin nata very weak ko tayi amai ne?
Umma tace"eh amai tayi sosai inaga ma duk ta amayar da d'an abunda taci,Nusaiba je had'o mata tea kinji tasha ko zata d'anji qarfin jikin nata.
Nan Nusaiba ta fita umma kuwa har zata koma bathroom dmn ta duba kayan zarah da tasa a washing machine,sei ga yusra ta shigo d'akin acewar Abba na kiran umma,nn umma ta fasa zuwa bathroom d'in ta kama hannun yusra suka fita.
Yayinda saif ya zauna a hankli kan bed tare da zarah dake manne a jikin shi,se kallonta yake tayi kafin yake kai hannun sa ya gyara mata towel d'inta da yake son zamewa daga kan qirjinta,snn da kulawa ya shafo cikin ta yana kallonta yace"sorry babyna ya baki wahala koh?
Zarah dake jin jiki da qyar ta d'ago ta kalle shi kmr da mamaki ta d'aura hannun ta akan hannun sa da ya dafa cikinta muryar ta a hankali can ciki tace"baby?
D'auke da murmushi ya lumshe idanun sa tare da ware su akan ta alamar eh.
Zarah dake kallon shi samun kanta tayi da yin murmushi cike da jin dad'in samuwar cikin da kuma jin kunya har ma tana 6oye fuskar ta a qirjinsa.
[4/26, 9:37 PM] Billy giro😊: _Thursday 26/04/2018_
*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
_Wannan page in naki ne my lovely besty fa'iza Anfa Allah ya bar min ke akan qaunar da kk min._
_I heart u irin sosai d'in nn💓_
_Kici gaba da yi mana muhimmancin budurci yana kawo light👍🏻_
*«»page«» 63*
Saif dake rungume da ita yayi murmushi kawai yana mai shafa gadon bayanta a hankali.
Jim kad'an se ga Nusaiba ta kawo tean tana bawa saif ta fita.
"Cutie"
Ya kira sunan ta a hankli ta d'ago yakai mata tean a baki tana sha kawai tayi saurin zamewa daga jikin sa ta tofar da