Showing 81001 words to 84000 words out of 145898 words
kitchen bari na kira miki ita"
Yana zuwa kitchen ya cire rigar sa tare da durqusawa a gaban ta yana fad'in"sorry zarah tashi kisa rigar nn kinji Hjy ce tazo"
Shiru zarah tayi ta daina kukan da take snn ta d'ago a hankli tana share hawayen fuskar ta,saif ya kai lallausan hannun sa yana taya ta se haquri yake bata wanda da kanshi yasa mata riga snn ya kama hannun ta suka tafi.
Thursday 22/03/2018
*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«» 41*
Koda suka isa falo se kallon ikon Allah hajiya keyi ita kam,tana kallon saif da singlet wanda yanzun nn fa koda ya tashi da riga ta ganshi a jikin sa amma se gashi rigar har ta koma jikin zarah,ko ina rigar zarah ta shiga a kitchen d'in ne? "ikon Allah"
Hjy ta fad'a a ranta kafin take amsa gaisuwar zarah snn da kulawa ta kama hannun ta ta zaunar da ita kusa da ita tana kallon zarah wacce ta sadda kanta qasa ta kasa kallon ta se faman kame kame take tana gyara wuyan riga se kace wuyan rigar ya mata ruwa bayan kuwa rigar collar ne ma da ita,kuma kaf botiran rigar ba wanda saif ya rage da be rufe mata ba.
Shiru Hjy tayi bata ce da ita komai ba se maida duban ta tayi gun saif wanda suna had'a ido yayi d'an murmushi cikin sauke idanun sa qasa yana d'an sosa bayan kansa irin na jin kunya d'in nn.
Hjy tayi murmushi kawai tare da girgiza kanta.
Snn ta kalli zarah d'auke da murmushin da ke kan fuskar ta,ta shiga magana da ita cikin harshen fulatanci.
Saif dake sauraren su in banda karatu,da kuma Alhmdlh da yaji zarah ta fad'a a cikin maganar ba abunda yaji.
Se binsu kawai yake da kallo har suka gama maganar su,snn zarah ta tashi a natse dmn kawowa hajiya ruwa.
Nan Saif ya kalli Hjy yanayin fuskar sa kamar qaramin yaro yace"wai ni kam hajiya meyasa kowa ya iya fulatanci nn banda ni why?
Hajiya tace"Sbd kai d'in na daban ne,tun kana yaro ba abunda za'a saka kayi se idan kana ra'ayi,kuma ko ubannan naka ae ba wani jin fulatanci suke ba dan ban wani koya musu ba shiyasa kaima baka iya ko bidib ba.
Fuskar sa cikin nuna rashin jin dad'i yace"Hajiya kice kece baki koya min ba,ba wai rashin ra'ayi na ne ba,amma tukuna dai hajiya shin a ina kika iya fulatanci dan naga a sani na Alhj (cewa da marigayi kakan shi)sam ba bafulatani bane mutumin kano ne.
Er dariya hajiya tayi tace"to kae in banda abun ka dan shi ba bafulatani bane nima haka,to bari kaji ni dama can asalin bafulatana ce koda mukayi aure dashi,kmr dai yanda ubananka sukayi.
Saif yace"knn kakata ta gefen su umma da ta rasu bafulatana ce itama.....yo naji shashan yaro mutum da ranshi kana saka ta a layin matattu,ba bakin ka ba maza tofadda yawu dmn kuwa tana nn raye cikin qoshin lfy,rashin zumunci ne kawai ke damunka da tun kana yaro baka son zuwa rimin dako kae a dole tashin birni baka son zuwa qauye awa a kanka aka fara rayuwar birnin.
Saif da duk yaji zancen wani iri,yace"kmr ya hajiya tun ina yaro fa ban manta ba dana tambaye ki wace ce kakata ta gefen ummana kika ce min ta rasu bata raye.
Shiru hajiya tayi tana tuna lokacin lallai haka ta gaya mishi amma ita a nufin ta mahaifiyar mom d'in sa ta ainihi ce take nufin ta rasu,ba mahaifiyar umma ba.
Ta numfasa tace"hakane mana amma ai ko ita ta qauyen kakar ka ce kai d'in ne kawai ka qiya musu.
Saif yayi shiru yace"Hjy ban sani bane wlh shiyasa ma bansan zarah er uwar mu bace daga sama kawai naji abun,ashe kakanin mu d'aya ma da ita,but hajiya ina son in sani ita kaka ta qauye yayar kaka da ta rasu ce ko qanwar ta?
Shiru hajiya tayi snn da saurin ta tace"kaga na gaji da wa en nn tambayoyin naka abu awa d'an jarida,se tamboyoyi kake ta min ko ruwa baka bar nasha ba kinga zarah er albarka tsiyaya min ruwa nasha dmn na fahimci wnn sakaran so yake na bar gidan nn maqoshi na a bushe.
Zarah wacce bata jima da ajiye ruwan ba ta zame daka kan kujera ta tsiyaya mata lemu a cup ta bata had'e da komawa ta zauna.
Hajiya ta kur6a lemun yayinda saif ke fad'in"ba haka bane hajiya is gud nasan sauran en uwana akan inzo inata wulaqan ta su ban sani ba.
Hjy tace"Au kaddai lokacin da suka ta6a zowa wulaqan tasun kayi?
"No Hajiya"
Ya fad'a yana me kallon zarah da ita ma shi take kallo.
Snn ya maida duban sa gun Hjy yace"ni ban wulaqan ta su ba,ina magana ne kan kar hakan yazo ya fara faruwa cikin rashin sani.
Hajiya tace"kaga nifa zowa kawai nayi in ganku na kuma ganku to sai watara nn ku,ta miqawa zarah kofi tare da fad'in"Allah yayi miki albarka kinji zarah kiyi ta haquri nasan halin saifuddeen se haquri.
Ta qarashe mgnr ne had'e da miqewa tsaye
Cikin rashin son ta tafi Saif yace"plz Hjy ki zauna yanzun nn fa kika zo be kamata ace har zaki tafi ba.
A'a sai dai wani lokacin idan na koma dawowa,Alu driver na can a waje yana jira na kar yaga na jima bayan ce masa nayi ba wani jimawa zanyi ba ina so zan biya wasu guraren kuma.
Daga haka bata jira me zai ce ba ta nufi qofa.
Ba yanda ze yi haka suka tafi zasu rakata.
Suna kai qofa ya bud'ewa Hjy qofa ta fita shima ze fita knn ya tsaya yana kallon zarah da itama niyyar ta fita zatayi ta raka hajiya ya dalla mata harara yace"kina hauka ne ina zaki je da wa en nn kayan a jikin ki.
A hnkli Zarah ta sauke idanun ta kan wandon da ke jikinta skinny ne gold in colour se shining yake irin me attraction d'in nn sbd yanayin material d'in sa kmr leather da ya kama jikinta sosai.
Ita kanta tasan lallai be kamata ta fita haka ba hakan yasa bata ce masa komai ba,se Allah kiyaye ta yiwa hajiya a nn inda take tsaye.
Shi kuma ya tafi har mota ya raka ta snn ya dawo.
Ya samu zarah ta mayyad lemu a fridge zata je kitchen riqe da d'an small trayn da ta d'aura cup akai zata mayar.
Ya riqo hannun ta had'e da kar6e trayn ya ajiye kan stool,ya tafi da ita kan kujera suka zauna ya kama duka hannayen ta biyu ya riqe a cikin nashi yana kallonta da kulawa yace"kinga Hjy taqi ta snr dani sauran en uwan mu da ban sani ba,gashi se naji ina son in sani musamman ma ummar ki ina so in santa dmn zuwan da mukayi qauye ban ganta ba kuma abunda na fahimta wnn mutumen da ya shiga damu cikin gida like kawun ki ne ko?wanda matar sa ita ce muka samu tana miki kalaba hakane?and se wnn tsohuwar ita kuma granny ko?to ummar ki fa?
Zarah da tun lokacinda ya fara zancen sa kallon sa kawai take,fuskar ta a d'aure ta kwace hannayen ta tare da fad'in"kaga ni ba er uwar ka bace gaba da baya,mahaifiya ta kuma bazan fad'a ba ka fara tambayar kanka waye taka mahaifiyar tukun.
Daga haka kawai ta miqe tsaye zata bar gurin ya tad'e mata qafa ta fad'i kan rug kafin ta tashi ya tafi jikinta ya mata rumfa yana kallonta d'auke da murmushi yace"kin raina ni ko"
Zarah da duk haushin sa take ji tace"wane rainin ae gaskiya na gaya ma kaf dangin ku ina kuka had'u da en qauye bare har mu zamo en uwan ku,Allah sauwaqe bama ciki wlh,kaje can wani gurin ka nemi en uwanka,mu mun gode Allah a yanda muke qauyawan.
Saif da still murmushi na kan fuskar sa yana kallonta yace"hm kinji haushi ne akan abubuwan da na miki a baya,to kiyi haquri kinji a ajiye wnn mgnr ta wuce,ina so ki yafe min ki kuma snr dani sauran en uwan mu gabad'aya na ziyar ce su na kuma basu haquri akan rashin zumuncin da nayi a baya kinji.
Yana magana ne sosai cikin kwantar da murya.
Amma zarah se tsaki tayi tare da da qoqarin miqewa.
Saif be tashi daga kan jikin ta ba bare ta iya tashi se kallon ta kawai da yake.
Tace"kaga dan Allah ka barni in tashi yunwa nake ji"
Hannun sa kan lips d'inta yana shafawa yace"to gaya min yanzun zan barki ki tashi.
"Naqi"
Ta fad'a cikin turo baki.
Cike da sha'awa saif ya tura d'an yatsan sa da yake shafa lips d'in ta a cikin bakin nata da ta turo,ba shiri ya zare sbd gantsara mai cixo da tayi,snn da saurin ta ta ture shi tana dariya ta miqe zata gudu,saif ya tashi zaune tare da fizgo ta ta fad'o kan jikinsa,tana kallon shi ya 6ata fuskar sa awa qaramin yaro ya nuna mata yatsan sa wai ta gani har cizon da ta mai ya fito.
Kama hannun nasa tayi cike da ganin sha'awar yanayin shagwa6ar sa sosai ta masa kyau,idanunta akan shi tasa yatsan sa a cikin bakin ta tana tsotsa yatsan a hankli kafin take zare yatsan ta d'aura shi akan tafin hannun ta tana hura mishi iskan bakin ta.
Saif ya lumshe idanun sa,har ransa yake jin dad'in iskan bakin ta dake sauka akan d'an yatsan sa,ya tafi da fuskar sa gab da tata har tsinin hancin sa na ta6a nata ze had'e bakin su....
Zarah tace"meye haka?
Ta fad'a tare da ture shi daga jikinta tana dariya d'auke da mamaki a fuskar ta,saif ya kalle ta a kasale cike da sha'awa yana kallon dimples d'inta dake lotsawa,zata tashi ya kamo ta yana fad'in"oya bring my shirt tunda baza ki gaya min abunda na tambaye ki ba.
Cikin dariya ta ture hannun sa da yake qoqarin bud'e buttons d'in rigar tace"na baka me kaifa ka yaga min riga ka biya ni tukun ko zan baka wnn.
Be kula ta ba se qoqarin cire rigar yake wanda ba komai ne yasa yake son cire rigar ba irin yayi wasa da dukiyar fulanin ta.
Ita ma ta fahimci abunda yake niyya tayi nasarar qwace kanta ta tafi da gudu zuwa kitchen ta kullo qofar da sauri tasa key.
Saif da ya bita da kallo yayi murmushi cikin sauke numfashi.
Se kuma da saurin sa ya miqe zumbur sbd ihun da yaji zarah ta fasa ya tafi da sauri dai dai ta bud'e qofa ta fad'o jikin sa ta rirriqe shi cikin yanayin jin tsoro ta nuna mishi store tana fad'in"inaga wnn farar kyanwar ce a cikin store naji abu ya fad'i.
Saif dake kallonta a hankli ya sauke ajiyar zuciya cikin murya me natsuwa yace"Allah zarah har kinsa na tsorata da naji ihun ki na d'auka ko wani abu ne ya same ki,abu ne kawai ya fad'i a store bcos kitty da kk fad'a ae tuni bata gidan nn,tun rnr da muka je gidan su jamil kika musu gaisuwa a washe garin rnr da naje Hospital jamil ya d'auke kitty ya tafi da ita tana can hannun shi still yaqi ya bani har yau,kawai dai kullum yana zuwa min da ita Hospital,amma yaqi yarda na dawo da ita.
Zarah da tayi shiru tana tuna lallai fa rabon da tasa kitty a idon ta har ta manta,ta d'ago daga kan jikin sa tana kallon sa tace"meyasa to ya d'auke ma ita?
"Oho masa"
Saif ya fad'a cikin d'aga kafad'un sa,wanda da sanin sa yaqi gaya mata gaskiyar dalilin da yasa jamil ya d'auke ta,sbd yasan yana gaya mata yanzu ne zata hau yabon halin jamil,shi kuma a ransa baya so haushi yake ji idan tana yabon jamil.
Me zaki dafa?
Ya tambayi zarah.
Tace"indomie "
Bai ce mata komai ba se hannun sa yakai kan rigar jikinta ya bud'e mata button d'in farko da na biyu ya qara gyara mata collar rigar snn yace"ki dafa dani zanci"
Gyad'a masa kai kawai tayi tana kallon sa ya juya ya fita daga kitchen d'in,snn a hnkli ta sauke idanunta a kan buttons d'inda ya bud'e mata,ta d'aura hannun ta a gurin d'auke da d'an murmushi a fuskar ta.
Kana ta wuce store ta d'auke abunda ya fad'i snn ta hau zirga zirgar dafa indomie.
Koda ta gama dafa indomie d'in ta fito bata same shi a falo ba,har tayi tunanin ko taje ta kira shi se kuma ta fasa dan yanzu ko hanyar qofar d'akin nasa bata son zuwa sbd en matan da yaci gaba da kawowa,haushin abun take ji sosai.
Nan kawai tayi zaune kan rug ta ajiye plate d'in indomie a gabanta ta lanqwashe qafafu ta fara ci knn ta ganshi ya fito still yana nn daga shi se singlet da dogon wandon da ke jikinsa.
Kae tsaye ya nufi fridge ya d'auko fresh milk,yazo ya zauna suka hau cin indomien tare har suka kammala snn ya tsiyaya fresh milk a cup ya bata,bata kar6a ba se girgiza kanta tayi alamar bata sha,bai ce mata komai ba shi kam yasha dan yasan tun daga rnr bata sake shan fresh milk ba.
Yana kallo ta tashi riqe da plate d'in da suka gama cin indomie ta tafi dashi kitchen ta wanke duk wani abunda ta 6ata snn ta fito,still ya koma binta da kallo har sai da ta haura sama zuwa d'akin ta snn ya tashi riqe da cup da fresh milk a hannun sa ya tafi d'akin shi.
Washe gari koda yaje ya tashe ta sllr asuba ya same ta kwance a tsakiyar tiles d'in d'akin se juyi take tana kuka.
Da saurin sa ya qarasa gurinta yana riqa ta kawai yaji ta sake mishi gabad'aya ta some mishi a jiki.
Oh my God!
Ya fad'a a rud'e yana kallon jinin da ke fitowa a qasan ta yana biyowa ta qafafun ta,da sauri ya tashi yaje d'akin sa ya d'auko laptop ya hau duba me ya same ta har hakan ta faru byn jiya da dare guraren sha biyu koda yazo d'akin ta ya same ta lafiya lau se bacci take.
Bakin sha biyu d'in ya maida yana dubawa,har qarfe biyu duk lafiya lau take tana bacci to 3 ne ciwon mara ya tashe ta har zuwa yanzun qarfe biyar da wani abu da yazo ya same ta ciwon be sassauta mata ba se somewa ma da tayi.
Rufe laptop d'in yayi ya dawo kanta riqe da ruwan gora da ya d'auko a fridge ya shiga yayyafa mata yana kiran sunan ta.
Amma ina ba alamar zata farka ga jinin da ke fita a jikinta se qaruwa yake sosai awa me miscarriage,duk yabi ya rud'e,shi kam yasan bata da ciki bare yace ko cikin ne ke zubewa asalima duka duka yau satin ta d'aya da gama on,bare yace ko On d'in ne yazo mata haka.
Gabad'aya ma ya rasa me zai yi se ciro wayar sa yayi ya kira umma ya gaya mata halin da ya samu zarah a ciki.
Snn byn sun gama waya yaci gaba da yayyafa mata ruwa yana jijjiga ta yana kiran sunan ta still bata farka ba har se da umma tazo yaje ya bud'e mata qofa suna shigowa d'akin suka samu Zarah na motsi,saif ya tafi da saurin sa ya kama ta had'e da rungume ta a jikin sa yana fad'in"Zarah mene ne me yake faruwa dake haka gaya min kinji dan Allah"
Duk yana maganar ne a rud'e kmr zeyi kuka.
Zarah kam ko magana bata iya yi,se hannun ta takai kan marar ta,ta riqe sosai kmr me shirin ciro ta gabad'aya,wacce da qyar ta iya bud'e idanuwan ta dake rufe tana kallon saif lips d'inta na rawa tana son yin magana amma ta kasa,se rufe idanun ta ta koma yi.
Umma tayi kanta da sauri tana kiran sunan ta.
Nan mahaifiyar saif ta saki wata irin dariya wacce ke zaune a gaban boka tana kallon abunda yake faruwa a jikin qwaryar da bokan ke nuna mata.
_Friday 23/03/2018_
*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«» 42*
Tace"Gud boka tsafi ya dafa maka,aikin ka na kyau,ina fatar se da cikin nata ya gama zubewa snn ka aikata lafira,dmn ko a lafira bazan ta6a yarda d'ana ya had'a zuri'a da wa en nn matsiyatan ba.
Wata irin dariya bokan yayi snn yace"Ae ban kashe ta ba tukun Hjy zafin ciwon ne ya koma sumar da ita amma yanzun zan aikata lafira dmn tuni cikin ya gama zubewa.
Nan kawai yayi wani irin ihun tsafi tare da saka hannayen sa duka biyu a cikin qwaryar tsafin ya shaqe wuyan zarah wacce take ta hau yin shure shure.....firgigit Abba ya farka daga mummunan mafarkin da yake,ya tashi zaune yana fad'in"innalillahi wa inna ilaihi raji'un!x3
Snn da saurin sa ya d'auki wayar sa dake ajiye kan bedside drawer ya kira saif.
Saif na cikin bacci ya soma jin wayar sa na ringing.
Ya tashi cike dajin bacci ya kunna bedside lamp yana kallon agogon bangon d'akin qarfe uku na dare.
Ya d'auki wayar a ransa yana mamakin lafiya Abba ya kirasa a irin wnn lokacin.
Wanda ya d'aga kiran ne had'e da yin sallama,Abba ya amsa sallamar tare da fad'in"ina zarah take tana lafiya ba abunda ya same ta?
Saif yace"eh..Abba tana..lafiya..me yake faruwa?
Abba ya sauke ajiyar zuciya tare da fad'in"ba komai ka bani ita muyi magana"
Saif da duk ya shiga tunanin wae me yake faruwa yace"to Abba bari na tashe ta"
"Yauwa ina jiranka"
Abba ya fad'a kafin saif ke tsinke kiran ya tafi d'akin zarah,ya kunna hasken d'akin ya ganta kwance kan bed se sharar baccinta take tayi.
Yaje ya zauna gab da ita yana kallonta se jin yake kmr kar ya tashe