Showing 3001 words to 6000 words out of 145898 words
ya zauna ya kalli umma wacce tayi saurin d'auke idonta akan shi nn ya maida duban sa gun Zarah yace"kiyi haquri Zarah halin saifuddeen ne se shi kuma be san waye ke ba shiyasa"
Muryar ta a hnkli can ciki da alama taji zafin yanda saifuddeen ya mata tace"ba komai Baffa"
Nan sukayi breakfast har suka gama ba wanda ya sake cewa uffan.
Suna gamawa Abba ya fita shida yusra acewar zasu je granny house kasancewar yau weekend ne ba aiki.
Saifuddeen kuwa yana zuwa d'akin sa kae tsaye kan sofa yaje ya zauna ya dafe kansa idanuwan sa a rufe,Zarah kawai yake gani,a ransa yana mamakin ina umma ta kwaso ta da har ake alanqanta shi da ita ace wai er uwar sa ce ta jini wacce kaf dangin su yasan babu kucaka irinta.
Lallai idan har er aiki ce aka kawo zai yi maganin abun dan bazai ta6a barin ta ta zauna gidan ba,se dai a nemo wata da ta cancanci zama er aikin gidan.
[11:13AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Tuesday/06/02/2018_
*芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
_Monday/05/02/2018_ *«»»««»SAIFUDDEEN«»»««»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«» 3*
Tun daga lokacin saifuddeen bai sake komawa 6angaren ba har se a washe gari snn,koda yazo ya sami driver ya sauke su umma knn sun fito daga anguwa gurin tela sbd sabbin d'inkunan da za'a ma zarah.
Yana tsaye hannayen sa duka cikin aljifan wandon sa,da suka qaraso zarah ta duqa har qasa tana gaishe shi yayi kmr be jita ba ko gefen ta ma yaqi ya kalla se umma yake ma sannu da zuwa wacce ta amsa tare da nuna mishi Zarah dake durqushe still bata tashi ba tace"baka ganin Zarah na gaida ka"
Kallon Zarah yayi tare da dalla mata uwar harara ae kuwa ta tashi sum sum ta wuce ya bita da wani irin kallon tsana.
Umma ta girgiza kanta d'auke da d'an murmushi tace"saifuddeen wai meye aibun Zarah ne,naga ni banga wani abun nuna qyama a gare ta ba jiya jiya da fara ganin ta duk kabi ka d'aura mata karan tsana"
Fuskar sa a yatsine kmr umman ce Zarah yace"kawai umma ni bata min ba,i dnt wnt see her any more,plz ki nemo wata er aikin da ta cancanci zama a gidan nn not dis one"
Umma dake kallon sa tace"saifuddeen ka daina kallon Zarah a er aiki ita ba er aiki bace fa"
Yace"to waye ita?
Tace"very soon zaka san wace ce ita"
Daga haka taja hannun yusra suka wuce ba tare da ta jira me ze ce ba,
"very soon"
ya fad'a yana me kallon ta har ta shige.
In a shrug way ya kad'a kafad'un sa yayi gaba.
Umma kuwa tana shiga kae tsaye d'akin Nusaiba ta nufa gun Zarah,ta same ta zaune kan bed kanta qasa,ta qarasa gurinta ta zauna tare da dafa ta.
Zarah ta d'ago ta kalle ta idanuwanta cike tap da qwallah tace"inna ni bazan sake gaida shi ba tunda baya so"
Umma tace"No Zarah yayanki ne kiyi haquri kici gaba da gaida shi kinji"
Muryar ta kmr zata fashe da kuka tace"to inna baya so fa"
Umma tace"halin shi ne haka amma idan kika ci gaba da gaida shi ze daina kinji"
Tace"sikenn naji zanci gaba da gaida shi d'in tunda kince,yause ne Nusaiba zata dawo to?
Umma tace"ae nusaiba na jin kinzo ta fasa qarasa hutun ta acan tana nn dawo wa jibi jibin nn inshaa Allah,idan ta dawo zan baki kud'i ta rakaki kasuwa ki siyo kayan kwalliya dama sauran abubuwan da kk buqata ko".
D'auke da murmushi Zarah ta gyad'a kai cike da jin dad'i zata zama er bunni ga sabbin d'inkuna za'a mata snn kuma za'a je da ita kasuwa ta siyo kayan kwalliya,lallai kuwa zata yi ja gira tayi kwalliyar en bunni,in ma dan qauyan cin ta ne saifuddeen ke nuna mata tsana ko gaisuwar ta baya amsa to ze daina.
Bayan kwana biyu da faruwar haka ne Nusaiba ta dawo wato 'ya ga umma wacce bazata wuce 15 yrs ba,amma kasancewar girman jiki ne da ita zaka d'auka shekarun su d'aya da Zarah dan ta cimma Zarah da komai.
A washe garin rnr da Nusaiba ta dawo ne umma ta basu kud'i su tafi kasuwa.
Nusaiba tayi kwalliyar ta acan acan ta zamani ta kuma yi kyau sosai dan ta iya kwalliyar kuma kwalliyar na mata kyau.
Zarah kam powder kawai ta shafa a fuskar ta se kwalli da red lip-stick da tasa a lips d'inta, dan tunda taga kwalliyar da nusaiba tayi tasan in tayi tata kwalliyar tantagaryar baqauya zata fito,amma duk da haka se tayi kyau hasken ta ya qara fitowa sosai sbd fara ce sol.
Gudun kar ta saka kayan da basu dace da fitar birni ba tace da Nusaiba ta za6ar mata kayan da zata sa,Nusaiba kuwa ta za6ar mata wata atamfa Holland ja da akayi zanen manya manyan leaf a jikinta milk in colour,ta had'a mata da wani hijab milk me hannu da ta gani a cikin kayanta da bazai wuce iya guiwa ba.
Ita kuma ta shirya cikin black arabian gown snn tayi rolling da d'an kwalin arabian gown d'in.
Koda suka fito garin luf luf dashi ba rana se iska me dad'i dake ta kad'awa.
Saifuddeen na zaune a farfajiyar gidan can kusa da flowers kan kujerar shan iska shida wani abokin sa da sukayi krt tare,ipad a hannun shi da alama wani abu yake dubawa ta yanda yake scrolling da 'yan yatsun sa.
Tare Nusaiba da Zarah suka gaida su,abokin ne ya fara amsa musu,saifuddeen kuma gaisuwar Nusaiba kad'ai ya amsa wato ya amsa gaisuwar ne had'e da kiran sunan ta har yana tambayar ta ya mutan kd tace mishi lafiya qalau.
Bayan sun wuce abokin nasa ke cewa"A ina kuka sami fine yellow girl like nucy?
Ba tare da Saifuddeen ya kalle sa ba yace"ae Nusaiba d'in ce baka gane ta ba?
Abokin sa ya kalle sa had'e da girgiza kansa yace"ae kasan wacce nake nufi tafi nusaiba haske wnn d'ayar da kaqi amsawa gaisuwa@Fulani girl"
Still Saifuddeen be kalle sa ba se ta6e bakin sa da yayi had'e da fad'in"oho ni ban san a ina aka samo ta ba"
Ae da ganin ta er uwar ku ce kan yanda kuke kama kaida ita.
Abokin nasa ya fad'a.
Saifuddeen ya tsaya cak da abunda yake tare da sauke qafar sa dake kan d'aya yana kallon abokin nasa da fuskar sa da ta sauya lokaci d'aya,ya nuna kansa da yatsa cikin muryar 6acin rai yace"ni d'in zaka ce wae munyi kama da wnn abar!
Abokin nasa yayi dariya tare da dafa shi yace"wnn abar fa kace to maida wuqar ni da wasa nake maka,kawai so nake inji wace ce?
A fusace Saifuddeen ya buge hannun abokin nasa ya kuma nuna sa yace"to wlh kar ka sake min haka jamil bana so"
A hnkli jamil d'in yace"to naji yi haquri gaya min wace ce?
Tsaki Saifuddeen yaja ya tashi ya bar gurin dan jamil ya gama 6ata masa rai shida yau yake jin er fara'ar sa amma jamil yazo ya 6ata masa komai.
Jamil ya bisa da kallo d'auke da murmushi har se da ya daina ganin sa snn ya girgiza kansa yace"hm Saifuddeen halinka se kai"
Nan ya tashi yaja motar sa ya bar gidan cike da tunanin sanin wace ce Zarah dan shi haka kawai yaji lokaci d'aya tayi mae,lallai bazai yi qasa a guiwa ba da wuri ze bayyana soyayyar sa gare ta bazai tsaya zurfin ciki ba ya rasata kmr yanda ya rasa Nusaiba aka riga shi.
Dan yaso Nusaiba sosai amma ko Saifuddeen bai ta6a gayawa ba bare Nusaiba.
*«»*
Bayan sun dawo da kasuwa Nusaiba ce zaune a d'akin umma,umma na duba kayayyakin da suka siyo kayan kwalliya ne da turarukka se inner wears da kuma kayan bacci kala biyu.
Nusaiba dake danne danne a waya tace"umma ashe dama yaya saif yana nn?
Umma tace"eh yana nn me ya faru?
No umma ba komai kawai na d'auka ko yayi tafiya ne naga tun jiya da safe dana dawo bangan shi ba har se d'azun da zamu je kasuwa.
Umma tace"to ai kinsan halin yayan naki ba kasaifai yake shigowa 6angaren nn ba se cin abinci ke kawo shi ko kuma idan ze fita,kwana biyun nn ma ko cin abinci ya daina shigowa se idan ta mishi dad'i.
Nusaiba tace"hm yaya saif manya ne zanso inga mtr da zai aura dan nasan se ya darje ya za6o dai dai dashi"
Murmushi umma tayi tare da fad'in yayanki da baya ko son a masa zancen aure wai bai tashi ba tukuna.
Tace"to umma may be gimbiyar tasa na can waje tana karatu ita yake jiran se ta kammala tukun musha biki.
Murmushi kawai umma tayi bata sake cewa komai ba.
Se duba kayan taci gaba dayi bayan ta gama duba kayan ta maida su a leda ta miqawa Nusaiba tare da fad'in"to gashi naga kayan sunyi se ki maidawa zarah nata ne ita kad'ai kin sani,kinada naki dan haka kowa ya tsaya kan nashi bana so inga wani na aiki da kayan wani dan nasan halinki ga me da kayan kwalliya ko kinada naki se kinzo har d'akin nn kinyi kwalliya da kayan kwalliya na na rasa wane irin ruwan ido ne dake"
Cikin turo baki Nusaiba tace"kai umma jefi jefi ne fa kawai nake d'an zowa d'akin nn ina yin kwalliya ko shi sbd mirror d'inki yana fitowa da mutum sosai amma bawai ruwan idon kayan kwalliya nake ba,bare Zarah da kwana biyu tafiyar ta zatayi"
Umma tace"Waya gaya miki Zarah kam tazo knn nn zata ci gaba da zama tare da mu.
Cike da murna nusaiba tace"da gaske umma!
Umma ta gyad'a mata kai d'auke da murmushi.
Tsalle Nusaiba ta daka tace"kae amma wlh naji dad'i dama zaman gidan nn ni kad'ai ya ishe ni yusra ce tayi qarama ba fira take taya mutum ba.
Nan ta kwashi kayan cike da murna ta fita umma ta bita da kallo d'auke da murmushi a fuskarta har ranta tana jin dad'in yanda Nusaiba bata d'auki kanta kowa ba,duk yanda d'an uwanta yake,talaka ne ko baqauye bata nuna masa qyama se ma qoqarin take ta shigar da shi a jikinta sam halin su ba iri d'aya ne dana Saifuddeen ba.
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 4&5*
Nusaiba na zuwa d'akin su ta tarar da Zarah ta cire kayan jikinta ta sauya wasu,taje ta rungume ta cike da murna tana er qaramar rawa a jikinta"
Zarah ta d'ago ta tana kallon ta d'auke da murmushi wacce hkn ya bayyanar da dimples d'inta tace"lafiya dai me kike ma murna haka Nusaiba?
Nusaiba tace"umma tace min kinxo knn baza ki koma ba zaki ci gaba da zama tare damu shine nake murna"
Murmushi Zarah tayi amma aranta addu'a take Allah yasa zata iya zaman gidan to,dan yanda Saifuddeen ke mata be mata dad'i ko kad'an,sam bata son wulaqanci shi kuma ta fahimci saren saren wulaqanci ne dashi,amma in dan qauyan cinta ne sannu a hnkli zatayi maganin abun.
Tana nazarin ne d'auke da murmushi a fuskarta,hakan yasa Nusaiba bata fahimci komai ba se miqa mata ledar kayan ta tayi tare da fad'in"umma tace sunyi kyau mun iya siyayya kiyi amfani da duk abunda ke ciki u are free duka naki ne kin sani"
Murmushi kawai zarah ta koma yi snn ta zauna a hankli kan bed kmr wacce qwai ya fashewa ta bud'e ledar ta ciro kayan kwalliya ta kalli Nusaiba tace"in tambaye ki.
Nusaiba ta zauna kusa da ita tace"fad'i man ina jinki"
Muryar ta a hankali tace"yanzu idan kika koya min irin kwalliyar ki zan iya,ko se d'an bunni kawai ke iya irinta?
Nusaiba dake kallonta tace"Of course zaki iya mana ae komai sa kai ne"
Tace"to ina son kullum ki riqa koya min har in iya,nima na zama er bunni a daina wulaqanta ni ana min kallon er qauye"
D'auke da murmushi Nusaiba taja karan hancinta da ya tafi tsaye har baka kmr jinjirin karas,tace"wake miki kallon er qauye ae ba wanda ya isa dan ke ba baqauya ba ce"
Murmushi kawai Zarah tayi tasan Nusaiba fad'a kawai tayi amma ita baqauyce sosai ta sani.
The following day ne mai d'inki ya kawo ma Zarah d'inkunan ta ciki har da hijabin uniform na islamiyya school.
Islamiyyar ba nisa da gidan a qafa suke zuwa su uku,wato zarah,Nusaiba,da kuma yusra,dan makarantar har da ajin yara akwai bata manya kad'ai bace,kuma safe da yamma ake zuwa kasancewar ana hutun makarantar boko.
Ranar wata assabar da yamma zarah da nusaiba sun shirya zasu tafi islamiyya su biyu sbd yau yusra bata jin dad'i tun da safe ta tashi da jin zazza6i.
Falo suka bar mami tare da yusra tana jiran Saifuddeen yazo ya duba mata ita dan Abba baya nn yayi tafiya zuwa Abuja.
Koda zarah da nusaiba suka fita se gashi sun had'u da saifuddeen d'in shida jamil wa enda shigowar su knn gidan sun fito daga cikin mota.
Jamil kallon zarah yake dake sanye cikin hijabin uniform d'inta blue mai hannu dake kai mata har qasa,fuskar ta fayau ba kwalliya se powder da kwalli da ta shafa,haka nn d'an bakinta d'an daidai me kmr an shafa janbaki se qyalqyalin lip gloss yake,bai d'auke idon sa a kanta ba har suka qaraso gurin su suka gaida su,ko wnn karon shi ya fara amsa musu,snn can ciki Saifuddeen ya amsa gaisuwar Nusaiba wacce yake jin itama ya kusa daina amsa gaisuwar ta idan har yaci gaba da ganin ta tare da zarah.
Yana jin jamil yana tambayar Nusaiba ya sunan baquwar tamu tace mishi Zarah.
"Nyc name"
Ya fad'a
murmushi kawai nusaiba tayi suka wuce Saifuddeen ya ta6e baki jamil yace"lafiya"
Yace"surutun naka ne naga yayi yawa har da wani tambayar suna,kaci sa'a Nusaiba ce ta fad'i sunan da yarinyar ce se kaji voice d'in nata wani iri ba dad'i,rnr fa kawai ina zaune ina cin abinci kan dining,ban ta6a ganin ta ba ma se a rnr,kaina a duqe banji motsin isowar su gurin ba ita da umma,kawai kmr daga sama naji muryar ta tace"hai shannun ka,Fad'ima shuna na kaifa ya shunan ka"
Yayi mgnr ne fuskar sa a yamuste,jamil kam se murmushi yayi yana mae qara jin son zarah a cikin ranshi,dan yasan halin abokin nasa idan baya ra'ayin abu qara 6ata abun yake.
Shiga sukayi daga ciki suka sami umma,jamil ya durqusa cike da ladabi ya gaida umma ta amsa cike da fara'ar ta har tana tambayar sa ya mutanen gida yace mata duk suna lafiya,snn ya zauna kan kujera yana kallon yusra dake rungume a jikinta yace ashe yusra ba lafiya"
Tace"eh wlh ka ganta gata nn se fama nike da ita jikin nata duk yayi zafi"
"Oh no"
Jamil ya fad'a cikin yanayin tausaya wa,kana yakai hannu yana ta6a jikin nata a lokacinda Saifuddeen ya kar6e ta yana duba ta.
Ledar magunguna da alluran da ke hannun sa ya ajiye gefe a kusa dashi yace da jamil ya 6alle allura ya had'a mishi.
Nan fa yusra na jin zancen allura ta ajiye kuka bata so har tana neman guduwa daga jikin Saifuddeen,lalla6a ta yake kmr er cikin sa dan sosai yake tausayin yaro qarami idan bashi da lafiya,cikin lallami har ya samu ya mata allurar se kuka take ta mishi yana ta rarrashin ta har tayi bacci kan jikin shi,nn ya shiga shafa bayanta a hnkli har sai da baccinta yayi nisa snn ya bawa umma ita suka fita.
Kae tsaye 6angaren shi suka tafi.
D'akin tsaf tsaf very neat koh mace albarka se wani irin daddad'an qamshi ke tashi.
Jamil ya zauna kan sofa tare da sauke idon sa kan wani qaramin frame dake ajiye kan bedside drawer photon Sophie da Saifuddeen ne a jikin frame d'in sunyi kyau sosai kmr masu gasar kyau dan se ka rasa gane shida ita wa yafi wani kyau duk da cewa ita baturiya ce amma ita kyaunta daban ne a cikin turawa.
Jamil ya maida duban sa gun Saifuddeen wanda ke tsaye gun fridge yana tsiyaya musu lemu a cup yace"ni kuwa Saifuddeen har yanzu shiru banji inda aka kwana zancen ka da Sophie ba.
Sai da Saifuddeen yazo ya zauna kusa dashi riqe da cup biyu a hannun shi d'auke da lemun da ya tsiyaya musu a ciki.
ya miqa masa d'aya snn yakai d'aya a bakin sa ya kur6a kad'an snn a hankli ya sauke numfashi yace"jamil ban san ya zan tunkari Abba ba ina tsoro kar yaqi amincewa da zance na"
Jamil ya kur6a lemu snn yace"tunda umma na da sauqin kai kayi mata magana mana se ta tuntu6e shi ko Allah zai sa ayi nasara"
Hum jamil kasan na gaya maka rnr Abba ya ganni da Sophie at my office,just ganin ta da yayi kan laps d'ina muna magana yayi ta fad'a har yace se na rabu da ita.
Be bar maganar ba sbd abun ya masa zafi ya gayawa umma wacce na fahimci tun rnr da na kawo mata Sophie dmn ta gaishe ta naga alamar sam bata ra'ayin Sophie,to ta yaya kake ganin zan shawo kan wnn al'amarin?
Jamil ya numfasa tare da ajiye cup d'in hannun sa kan stool d'inda ke ajiye a gaban su snn yace"ba mamaki idan Abba yaji aurenta zakayi ze amince kawai ka same shi ka gaya mishi"
Saifuddeen yayi d'an guntun murmushi me nuna alamar da kmr wuya yace"hum jamil na san halin Abbana yana da tsauri sosai,shiyasa a duk lokacinda ya min zancen aure gabana har fad'uwa yake dan bansan ya zai d'auki abun ba idan nace masa