Showing 57001 words to 60000 words out of 145898 words

Chapter 20 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24758

yaya saif ya fito dake a gabana Abba ke tambayar sa kina yin amai sosai ne yace a'a zafin jiki kawai ne da zarar kuma kinsha magani kinyi bacci shikenan komai ze dawo miki normal,ko kuma duk dai ba zancen me ciki akeyi ba a gurin.
Ta qarashe mgnr ne tare da tsare ta da ido.
Zarah tayi murmushi had'e da girgiza kanta tace"Au Allah sarki baxa ki gane ba ne,kuma ae in cikin ne ba abu ne me 6oyuwa ba bayyana zai yi,bare ma ina roqon Allah kada ya kawo qaddarar da zai sa na sami ciki da yayanki,wnn...hum um!Allah raba 'ya'yana da uba irin shi.
Daga haka ta sauko ta zauna kan rug tare da lanqwashe qafafu ta had'a d'an waken ta ta soma ci.
Nusaiba da ke kallon ta tayi murmushi kawai,haka ma saif wanda yana can d'akin sa yana kallon su a laptop yayinda yake jin shima dai koda ace ya d'auki hukincin da yaso d'auka akan ta na kiran shi fanko da tayi,har akayi akasin ciki ya shiga,to lallai da kanshi ze mata allurar zubar da shi dan ya riga ya tsara a rayuwar shi babu wata uwar 'ya'yan shi face Sophie da tuni suka aje akan 'ya'ya biyu kacal zasu haifa.

Washe gari koda qarfe goma tayi tuni sun shirya har sun fito,zarah na can tsaye gefe riqe da er traveling bag d'inta a hannu ta shirin tafiyar ta rimin dako.
Sbd so take daga can gida idan sun gama magana da Abba umma tasa driver ya kaita kmr yanda ta mata alqawari.
Saifuddeen kuma kitty ce a hannun shi tsaye a gurin mota yana qwalawa me gadi kira,mai gadin na zowa ya bashi yace"ba jimawa zanyi ba ka kula min da ita.
"To a dawo lfy"
Mai gadi ya fad'a wanda yana rungume da kittyn ya tafi da sauri dmn bud'e musu gate,se a snn zarah ta yarda taje ta shiga mota dan dama ganin yana riqe da kitty ne yasa tayi tsaye can gefe tana jiran har se ya bada ita tukun.
Wacce byn ta shiga har ta rufe ganbu saif ya kalle ta yace"zan gaya miki abu d'aya shine bana son wawanci a harakar nn i mean kar ki gayawa kowa wai nace zan sake ki,kawai idan kin min yanda nace zan cika maki alqawarin ki.
Gyad'a masa kai kawai zarah tayi yayinda shi kuma yaja motar suka fita daga gidan.
Da suka isa tare suka fito cikin motar suka shiga daga ciki,Nusaiba ce ta fara ganin su wacce ta dawo daga islamiyya knn zata haura sama tayi tsaye tana kallon yanayin shirin su tamkar wasu couples d'in da ke qaunar juna sunyi kyau sosai se zuba qamshi suke,ba abinda ma yafi bata shawa kmr klr kayan su iri d'aya.
Zarah na sanye da atamfa super Holland navy blue da akayiwa zane me ratsin sky blue wato klr gyalen ta dake yafe tun daga smn kai,haka ma takalmin qafar ta klr ne,amma hand bag d'inta klr navy blue ce.
Yayinda shi yake sanye da tsadadden yadin shi sky blue hadda hula qubbe klr kayan a saman kanshi kmr wani na Allah kan yanda kayan suka kar6e shi sun fiddo mishi da kamala sosai,dan ba kasaifai yake saka hula ba ra'ayin sata ne kawai ya biyo mishi yau,wanda dashi har zarah ganin kawai sukayi sunyi to match d'in ba wanda yasan klr da d'ayan ze sa.
D'auke da murmushi Nusaiba ta gaida su had'e da kar6ar travelling bag d'in da ke riqe a d'ayan hannun zarah nn se ga Abba da umma suna saukowa daga staircase,Abba ne zeyi tafiya zuwa kd shine umma ta rakoshi.
Wa enda sun qarasa saukowa ne cikin fad'ad'a murmushin da ke kan fuskar su,suna masu amsa gaisuwar su zarah.
Abba da har ransa yaji dad'in yanda ya gansu haka abun sha'awa yace da zarah"ya jiki zarah kinji sauqi?
Zarah kanta qasa cike da ladabi ta gyad'a masa kai alamar taji sauqi.
Yace"to Allah ya qara baki lafiya ni zan tafi kaduna ne yanzu,idan kinje Rimin dako ina gaida inna sosai dama mutanen gida gabakida'aya kinji"
Sake gyad'a masa kai zarah tayi zata basu hanya dmn su wuce dan kan hanya suke tsaye,a kafaice saif ya riqo hannun ta da sauri had'e da kai d'ayan hannun sa ya d'an sosa bayan kansa irin na jin kunya d'in nn yace"plz Abba muna son zamuyi magana da kai ne"
Abba ya kalle sa da kulawa kafin yake gyara babbar rigar sa yace to muje inji.
Nan umma da Nucy suka haura sama,yayinda Abba ya qarasa daga cikin falon ya zauna kan doguwar kujera 3seater su kuma su saif suka zauna kan rug suka sadda kansu qasa.
A natse Abba yake kallon su yace"ina jinku mene ne?
Saif yace"Abba dama...se kuma yayi shiru yana d'an sosa bayan kansa.
Abba wanda ya d'an shiga tunanin ko zai gaya masa cewa zarah na d'auke da ciki ne,yayi murmushi yace"kayi maganar ka mana saifuddeen ina jinka kar kaji komai.
Saif ya kalli zarah snn ya kalli Abba yayi qasa da kansa yace"dama Abba mgnr aure na ne da Sophie,tace ita a gurin ta ba matsala ta amince kuma Sophie d'in ma ta amince zata musulunta indai har ka yarda zan aure ta.
Abba dake kallon saif d'auke da murmushi,yana jin zancen sa lokaci d'aya fuskar sa ta canza cikin 6acin rai
yace
"Ga d'an rainin hankali kan wnn banzar maganar ne kasani a gaba wai zaka gaya min sbd ka maida ni sha sha sha wanda ban isa in gaya ma magana ka bi ba,har ni zan rantse kan har abada kar ka sake kula wnn baturiyar ashe har yanzu baka ajiye zancen ta ba ko!.
A sanyaye saif yace Abba kayi haquri ka taimaka min dan Allah.....ka min shiru very stupid! wlh ko bayan raina ban yarda ka auri wnn baturiyar ba koda ace zata musulunta kuwa ni bana ra'ayin ka aure ta har abada ba kai ba ita,dan haka kar ka sake zo min da zancen ta idan har baso kake na maka abunda baka ta6a tsamani ba,sha sha sha kawai fitsararre get out! in daina ganin ka a nn!.
Ba musu saif ya tashi ya fita d'auke da idanuwan sa da duk sukayi jajur suka ciko tap da qwallah
Nan ita ma zarah kafin Abba yace da ita komai ta tashi sum sum ta miqe ta haura sama da sauri sbd kukan da taji yazo mata.
Umma dake tsaye ta bita da kallo kawai,wacce saukowar ta knn daga sama kan jin fad'an Abba wanda kana ta nufi gurin shi ta zauna a natse ta soma magana dashi.
_Tuesday 05/03/2017_
*«»»««»SAIFUDDEEN!«»»««»*






By
*Billy giro😊*



*Dedicated to»»»Zarah gwandu*



*«»Page«» 30*
Kan yayi haquri ya bar saifuddeen ya auri Sophie.
Abba da duk ransa a 6ace yace"plz Mmn yusra kar ki qara 6ata min rai,akan me zan barshi ya aure ta,baturiya ce fa fitsararriya mara kunya wacce bayan tana samun sa a office be ishe ta ba har nn gida ta fara biyoshi tana qoqarin lalata min yaro a banza.
Shiru umma tayi snn tace"Amma Alhj tunda har ta yarda zata musulunta plz ka bar shi d'in ya aure ta ko dan musuluntar da zata yi.
Hm maman yusra na fahimci dan ba ke kika haife sa ba shiyasa kika kasa hango abunda nake hangowa ko.
Cikin mamaki da rashin jin dad'in mgnr sa umma tace"haba Alhj wace irin magana ce kake gaya min haka"
Kiyi haquri maman yusura ba wai ina nufin in 6ata miki bane ya kamata ki natsu kiyi tunani idan na barshi yayi auren wace irin tarbiyar kike ganin yaran su zasu d'auko,ko kin manta gado a cikin jini yake duk abunda uwar su tayi shi zasu zo sunayi ko ma fiye,ba lallai bane su kasance masu kirki.
Amma Alhj musulunta fa tace zatayi ko dan haka inshaa Allah,Allah bazai bar yaran su d'auko wata banzar dabi'a ba....a'a maman yusra ni na tabbata hauka kawai yakeyi iyayen ta baza su ta6a yarda su barta ta musulunta ba,dan haka ya isa dan Allah bana son sake jin wata magana.
Daga haka be jira me umma zata ce ba ya fita.
Umma da ta bisa da kallo tayi shiru har ranta ita kanta ba son auren take ba,da dai wata ce a cikin Hausa fulani ba baturiya ba amma saif d'in ne ya bata tausayi,cikin baya son zarah aka tursasa mishi auren amma gashi yanzu ya saduda suna zaune abin su qalau be ta6a kawo wani qorafi ba,ko dan hakan taso Abba ya tausayawa mishi wnn karon a bashi dama shima.
Tashi tayi ta leqa ta window ga mamakin ta ta hango motar saif ajiye be tafi ba wacce tunanin da tayi knn dan bata ji tashin motar sa ba fitar Abba kawai taji.
Nan ta fita taje ta same shi a cikin mota ya had'e kansa da sitari se kuka yake kmr wani qaramin yaro,cikin rarrashi ta d'ago fuskar shi tare da share mishi hawaye snn ta kama hannun sa suka koma daga ciki sukayi zaune a nn falo kan doguwar kujera tana kallonsa cikin yanayin damuwa tace"saif kayi haquri kaji kasan halin mahaifin ka idan ya fad'i magana baya canzawa,kuma tunda har kaga auren nn yaqi yiyuwa tayu ba alheri bace a gare ka.
Saif dake jin wani qololon baqin ciki a ranshi ya girgiza kansa yace"No umma ki daina fad'ar haka musulunta fa tace zatayi a kaina,ta yaya baza ta zama alheri a gare ni ba,kawai dai Abba ne bazai barni na aure ta ba.
umma na rasa meyasa kwata kwata Abba baya son farin ciki na....haba saifuddeen ka daina fad'ar irin wnn magana haka ae duk duniya babu me son ganin farin cikin ka irin shi....No umma zan de fi yarda duk duniya shine baya son farin ciki na,akan kawai yayi farin ciki fa nake nuna muku muna zaune qalau nida wnn abar bayan kuwa ko kad'an ba haka bane sam bata cikin tsarin rayuwata ina yin haka ne kawai dmn a tunani na farin cikin ganin nayi mishi biyaya muna zaune qalau nida ita zesa ya barni na auri Sophie amma se gashi a banza umma.
Umma da taji wani abu a ranta tayi shiru tana kallon shi snn tace"me kake son gaya min saifuddeen,kana nufin kaida zarah babu wata kulawa a tsakanin ku kana nuna mana ne kawai?
Of course umma ni bana son wnn abar dmn duk ita ce silar lalata min komai,abinda yafi sauqi ma a gare ta idan taje wnn qauyen kar ta dawo bana son sake ganin ta a gidana.
Umma dake kallon sa komai bata ce dashi ba tana kallo har ya tashi ya fita,a ranta tana tunanin knn ko cikin da suke zargin zarah na d'auke da shi kusan hasashen banza ne suke dmn yanayin maganar sa kad'ai ya nuna mata da kmr babu wata alaqa da ta ta6a shiga a tsakin su,ashe rnr ba fushin masu ciki ne ya d'ebo zarah tazo tana fad'in ita ta gaji da auren ba zancen gaskiya dai tazo tana gaya mata.
Nan ta numfasa a hankli zata tashi se ganin saif tayi ya dawo ya zauna yana kallon ta yace"plz umma bana son Abba yasan gaskiyar zaman da mukeyi nida ita,na fison naci gaba da bin sa a haka har Allah yasa wata rana ko zai janye rantsuwar da yayi ya barni na auri Sophie.
Umma tace"saif bana tunanin Abbanka zai ta6a janye rantsuwar da yayi haka kuma zarah idan taje wnn qauyen ba dawowa zata yi ba ta tafi knn kmr yanda ka buqata.
Yanayin fuskar sa kmr wani qaramin yaro yace"No umma na canza shawara ne,akan samun auren Sophie wlh zan iya jure komai,ki barta kawai ta dawo na d'ora inda na tsaya ko Allah zai sa nayi nasara.
Aa dawowar zarah baza ta amfane ka da komai ba dmn babu nasara a cikin yaudarar Abban ka da kake son yi kawai kaje ka sake wani tunanin.
Daga haka ta tashi ta barshi nn gurin ya bita da kallo cike da damuwa a ranshi.
A 6angaren Zarah kuwa a lokacin da ta haura sama kae tsaye d'akin su Nusaiba taje ta zauna kan bed tare da had'iye kukan da take ji wanda ita kanta bata san dalilin zuwan kukan ba kawai dai tasan bata ji dad'in da Abba yayi fad'a ba,dmn da tasan mgnr 6atawa Abba rai zatayi da baza ta biyewa saif ba sai dai ta bar tsarin ta akan idan taje rimin dako baza ta dawo ba wanda ko yanzu kuwa hakan ne kad'ai mafitar ta.
Nusaiba da itama duk fad'an da Abba keyi ya iso kunnen ta tazo tayi zaune kusa da zarah cike da mamaki tace"lallai 6ter me yake damunki da har kika yarda yaya yaje dake gurin Abba kan neman alfarmar auren wnn baturiyar,ko ba kya son sa ae ya kamata kiyi kishin sa a matsayin sa na mijinki.
Shiru kawai zara tayi tana kallon ta taqi tace da ita komai har umma tazo ta same su.
Zarah na ganin shigowar ta ta sadda kanta qasa tace"inna dan Allah ayi haquri shi ne yace na raka shi bansan maganar zata 6ata ran Baffa haka ba.
Umma tace"ba komai maganar ta wuce,and u Nusaiba idan har zaki je d'in to kiyi ki shirya dmn Alu driver na zowa bazai tsaya jiranki ba sai dai suyi tafiyar su shida zarah.
A'a umma Allah yanzun nn zan shirya.
Nusaiba ta fad'a wacce tayi saurin bud'e wardrobe ta ciro kayan da zata sa snn ta kalli umma cikin marairai ce fuska tace"plz umma tunda rnr sunday 6ter zata dawo nima zan d'ebi kayana mu kwana a can se mu dawo tare.
Umma tace"A'a bazai yiyu kiyi missing d'in islamiyyar yamma ba snn kuma gobe tazo baki samu zuwa ba kwata kwata.
Ba tare da Nusaiba ta musa ba ko nuna rashin jin dad'in ta ta tafiyar ta kawai zuwa bathroom dmn ta d'an watsa ruwa duk da tayi wanka da safe da zata je islamiya.
Umma kuma zama tayi a hankli kusa da zarah tana kallon ta kawai ta kasa ce mata komai bata san meyasa ba haka kawai se tausayin ta take ji.
Inna lafiya?
Zarah ta tambaya wacce ke kallon umma a natse.
Umma ta sauke numfashi a hankali tare da fad'in"ba komai kawai dai idan zaku tafi da akwai turarukkan fesawa da turarukkan d'aki na tsintsiya da kuma tokunan wanka da nake son baki kije dasu a matsayin en tasarabar ki da kika kai musu.
Byn haka zaku biya gurin hajiya ku d'auki yusra dan nasan tana buqatar zuwa itama d'azun ma na kira hajiya na snr da ita.
Snn da akwai shawarar da nake d'an yi a raina idan na yanke shawarar to wata qil gobe zanje rimin dako d'in wata qil kuma bazan je ba sai dai na tura Alu driver ya d'auko ki.
Gyad'a mata kai zarah tayi wacce bata ko san umma taje d'in duk da bata san dalilin son zuwan nata ba,amma gwanda ta tura mata Alu driver kawai dan shi tana iya liqewa tace baza ta dawo ba tunda yanzu bata san makomar akqawarin da saif ya mata ba,ga rayuwar gidan nashi ta ishe ta gabad'aya,gwanda kawai tayi zamanta a mahaifar ta inda ake ganin mutuncin ta,daga nn idan ta samu yanda take so yayan ta ya sake nema mata wata makaranta taci gaba da karatun ta koda kuwa school d'inda yake karatu ne zata iya kasancewa a garin dan so take tayi ilimi sosai ta waye dmn ta samu damar cika burin ta akan saif so take ko yaya se tasa yayi nadamar tsanar ta da yayi.
Koda Alu driver yazo har Nusaiba ta kammala shirin ta tsaf,umma ta bawa zarah abubuwan da tace snn ta rakasu har mota tana musu Allah kiyaye hanya.
Da fitar su gidan basu zarce koina ba se gidan Hjy suka d'auko yusra snn suka kama hanyar rimin dako.
Cikin mota tsif ba mai cewa komai tsakanin Nusaiba da Zarah kowa da abunda ke zuciyar shi musamman Nusaiba da ta rasa gane kan yayanta da zarah,ita da take ganin kmr sun fara qaunar juna se gashi sun wani je sun sami Abba kan neman alfarmar auren wata banzar baturiyar can har zarah d'in ta yarda suka je wai,sosai abun ya bata haushi da har yanzu yayanta ya kasa fita hararkar wnn baturiyar bayan umma da Abba duk ba me son alaqar sa da ita.
A hankali ta sauke numfashi tare da kallon zarah cike da niyyar mata magana se taga karatun qur'ani take a wayar ta hakan yasa tayi shiru bata ce mata komai ba,se bud'o qur'anin tayi ita ma a wayar ta ta soma karantawa har suka isa rimin dako.
Dije suka samu a tsakar gida tazo aguje cike da murna ta tarbe su tare da kar6ar kayan da ke hannun su suka shiga ciki yayinda inna washe da baki ta shiga musu sannu da zuwa.
Basu sami yayan zarah ba baya nn ya koma school amma kawun ta yana nn wanda da kanshi yazo har d'akin inna shida innan dije suka musu ya hanya ya kuma suka baro su umma.
Suka ce suna nn qalau sun ma ce a gaida ku.
Kawun zarah yace"to muna amsawa ya kika baro mijin naki?
Ya tambayi zarah a cikin harshen fulatanci wacce sai da ta sadda kanta qasa snn ita ma a cikin harshen fulatanci tace mishi yana nn qalau.
Nan bayan sun gama gaisawa snn suka bar d'akin.
Dije ta kawo musu abinci da kuma lafiyayar hurar da aka dama musu an saka qanqara tayi sanyi sosai,suka ci suka sha se fira suke tayi a tsakanin su su duka har inna wacce duk ta kalli zarah wani irin farin ciki take ji sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login