Showing 15001 words to 18000 words out of 145898 words

Chapter 6 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24762

dai dai, ba kai ba wnn arniyar snn auren ka da zarah ba fashi dmn baza mu zuba maka ido ka kunyata mu a idon duniya ba.
Saifuddeen ya kalle sa kmr zai yi kuka muryar sa na rawa yace"Abba wlh da Aure nake son Sophie na jima ina son snr da Abba amma kullum ina tsoro kar yace bazai amince ba"
Abban kd dake kallon sa yace"Saifuddeen dukkan mu nida Abbanka a England mukayi krt amma ba wanda ya d'auko baturiya yace ita zai aura,asalima iyayen mu ne da kansu suka za6a mana matan da muka aura,wanda gashi yanzu Alhmdlh har kullum cikin farin ciki muke da godiyar Allah kan za6in da suka mana,dan haka ina son kayi haquri ka ajiye auren wnn baturiyar gefe ka amince da za6in Abbanka dmn shine mafi alhairi a gare ka.
Shiru Saifuddeen yayi idanun sa suka qara yin jajur suka ciko tap da qwallah,dama yasan da kmr wuya ya samu auren Sophie da amincewar su, shiyasa kawai ya tsara ya aureta a 6oye ba tare da sun sani ba se gashi kwana d'ayan da tazo ta mishi ya lallata komai,yanzu ba yanda zai yi tunda Abba ya mai iyaka da ita.
Kana cikin muryar kuka yace"Abba naji zan fita harakar Sophie amma dan Allah a bar ni na za6o wacce zan aura da kaina"
Shiru Abban kd yayi lokaci me tsawo se can yace"shikenan gobe zanje kano na sami Abban naka muyi magana"
Godiya Saifuddeen ya mishi snn ya tashi ya fita.
Bai zarce koina ba se gidan kakar jamil,ya faka motar shi a gefen gate d'in gidan snn ya ciro wayar sa a aljihu ya kira jamil.
Koda jamil ya fito ya leqa motar ya ganshi ya had'e kanshi da sitarin motar,
nn ya zagaya ya bud'e motar ya shiga ya zauna yana mai kallon shi yace"lafiya dai Saifuddeen baka ta6a zowa ka tsaya a qofar gida ba se yau"
A hnkli Saifuddeen ya d'ago yana kallon sa yace"ina cikin damuwa ne bana son in shiga ya jikin kaka"
Jamil dake kallon yanda idanun Saifuddeen sukayi jajur yace"taji sauqi sosai amma me yake damunka ban ta6a ganin ka a cikin irin wnn yanayin ba se yau.
Saifuddeen yace"jamil Abba ne ya min iyaka da Sophie yace baya so ya sake gani na da ita har abada,a waya ko a bayan idon sa na sake kula ta bazai ta6a yafe min ba.
Cikin damuwa Jamil yace"subhanallah me ya faru har hakan ta faru ko zuwa kuka yi kaida ita da niyar mishi magana?
No,it's all my fault da na amincewa Sophie kan matsa min da tayi ita tana son se taje tamin kwana d'aya,byn naje da ita se gashi da safe umma ta aiko wnn banzar yarinyar ta kawo min breakfast ta shigo mana d'aki haka kawai ba sallama ba knocking shine ta ganmu taje ta snr bansan jakar ina ce ba ita.
Jamil da ya fahimci Zarah yake nufi ya numfasa yace"kayi haquri amma yanzu ya za'ayi and ita Sophie meyasa ta nemi hkn byn ka snr da ita cewa this coming week zakuyi aure.
Bari kawai ta mugun 6ata min rai,kawai naje in ganta tace se ta bini yanzu gashi ta 6arar mana da komai snn tasa Abba ya min mummunan hukuncin da yake neman had'a aure na da wnn banzar yarinyar bagidajiya er qauye da bansan ta yaya ma za'ayi na iya rayuwa da ita ba"
Da kmr rashin fahimta jamil ya kalle sa yace"ka..min..bayani...ban...gane ba,wa..ce ce Abba ke shirin had'a ka da ita ba dai Zarah ba ko?
Rai 6ace Saifuddeen yace"ita man wacce nake tunanin ko tsinto ta akayi,wae ashe dama can Abba ya kawo ta ne da niyyar had'a mu aure,kaji min!abu se kace wasan kwaikwayo,kai ko a wasan kwaikwayo ma wnn sam beyi ba,it doesn't making sense a had'a ni da wnn,na rasa me yake damun Abba da yayi wnn tunanin,da ya ta6a accident se ince ko ya sami matsala ne a qwaqwalwar sa ba'a sani ba but...se yayi shiru yana mai kallon jamil da ya dafe kansa sbd mugun sara masa da yayi.
A hankali ya dafa shi yana kallon sa yace"jamil?
Da qyar jamil ya iya d'ago kanshi idanun sa har sun canza kala zuwa launin ja ya kama hannuwan saifudden cikin yanayin begging lips d'insa na rawa yace"Ni ina sonta Saif dan Allah ka taimaka min Abba ya bani auren ta tunda kai baka so"
A hnkli Saifuddeen ya zare hannayen sa daga riqon da jamil ya mishi yana kallon jamil kmr yaga wani zautacce yace"jamil wae ka fahimce wacce nake nufi kuwa?
Jiki sa6ule jamil yace"na fahimce ka mana wnn baquwar da kukayi zarah wacce suke fita tare da Nusaiba"
"Ya salam"
Saifuddeen ya fad'a yana mai kallon jamil cike da mamaki yace"me ka gani a tare da wnn bagidajiyar da har zaka sota jamil?
Jamil yace"komai na gani a tare da ita,ba abinda ta rasa a tsarin irin macen da nake so na aura.
Saifuddeen ya leqa fuskar jamil d'in snn yace"amma dai da wasa kake min ko?
Wlh da gaske nake gaya maka saif tun rnr da na fara d'aura idona a kanta naji ta kwanta min arai,har ma jiya na yanke shawarar muna kammala cin abinci zan snr da umma se gashi Abba ya kirani jikin kaka ya tashi ba dan haka ba da na gaya mata wlh.
A sanyaye Saifuddeen ya numfasa ganin yanda jamil ke magana seriously idanun sa tap da qwallah se duk gabad'aya ya cika da mamakin jamil d'in.
Girgiza kansa kawai yayi snn yace da jamil"kar ka damu tunda har kana sonta kmr ka same ta ne dmn gobe ma Abban kd zai je kano ya roqa min Abba ya barni na za6i wacce zan aura da kaina.
Jamil dake kallon sa ya sauke ajiyar zuciya a hnkli snn yace"nagode sosai Saifuddeen and idan har Abba ya amince ka kawo macen da kake so,plz ka za6i salima dmn a cikin en matan da ke son ka duk tafi su sonka tsakani da Allah snn mace ce har mace bata da wani abu da d'a namiji ze kalla yace baya so son kowa ce qin wanda ya rasa.
A hankli Saifuddeen ya girgiza kansa yace"ni Sophie kawai zan iya rayuwa da ita a matsayin mata ta kuma inshaa zan aure ta da izinin Abba bama a 6oye ba.
Jamil yace"ta yaya saif?
Yace"jamil kafi kowa sanin irin qaunar da Sophie ke min,akaina ta gudo ta baro iyayen ta snn aikaina zata iya musulunta dmn ta aure ni,da haka ne nake tunanin idan ta musulunta Abba ze barni na aure ta.
Jamil yace"hakane tabbas Sophie ba abinda baza ta iya ba akan ka ina maka fatan alhairi Allah yasa ayi nasara"
"Amin"
Cewar Saifuddeen.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Monday 12/02/2018_ *芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*






By
*Billy giro馃槉*



*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*



*芦禄Page芦禄 11*
Washe gari shigar sa office knn ko zama beyi ba se ga Sophie ta shigo,tsaye yayi yana kallonta lokaci d'aya duk ta rame idanuwan ta duk sun kumbura da gani tun rnr da abun ya faru take kuka har yau dan still qwallah ne tap a idon ta tana kallon shi.
Kafin tace komai yazo ya ra6a ta gefen ta ya fita,ta bisa da kallo hawaye na silalowa a hankli kan kumatun ta,Saifuddeen bai ta6a fushi da ita irin haka ba se wnn karon,gashi ta biyoshi har office d'insa dmn ta bashi haquri amma ya fita ya bar mata office d'in.
A hankli ta zube gurin tana kuka.
Saifuddeen kuwa da fitar sa kai tsaye office d'in jamil ya tafi Jamil da har ya zauna ze fara duba wasu files ya tsaya yana kallon saif har ya qaroso yaja kujera ya zauna muryar sa cikin yanayin damuwa yace"plz jamil kaje ka sami Sophie tana office d'ina ka mata bayanin komai and ina son ka kwantar mata da hankali ta yanda baza ta shiga damuwa sosai ba snn kuma ka gaya mata ko bayan ta koma England zan dawo gare ta very soon inshaa Allah zamu yi aure.
Jamil ya numfasa yace"Aa Saifuddeen kar fa a gaya mata abunda bazai yiyu ba taje tayi ta faman jiran ka a banza......Bakin ka ya sari d'ayan kashi,da Allah ni je ka gaya mata nasan tana can ta soma kuka.
D'an guntun murmushi kawai jamil yayi snn ya tashi ya fita.
Saifuddeen kuwa cike da damuwa ya had'e kansa da desk.
Can jamil ya dawo jikin sa duk a sa6ule ya zauna Saifuddeen da ya d'ago yace"what! ta fahimce ka ko kuwa?
A hnkli jamil ya lumshe idon sa tare da ware su akan shi snn yace"ta fahimce ni dmn sosai na kwantar mata da hankli amma duk da haka se da tayi ta kuka ita bata so ta tafi England tafi so ta zauna tayi ta jiranka har ko yaushe ne dmn tana tsoron yanda zata je ta fuskanci iyayen ta wa enda ba lallai bane su barta ta samu damar sake had'uwa da kai ba har kuyi aure.
Saifuddeen ya numfasa snn yace"kira ta awaya ka gaya mata ta tafi kawai komai zaiyi normal inshaa Allah da izinin iyayen ta ma za'a yi auren kar ta damu.
I have already told her but still dai ta tafi tana kuka,she dnt wnt miss u,and ga short note d'in da ta rubuta ta bani tace na baka.
Saifuddeen ya kar6i takadar ya ware ya fara karanta content d'in da ke ciki"
_Dear,am very sorry 4 wat i have coused for us,of course i should punished my self 4 that,bye take care of ur self and my kitty._
_Miss u!_
Saifuddeen da ya gama karantawa yasa hannu ya goge en guntayen hawayen da suka gangaro ta gefen idon sa kana ya tashi ba tare da yace da jamil komai ba ya fita.
Jamil da ya bisa da kallo ya girgiza kansa cikin yanayin tausayawa sbd yanda suke matuqar son junan su dole ka tausaya musu musamman yanda suka dad'e cikin qaunar juna.
Zarah ce ta fad'o mishi a rai wacce basu ko fara soyayyar ba,asali ma ko cikakken wata d'aya beyi da fara ganin ta ba amma da Saifuddeen ya gaya mishi Abba zai had'a shi aure da ita,wani irin yanayi ya tsinci kansa a ciki da baisan ma ta ya zai fisalta ba,wanda shi kansa yana mamakin yanda akayi soyayyar zarah ta kama shi lokaci d'aya haka da yawa duk da kasancewar ta baqauya amma shi sam qauyancin nata bai dame sa ba burin sa kawai ya mallake ta,kuma inshaa Allah zai mallake ta kmr yanda Saifuddeen ya masa alqawari,kul ba dad'e kul ba jima ze iya jira koma yaushe ne.
芦禄
Saifudddeen na ganin abun kmr wasan yara amma se shiryen shiryen auren ake da gaske ba kama hannun yaro dan kaf dangi da abokan arziki kowa ya sani,amma shi kam in banda jamil bawani abokin sa da ya sani dan hana jamil yayi ya snr da kowa acewar sa ba auren da zai snr da frnds d'insa ba ne wnn,auren takaici da har kullum mamakin Abba yake da har yayi tunanin had'a shi da wnn yarinyar,gabad'aya takaici da kewar Sophie duk suka tara mishi har ma ko yaje asibiti baya iya wani abun kirki yake dawowa.
Nusaiba kam duk da tasan halin yayan ta ko kad'an baya son zarah amma tayi farin ciki sosai dmn ganin take zai daina duk wani abun da yake yiwa zarah su koma son juna,duk qyamar da yake yiwa ba qauyen mutum dai se gashi baqauyar ce zata zamo matar shi,kai ba kad'an ba tsarin Abba ya birge ta dmn sam bata son halin yayan nata na tsanar da yake yiwa qauyawa abun na damunta sosai.

Saura en kwanaki da d'aurin auren ne Saifuddeen ya fito 6angaren su umma riqe da invitations d'inda Abba ya bashi na d'aurin aure dmn ya bawa abokan sa.
Umma na kallon sa ta windown falo gabad'aya ya keta su ya zuba su a cikin dustbin ya kakka6e hannun sa yayi ficewar shi,bata yi mamaki ba dan dama tasan abunda zai faru knn,girgiza kanta kawai tayi snn ta kalli Abba da ya haura sama se waya yake abun sa cike da fara'a.
Bin sa tayi zuwa d'akin nasa bayan ya ida waya ne ya kalle ta da fara'ar sa yace"ya akayi ne Maman yusra?
Tace"plz Alhj ka zauna ina son zamuyi magana"
Ba musu ya zauna kan bed itama ta zauna tana kallon sa a natse snn tace"nasan baka so amma kayi haquri abu ne da ya zama dole,kasan mahaifiyar saif dole ne tasan da auren nn amma naga ga dukkan alama baka snr da ita ba se ma harkokin gaban ka da kake.
Take duk wani farin cikin sa ya 6ace 6at ransa a 6ace yace"da wane dalilin zata sani mtr da sam bata qaunar shi tun yana d'an wata shida da ta barshi ta tafi ko da kuskure bata sake waiwayar sa ba.
Umma tace"Alhj kar fa ka manta kaifa ka sake ta ba wai ta tafi ne ta barshi ba.
Nasan ni na sake ta amma sam bata son Saifuddeen na gaya miki dmn a lokacinda ta sami cikin sa ba irin abinda bata yi ba dmn cikin ya zube amma Allah da ikon sa bata yi nasara ba har ta haife shi,a tunani na renon cikin sa da tayi na tsawon wata tara da yanda tasha wahala a gurin haifuwar shi zai sa ta so shi amma sam hakan besa ta damu dashi ba,masu aiki kawai ta barwa suna hidima dashi,nono ma se ta ga dama take bashi,har na gaji da baqin halinta na sake ta.
Umma tace"amma dai duk da haka haqqi ne akanta a snr da ita"
Yace"maman yusra kinfi kowa sanin bana son Saifuddeen yasan wace ce mahaifiyar sa dmn baqin ciki ne kawai a gare shi,a gurin hajiya ya tashi tun da yayi wayo ya fahimci cewa hjy kakar sa ce,ya fara damuna ina mahaifiyar sa,ban ta6a gaya masa ba sai dai kawai nace tayi tafiya da haka har Allah yasa mukayi aure nida ke,a gabanki na kawo shi nace masa gaki kece mahaifiyar sa da yake damuna kullum,kina kallon yanda ya rungume ki cikin tsananin farin ciki da jin dad'i wanda tun daga lokacin ya d'auka kece mahaifiyar sa da ta haifeshi har yau baisan bake kika haife sa ba and still bana so ya sani dan haka kar ki qara min zancen wnn banzar matar bana so.
Kayi haquri inshaa Allah hakan bazai sake faruwa ba.
umma ta fad'a tare da tashi ta fita daga d'akin.
kici6us tayi da Nusaiba tsaye a bakin qofar d'akin idonta tap da qwallah da alama ta ji duk abinda suke fad'i.
Wani irin kallo umma ke mata da kmr mamaki snn taja hannun ta da sauri ta tafi da ita zuwa d'akin ta,
tace "Nusaiba uban me kikeyi a bakin qofar Abbanku kika la6e kina sauraren abinda muke fad'i iye!
Da sauri ta girgiza kanta tare da share hawayen da suka zubo mata tace"wlh umma ba la6e nake maku ba,umman kd ce ta kira a waya ta tace na kai maki wayar tayi ta kiran wayar ki baki d'aga ba shine naje ban same ki a d'aki ba nazo d'akin Abba da niyyar maku knocking shi ne se.....
Shine se kika ji muna magana kika tsaya kina sauraren mu ko!to bari kiji in gaya miki wlh kar inji mgnr nn ta fito kinji ko!
Da sauri Nusaiba ta gyad'a kanta alamar taji snn ta fita daga d'akin kmr yanda umma ta umarce ta.
Taje d'akin su tayi kwance kan bed kmr wata marar lafiya dan gabad'aya se taji tausayin yayan nata ya kama ta yazai ji idan ya gano umma ba mahaifiyar sa bace bayan yana mata kallon ita ce ta haifeshi....."Nusaiba lafiya me yake faruwa?
zarah ta tambaya wacce tana zaune kan bed koda Nusaiba tazo ta kwanta.
A kafai ce Nusaiba tasa hannu ta share hawayen da suka sakko kan kumatun ta sbd ta bawa zarah baya bata iya lura da abinda take ciki,byn ta share hawayen ne snn tace"ba komai kaina ne naji ya d'an sara min shine na kwanta"
Muryar ta a sanyaye ta mata sannu.
Snn taci gaba da duba littafan ta na islamiyya da take dubawa sbd dama aikinta knn idan bata yin komai,wacce duk ta d'an fad'a sbd zullumin auren da za'a mata da wanda bata san ya rayuwar ta zata kasance ba,wanda tun rnr ta ganshi da Sophie suna wnn iskancin wani irin tsanar sa take ji a ranta ko ganin sa bata son yi asalima bata sake ganin sa ba d'in tun daga rnr dan kwata kwata ya daina shigowa cin abinci,gidan su jamil yake zuwa can yaci.

Saura kwana d'aya asa lalle suka tafi Rimin dako ita da Nusaiba da kuma Nadiya wato 'ya ga umman kd wacce shekarun su d'aya da Nusaiba sune suka zama en matan amarya tare da dije dake can.```
```A washe gari aka sa lalle snn suka dawo kano akayi sauran bukukuwa rnr juma'a aka d'aura aure and by 10pm aka kai Amarya ba kad'an ba zarah tayi kuka har ta gode Allah shike nn da gaske dai an d'aura auren nn har gata a d'akin ta an kawo ta,tana zaune kan bed kanta qasa fuskar ta a rufe da gyale kmr dai kowace amarya,su Nusaiba,nadiya da dije se sheri suke ta mata kmr yanda en matan amarya keyi tana jinsu bata tanka su ba dan ita kad'ai tasan irin baqin cikin da take ji a ranta an had'a ta da miji d'an iska dako qaunar ganin sa bata yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login