Showing 39001 words to 42000 words out of 145898 words
ruwan da ke ajiye kan bedside drawer ya d'auki gorar ruwan ya bud'e ya d'an zuba ruwan a hannun sa snn ya yayyafa mata kan fuskar ta.
Rae 6ace ta bud'e idanunta a hankli tana kallon shi,shima fuskar nn tasa ba annuri yake kallonta snn yace"wawiya uban me kike yi har qarfe shida da rabi baki tashi ba,wlh ina gaya miki idan driver yazo ko kin kammala shiri ko baki kammala ba haka zaki bishi ku tafi,kisa wasa kuma ki gani.
Yayi qwafa snn ya fita yaje d'akin shi ya bud'e laptop d'in sa yana kallonta,yanda ya barta still tana nn kwance abunta se can ta tashi ta bud'e windows d'in d'akin ta yaye curtains kmr yanda taga Nusaiba nayi a gida idan sun tashi daga bacci haka take yi sbd iskan safiya ya shigo,d'umin bacci ya fita,yana kallo har ta gyara d'akin tsaf ta fesa room fresh,ta kuma ciro kayan da zata sa ta ajiye kan bed snn ta jawo towel zata cire rigar baccin da ke jikinta nn ya rufe laptop d'in ya kwanta tare da lumshe idanun sa ya hau bacci se qarfe takwas saura ya tashi lokacin zarah ta kammala shirinta tsaf har tayi breakfast taci aikin gidan ne bata samu tayi ba.
Ta fito da sauri ta shiga mota dan har driver yazo yana jiran ta,wacce garin rufe ganbun mota ta had'a da gefen gyalenta ta rufe bata sani ba har ana hango gyalen ya fito a waje.
Saifuddeen dake can d'akin sa laptop a gaban sa yana ganin su,yayi tsaki tare da d'aukar wayar sa ya kira driver da har ze tashi mota yace ya bawa zarah waya wacce tana kar6a se jin tayi yace"bagidajiya shiga motar ma ba'a iya ba,da Allah bud'e ganbun kija gyalen ki ki matsa can er qauye kawai yayi tsaki tare da tsinke wayar.
Zarah da ta fahimci waye kan wayar tayi mamaki tana dubin ta ina yake,bata ganshi ba kawai ta miqawa driver wayar sa snn tayi kmr yanda yace.
Shi kuma yana kallo har se da suka fita gate d'in gidan suka hau hanya snn ya rufe laptop ya koma bacci se 9 ya tashi ya shiga bathroom zuwa wanka.
Zarah kuwa se 4 ta dawo gidan,tana shiga d'aki wayarta ta soma ringing se da ta cire mayafin ta ta ajiye snn ta bud'e jakar ta ta ciro wayar,da sauri ta d'aga kiran sbd umma ce me kiran,wacce suna gama gaisawa take tambayar ta ko ta dawo daga school tace mata eh,tace"to gasu inna nn zuwa da yayanki tunda safe suka zo nace musu kina makaranta shine suka jira har se kin dawo.
Sosai Zarah taji dad'i har tana tsallen murna.
Wacce suna kammala waya ta sauko downstairs da sauri ta d'auko tsintsinya ta share falon duk da ba wani datti ne dashi ba se dan ganin bata samu ta share shi da safe ba.
Ta mofe shi tas snn ta fesa room fresh take gidan ya d'au qamshi kmr yanda take yi kullum idan ta gyara.
Tana kammalawa ba jimawa taji qarar doorbell har sun iso.
Da murnar ta ta bud'e musu qofa tare da qanqame yayanta wanda dama haka take tarbon shi duk ya dawo daga zariya dan can yake karatu tun kan secondary school har yanzu da yake high school ABU,d'an wayayye dashi fari sol kmr ita kama ce kawai basa yi dan shi mahaifin su ya d'auko.
Cike da murmushi yayan nata yaja karan hancin ta cikin harshen fulatanci,yace"wae baki san kin girma bane zarah"
Kafin zarah tace komai inna tace"yo ina zata san ta girma wnn kam,ko kunya bata ji ta barni tsaye ta rungume ka kai akeyiwa maraba.
Zarah dake kallonta d'auke da murmushi tayi saurin sakin yayan nata taje jikin inna tana mata oyoyo.
Da sauri inna ta janye ta tare da kutsowa ciki tana fad'in ni kinga karki kada ni bani guri in zauna wad'an nn qafafuwan nawa ba qarfi ne dasu ba.
Nan Zarah ta kaita gun doguwar kujera 3seater ta zauna shima yayan nata ya shigo ya zauna ta kawo musu ruwa da lemu suka sha.
Inna se kallon falon take ganin irin had'uwar da yayi.
Tace"barikallah fad'ima kinyi qosin miji wnn irin gida haka awa aljannar duniya,hai kiran min si mu gaisa d'an albarka.
D'an murmushi Zarah tayi tare da fad'in"ae inna baya nn ya fita.
Wacce ta fad'i haka ne kawai amma yana nn,tace musu hakane dan tasan ba qaramin wulaqanci ze musu ba in yazo,ba kuma zata so hkn ba ga inna har da wani sa mishi albarka.
Ya school Ammi tace kin fara zuwa ko?
Yayanta ya tambaya.
Zarah tace"eh na fara zuwa tun wancan satin"
Yace"to Allah ya taimaka"
Tace"amin"
Nan inna itama tasa bakin ta tare da mata fatan alheri,snn kuma ta shiga yi mata nasiha kan yanda zatayi haquri da zaman rayuwar aure,duk da sosai tayi mata nasiha a can Rimin dako lokacinda aka je sa lalle.
Zara dai tayi shiru se sauraren ta take amma a ranta se Allah Allah take kar saifuddeen ya fito har se sun bar gidan.
Bai fito ba kuwa har suka tashi tafiya.
Sun fito zarah ta rakosu inna ta hango mota ta shigo tace"yauwa ga d'an albarkan nn ma ya dawo.
Murmushi yayan zarah yayi ya kalli inna yace"inna baki gane shi ba ae wnn drivern da Ammi ta turo ne yazo ya tafi damu.
Inna tace"Ayyo ban gane si ba ai ca nake d'an albarkan ne ya dawo.
A'a bashi bane cewar zarah snn yayan ta yace"idan ya dawo se ki gaida mana shi...eh kice munzo bamu same si ba muna gaida si kinji koh.
Ita kuma inna ta fad'a.
Zarah tace dasu
"to"
wacce tana tsaye har sai da suka shiga mota suka wuce snn ta juya zata koma daga ciki,se hango saifuddeen tayi tsaye a bakin qofar shiga falo riqe da waist d'in sa yana mata kallon lallai ma.
Tana qarasawa sosai cikin d'aure fuska yace"uban waye yabawa wa en can qazaman izinin shigo min cikin gida,tambayar ki nake su waye!
Ya daka mata tsawa zata ja baya sbd tsoro,ya fizgo ta da qarfi har se da ta fad'o kan jikin sa,da saurin sa kuma ya ture ta tare da kai mata mari snn ya nuna ta yace"bari kiji in gaya miki nn ba irin gidan ubanki bane da kowane kucaki ke shigowa dan haka wlh duk na qara ganin su a gidan nn se na illata ki er iskar yarinya wuce in daina ganin ki a nn very stupid!
Ya fad'a yana kallon ta a fusace,yayinda ta wuce ciki da sauri tana kuka.
Kana shima ya koma daga ciki yayi tsaye a falo fuskar sa a yatsine wai duk falon ya 6aci da warin fulani se masifa yake tayi,ya yaye curtains d'in windows ya d'auko room fresh ya feffesa.
Snn ya fito se qwalawa me gadi kira yake wanda yazo aguje da sauri ya durqusa a gaban sa yana fad'in gani yalla6ai.
Saifuddeen yace"kana jina!
wa en nn qazaman mutanen da suka fita yanzun nn kar in qara ganin qafar su a gidan nn,idan kuma ka sake kuskuren barin su suka shigo wlh a bakin aikin ka!.
Da sauri me gadin ya shiga bashi haquri yana fad'in"inshaa Allah hkn bazai sake faruwa ba yalla6ai sunyi na farko sunyi na qarshe bazan sake barin su su shigo ba ko yanzu dan naga drivern Hjy ne ya kawo su shiyasa.
Saifuddeen da ke kallon sa cikin daka tsawa yace"naji da Allah tashi ka tafi ban neme ka wani dogon surutu ba
sha sha sha kawai da be san aikin sa ba,kana barin kucakai suna shigo min cikin gida..mtsw!
yayi tsaki tare da komawa ciki,jim kad'an ya fito riqe da makullin motar sa ya bar gidan shida kitty da kusan ko yaushe da ita yake fita.
Be dawo gidan ba se bayan isha'i,kitty na biye dashi kmr jela suka nufi d'akin shi.
Dama sunci abinci a waje,cire kayan jikin sa kawai yayi ya fad'a bathroom yayi wanka,yana fitowa yayi shirin bacci,snn ya janyo laptop d'insa ya bud'e yana kallon zarah dake zaune kan bed ta had'e kai da guiwa,bazai iya fahimtar me take yi ba is she crying or no hkn yasa ya maida abun baya yaga tun lokacinda taje d'aki cikin kuka ta hau kan gado tare da had'e kanta da guiwa she is still like that bata sake d'agowa ba har yanzu.
Nan ya rufe laptop d'in ya nufi d'akin ta,inda jelar shi kitty na can ya bari kan sofa tayi bacci.
Qarar bud'e qofar da yayi ne yasa zarah ta d'ago fuskarta ta kalle shi hawaye na gangarowa a hankli kan kumatun ta.
Tana kallo har yazo ya zauna kusa da ita,zata tashi knn ya kama hannun ta ya maida ta yana kallon idanunta da duk sun kumbura kan kuka.
Fuskar sa ba yabo ba fallasa snn muryar sa a natse yace"wa enda suka zo su waye a gurin ki?
Komai bata ce dashi ba se fizge hannun tayi ta miqe tsaye,ba shiri ta dafe goshin ta snn ta tafi suuu zata fad'i sbd wani irin jiri da ya d'ibe ta,saif ya tashi da saurin sa ya tarbo ta ya zuba mata ido yana kallon yanda ta dafe goshin ta sosai snn ta runtse idanunta gam can yaji gabad'aya ta saki har hannun ta dake kan goshin ta ma duk ta sake,ta some mishi a hannu.
Nan ya d'aura ta kan bed ya kwantar snn ya d'auko ruwan gora a fridge ya yayyafa mata har kusan sau ukku snn ta fitar da dogon numfashi amma idanuwan ta a rufe bata bud'e ba haka kuma ba alamar zata bud'e dan ko motsa su ma bata yi ba.
Saifuddeen dake kallonta ya dafa goshin ta yaji yayi zafi sosai be sake yayyafa mata ruwa ba se tashi yayi ya tafi zuwa d'akin sa jim kad'an ya dawo riqe da d'an small syringe d'auke da ruwan magani a ciki,ya zauna tare da kama hannun ta na hagu ya soka allurar sannu a hankli kan jijiyar hannun har se da ruwan maganin suka qare snn ya zare yana d'an murza mata hannun.
In seconds ta sauke ajiyar zuciya a hankli,ya kafe idanun sa se kallon fuskar ta yake can yaja blanket ya rufa mata jikinta snn ya kashe wutar d'akin ya fita.
Se sha biyun dare ya koma dawowa yana mird'a qofar d'akin nata ya jita a rufe da key knn ta farka ta rufe d'akin.
Da ya koma d'akin sa ya duba laptop ya ganta zaune qasa kan rug kusa da sofa fresh milk a gaban ta da cup tasha ta d'aura kanta kan sofa se bacci take wutar d'akin a kunne.
Washe gari koda ya dawo daga sllr asuba ya sami d'akin nata a bud'e ta cire key.
jikin wardrobe ya same ta daga ita se towel d'aure a jikinta,girshi ta gan shi da sauri ta ciro hijab a cikin wardrobe tasa,snn fuskar ta a d'aure ta kalle sa,kafin tace komai ya ta6e bakin sa cikin girgiza kae snn a hankli ya soma tako zuwa gurin ta yana fad'in"Allah wadarai meye a jikin naki to har na 6oyo,baki ga en matan da ke zuwa gurina bane tamkar su sukayi kansu,full option ba kmr ke da kallon ki ma asara ne.
"Look this"
Ya fad'a tare da kama d'ayan mamanta yace"boob ne ko abu da kama"
Qara zarah ta saki tare da saurin buge masa hannu dan sosai ya kama mamman ba tare da tasan ma ze kama ba kae tsaye taji hannun shi,wacce tana buge mishi hannu ya manna ta da qarfi jikin wardrobe tare da kama hannayen ta gabad'aya ya maida su baya ya riqe da d'ayan hannun sa,d'ayan hannun sa kuma ya kama wuyan hijabin ta yace"zan miki zir wlh a nn gurin inga tsiyar da kk 6oyo na kuma yi abunda naga dama,er rainin hankali a banza dai an bani bare da igiyar aurena shine har kina da qwarin guiwar da zaki buge min hannu sbd kin raina ni ko!
Wani kallo zarah ta mishi ranta a 6ace se qoqarin qwatar kanta take.
Yace"all right ni kk ma wnn kallon lallai yanzun nn zan nuna miki ke qaramar er rainin wayo ce zan tu6e ki na kuma fitar dake a cikin gidan se kowa a anguwar nn kaf ya gama ganin ki.
Nan kawai ya fizge hijabin ta ya cire ya jefar snn ya kama towel d'inta ze fizge da sauri zarah ta fashe da kuka cikin girgiza kai tana fad'in"a'a dan Allah kayi haquri bazan sake ba".
Kafin yayi komai qarar wayar sa ta katse shi kuma Abba ne me kiran dan ringing d'inda ya sa mishi daban nn ya sake ta tare da tura ta da qarfi har se da ta fad'i zaune snn da sauri ta riqe towel d'inta da taji ya kunce ze sa6ule mata.
Saif be fita a d'akin ba se kallon ta yake yana waya da Abba kana yazo gab da ita ya durqusa tare da d'aura mata wayar a kunnen ta.
Jin Abba ya kira sunan ta yasa tayi saurin share hawayen fuskar ta kmr wanda yana kusa bata so ya gani snn ta saisaita kanta muryar ta a hankli ta shiga yin waya dashi har suka gama.
Saif ya maida wayar sa a aljihu ya kalle ta tare da kallon bathroom ya kuma kalli agogon bangon d'akin ko be fad'a ba tasan me yake nufi,ba musu ta tashi se bayan ta shiga bathroom ya miqe tsaye a hankli yana kallon hannun sa da ya kama mammanta dashi a ransa yana mamaki ba yau ya fara ta6a nonon mace ba amma ya akayi da ya ta6a nata yaji wani abu daban kmr be ta6a ta6awa ba.
Am sorry plz gobe bazan sami damar yi muku ba sbd wata exam da zan rubuta ina neman addu'ar ku plz馃憦馃徎.
*Dedicated to 禄禄禄zarah gwandu*
[11:15AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Sunday 25/02/2018_
*芦禄芦禄芦禄SAIFUDDEEN!芦禄芦禄芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄page 24芦禄*
Nan de ya basar ya fita daga d'akin.
Zarah kuwa bayan ta kammala shirin ta,dama komai ta fito zata fita,ta sami saifuddeen zaune a falo ya jingina bayan sa a jikin kujerar da yake zaune idanuwan sa a lumshe kitty kan laps d'in sa se shafa jikin ta yake a hankli wanda ba abinda yake tariyo wa se rayuwar shi shida Sophie da tun secondary school suka had'u da juna har zuwa university,primary school kawai yayi a Nigeria.
Qamshin turaren zarah ne ya dawo dashi duniyar tunanin da yake ya bud'e idanun sa da duk sukayi jajur suka canza launi.
Zarah da tayi tsaye ta kasa wucewa sbd tsoron kitty ya sakar mata wani mugun kallo.
Kallon da ya mata ne yasa dolen ta ta nufi qofa zata fita se kawai kitty ta nufo ta aguje tare da yin kukan su na kyanwa.
Ae kuwa a tsorace ta fasa ihu bata riga ta bud'e qofa ba taje da gudu tayi tsalle ta hau kujerar da saif yake zaune tana neman 6uya a bayan shi.
Da sauri Saifuddeen ya miqe yana mamakin me kitty keyi haka wacce da gudun ta zata hau kujera cike da son cafko zarah da gabad'aya ta cukuikuiye saif se ihu take.
Cikin daka tsawa yace"kitty stop it!"
Se kuwa ta tsaya cak bata hau kujerar ba se ma ja baya da tayi.
Nan ya fizgo zarah ya dawo da ita gaban shi yana fad'in"ke kuma ki min shiru ko in 6a66ala ki a nn gurin wlh munafuka me kika mata da har take binki kin qara mata wata muguntar ko"
Zarah bata iya bashi amsa ba se qara rirriqe shi tayi cikin kuka tana ihu sbd yanda kitty ta sake yunqurin cafko ta.
Nan saif ya kore ta ta bar gurin,snn a natse ya kafe idon sa akan zarah dake rungume jikin shi duk ta cukuikuye shi bata ma san ya kori kitty ba se kuka take tana fad'in ita wlh bata mata komai ba dan Allah ya kore ta.
Be ce mata komai ba se d'agota yayi tare da nuna mata kitty da idon shi.
Nan ta juya taga kitty can nesa dasu near kitchen ta kame guri d'aya se kallon su take.
Saifuddeen yace"kayan jikin ki ne fa idan baki je kin canza su ba zata sake biyoki dan yunwa take ji"
Da sauri zarah ta kalli kayan jikinta atamfa ce me hoton kifi da aka d'anyi su manya jefi jefi a jikin atamfar se tayi kyau ba laifi.
Ta juyo ta kalli saif idonta tap da qwallah tare da qara rirriqe shi.
A hankli ya lumshe idanun shi tare da ware su akanta yace"No jeki kawai baza ta miki komai ba"
Kallon kittyn tayi ta kuma kalle shi tana son wucewa amma kuma tana tsoron kar se ta kama hanya kitty ta bita.
Saifuddeen da ya fahimci bata iya wucewa ga lokaci se tafiya yake driver na waje yana jiran ta,ya kama hannunta ya tafi da ita har bakin qofar d'akinta,byn ta shiga ya dawo downstairs ya zauna kan kujera tare da jingina bayan sa snn ya lumshe idanun sa a hankli yana jin yanda qamshin turaren zarah me dad'i ke tashi a jikin shi.
Sosai turaren ya masa dad'i sbd cool qamshi ne dashi ba me irin hawa kai d'in nn bane,se ma natsuwa da mutum ke tsintar kanshi a ciki.
Kmr wanda aka tsakura ya bud'e idanun sa da sauri ya kalli kitty still tana can kame guri d'aya.
Murmushi ya sakar mata kmr wata mutum ya tashi yaje ya d'auke ta yana bata haquri,snn ya shiga kitchen