Showing 69001 words to 72000 words out of 145898 words
firgita baqi masu shigowa.
Audu ya zame qasa cike da ladabi yace" inshaa Allah yalla6ai yanzun nn ma kuwa"
Daga haka ya tashi da sauri ya shiga d'akin shi ya d'auko kyanwar zai fita da ita.
Jamil da har ze wuce ya tsaya yace"kaga ba ina nufin ka jefar da ita ba dmn ba'a san halin da zata shiga ba,ka bincika maqota kaji idan da akwai me ra'ayin ajiye ta a gidan shi ba matsala bane se ka basu,amma dan Allah su kiyaye kar ta dawo gidan nn"
"To yalla6ai"
Mai gadi ya fad'a snn ya fita riqe da kyanwar a hannun shi"
6angaren su saif kuwa driving yake amma se yi yake yana kallon zarah wacce jikinta a sanyaye har yanzu sbd sam bata ta6a ganin baqar kyanwa ba a rayuwar ta,da ta ganta se ta d'auko ma aljana ce shiyasa duk ta firgita da yawa,wacce duk da taji cewa kyanwa ce besa tsoran da taji ya tafi lokaci d'aya ba shine take jin jikinta duk a mace kmr wata mara lakka.
Saif dake kallon ta a hankli ya kama hannun ta,zarah ta kalle shi,muryar sa a natse yace"sorry kin tsorata sosai ko"
Fuskar ta kmr yanayin shagwa6a tace"Ae kam ni bazan sake zuwa wnn gidan ba ma"
No ae indai jamil ne tunda yaga kina tsoron ta inshaa Allah daga yau ta bar gidan knn.
Meyasa?
Ya kalle ta kawai snn yace"halin shi ne kawai haka"
Tayi kasaqe snn tace"Allah sarki wlh har ya birge ni da yasan darajar d'an adam ba kmr kai ba"
Ta qarashe mgnr ne tare da zare hannun ta daga nashi snn ta kauda fuskar ta tana kallon gefen hanya.
Wani irin abu saif yaji fuskar sa a d'aure ya kalle ta kawai bai ce mata komai ba se tuqin sa da ya ci gaba dayi.
kae tsaye gidan su umma suka wuce se bayan isha'i snn yace ta fito su koma,koda ta fito ta same shi jingine jikin mota Apple fruit drink a hannun shi yana sha,ya kalle ta fuskar nn tasa ba annuri duk haushin ta yake ji a ranshi.
Wanda ba shiri ya saki gorar Apple drink d'in da yake sha sbd sarqe shi da yayi,se tari yake tayi,zarah tayi tsaye kawai tana kallon shi har sai da tarin ya tsaya mishi.
Ya dalla mata harara tare da fad'in"tafi can er qauye kawai mutum na faman tari ko sannu baza ki mishi ba kin tsaya se faman kallona da kike"
Ta6e baki tayi snn tace"da dai wanda yasan darajar mutane ne dana mishi sannu har in kawo mishi ruwa ma yasha.
Tana qarashe zancen taje zata zagaya ta shiga mota,se jin tayi ya fizgo ta ransa a 6ace yace"wlh kika sake yabon wani a gabana se nayi gutsu gutsu da wnn bakin naki wawiya kawai wacce bata san darajar aure ba.
Nan kawai zarah ta sami kanta da fashewa da dariya se kuma ta rufe bakin ta da sauri tana son mayadda dariyar.
Duk 6acin ran saif take ya neme shi ya rasa ya sassauta damqar da ya mata ya tsaya kawai yana ta kallon yanda dimples d'inta ke lotsawa dan still ta kasa had'iye dariyar.
Samun kansa yayi da d'aura en yatsun sa biyu ya lotsa dimples d'in d'auke da murmushi a fuskar shi yace"kin raina ni ko"
Girgiza masa kai tayi tare da kai hannyen ta ta saqalo su a bayan wuyan shi tana kallon shi d'auke da murmurshi a fuskar ta snn tace"ka ajiye zancen raini ae gaskiya na fad'a,snn ka daina fad'ar cewa wai bansan darajar aure ba dan dai ban auri wanda nake so bane,amma idan na aure shi zaka d'auka ma kmr nafi kowa sanin darajar aure.
Saif dake riqe da waist d'inta yayi murmushi tare da lakato hancinta yace"nima ki daina ce min bansan darajar d'an adam ba dan dai ban auri wacce nake so bane.
Far tayi da idanun ta tare da fad'in" Allah sarki"
Wacce daga haka ta janye jikinta daga nashi ta zagaya ta shiga mota.
Nan shima ya bud'e gambu ya shiga.
Abba dake can saman balcony yana hango su,d'auke da murmushi ya bisu da kallo har saif yaja mota suka fita daga gidan,wanda har ranshi dad'i yake ji sosai dmn duk a tunanin sa ko kalaman soyayya ne suke fad'awa junan su.
Yayinda su kuma tunda suka fita daga gidan suka hau hanyar komawa gidan su kowannen su shiru basu sake cewa komai ba asali ma zarah se gefen hanya kawai take kallo,amma shi kam saif se yi yake yana kallon ta,can ya kama hannun ta,ta juyo a hankli ta kalle shi ya d'an yi murmushi snn yace"idan na cika maki alqawarin ki waye kike nufin ki aura da kike so?
Murmushi zarah tayi snn tace"wanda nake so yafi ka komai,mutumen kirki ne wanda ke daraja d'an Adam komai qasqantar shi ba sai dan yana son shi ba"
Hararar ta yayi tare da kai hannun sa ze buge mata baki,tayi saurin kaucewa tana mishi dariya.
Ae fa se ya tsurawa dimples d'in ta ido,yana ji kmr ma kar ta daina yin dariyar,wanda sam ya ma manta cewa tuqi yake.
Sorry 4 this one.
_Wednesday 14/03/2018_ *«»»««»SAIFUDDEEN!«»»««»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«» 36*
Innalillahi wa ina ilahai raj'un!
Zarah ta fad'a da sauri ganin tsirif ya rage ya dagi wani mashin dake gaban su.
A rud'e cikin sauri saif ya samu ya kaucewa mashin d'in.
Zarah ta sauke gauron numfashi tare da fad'in"Allah mun gode ma"
Cikin harshen fulatanci.
Saif ya kalle ta kawai bai ce mata komai ba yaci gaba da tuqin shi.
Har suka isa gida wa enda da shigar su kowanen su ya nufi d'akin shi.
Yayinda zarah da shigar ta d'aki wanka kawai tayi tasa kayan bacci ta kwanta take tayi bacci abunta.
Akasin saif wanda tuni shima yayi wanka yayi shirin bacci amma har 12 still awake beyi bacci ba gabad'aya ya rasa me ke damun sa game da zarah se tariyo dariyar da take ta mishi yau yake.
Can ya miqe ya nufi d'akin ta yaje gab da ita kan bed ya zauna a hankli yana kallon fuskar ta ita kam se baccinta kawai take tayi tana sauke numfashi cike da natsuwa.
A hankali ya d'aura hannun sa gefen fuskar ta yasa d'an yatsan sa babba yana shafa dai dai inda dimples d'inta ke lotsawa,yana tuna Sophien shi in tayi dariya bata da shi,kawai dai tafi zarah kyau amma be ta6a shagala yana kallon ta ba idan tana yin dariya,kmr yanda yake shagala da kallon zarah but why?
Sbd dimples d'in ta suna matuqar yi mata kyau idan tayi dariya.
Ya tambayi kanshi,ya kuma bawa kanshi amsa,duk a cikin ranshi.
Wanda a natse yakai bakin sa a gurin ze mata kiss se kuma ya fasa sbd motsin da tayi tare da gyara kwanciyar ta ta bashi baya.
Nan ya miqe jikin sa a sanyaye dashi kansa be san meyasa yaji jikin nasa haka ba,ya d'auki remote ya qara mata qarfin sanyin split dan yaji sanyin bai wadatar ba.
Ya ajiye remote ya koma 6angaren da ta juya yayi tsaye yana ta kallon ta har sai da yaji sanyin split d'in ya wadatar snn ya fita.
2dayz later.
Sauri sauri zarah ke saukowa daga staircase,sbd sosai tayi latti kuma bata son ta fita bata sa wani abu a cikin ta ba shine take sauri zata je kitchen ta nemi abunda zata ci.
Saif dake zaune kan dining yana shan tea kmr wanda aka tsakura ya miqe zumbur da sauri tare da fad'in"ke ina zaki je haka?
Zarah da har ta kusa kai qofar kitchen taji maganar sa daga sama dan bata ko lura da cewa yana falon ba ta tsaya tace"sauri nake zan sha tea bana son fita da yunwa"
Saif yace"ba wnn na tambaye ki ba ina zaki je da wa en nn kayan dake jikinki.
Zarah ta kalli jikinta,er riga ce baqa mara nauyi mai siririn hannu kmr vest,wacce style d'in wuyan rigar duk ya fito da rabin mammanta a fili snn rigar tayi d'as a jikinta,kmr yanda leggings wato wandon da ke jikinta ya mata d'as da tsayin sa iya rabin qauri.
Tace"Hauka nake da zan fita haka doguwar riga fa zan d'aura akai.
Tana gama fad'a ta wuce kitchen ta bar shi tsaye.
A kasale ya koma ya zauna cikin sauke numfashi a hankli sbd abunda yaji dan yanda ta fito sauri sauri haka mammanta ke taya ta suna shaking da sauri wanda shi kanshi haka kawai yaga ya miqe zumbur yana watsa mata tambaya.
Zarah tana shiga kitchen sharp sharp ta had'o tea ta fito wacce har zata wuce sei kuma ta tsaya tana kallon saif da ya talla6e goshin sa ya tsurawa tean da ke gaban sa ido da alama ba a kan tean hankalin sa yake ba ma.
Nan taje taja kujerar da ke fuskantar shi ta zauna ta ajiye tean ta snn ta karkatar da kanta tana leqen fuskar shi cikin qyasta masa yatsu dai dai saitin kunnen shi,ya d'ago a natse yana kallonta ta sakar mishi murmushi tare da fad'in"kana tunanin gwanar ka...se tayi shiru cikin tunani ta kasa kawo sunan Sophie, tace"am meye ma sunan ta ni mantawa nake"
Saif dake kallonta yayi d'an guntun murmushi,ba tare da ya gaya mata sunan ba se kallonta kawai da yake.
Kafin yake sauke idon sa akan d'an mintsilin kofin da ta had'o tea a ciki da bai wuce kur6i d'aya ba.
Yana kallo ta d'auki kofin ta kai bakin ta,zama d'aya ta shanye tean ta ajiye kofin da bata jin sauri ze iya barinta taje ta wanke ta barshi nn ta tashi da hanzarin ta,ta bar masa qamshin turaren ta ta wuce.
"Ya salam"
Saif ya fad'a a hankli cikin tallabe goshin sa snn ya lumshe idanun sa ba abunda yake gani kmr rabin nonuwan ta da kuma bayanta da ta tashi zata wuce ba qaramin tafiya sukayi da imanin sa ba,sosai wandon ya kama ta yanda ya kamata ba qarya ya fiddo mata komai ta yanda dole duk lafiyayyen namiji ya kalle ta se yaji yar a jikin sa musamman yanda ta tashi da hanzari jikinta na karkad'awa ta wuce.
Can bayan minti biyu cool qamshin turaren ta ya sashi d'agowa a hankali ya kalle ta,ya ganta har ta shirya cikin arabian gown baqa tayi rolling da d'an kwalin arabian gown d'in kmr yanda taga nusaiba nayi se ta fito mishi kmr wata balarabiya wacce ba kad'an ba tayi kyau.
"Muje ko"
Zarah ta fad'a tana me kallon saif wanda lokaci d'aya yasha mata toka,a sanyaye tace"ko ba kai zaka kaini bane?
Ni zan kai ki amma se kinje kin sauyo wasu kayan,ko an gaya miki zuwa makaranta fashion ake hadda wani saka turare.
Zarah da ko kwalliya babu a fuskar ta ta kalli jikinta tana mamakin meye fashion a nn jallabiya ce fa doguwa har qasa se d'an kwalinta da ta lauya akai,turare kuma tunda tayi wanka ta shafa shi a jikinta shikenan bata sake sakawa ba,mtsw kae wnn mutum masifar shi yawa ne da ita,shikenan dan tunanin wnn baturiyar ya motsa mishi yanda yake jin takura an hana mishi auren ta haka yake qoqarin ganin ya takura mutum,ae kuwa baza ka sami wnn damar ba.
Tayi mgnr ne a cikin ranta snn tasa qafa zata wuce,cikin daka tsawa yace"ke! baki ji me nace bane ko so kk sai na 6ata miki rai!
Zarah ta juyo ta kalle shi yanayin fuskar ta cike da jin duk ya takura ta tace"to ae gani nayi duk abunda ka fad'a ba haka bane ba wani fashion da nayi,turare kuma fa tun d'azu yake a jikina ba sake sawa nayi ba"
To kije kisan yanda zakiyi qamshin turaren ya fita ki kuma sauyo wasu kayan idan ba haka ba ba inda zaki je.
Zarah da duk ranta ya gama 6aci cikin muryar kuka tace"to ni kam wae ina ruwanka da yanayin shiri na da ma komai nawa,shikenan dan kana cikin takura se kace zaka takura mutum ni gaskiya bazan iya yanda kace ba,sai dai kar inje d'in"
Ta qarashe mgnr ne tare da jefar da makullin motar shi dake hannun ta wacce ita kanta bata san ya akayi ya manta shi a d'akin ta ba se ganin sa kawai da tayi ajiye kan bedside drawer shine da zata fito ta fito masa dashi.
Wacce tana jefar da makullin ta wuce a fusace zuwa sama.
Saif da ya bita da kallo ya sauke numfashi a hankali yana tunanin gaskiya fa ta fad'a, meye ruwan shi da ita da har ze damu da dressing d'inta da kuma qamshin da takeyi...mtsw yayi tsaki dan se yaji haushin kanshi ya tashi jikin sa a sanyaye ya d'auki makullin motar sa da ta jefar yana tuna jiya da dare ne ya manta shi a d'akin ta bayan ya dawo daga gidan hajiya,da dawowar shi yaje d'akin ta kae tsaye ya samu ma ta yi bacci,wanda bai san ma tsawon lokacinda ya d'auka yana kallonta haka kawai ba,haka kuma be san ma ya manta makullin ba se yanzu da ta jefar yake tuna cewa ya shiga d'akin ne riqe da makullin a hannun shi,amma da ya fito babu makullin se bai fahimta ba.
A hankli ya koma sauke wani numfashi snn ya haura sama zuwa d'akin ta.
Koda ya shiga ya same ta har ta fincikar da top veil ta yar snn da sauri cikin 6acin rai take 6alle buttons d'in arabian gown d'in dake jikin ta,dan sosai gown d'in keda kyau har de yanda aka dazo aninnan tun daga kan shoulder suka gifta tsakanin boobs suka tafi har zuwa gefen waist.
Yayinda zarah kad'an ma ya rage ta qarasa 6alle aninnan.
Saif dake kallonta ya qarasa cike da son ya rarrashe ta ya riqo ta,ta qwace da qarfi tare da fad'in"ni ka rabu dani"
A natse ya sake riqo ta ya manna ta sosai a jikin sa ta yanda baza ta iya qwace kanta ba,yana kallonta muryar sa a natse yace"sorry am just kidding u,ina miki wasa ne but am sorry yi haquri kinji maida buttons d'in se mu tafi in kaiki"
Ya qarashe mgnr ne tare da kama hannun ta ya tafi da ita kan bed suka zauna ya shiga rufe mata buttons d'in da kanshi,wanda a cikin ranshi se fmn had'iyar yawu yake sbd rabin nonuwan ta da ke bayyane yana fmn satar kallon su har ya samu da qyar ya qarshe rufe mata buttons d'in duk yayi zufa sbd masifar abunda yake ji.
Ya sauke numfashi tare da ciro farin handkerchief ya shiga share zufar,yana mai mamakin duk irin sanyin split d'inda ke ratsa d'akin,shi gashi zufa yake hadda sharewa.
Kana yabi zarah da ido se kallonta yake wacce bata ma lura da yanayin da yake ciki ba se gun dressing mirro ta nufa tana lauya d'ankwalin ta.
Bayan ta idar ne ta d'auki jakar ta suka fita yaje ya sauke ta school ya dawo zuwa 10 snn ya tafi hospital,wanda ya fita ne kawai amma ba dan yana jin zai iya yin wani abu ba dan abunda yake ji ba dainawa yayi ba.
Hakan yayi ta fama har lokacin d'auko zarah yayi yaje ya d'auko ta,kmr yanda kullum idan sun gama lectures driver take kira ta gaya mishi,shi kuma drivern se ya kira saif ya gaya mishi kmr yanda saif d'in ya buqata.
Koda suka dawo gida qarfe shida tayi,zarah ko abinci bata iya ci ba sbd test d'inda aka ce za'a musu gobe,se cire arabian gown d'in jikinta kawai tayi ta ciro handout d'in da zasuyi test akai ta hau yin karatu se safa da marwa take a cikin d'akin ta tana faman cramming.
Saif dake d'akin sa yana kallonta a laptop ji yake kamar tana kashe shi ne dan yanda take safa da marwa a d'akinta haka abubuwan ta ke masa safa da marwa a ido,gashi baya jin zai iya daina kallonta,amma ya zama dole ya mata wayo ta sauya wasu kayan masu rufa mata jiki ko zai samu sa'idar abunda yake ji.
Nan ba 6ata lokaci ya tashi ya nufi d'akin ta wanda kai tsaye ya nufi gunta tare da tsaida ta ya kar6e handout d'in hannun ta,muryar sa cikin lallami kmr wata qaramar yarinya zeyiwa magana yace"karatun me kike yi haka da dawowar ki baki je kinyi wanka ba,baki kuma ci abinci ba.
Yanayin fuskar ta kmr me son yin shagawa6a tace"wai test zamuyi gobe kuma course d'in yana da matuqar wahala wlh,duk cikin courses yafi bani wahala shine nake son in d'an karanta snn ko zanje inyi wanka inci abinci se naci gaba,dan gobe tun da safe muke da shi qarfe 8 ga malamin ance mugu ne sosai sai ka dage sosai kake cin course d'in shi.
Saif dake ta kallon d'an bakin ta dake mishi bayani yace"duk da haka dai je kiyi wanka kici abinci zaki fi jin dad'in yin karatun dai dai brain d'in ki ta huta da lectures d'inda kukayi ko.
Gyad'a masa kai tayi tare da kai hannu zata kar6i handouts d'in ta yace"No barshi a hannu na ina son zan duba na koya miki yanda zakiyi karatun a sauqaqe idan kin kammala se ki same ni a downstairs.
"To"
Tace mishi kafin yake fita daga d'akin ita kuma ta cire kayan jikinta ta fad'a wanka.
Bayan ta fito ta shirya,taji anyi sllr magarib tayi sallah snn ta fito.
"Oh my God! wnn abar zata kashe ni"
Saif ya fad'a wanda dawowar sa knn daga masallaci.
Yayi arba da ita ta fito sanye cikin irin qananun kayan da ta cire sak komai iri da'ya da rigar da wando duk irin wa enda yaje ya mata yawo dan ta cire ya samu sa'ida,kawai dai wa en nn farare ne tas kuma kmr ma sun