Showing 24001 words to 27000 words out of 145898 words

Chapter 9 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24761

ta turo text"
Me tace?
Saifuddeen ya tambaya a natse yana me kallon sa da kulawa.
jamil yace"kawai tace tana kewar ka sosai snn ya kitty"
Shiru Saifuddeen yayi be ce komai ba har se da jamil yace me za'a ce mata?
Kawai duk abinda kace mata yayi dmn bana son nida kaina in riqa fad'a har ya zamo na bata kulawa byn Abba ya hana ni,ina jinka fad'i na biyun mene ne?
Jamil dake kallon sa yace"kd zan tafi gun kaka ban sani ba ko zaka tafi naji kana magana kan zaka je ka duba jikin ta"
A sanyaye saifudden yace"Naso inje amma damuwar rashin Sophie ya motsa min bazan iya zuwa yau ba sei dai gobe da safe zanje inshaa Allah.
Jamil yace"ba matsala zan jira ka mu tafi tare amma da safe ne tafiyar zaka iya?
Zan iya but yaushe zaka dawo?
Sunday da safe
Ok shikenan nima zan kai Sunday d'in se ka biyo min muje a motar ka.
"Olryt"
Cewar Jamil snn sukayi sallama saifuddeen ya koma daga ciki jikin sa duk a sanyaye.
9:00pm
Kallo take tana cin abinci,tana ji se doorbell ake ta fmn dannawa amma tayi biris se ci gaba take da cin abincin ta,dan tasan ba kowa bane face en matan Saifuddeen dake samun sa har gida.
Har sei da aka gaji da danna doorbell aka bud'e qofar aka shigo sbd dama qofar ba'a rufe take da key ba.
Qananun kaya ne a jikinta riga da wando da suka bayyana tsiraicinta kan yanda suka matse ta sosai snn taci uban kwalliyar nn crazy makeup,ga kitson attachment dake saman kanta tsorayen sun sauka har tsakiyar gadon bayan ta kmr wata arniya,d'an qaramin veil ne akanta da ta d'auro shi tun daga bayan qewar kanta tazo dashi kan goshin ta tayi rolling d'insa.
Ba jaka a hannun ta bare purse wayar ta ce kawai se key d'in motar ta dake saqale a d'an yatsanta,ta riqe waist d'inta tana kallon zarah tace"hm!wai dama da akwai mutum a falon nn ne ina ta faman danna doorbell kika yi banza dani baza ki gaya min na shigo kawai qofar a bud'e take ba.
Kallon ta kawai zarah tayi yau ma wata sabuwar fuskar ce ba wa enda ta saba gani ba kuma,ita abun mamaki ma yake bata iyayen su basa raye ne ko me da suka barsu suna yawon iskanci har suna zowa su kwana a gidan wani qaton banza hankalin su a kwance.
Allah kyauta.
Ta fad'a a cikin ranta snn ta maida duban ta gun abincin ta taci gaba da ci.
Da mamaki take kallon zarah kafin tace komai se ga Saifuddeen yana saukowa sanye da white bathrobe a jikin shi da alama fitowar sa knn daga wanka.
Yana qarasowa ta riqo hannun sa tare da nuna masa Zarah tace"my beloved halan kurma aka ajiye maka a cikin gida,na jima ina danna doorbell tana zaune a falon nn bata bud'e min ba snn byn na shigo ina mata magana kallona kawai tayi ta kauda kai taci gaba da cin abincin ta.
Saifuddeen ya kalli zarah dake ci gaba da cin abincin ta tana jinsu amma ko gefen su taqi ta kalla.
yace"iskanci ne tana dik jinki"
Nan ya tafi ze d'auko abu a fridge zarah na ganin sa tafe ta d'auka ko wani abu ze mata ta tashi da sauri riqe da plate d'in abincin ta ta koma bayan kujera ta tsaya,tsaki yayi tare da girgiza kansa snn yaje ya bud'e fridge ya d'auko fresh milk ya wuce sama zuwa d'akin sa tare da wacce tazo gurin shi.
Ta6e da baki Zarah ta bisu da kallo har suka shige ta girgiza kanta snn ta koma kan kujera ta zauna taci gaba da cin abinci tana mai ci gaba da kallo,Tom and jerry ne ake a tashar MBC 3 se dariya take kwasa kmr wata qaramar yarinya.

Da safe bayan saifuddeen ya kammala shirin sa na zuwa kd ya tafi d'akin zarah kitty na biye dashi.
Da shigar sa d'akin kae tsaye gun fridge ya nufa ya d'auko ruwan gora da sukayi mugun sanyi ya nufi gun zarah dake kwance kan bed tana bacci gabad'aya ta rufe jikinta da blanket fuskarta ce kawai bata rufe ba.
6alle gorar yayi ya shiga zuba mata ruwan kan fuskarta,zarah ta tashi a firgice cikin fasa ihu tana neman guduwa daga kan gadon,Saifuddeen ya riqe ta yana ci gaba da qwara mata ruwan har se da ya qarar da ruwan gorar a kanta,se kuka take tana zagin sa tana mishi Allah ya isa.
Marin da ya saukar mata ne yasa tayi shiru tare da cusa fuskarta gabad'aya cikin cinyoyin ta ta saki wani sabon kuka.
Yasa hannun sa ya d'ago ta da qarfi yace"kalli nan kin ganta!ya nuna mata kitty da ya riqo a hannun sa"
Zarah ta kalle ta tare da saurin kamewa a jikin gadon sosai kmr zata shige ciki,jikinta se rawa yake haka ma muryar ta tace"eh na gani dan Allah kar ka liqa min ita wlh bazan sake zagin ka ba"
Sake kittyn yayi tare da d'aura d'ayar qafar sa kan gadon ya ranqwafa sosai kusa da zarah yana kallon ta yace"zanyi tafiya se gobe zan dawo ban gaya miki ba se dan kisan cewa ke zaki kula da kitty kuma ki tabbatar kin kula da ita yanda ya kamata"
Yana kaiwa nn ya juya ze tafi tayi saurin riqo rigar shi ya mata wani irin mugun kallo tare da kama hannun nata da ta riqo rigar shi ya mird'e hannun kmr ze karya ta,ta saki ihu tana fad'in yi haquri dan Allah dama zan gaya maka ne wlh bazan iya kula da ita ba tsoron ta fa nake ka sani.
Yace"Right tunda kina tsoron ta ki barta kar ki kula da ita kinji"
Yayi qwafa tare da fita d'akin kitty na biye dashi.
Zarah ta taso da gudun ta ta rufe d'akin da makulli.
Bata fito ba se da ta tabbatar ya bar gidan wacce duk a tunanin ta ya tafi da kitty amma se hango ta tayi kwance kan 2seater tana bacci.
A tsorace taja baya da sauri riqe da tsintsiyar da ta d'auko zata yi shara.
Fuskar ta kmr zatayi kuka tana kallon kitty tace"Oh oh wato da kika bishi baije dake ba.
Mugu kawai azzalumi wlh ka cuce ni da ka bar min ita ni yanzu ya nasan zanyi.
Ta jefar da tsintsinya tana kallon falon taso ta share shi amma bazata iya ba dan baza ma ta iya qarasawa daga cikin falon ba,bare tayi zancen fita ta share harabar gidan da kuma ban ruwan flower dan duk ita keyi sbd suna cikin ayyukan da gateman keyi da saifuddeen yace duk ita zata riqa yi abu d'aya ne bata yi shine bud'e gate.
Ba yanda ta iya haka ta d'auki tsintsinyar ta mayar.
Snn ta had'awa kanta breakfast taje d'akinta ta rufe da makulli.
Se byn ta gama breakfast har tayi wanka zuwa 12 snn ta fito.
Tsoro tsoro take saukowa daga staircase tana leqen kitty still bacci take haka ta lalla6a da saurin ta ta shiga kitchen ta rufe bata fito ba har sai da tayi girkin ta da tasan ze kai mata har dare ta zuba a kula ta kuma d'auki duk wani abu da tasan zata buqata dan bata son in ta shiga ta koma fitowa.
Dama ta d'ibarwa kitty nata a plate d'inta,da ta fito ta ajiye mata abincin nesa da ita,tsoro da gudun kar qamshin abincin ya farkar da ita bata riga ta shige d'aki ba.

Guraren 9 duk taji zaman d'akin ya isheta ta fito sanye da kayan bacci.
Kmr dai d'azu tsoro tsoro take saukowa tana leqen kitty amma se bata ganta ba,bata damu ba kawai dai tayi mamakin ko ina ta shiga ne oho,nn dai ta basar taje tayi zaune kan 3seater ta kunna kallo.
Can hankalin ta gabad'aya ya tafi gun kallo ta soma jin kukan kitty.
A tsorace ta tashi tana dube dube ta ina kitty zata fito.
Ae kuwa se ta hango ta tafe tana saukowa daga staircase,nn ta kwasa aguje zuwa kitchen ta shiga ta rufe da key.
Da sauri ta janye daga jikin qofa sbd kukan kitty da taji gab da bakin qofar kitchen d'in har tana sa nails d'inta tana kokawa da gambun kmr zata tsaga shi ta shigo.
Kuka zara ta fashe dashi ta tafi da gudu zuwa store ta rufe.
Amma duk da haka sosai take jin kukan kitty a kunnen ta,gabad'aya ta rud'e jikin ta se rawa yake ita ya tasan zatayi,lokaci d'aya ta tsaya sbd tunanin da ya fad'o mata ba makawa yunwa kitty keji shine take wnn kukan haka sbd abincin da ta zuba mata a d'azun ta ganshi bata wani ci sosai ba naman kawai taci.
Nan ta d'auko kifin gwangwani,ta bud'e ta zuba mata a plate kmr yanda taga Saifuddeen na mata.
Amma kuma ta rasa ta ya ma zatayi ta fita har ta bata kifin,ta san kyanwa da mugun son kifi bare yunwar nn da taji tana tsoron kar tana bud'e qofa tayi super zuwa cafkar kifin,ae kuwa da an kwashi gawar ta a gurun dan ta tabbatar tana yin super to lallai zubewa kawai zatayi somammiya.
Safa da marwa ta dinga yi a kitchen d'in kmr zatayi kuka tana neman mafita ga qarin kifin duk ya cika mata hanci kmr tayi amai take ji dan ko kad'an bata son warin kifi shiyasa ma kwata kwata ko cin kinfi bata yi.
Can ta shiga store da saurin ta ta d'auko sweeper tazo zata bud'e qofa gaban ta se wani irin dum!dum! yake hkn ta jure sannu a hnkli jikinta na rawa har ta bud'e qofar,hannun ta a baya ta 6oye plate d'in kifi tasa sweeper se kora kitty take cike da qarfin hali har ta fitar da ita waje tare da tura mata plate d'in kifi ta rufo qofa da sauri,kana ta zube qasa a gurin ta had'e kai da guiwa tana faman sauke ajiyar zuciya.
Can ta tashi ta leqa kitty ta jikin door ta ganta se cin kifin ta take tayi.
"Alhmdlh"
ta fad'a snn taje kan kujera ta kwanta tana jiran idan kitty ta gama se ta bud'e mata qofa ta shigo dan ita qarin kifin ne da bata so yasa ta fitar da ita waje.
Bacci ne ya kwashe ta a gurin batare da ta sani ba.
Har se washe gari snn ta farka sbd mugun sanyin da taji na ratsa dukkanin ilahirin jikinta har da mafarkin gata a cikin qanqara se ruwan sama ake.
Da tashin ta kan agogon bangon falon ta fara sauke idanun ta qarfe goma na safe.
"Kae!"
Ta fad'a tare da saurin tashi taje ta leqa window hankalin ta ne ya tashi ganin da gaske dai ruwan sama akayi gashi ta bar kitty a waje.
Dafe da qirji tace"na shiga uku wnn wane irin bacci ne haka nayi,se kuma tayi shiru tuna cewa in tana al'ada fa se a hankli bacci take me nauyin gaske da take jimawa kafin ta farka.
Tausayin kitty ne ya matuqar kamata ta fita da saurin ta riqe da sweeper tana dube dube ta ina zata ganta ta korata ta koma ciki kafin Saifuddeen ya dawo ya nemi halaka ta.
Bata ganta ba se plate d'inda ta sa mata kifi ta gani cike tap da ruwan sama,kafin tayi komai se odar mota ta jiyo mai gadi ya fito d'akin sa da sauri yaje ya bud'e gate.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Sunday 18/02/2018_ *芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*






By
*Billy giro馃槉*


*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*



*芦禄Page芦禄 16*
Tsaye tayi a gurin kmr wacce aka dasa,tana kallo har motar da aka bud'ewa gate ta kunno kai ta shigo,jamil ne da Saifuddeen suka fito a ciki.
Se dai Jamil na hango ta ya koma cikin mota sbd kayan baccinta riga da wando ne,da tsayin wandon iya guiwa,en dogayen fararen k'aurin ta suna a bayya ne.
Kanta ta sadda qasa dan se taji kunyar ganin ta da yayi,snn a hankli ta 6oye sweeper a bayan ta,idanuwan ta qasa tana kallon qafafuwan Saifuddeen dake qarasowa kusa da ita gaban ta se dukan tara tara yake tana tunanin abinda zata ce masa ba tare da yaga laifinta ba.
Saifuddeen na qarasowa gurinta yasa hannu ya tallabo fuskar ta yana kallonta fuskar sa a d'aure yace"uban me kika fito yi a waje kin wani tsaya se kallon mutane kike.
Shiru tayi ta kasa ce masa komai ya kalli sweeper da ta 6oye a bayan ta yace"shara zakiyi ne ko me?
Still ta mishi shiru
Cikin d'aga murya yace"ki bani amsa ina tambayar ki kin min shiru!
Girgiza kanta tayi snn cikin inda inda tace"A'a..wnn farar kyan..war...nake nema...ban...ganta ba"
What!
Saifuddeen ya fad'a da qarfi har sai da taji tsoro taja baya da sauri.
Ya riqo ta a fusace yace"dan ubanki gaya min a ina kika kaita!
Tace"ni ba inda na kaita kawai dai ban ganta ba.....wani irin mari ya saukar mata yace"ki fito da ita yanzun nn wlh ko na kakkarya ki.
Kuka ta fashe dashi se ga jamil yazo da gudun sa yana fad'in haba Saifuddeen meye haka!.
Saifuddeen yace"wai gaya min take kitty ta 6ata bata ganta ba,this can never happen!
Kitty!! kitty!!kitty!!!
ya shiga kiranta yana zaga gidan hankalin sa duk a tashe kyace uwar sa ce ta 6ata.
Duk girman gidan haka ya zagaye shi yana ta faman kiranta be ganta ba.
Ya dawo gadan gadan cike da niyar shaqar zarah har se ta fad'i inda ta kaita.
Se kuma ya tsaya cak idon sa akan flowers da yaga suna motsi irin motsin da ba iska ne ke kad'a su ba ta6a su ne ake suna yin motsin.
Be tsaya wata wata ba yaje da hanzarin sa yasa hannun sa ya ware flowers d'in,kitty ce ta 6uya a ciki duk ta jiqe,jikin ta se wani qyarma yake tana son fitowa amma ta kasa sbd gabad'aya bata da wani qarfi.
Hannu biyu Saifuddeen yasa ya d'auko ta,ya miqe tsaye tare da ciro farin handkerchief d'insa a cikin aljihu ya rufa mata,snn ya sata gabad'aya cikin suit jacket d'issa ya rufe ya rungume ta kmr jariri.
Yazo a fusace gurin zarah yayi tsaye yana kallonta d'auke da idanun sa da sukayi jajur,kana ya fizgi hannun ta da qarfi ya tafi da ita.
Jamil ya bishi yana fad'in"saif tsaya mana meye haka wae!" Saifuddeen be saurare shi ba se ci gaba yake da jan zarah wacce keta qoqarin qwace hannunta,amma bata iya qwatar hannun nata ba har ya tafi da ita gun swimming pool ya jefa ta da qarfi ta fad'a ciki.
Wani irin Ihu ta saki me qarar gaske sbd masifar sanyi ne da ruwan,ta taso da qarfi cikin jan numfashi kmr zata shid'e,yayinda jamil ya dafe kansa tare da fad'in"innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
snn cike da mamaki ya saki ido yana kallon Saifuddeen wanda ko a jikin sa,yana jefa ta ya juya abin sa ya tafi.
Ga zarah se wahala take a cikin ruwan tana neman shid'ewa bata iya fitowa.
Hakan yasa gabad'aya hankalin jamil duk ya tashi wanda a rud'e ya shiga kiran Saifuddeen yazo ya taimaka ya fidda ta zata shid'e bata iya fita amma Saifuddeen ko jiyowa beyi ba har ya shige.
Nan Jamil yaje aguje ya d'auko sweeper wacce zarah ta saki a lokacin da Saifuddeen ya fizge ta.
Ya tafi da saurin sa ya miqa mata sweeper d'in yace ta kama ya fidda ta.
Da qyar zarah ta iya kamawa,da hakan jamil ya tafi da ita sannu a hankali har gurin matattakala ta tattaka ta fito,jikinta se wani irin qyarma yake ba sauqi ko tsayuwa bata iya yi se zubewa tayi kan guiwoyin ta,kanta qasa ta kame hannuwan ta sosai a qirjinta tana fmn rawar d'ari.
Cike da tausayi jamil ya cire suit jacket d'isshi ya rufa mata yana kallon ta idanuwan sa tap da qwallah yace"tashi muje kafin sanyin nn ya miki illah ki samu ki shiga ruwan zafi kinji.
Gyad'a masa kai zara tayi tare da share hawayen da suka zubo mata snn ta tashi.
Koda suka zo bakin qofar shiga falon se ga Saifuddeen ze fito wanda still yana rungume da kitty a jikinsa riqe da makullin motar sa zai kai ta veterinary hospital.
Kallon sa jamil keyi cikin qunan rai yace"mahaukaci kawai marar imani akan kyanwar banza zaka nemi illata rayuwar d'an adam da bata da laifi ko d'aya.....kaga dakata da Allah! da akwai marar imani mahaukaciya banza irin wnn!
Saifuddeen ya fad'a tare da nuna zarah snn yace"kalli wancan plate d'in kaga shi zai tabbatar maka cewa da sanin ta komai ya faru dmn kitty baza ta ta6a d'auko plate d'in abinci da kanta ta fito dashi ba,itace munafukar da ta wurgo ta tare da plate d'in abincin ta rufe qofa ta barta ta kwana a waje tasa duk ruwan da akayi a daren jiya suka qare a kanta,very stupid! wlh duk wani abu ya sami kitty ki kuka da kanki!
Daga haka ya wuce ya var su tsaye a gurin.
Jamil ya kalli zarah ita ma ta kalle shi idanuwan ta tap da qwallah ba tare da tace masa komai ba ta shiga daga ciki.

Sha biyun rana tana kwance kudundune cikin blanket sbd zazza6in da ya saukar mata tana ji se knocking ake ta mata a qofar d'akin ta ta samu da qyar ta tashi taje ta bud'e qofa.
Wata ta gani da baza ta wuce 22yrs ba tsaye a bakin qofar,da fara'ar ta tace"sannu ni qanwar yaya jamil ce ga wnn magunguna ne yace na kawo maki kowanne da akwai yanda zaki sha shi a rubuce"
Zarah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login