Showing 96001 words to 99000 words out of 145898 words
takardar sakinta mune kake rainawa hankali,ransa ya qara 6aci ya girgiza kai yace"wlh ka bani mamaki wae ace rnr da Abban naka ya rasu har ka iya rubutawa zarah saki sbd kai a gurin ka burin ka ya cika mai takura makan ya tafi yanzu zakayi rayuwa yanda kake so ko,to kaje kayi tayi indai duniya ce zaka gani.....kul ba bakin ka ba wlh kar ka sake kace zaka yiwa d'ana baki.
Mom d'in saif ta fad'a cike da masifa.
Yayinda saif a rikice cikin kuka yace"wlh Abba ba haka bane kafin nasan da rasuwar Abba ne na rubuta wnn takadar wanda 6acin rai ne kawai yasa na rubuta sbd sa6anin da muka samu da zarah amma bada niyya ba.
Abban kd dake kallon sa cikin girgiza kai yace"sam ni yanzu ba abunda zaka fad'a na yarda da kai,baqin hali ne ka riga ka gado shi a gun uwar ka gata nn,sai ka bita ku tafi can ka d'aura inda ka tsaya tunda haka kake ganin zai fisshe ka.
Daga haka Abban kd ya fita daga fallon duk ransa a 6ace.
Yana jin Mom d'in saif se masifa take tayi dashi.
Saif kuwa ya tafi gun Hjy cikin kuka yana fad'in"Hjy wlh ba haka bane dan Allah ku fahimce ni"
Hjy da duk haushin sa take ji tace"Allah dai ya shirye ka ni kaga tafiya ta bazan tsaya sauraren shashashan yaro irin ka ba marar tarbiya da baya son bin umarnin iyayen shi se qarya da kasa a gaba kana gaya mana dan kar muga laifin ka a dole ka maida mu shashashai to kaine shashashan in gaya maka.
Nan ta tashi ta fita daga falon se masifa take tayi dashi,ya bita da kallo d'auke da idanun sa da duk sukayi jajur suna fidda qwallah,hakan ya koma gun umman kd bata ko tsaya ta saurare shi ba ta wuce,haka ma umma wacce a tunanin sa zata tsaya ta saurare shi,amma hkn ta tafi itama ta barshi,gabad'aya ma falon kowa ya watse se mom d'in sa da jamil da duk tausayin sa yake ji,mom d'in sa kam farin ciki take sosai dan ganin take hakan zai sa dolen shi ya haqura ya bita,dan burin ta knn in ta tafi dashi ya zama nata ita kad'ai bata son ya sake kula su umma dama duk wani dangin Abba,hakan yasa a ranta ta tanadar mishi gatar da zata bashi ba er qarama ba wacce zata sa ya manta su gabad'aya,se abunda ta d'aura shi akai.
Nan ta qarasa gurin shi zuciyar ta na mata zafin kukan da yake zata rarrashe shi ya tashi da sauri ya fita se part d'in sa ya rufe kansa a d'aki suka bishi se faman knocking suke mishi da ita har jamil suna bashi magana amma fir yaqi bud'e qofar.
6angaren umma kuwa qarfin hali ne kawai tayi ta tafi ta barshi amma a ranta duk taji ba dad'i,wacce tana barin gurin kai tsaye d'akin su Nusaiba ta nufa taje ta sami zarah kwance kan bed tana kuka,Nadiya da dije sunyi zugum se kallon ta kawai suke sun kasa rarrashin ta Nusaiba kuwa na zaune a kusa da zarah d'in ta had'e kanta da guiwa se kuka take itama,wacce bata ta6a sanin ainihin alaqar su da zarah ba se yau,da can duk a tunanin ta ko en uwan juna ne kawai ashe uwar su d'aya bata sani ba dmn koda kuskure umma bata ta6a gaya musu ba.
Shigowar umma ne yasa Nadiya da dije suka fita daga d'akin,haka ma Nusaiba a hankli ta tashi ta fita daga d'akin ganin magana umma ke son yi da zarah.
Bayan sun fita ne Umma ta zauna a hankli kan bed tare da janyo zarah jikin ta cikin muryar rarrashi tace"kukan ya isa haka zarah yi shiru kinji gaya min meyasa tun lokacin da saif ya sake ki baki gayawa kowa ba se yau?
A hankli zarah ta d'ago daga jikin umma kanta qasa hawaye na kan fuskar ta bata share ba se en yatsun ta da ta kama tana wasa dasu kmr me jin nauyin umma cikin muryar ta da tasha kuka tace"tsinta nayi a d'akina ba bani yayi ba"
Umma dake kallon ta tace"tsinta kikayi amma shine kika san rnr da ya rubuta miki sakin"
Eh a rnr ne da muka....se tayi shiru ta kasa qarasa zancen,umma tace"rnr ne da kukayi me?
Muryar ta can qasa kmr baza ta iya fad'a ba tace"sa6ani muka samu a rnr shine nace se ya sake ni,shi kuma yace bazai sake ni ba haushin hakan yasa nace ni kuma idan bai saken ba se na kira Baffa na gaya mai abunda ya min,shine haushin ganin dagaske zan kira Baffa ya kar6i wayata ya jefar duk ta faffashe,a lokacin ne inaga ya rubuta min saki ban sani ba dmn hankalina na gun wayata da ya farfasa min ina kuka,ina cikin kukan ne kawai naga yazo yana bani haquri har yana ce min zai saya min wata waya,hkn yasa na haqura har ma na shirya zamu zo gida sbd Abban kd da ya kirashi yace muzo yana son ganin mu,shine bayan na shirya zan fita daga d'aki naji
na taki abu koda na duba se naga dunqulalliyar takarda ce bansan ta mece ce ba hakan yasa na d'auka na ware na duba,inda ko kad'an banyi mamakin abunda na gani a rubuce ba se ma qoqarin yaga takardar nayi,dmn yanayin yanda na ganta a dunqule kad'ai ya fahimtar dani fasawa yayi ya jefar,amma se ban samu na yaga takardar ba naji ya soma kirana kan na fito muje,shine ina sauri na koma dunqule takardar na saka a jakata.
A lokacin ne koda muka zo gida se muka tarar da ashe baffa ne ya rasu.
Ta share qwallar da suka zubo mata snn ta ci gaba da cewa"Sam abunda Abban kd yayi tunani ba haka bane,ba bayan rasuwar Baffa ne ya sake ni ba kafin haka ne kuma se ya fasa bai bani ba,ni kuma dana ganta banyi niyyar snr da kowa ba,haka ma sakata da nayi a cikin jakata ba ina nufin in nuna ma wani ba,sai dan idan na samu lokaci in yaga,amma se abubuwan da suka faru yau yasa na kasa jurewa naga gwanda kawai in fitar da takardar dmn ba kad'an ba naji zafin yanda mahaifiyar shi ke zagin ku har tana gaya muku maganganun marassa dad'in ji.
Ta qarashe mgnr ne sosai cikin muryar kuka.
Umma dake sauraren ta shiru tayi ta kasa cewa komai duk tausayin saif take ji a ranta.
Umman kd kuwa wacce tun d'azun ta shigo d'akin tana tsaye a bakin qofa taji komai,hakan yasa jiki sa6ule ta qarasa gurin su ta zauna tana kallon zarah tace"kunyi kuskure dake har shi Zarah sam bai kamata ace da iliminki kin nemi saki a gun mijinki ba a kan wae dan kun samu sa6ani,shi kuma bai kamata ace ya biye maki ba har yabar zuciya ta d'ibe shi yakai ga rubuta miki saki.
Umma tace"haka ne kam zarah yarinya ce bai kamata ace ya biye mata ba,ita kuma bansan jahilci me ne ya d'ibe ta ba kmr wacce bata je islamiyya ba,wayiwa kawai!
Umma ta fad'a cikin d'aure fuska tana kallon zarah,wacce da saurin ta ta sadda idanunta qasa qwallah cike a idanun nata har suka shiga silalowa a hankli kan kumatun ta.
Umma bata damu ba se kallon umman kd tayi tace"yanzu abunda ya kamata yaya kiyiwa Alhjn kd bayani a wanke saif daga gare shi har ma da Hjy da duk suka fita cike da jin haushin sa,amma maganar gaskiya saki kam ya zaunu dmn hakan shine mafi a'ala bazan iya jure cin mutuncin mahaifiyar sa ba.
umman kd tace"gaskiya kam cin mutunci nata yayiwa harda tozarci,amma ina tausayawa saif sam bazai ji dad'in hakan da zamu yi mishi ba musamman ma yanda har ya kasance zarah na d'auke da cikin sa.
Umma dake kallon ta tace"hm yaya knn zarah fa bata da komai"
D'auke da mamaki umman kd tace"kmr ya cikin ya zube ne?dmn da jimawa fa Alhj ya gaya min yace Abban saif ya gaya masa har yana murna ze fara ganin en jikokin sa.
"Allah sarki"
Umma ta fad'a wacce take taji qwalla sun ciko mata a ido.
Tace"wani zazza6in mura ne fa da zarah ta ta6a yi shine ya d'auka ko ciki ne da ita har nima na d'auka ko haka ne,se gashi saif d'in da kanshi yake gaya min shi ba abunda ma ya ta6a shiga tsakanin sa da zarah,ko da akwai?
Ta tambayi zarah tana mai kallonta wacce kanta qasa ba tare da ta iya kallon umma ba ta girgiza kanta alamar a'a.
A sanyaye Umma tace da umman kd"kin gani ko,shiyasa kawai naga rabuwar auren shi yafi tunda dukkan su ba son junan su suke yi ba.
Umman kd da tayi shiru can ta numfasa snn tace"to Allah sauwaqe yasa hakan shi yafi alkhairi.
Umma tace"Amin tare da share en guntayen hawayen da suka fito gefen idon ta.
Zarah kuwa tana jin hukuncin da umma ta yanke bata san meyasa ba se jin tayi ta saki kuka a hankli.
Umman kd ta tafi da ita jikinta se rarrashin ta take tana fad'in"kar ki damu daina kuka komai ya wuce kinji,a hankli zara ta gyad'a mata kai.
Umma dai sae kallon su kawai take.
Su jamil kuwa suna can se rarrashin saif suke ya bud'e qofa amma still yaqi bud'ewa suna jinsa se kuka kawai da yake,duk jamil yabi ya damu ga haushin mom d'in saif da yake ji sosai a ranshi har ganin yake kmr a dalilin ta ne saif yaqi bud'e qofa shiyasa kawai yayi tafiyar sa ya barta gurin se ci gaba take da doka qofa tana rarrashin saif cikin lalla6awa dan so take ko yaya ta shawo kansa har ya haqura ya yarda ya bita shiyasa ma sam bata ji ta gaji da rarrashin nasa ba,amma kiran gaggawan da aka mata a waya ne yasa dolen ta ta bar gidan ba dan taso ba.
Jamil kuwa da yaje gida kasa zama yayi ya koma dawowa amma se ya tarar saif d'in baya nn ya fita,hankalin sa yaji ya tashi kaddai mom d'in tashi ta samu nasarar shawo kanshi ya bita sun tafi.
Bai ko iya shiga cikin gida ba yaje gun gateman ya tambaye shi ko wnn mtr da tazo tare suka fita da saif?
Gateman yace masa"a'a ta riga shi fita dmn kafin ma ta fita sai da ta min alheri mai tsoka ta kuma bani numbar wayar ta tace idan naga ya fito na kira ta na snr da ita.
Jamil dake sauraren shi yace"to ae saif d'in ya fita ban ganshi a d'akin sa ba kuma motar shi bata nn kana nufin baka ga fitar sa bane ko me?
Aa naga fitar sa yanzu yanzu nn nima na bud'e masa gate,kuma har na kira wnn Hjyr na gaya mata,ina gama waya da ita ne ma ka shigo.
Tsaki kawai jamil yayi ya tafi da sauri yaja motar sa ya bar gidan,yaje duk inda yake tsammanin zai samu saif bai ganshi ba,duk ya rasa me zaiyi ya sake komawa gidan su saif wae ko zai ganshi ya koma,amma bai ganshi ba sai mom d'in saif d'in ya gani wacce tana mishi magana ko kula ta bai yi ba ya shiga motar sa ya wuce,bata ji haushin sa ba sema shiga motar ta tayi itama tasa dirvern ta ya bishi baya,yayinda shi kuma jamil bai zarce koina ba se maqabarta a mamakin sa kuwa se ya samu saif a can gurfane a gaban kabarin Abba yana kuka bana wasa ba duk idanun sa sun kumbura sunyi wani irin jajur da lokaci d'aya jamil ya samu kansa da jin kuka shima,ya tafi sannu a hankali ya qarasa inda saif d'in yake,mom d'in saif kuwa da ke biye dashi kasa qarasawa tayi gurin su se juyawa tayi ta fita daga maqabartar jikin ta duk a sa6ule wacce kallo d'aya zakayi mata ka fahimci cewa tunanin ne fal a ranta da kuma nadamar da ta bayyana qarara a fuskarta.
[4/2, 6:27 PM] Billygiro😊: _Monday 02/04/2018_
*«»«»«»SAIFUDDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«»49/50*
Koda jamil ya qarasa gun saif se jin yayi kuka ya qwace mishi hakan yaje cikin kuka ya kama saif ya rungume shi se rarrashin sa yake yana bashi magana amma saif bai iya daina kukan ba har sai da jamil ya jashi suka fita daga maqabartar.
*Ci gaban labari*
Mom d'in saif na tsaye agun inda suka faka motocin su,tana kallo jamil ya wuce da saif suka je suka shiga mota,taji duk ranta ba dad'i ganin irin kukan da saif keyi gashi tasan bata da damar da zata je ta rarrashe shi,hakan yasa kawai taje zata shiga mota drivern ta yayi saurin bud'e mata ganbu ta shiga tare da d'aga wayar ta dake ta faman ruri,wacce da alama patient take da a gida unconscious shiyasa duk hankalin ta ya rabu gida biyu,dan tana d'aga waya se cewa tayi ya akayi ne ya sake farfad'owa ne inzo?
Se tayi shiru tana sauraren amsar da ake bata da ba'a jin mene ne kawai dai yanayin fuskar ta ya nuna ba hakan taso ji ba,can tace"ok naji amma ka tabbatar kayi gaggawar snr dani idan ya sake farfad'owa,bcos i dnt wnt him die ba tare da yasan wanda ya aikata hakan a gare shi ba,nn suna gama waya ta tsinke kiran.
Yayinda jamil shi kuma da shigar su mota ya ciro wayar sa yana tunanin wanda zai kira yazo ya d'auki tashi motar sbd motar saif suka shiga tashi motar na can fake,gashi Alu driver tunda sukayi accident da Abba,unconscious yana asibiti bai ko san inda yake ba,hakan yasa ya kira drivern gidan su,suna gurin har sai da yazo snn ya bashi key suka wuce gabad'ayan su se gidan su saif,har mom d'in shi dake biye dasu a baya.
Saif da bai ko san da mom d'in tashi tana tare dasu ba sbd yanayin da yake ciki,yana fitowa mota se jin yayi kansa ya wani irin sara masa da kuma jirin da ya d'ibe shi lokaci d'aya yayi taga taga zai fad'i jamil yayi saurin kama shi,haka ma mom d'in sa tazo da sauri zata kama shi,shaye da toka jamil yayi saurin cewa a'a ta barshi zai iya,hakan ta tsaya bata ce masa komai ba se kallon sa kawai tayi dan ta fahimci haushin ta yake ji,amma be hana tabi bayan shi ba har ya tafi da saif d'akin shi ya kwantar dashi snn ya masa allura da lokaci d'aya ya hau yin bacci.
Yana gama masa allurar ne ya fita daga d'akin,nan mom d'in saif taje ta zauna kan bed kusa da saif tare da d'aura hannunta a hankli kan goshin sa tana shafa goshin nasa har zuwa kanshi cikin sauke ajiyar zuciya sbd wani sanyi da taji a ranta na qaunar d'an nata da ya ratsa ta wacce yau ce rnr farko da ta ta6a shafa kansa tun yana jinjiri bai ta6a samun wnn damar daga gare ta ba se yau.
Jamil kuwa da fitar sa cikin gida ya tafi ya snr da umma halin da saif yake ciki dan yasan idan kowa zai iya yin fushi da saif ita kam baza ta iya ba ko d'azun ma ya fahimci qarfin hali ne kawai tayi,ae kuwa se gashi sun dawo tare shida umma d'in,mom d'in saif na ganin su bata ko bar umma ta qarasa cikin d'akin ba ta dakatar da ita tana fad'in"me kuma ya kawo ki a gurin d'ana bayan wulaqanta shi da kukayi kuka saka shi a cikin wnn halin,bai ishe ku ba shine kinzo zaki qarasa shi to kinyi kad'an in ke mayya ce sei dai kici kanki wlh.
Rai 6ace Jamil ya kalle ta yace"haba dan Allah wae ke kam masifar ki bata qarewa ne duba shi fa tazo yi.
Kafin mom d'in saif tace komai umma tace"no jamil ba halinka bane wnn ka barta kawai indai saif ne gata nn gashi Allah ya bashi lfy.
Daga haka umma ta juya ta fita jamil yabi bayan ta suna jin mom d'in saif se masifa take tana fad'in "Allah raka taki gona dukkan ku bana buqatar in sake ganin ku a kusa da d'ana ni kad'ai zan iya kula da abuna matsiyata kawai masu neman rabani da farin ciki na to ta Allah ba taku ba d'ana se ya dawo gare ni da yardar Allah kuwa.
Ba wanda ya kula ta a cikin su dan tuni sun ma daina jiyo me take cewa kasancewar har sun kawo qofar falo,suka tsaya jamil ya kalli umma yace"umma yanzu kina ganin ba matsala bane idan muka barta da saif ni ina tsoro dmn ganin nake matar nn kmr ba tsakani da Allah ne yasa ta dawo gare shi ba da akwai dai.
Umma ta numfasa tace"bana tunanin haka kuma indai saif ne da kmr wuya ya yarda ya bita shiyasa kaga ban damu ba kawai ina tausayawa halin da yake ciki ne dmn d'azu zarah ta mana bayanin komai ashe duk bayanin da yake da gaske ne,asali ita ma ta nemi sakin da kanta sbd kawai sun sami sa6ani shi kuma zuciya da 6acin rai yasa ya rubuta mata sakin se kuma nn take ya fasa be bata ba ya jefar,ita kuma shine ta tsinci takadar byn har sun haqura sun sasanta kansu,wacce ta ajiye takadar ne a niyyar zata yaga amma abubuwan da suka faru yau taga gwanda kawai ta fidda sbd ta kasa jure cin mutuncin da taji ana mana,wacce har yanzu tana d'aki still abun bai daina damun ta a ranta ba se kuka take shine muka yanke shawarar anjima da yamma idan su yaya zasu koma kd se suje tare da zarah d'in har komai ya lafa snn ko zata dawo.
Shiru Jamil yayi can yace"amma umma karatun ta fa baza ya shiririce ba?
Umma tace"to haka ne kam amma shi Alhjn kd cewa ma yayi idan taje baza ta dawo ba ze nema mata wata school a can taci gaba dayin karatun ta