Showing 99001 words to 102000 words out of 145898 words
har Allah ya kawo mata wani mijin tayi aure.
Ras jamil yaji gaban sa ya fad'i ya kalli umma da sauri yace"tayi aure umma shi saifudeen d'in fa?
Umma ta numfasa tace"a gaskiya jamil zarah baza ta komawa saifudeen ba sbd dukkan su ba son junan su suke ba,dan ko Alhjn kd da ya shigo d'azu d'azun nn bada jimawa ba,muka mai bayanin duk da zarah ta mana se duk yaji tausayin saif amma kuma yace rabuwar auren dai shi yafi sbd sake maida auren kmr wani qalubale ne,na d'aya ba son junan su suke ba na biyu kuma shine babban qalubale dan mahaifiyar saif d'in sam baza ta ta6a barinsu su zauna ba tunda har bindiga fa ta nunawa zarah tana ikirarin zata kashe ta idan ta koma ganin ta a kusa da saif wacce ba barazana kad'ai bace zata iya aikata hakan,dmn ba imani ne da ita ba tun daga kan yanda taqi qaunar d'an cikin ta komai zata iyayi akan d'an wani bare mu da ta d'auka en adawar ta ba abun da baza ta iya aikata mana ba,sai dai kawai mu roqi Allah ya ratse mu daga sharrin ta,shi kuma saifudeen Allah ya sasanta tsakanin su shida mahaifiyar tashi indai har da gaske take ba wata manufa ce a tare da ita ba.
"Amin"
Jamil ya fad'a wanda daga haka bai sake cewa umma komai ba,se sallama da ya mata snn yaje yaja motar sa ya bar gidan cike da tunani fal a ransa.
Saif kuwa koda ya farfad'o a mamakin sa se ganin kansa yayi kan wani makeken bed irin tsadaddin gadajen nn an qawata shi awa wani gadon saurata,d'akin na fidda wani irin lafiyayyen sanyi snn kuma an sauya mishi kayan jikin sa da alama wanka aka mai ba haka kawai aka sauya mishi kayan ba dan se wani irin daddad'an qamshin turare ke tashi jikin sa,yana kallon kansa ta mirror har gashin kansa ma duk an taje ya kwanta sosai,snn can ya hango wata qatuwar dardamu shimfid'e a tsakiyar d'akin an jera masa abinci kala kala har da su fruit duk gasu nn ba wanda babu a gurin kmr wani d'an saurata.
A hankli ya sauka daga kan gadon ya tafi gun wani makeken hoton su da ya gani manne a jikin bangon d'akin shida mom d'in tashi da aka had'a ya rungume ta suna dariya tamkar tare suka yishi,wanda ko ba'a fad'a ba ya fahimci inda ta samu photon a instagram ne,kuma yayi hoton ne shida umma a lokacin da suka ta6a kai mishi ziyara England shine tasa aka canza shi izuwa kanta,ae kuwa lokaci d'aya ransa yayi mugun 6aci ya cire photon ya jefar take photon ya rabu gida biyu sbd yanda ya jefar da shi a fusace snn ya nufi gun dardumar da aka jera masa abinci ya hau yin ball da duk wani abun da ke jere akai.
Nan se ga mom d'in tashi ta shigo d'akin da sauri sanye cikin kayan bacci dan lokacin qarfe tara tayi na dare.
Taje zata kama shi cike da son ta rarrashe shi yayi saurin ja baya tare da d'aga mata hannu snn cikin wata irin kakkausar murya me cike da 6acin rai yace"ki gaya min ina ne nn kika kawo ni!
Mom d'in tashi da duk ta marairaice fuska tace"plz calm down my son we are in d town a cikin kano muke ba wani guri na kawo ba,nn gida na ne da na siya kafin na samu na rarrashe ka ka yarda ka bini dmn ko kad'an bana son takura ka my son,but yi haquri zo zauna na kawo ma wani abincin kaci kaji"
Ta qarashe mgnr ne had'e da kama hannun sa ya qwace hannu da sauri cikin dafe kansa yace"dan Allah ki rabu dani bana sonki ke ba mahaifiya ta bace umma ce kad'ai uwata da haife ni.
Wani irin ciwo mom d'in sa taji a ranta ta kama hannun sa duka biyu qwallah tap a idon ta tana kallon sa tace"Haba my Son for God sake ka yafe min abunda na ma,nasan a baya na tafka babban kuskure amma yanzu ba kad'an ba nayi nadama wlh bani da burin da ya wuce in dawo da qaunar da ban nuna ma a baya ba,na kasance uwa ta gari a gare ka da zakayi alfahari dani,saif dake kallon ta ya qwace hannayen sa cikin girgiza kansa yace"Never wlh har abadah kin makara wnn qaunar ta riga ta wuce baza ta6a dawowa ba,dmn babu wata qauna mafi soyuwa da tafi ace d'a ya same ta tun yana jinjiri agun uwar sa,ni kuma gashi tun ina cikin ciki na rasa wnn qaunar a gurin ki ta yaya to kike ganin zaki iya dawo da ita how?
Yana mgnr cikin 6acin rai kmr zai yi kuka dan idanuwan sa cike suke tap da qwallah.
Yayinda Mom d'in sa tuni nata hawayen suka sauko kan kumatun ta ta share hawayen snn ta kama hannun sa ta tafi dashi kan bed suka zauna tana kallon sa da kulawa snn muryar ta a sanyaye tace"my son haqiqa na tabbata wnn abun duk ya faru ne a dalilin kuskuren da muka aikata nida mahaifin ka na bijirewa iyayen mu da mukayi shine Allah ya nuna mana.
Nida shi mun kasance muna matuqar qaunar junan mu sosai da sosai amma se ya kasance dukkan mu da za6in da iyayen mu suka mana,shi Abban ka umma nn taka itace mahaifin sa yaso tun farko ya aura amma fafur Abbanka yace bazai aure ta ba sai ni,nima kuma da akwai wani d'an uwan mu da ummana taso na aura wanda tun ina yarinya yake sona nima na taso ina son shi sbd yana kula dani sosai yana min duk wani abunda nake so,kowa kaf dangin mu yasan da soyayyar mu dmn tun ina yarinya aka bashi ni jira kawai yake in na girma muyi aure amma tunda na girma muka had'u da Abbanka se naji duk duniya ba wanda nake so kmr shi,a dalilin qaunar shi ne na bijirewa iyayena fafur nace sai shi bazan auri wancan ba,umma na tayi baqin ciki sosai haka har yasa ta kwanta ciwo sbd dama can tanada ciwon zuciya,amma hakan be damen ba mukayi auren mu nida Abbanka,auren da bamu ta6a jin dad'in sa ba knn kullum cikin masifa babu zaman lafiya tamkar ba wa enda sukayi auren so ba haka har muka rabu,yayinda rabuwar bata min zafi ba se bayan na koma gida,na tarar mahaifiyata ta rasu sbd tun lokacinda ta kwanta ciwo kullum se gaba gaba ciwon yake bata tashi ba har Allah ya kar6i ranta,shiyasa duk dangin mu ba ruwan kowa dani suka fita haraka ta kwata kwata har Abba na kuwa,wanda hatsarin mota ne yayi ajalin sa,a lokacin ne rayuwa ta qara min zafi,amma Abbanka tuni ya shirya da mahaifin sa har ma ya auri ummar ka suna rayuwar su me dad'i ya manta ni gabad'aya,wanda na tabbatar bazai rasa jin labarin rasuwar mahaifyata ba har ma da ta mahaifina amma ko a text be min gaisuwa ba hakan ya qara min ciwo tun daga lokacin se ban sake bincikar rayuwar sa ba dan dama ina bincikawa ne,dmn ni ba er nn kano bace,asalin mu shuwa Arab ne a Maiduguri can muke da zama can ne asalin mu.
Ina cikin wnn halin ne Allah ya taimake ni nayi auri se na bar zama qasar nn gabad'aya wanda ya aure ni ya tafi dani Thailand yana aikin sa a can ni kuma ya saka ni a school har na zamo cikakkiyar likita na fara aiki nima a can,inda ba wani ne ya aure ni ba face wnn d'in dai na farko da naqi,still shi bai yi aure ba har lokacin kuma abun mamaki abubuwan da suka faru a dalili na baisa ya tsane ni ba hkn ya aure ni muna zaman mu lafiya lau ba wata matsala da kuma ta6a fuskanta a tsakanin mu.
Amma duk da haka bana jin dad'in rayuwa yanda ya kamata a kullum naga en yara se kawai naji wani qaunar su a raina,se in ta tuna ka har inaji dama ban barka ba kmr inje inzo da kai amma sanin cewa ko nazo mahaifnka bazai ta6a yarda ya bani kai ba yasa kawai na haqura,a tunani na ko zan sami haifuwar wasu yaran da zasu maye min gurbin ka amma shiru har yau ko 6atan wata ban ta6a yi ba,gashi a kullum da qaunar ka nake kwana nake tashi ina tunanin ta yanda za'ayi ka dawo gare ni,kwatsam se naji labarin rasuwar mahaifin ka,a gun wanda nake sa yana bincika min rayuwar ka dama abunda kake ciki,wanda har auren da aka ma baka so duk agun sa naji hakan yasa na bayyana agare ka dmn na qwatar ma haqqin ka na kuma tafi dakai kayi ingatacciyar rayuwa da baka samu kayi ta a baya ba.
Nan ta kama kumatun sa tace"plz my son ka yarda ka bini kaji,idan kuma kafi son mu zauna a nn i will zan maka duk abunda kake so,amma wad'an can mutane nn ne bana son ka sake kulawa dmn ba masu qaunar ka bane so kawai suke su raba tsakanin mu,wnn matsiyaciyar kuma dan ka sake ta ka daina damuwa,da kaina zan tafi dakai England na nemo maka auren Sophie kaji"
Saif dake kallon ta fuskar sa a d'aure ya janye hannayen ta daga kan kumatun sa yace"bana buqata"
Snn ya miqe ya fita daga d'akin yana bin hanyar duk da ya gani,ta bishi se rarrashin sa take amma be saurare ta ba har ya fita daga gidan.
Ba yanda ta iya se komawa tayi daga ciki ta tura mishi drivern ta acewar yaje ya sauke shi a gida.
Saif da har yayi nisa da tafiya,yana kallon yanayin anguwar tsit ba alamar zai sami abun hawa nn kusa gashi ko waya babu a tare dashi bare ya kira jamil yazo ya tafi dashi da baisan ya akayi jamil d'in ya bar aka zo dashi nn ba dan se ma yaji haushin jamil d'in sosai.
Ganin mota tafe yasa ya d'an had'iye 6acin ransa ya tsaya da niyyar zeyi wa motar hannu ta tsaya kawai yaga an faka motar a gaban shi,drivern ya fito da sauri har yana ajiye masa takalmi dan ko takalmi babu a qafar sa haka nn ya fito,wanda ganin haka ya fahimtar dashi aikin mom d'in sa ne kawai yasa takalmin ya kuma shiga motar aka sauke shi se gida.
Kae tsaye ya wuce 6angaren su umma tunani fal a ransa bai san ta yaya zai fuskanci umma ba,hakan yasa ya kasa zuwa d'akin ta ya tafi d'akin su nusaiba dan sosai yake son yaga zarah,amma koda yayi knocking Nusaiba kawai ya gani da ita ce ta bud'e masa qofar,wacce tana ganin shine kawai ta fad'a jikin sa cikin kuka tana fad'in"yaya ina taje dakai tun d'azun hankalin mu duk ya tashi mun d'auka ko ta tafi da kai knn"
Ta qarashe mgnr ne tare da d'ago fuskar ta tana kallon shi,saif yasa hannun sa ya share mata hawaye snn a natse yace"gidan ta kawai taje dani dake nn garin amma kar ki damu baza ta sake tafiya dani ba ina nn tare da ku ina zarah ina so zan ganta?
A sanyaye tace"su Abba sun tafi da ita kd kuma wae shikenan a can zata ci gaba da zama gabad'aya har ma karatun ta duk a can zata ci gaba dayi.
Komai Saifudeen kasa ce mata yayi se janye ta a hankli yayi daga jikin sa qwalla cike a idon sa ya juya ya bar gurin a ransa yana tunanin dolen sa yaje kd yanzun,ko wane irin hukunci Abba zai mai ya mai amma banda rabashi da zarah.
_Tuesday 03/04/2018_
*«»«»«»SAIFUDDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«»51*
Yana sauka downstairs yaji muryar umma ta kirashi,tako d'aya bai qara ba ya tsaya had'e da juyawa ya kalle ta sau d'aya ya sadda kansa qasa baya iya kallon ta dan duk kunyar ta yake ji shi kam,umma kuwa da saukowar ta kama hannun sa tayi taje dashi kan doguwar kujera suka zauna,tana kallon sa da kulawa tace"hankalin mu duk ya tashi saif ina taje da kaine koda Nusaiba taje zata duba ka ta samu 6angaren naka ba kowa haka jamil ma ya dawo be same ka ba,gabad'aya duk hankalin sa ya tashi da yaji cewa ta tafi dakai yanzun nn ma na gama waya dashi yana tambayar ko anji labarin inda taje dakai nace masa har yanzu shiru bamu samu wani labari ba,gashi wayar ka idan an kira tana ringing amma ba'a d'agawa da qarshe ma aka kashe wayar.
Saif da still baya iya kallon umma kansa qasa yace"may be phone d'in tana d'aki ta fad'a wani gurin i dnt know,kawai dai koda na farfad'o se ganin kaina nayi ta kaini gidan ta dake nn garin.
Umma dake kallon sa tace"dawowa kayi ko ita ce ta maida ka?
Yace"dowowa nayi umma kuma se na samu banga zarah ba"
Ya qarashe mgnr ne had'e da kallon ta cikin yanayin nuna rashin jin dad'in faruwar hakan"
Umma ta numfasa tace"to saif zarah d'in ce se kuka take tayi sbd abunda ya faru shine Alhjn kd da zasu tafi suka tafi da ita.
Yace"amma umma Nusaiba ce min tayi wae zarah ta koma can gabad'aya da zama har za'a nema mata wata school a can.
Eh haka Alhjn yace.
Idanun sa cike da qwalla yace"Why umma meyasa kuke son ku raba auren mu wlh bada niyya nayi wnn sakin ba 6acin rai ne kuma nn take na fasa ban bata ba"
Umma dake kallon sa cikin yanayin tausayi tace"ae zarah ta mana bayanin duk yanda abun ya faru kusan duk laifin ta ne ma kuskuren ka d'aya ne biye matan da kayi amma yanzu ae komai ya wuce a idon kowa baka da wani laifi har Alhjn kd da duk yafi d'aukar abun da zafi haka ma Hjy da kaina ma na mata bayani,damuwar mu d'aya ita ce mahaifiyar nn taka dake son zata tafi dakai yanayin ta ya nuna gabad'aya take son ta rabamu dakai kwata kwata,ni kuma zan so ace ko ziyara ce ka riqa d'an kawo mana dmn bana jin zan iya jure tafiyar ka gabad'aya.
Saif da ko kad'an baya son ana maganar mom d'in shi ya share hawayen da suka zubo mishi snn yace"plz umma ki daina min mgnr wnn matar ni ba inda zanje ina nn tare daku ae ba qaramin yaro bane ni da za'a ce wae anzo za'a tafi dani ta fad'a ne kawai dmn tasan hakan bazai ta6a faruwa ba ma.
Umma tayi shiru tana kallon shi can ta numfasa tace"Amma saif....yace"plz umma ni ki daina min maganar ta maganar zarah nake son ji.
Nan kawai ya zame qasa gan guiwoyin sa ya hard'e hannayen sa fuskar sa cike da nadama yana kallonta yace"plz forgive me umma nasan nayi kuskure a baya bansan zarah erki bace wlh shiyasa duk nayi wa en nn abubuwan amma dan Allah kiyi haquri ki yafe min rashin sani ne.
Ya qarashe mgnr hawaye na sauka kan kumatun shi yayi saurin share hawayen,umma dake kallon sa ta kama kumatun sa tana mai qara share masa hawayen snn a natse tace"ko kad'an ban riqe ka da wnn ba dmn nasan rashin sani ne dan haka kar ka damu kaji komai ya wuce.
Yanayin fuskar sa kmr qaramin yaro yace"nagode umma amma dan Allah kar ace za'a raba aurena da zarah bana so"
Da kulawa umma tace"saif meyasa duk kabi ka damu in dan nice dama nasan ba son junan ku kuke yi ba bazan d'auke shi komai ba bare kuma zarahn ce ta nemi sakin da kanta ba laifin ka bane"
Cikin yanayin damuwa saif yace"plz umma ba haka ba ni ki daina fad'ar haka dmn babu wata macen da nake jin zan iya rayuwar aure da ita face zarah,dan Allah umma ki taimaka min wlh nida ita munyin alqawarin zamu samarwa Abba farin cikin sa,bai kamata ace dan ya mutu muyi fatali da burin sa ba.
Nan take qwalla suka ciko a idon umma tace"saifudeen haqiqa ina so inga cewa kun cika masa burin sa,amma shi kansan yasan ya bar baya da qura,wanda da alama yaji a jikin sa cewa mutuwa zaiyi shiyasa da zaiyi tafiya ya maka duk wad'anan maganun da za'a iya kiran su da wasiyya,amma se mahaifiyar ka tazo ta lalata komai dmn kasan maida auren ku kmr wani qalubale ne sam mahaifiyar ka baza ta ta6a barin ku ku zauna lafiya ba komai zai iya faruwa idan aka maida auren,mafi a'ala shine idan zarah ta sami wani mijin tayi aure haka kaima idan ka sami wacce kake so kayi aure.
Da sauri cikin girgiza kai yace"no umma nifa zarah she is still my wife na gaya muku wancan sakin kuskure ne kuma a take na fasa babu shi dan haka ni wnn matar bata isa ta rabani da zarah ba,kd zan tafi yanzun nn in dawo da ita.
Aa saif kayi haquri ni bazan iya da rashin mutuncin wnn matar ba,burina kawai inga kun shirya tsakanin ku kaida mahaifiyar taka,bana son wata masifar kuma dmn zancen kace zaka
dawo da zarah kmr wata masifar ce kake son sake tadawa bayan bamu ko fita daga cikin wnn ba.
Fuskar sa kmr zeyi kuka yace"No umma sai dai idan fushi kikeyi dani ba kya son zarah ta dawo gareni amma ba hujja bace wae ace a kan wnn matar za'a raba aurena da zarah bayan kinsan Abba bayada wani burin da ya wuce ace mun kasance tare nida zarah har abadah.
Umma da har ranta masifar mom d'insa ce bata iyawa da ita tace"ko kad'an ba haka bane saifudeen bayanin da na maka dai shine"
Yace"to dan Allah umma ki fita harakar wnn matar ki barni da ita kawai ni nasan me zanyi kuma dan Allah ki barni inje inga zarah.
Umma tace"shikenan zan barka kaje kaga zarah d'in amma ba