Showing 108001 words to 111000 words out of 145898 words
ta faman jinjina kanta dan al'amarin ya girgiza ta matuqa.
Can Abban kd ya numfasa cikin jinjina kai yace"Haqiqa wannan al'amari da ya faru ba abunda zamu iya cewa sai dai muce Allah ya kyauta,shi kuma Alhj Hussain Allah ya bashi lfy ya kuma qara tsare shi damu baki d'aya,ita kuma Allah ya shirye ta.
Amin suka fad'a snn yace"Inshaa Allah idan na samu yanda nake so gobe gobe nn zan tafi da Alhj Hussain England domin jikin nashi yana buqatar kulawa sosai duk da ko nn d'in ni mai iya kula dashi ne amma dole a can d'in zai fi samun kulawa sosai da sosai.
A hankli Saifuddeen ya d'ago kansa ya kalle sa yace"zan bika Abba"
Abban kd yace"Aa kana buqatar ka qara samun lafiya kaima snn ina kabar zancen maida zarah d'akin ta ko kafi so sai an gama jinyar Abban naka?
Duk da irin yanayin da saifudeen yake ciki amma lokaci d'aya yaji wani dad'i a ranshi har ma ya samu kansa da yin murmushi snn ya sadda kansa qasa cikin sosa bayan kansa irin najin kunya d'in nn yace"duk yanda kace Abba"
Abban kd dake kallon sa yayi d'an murmushi snn ya maida duban sa gun zarah yace"baza a miki dole ba zarah kina buqatar komawa d'akin mijinki?
Da sauri saif ya kalle ta haka ma kowa dake d'akin suka kalle ta har jamil dako qyafta idon sa baya son yi a kanta yana jin wani fad'uwar gaba a ranshi duk da yasan dolen shi zai haqura da zarah amma abun ne ya kasa daina mishi,dashi kansa baisan ya zaiyi ba sosai yake son yaga cewa ya haqura ya daina jin komai a ranshi a game da ita amma zuciyar sa ce still taqi bashi wnn damar da yake jin inama kakar sa na raye da kd zai koma can da zama gabad'aya ko zuciyar sa zata haqura idan ta daina ganin zarah.
Zarah kuwa Abban kd na tambayar ta,ta sadda kanta qasa cikin yanayin jin kunya,ta kasa cewa komai se en yatsun ta da ta kama tana wasa dasu,wacce ko bata fad'a ba dole duk mai kallon ta yasan amsar abunda ke ranta.
D'an murmushi Abban kd yayi snn ya kalli su umma da suma ya fahimci a gurin su ba matsala suna buqatar ta koma d'in yace"to Alhmdlh jibi ranar juma'a se ayi qoqari a maida zarah d'akin ta.
ko kafi buqatar a maida maka ita ne yau?
Abban kd ya tambayi saifudeen,saifudeen da still kallon zarah yake ya sadda kansa qasa yace"No Abba yanda kayi d'in nn ma yayi.
Yace"to shikenan abunda nake son gaya maka dai shine ita rayuwar aure da kake gani dole sai da haquri musamman kai da kake babba duk wani abu kaine zaka riqa haquri kana fahimtar da ita zaman rayuwar auren ba wai ka riqa biye mata ba har ka wani rubuta mata saki dan tace,kan kawai kun samu sa6ani,dan haka bari kaji in gaya maka saki ba abun wasa bane da har zaka ce wae a bisa kuskure kayi,idan har ka sake barin wnn kuskuren ya faru dakai to wlh sai dai ka nemi wata matar ba dai zarah ba dmn bazaka maida mu shashashai ba kana jina!
Hajiya tace"gaya mishi dai ni nn dakaina zan d'auke zarah in auradda ita ga wanda yasan mutuncin ta ya kuma san darajar aure ka kuma sake wnn kuskuren ka gani.
Saif da kansa ke qasa muryar sa a hankali yace"inshaa Allah ma hakan bazai sake faruwa ba Hjy.
Tace"yauwa d'an albarka haka nake son ji Allah yasa ka kiyaye d'in,dan iyayen ka gasu nn dai kana gani lafiya lau suke zaune da matan su ba abunda ya ta6a had'a su amma kai sbd yaran zamani ne ku baku d'auki aure a bakin komai ba da har wae ke zarah zaki nemi saki a gun mijinki ko!
Hjy ta fad'a cikin turawa zarah idanu.
ae kuwa da sauri Zarah ta sadda idanun ta qasa.
Hjy da ke kallonta taci gaba da cewa to bari kiji in gaya miki idan baki sani ba ki sani Allah ya la'ani duk matar da ta nemi saki a gun mijinta akan kawai d'an wani sa6anin da bai wuce ku shirya tsakanin ku ba,dan haka ki kiyaye kar ki sake kuskure irin wnn kinji"
A hankli zarah ta gyad'a mata kai.
Tace"yauwa er albarka Allah yasa rayuwar auren ku ta d'ore har jannatul firdausi ya kuma sa ina da rai da lafiyar da zan ganin en kamakunne na"
Amin suka fad'a amma saif ya riga kowa fad'a yana kallon zarah cikin sauke ajiye zuciya,se kuma a hankli ya maida duban sa gun jamil wanda shima ya d'ago idanun sa ya kalle shi,sosai saif yaji tausayin shi har yanayin fuskar sa ya nuna,jamil da ya fahimci hakan yayi murmushi kawai wanda ya qirqiro shi ne da qyar.
Da suka koma gida har washe gari mutane sai shigowa suke tayi suna ta jajanta musu abunda ya faru,sai gidan ya zamo kmr lokacinda aka yi rasuwa duk wanda yazo haka zai zauna cike da jimami da mamakin al'amarin,yayinda ake ta yiwa Abba addu'ar samun sauqi wanda har an wuce dashi England,mom d'in saif kuwa wasu su tsine mata wasu kuma suce Allah ya shirye ta,saif kuwa tausayin sa suke ji sosai har ma wasu suna samun sa a 6angaren sa suna jajanta mishi,dmn mutane da dama se a lokacin suka san cewa ba umma ce ta haife shi ba.
Ranar Friday tun da safe umma ta tura Nadiya da Nusaiba dmn su gyarawa zarah gida.
Koda suka dawo sun samu ana yiwa zarah lalle se yaba lallen suke tayi yanda yayi kyau,awa inji ne ya zana ba mutun ba dan sosai kam lallen ya tsaru gashi akan farar fata kuma simple ba wani hayaniya har ma an kammala na hannuwa za'a fara na qafa,mai kitso na zaune tana taje mata gashin kanta zasu fara kitso ita kuma,ran zarah baqiqirin kmr zata yi kuka dan ba yanda bata yi ba ita bata son kitso umma tace faffau se anyi.
Saif ne ya shigo falon ya tsaya yana kallon zarah da se hararar su Nusaiba take dake yaba lallen nata su har abun ma ya basu dariya dan sun fahimci haushin kitson ne yasa take jin haushin kowa.
Wacce tana ji saif na tambayar ta abunda yake faruwa taqi tace dashi komai dan ko magana ma bata son yi.
Su Nusaiba dake danne dariyar su suka ce"ae yaya baza ta ma magana ba haushin kowa take ji sbd kawai umma tace se an mata kitso.
Nan ya kalli zarah kafin yake maida duban sa gun mai kitson ya ciro 5k yace"yi haquri ki tafi kinji tunda bata so"
Mai kitso kam da murnar ta ta kar6i kud'in tana mishi godiya dan duk a kitse kitsen ta bata ta6a samun kyautar ladan kitson ta irin wnn ba,gashi bata mayi kitson ba amma ta samu har haka ae kuwa har ta miqe sei godiya take ta mishi.
Nan se ga umma ta fito kitchen da sauri tana fad'in"kmr ya tunda bata so ta tafi se anyi kitson ba zancen fasawa"
Zarah da har taji dad'i a ranta take ta 6ata fuska kmr zatayi kuka tana kallon umma.
Nan saif ya d'an marairaice fuska yana kallon umma yace"please umma tunda bata so a barta nima ba son kitson nake yi ba wlh nafi so taje saloon a gyara mata gashin.
umma dake kallon sa cikin rashin damuwa tace"to shikenan mai kitso tafi abunki kawai tunda duk taron zaka zani ne.
Kana ta koma gun su Nusaiba tace"har kun dawo inace kun gyara koina yanda ya kamata?
Suka ce eh.
Tace"to sannun ku kuje ku huta anjima sai ku raka zarah saloon.
Suka ce"to"snn umma ta juya ta koma kitchen.
Yayinda saif ya gurfana a hankali kusa da zarah ya kama hannuwan ta yana kallon lallen ba tare da ya damu da su Nusaiba dake tsaye ba bare ita mai lallen se ma ciro 10k yayi ya bawa mai lallen yace"na qafa ma kiyi shi sosai yayi kyau kmr yanda kikayi na hannuwan nn"
D'auke da murmushi mai lalle tace "to" har tana mishi godiyar 10k d'in da ya bata sosai cikin nuna jin dad'i.
Haka ma saif dad'i yake ji sosai a ranshi yau zarah zata koma gidan shi se murmushi yake yana ta kallonta haka itama.
"Kinga so wai hm wnn ranar ce na jima ina so in gani"
Nusaiba ta fad'a can ciki tana rad'awa nadiya a kunnen ta wacce tayi murmushi kawai.
Saif da baiji me suke cewa ba yadai ji qus qus d'in su ya miqe tsaye cikin tsare su da ido yace"me kuke cewa?
Uhm ba komai yaya Nusaiba ta fad'a tana mai d'an sosa gefen kanta d'auke da d'an murmushi a fuskar ta.
Ta6e bakinsa kawai saif yayi ze fita,se kuma ya juya da sauri gun zarah jin tace"wash ki d'aga min qafa a hankli mana zanji ciwo fa"
Saif dake kallon ta yayi murmushi dan bako wani d'aga qafar nata aka yi ba asalima abunda aka d'aura qafar nata akai guntu ne ba ya da wani tsayin da har za'a iya ji mata ciwo son jiki ne kawai irin nata,da ta d'auko ko in an d'aga qafar nata za'a iya ji mata ciwo,sbd ba wani sabawa tayi da lalle ba gashi kuma yau haka ta tashi bata son jin abunda ya ta6a jikin nata.
Saif da still murmushi na kan fuskar sa kallon ta yake a ransa yana tunanin lallai yau da dare da kmr se yayi da gaske ya cire mata duk wani tsoro da son jiki dmn ya samu ya maida ta cikakkiyar mace tare da fatar samarwa Abba farin cikin sa.
Kana ya maida duban sa gun mai lallai yace"ki mata hankli kinji amarya ce da za'a kaita yau yau d'in nn idan kika ji mata ciwo kuwa angon nata zai sa a d'aure ki.
Yayi mgnr ne cikin yanayin barkwanci da yasa suyin murmushi.
Nan kawai suka jiyo sallama,bayan sun amsa sallamar snn mai yin sallamar ya shigo,Zarah na ganin wanda ya shigo d'in ta miqe tsaye da sauri cikin murna ta rungume shi.
Ba shiri saif ya janye ta daga jikin sa cikin tsawar da bai ko san yayi ba yace"ke meye haka! waye shi da zaki wani rungume shi haka!
"Yayana ne fa" zarah ta fad'a tana mai kallon yayan nata cike da murna,dan jiya da mutan rimin dako suka zo shine kawai bai samu zowa ba sai yau sbd yana Zariya koda yaji labarin abunda ya faru da shima ya girgiza sosai,shine yazo domin jajantawa.
Saif ya kalle shi yace Yayanki?
Kafin zarah tace komai se ga umma ta fito d'auke da murmushi tace"eh shine yayanta da take bima.
Nan saif ya bashi hannu suka gaisa yana fad'in"am sorry plz ban sani bane yi haquri"
"Ba komai"
Yayan nata ya fad'a d'auke da d'an murmushi a kan fuskar sa,saif shima ya masa murmushi,snn ya fita.
Zarah tace"Allah yasa ban 6ata ma tufafi ba yaya"
Yayan nata dake sanye da fararen kaya ya kalli tufafin nasa ba inda ya 6aci dan cikin kiyayewa ta rungume shi sbd sanin akwai lalle a hannun ta.
Yace"A'a indai ke baki 6ata lallen naki ba.
Ta kalli lallen bai 6aci ba ta girgiza masa kai.
Yace"to zauna a qarasa lallen ko"
Nan ba musu ta zauna had'e da fad'in"su inna fa suna lafiya?
Yace"duk suna lafiya,kafin yake maida duban sa gun umma ya gaida ta cike da ladabi ta amsa,snn shima ya amsa gaisuwar su Nusaiba da suka gaida shi.
Daga haka Umma ta wuce dashi sama zuwa qaramin falo.
Bayan an yiwa zarah lalle har ma sunje saloon sun dawo.
Umma ta kira zarah a d'ikinta ta bata kazar amare ta haki da aka had'a ta musamman.
A yatsine zarah ta kalli kazar tace"inna wannan kazar fa awa an ciro a kwata.
Umma tace bana son shashashanci maza cinye ko yanzun na d'ura miki.
Ba yanda zarah ta iya haka ta fara cin kazar fuskar ta a yatsine har sai da ta cinye snn umma ta bata tsime ta d'aura dashi.
Bayan ta gama shan tsimen ne umma tace to saura dilka kin ganta gata had'i ne na en Maiduguri,idan kikayi ta sau d'auya tamkar kinyi wata kina gyaran jikin ki ne sbd yanda take da kyau,dan haka tashi yanzu ki shiga bathroom ki shafata ko'ina a jikin ki se kinyi 30 mnt sannan ko zaki wanke kiyi wanka.
Zarah tace"wae inna har minti 30 ina bathroom d'in ga magrib ta kusa fa"
Umma tace"shiyasa nace kiyi kiyi kije kafin magrib d'in tayi dmn ana gama sllr isha saif zai zo ya d'auke ki ne ku tafi,idan kuma kika tsaya shiririta zan zo na same ki har bathroom d'in na miki da kaina.
A d'an shagaw6a tace"a'a inna bazan ma tsaya shiririta ba dan bana son magrib ta min ina ciki amma to lalle na fa bazai fita ba idan na shafa ta?
Aa bazai fita ba inda haske ma zaki qara lallen ya qara fitowa maza tashi kije.
Nan zarah ta d'auki dilkar da akayi ta kmr wani cream ta wuce bathroom.
Koda ta fito ita kanta ta tabbatar lallai dilkar mai kyauce dan kuwa jin jikinta nata take awa an sauya mata fata sbd yanda tayi wani irin laushi da tsantsi har ma wani qamshi na fita a jikin nata da duk ya qara wani haske da sheqi.
Tana fitowa ne umma ta bata farin miski da wasu turarukkan shafawa a jiki da kowanen su da ga6ar da za'a shafa shi dmn haka ta mata bayani,zarah ta koma bathroom bayan ta shafa kowanne inda umma tace snn ta fito.
Umma tace"to yanzu se kije kiyi sllr magrib idan kin idar se kici abinci bayan isha'i ki shirya kizo da akwai mgnr da nake son zamuyi,nasa Nusaiba ta fitar miki da kayanda zaki sa kinji.
Zarah tace"to"snn ta fita daga d'akin.
Koda bayan isha'i tayi ta kammala tsirinta tsaf,Nusaiba ce ta mata kwalliya se ta fito sak amayar ta se zuba qamshi take tana zaune kan bed d'akin umma dake zaune kusa da ita tana qara bata shawarwarin yanda zata zauna lafiya da mijinta ba tare da wani yaji kansu ba.
Zarah dake saurarenta tayi shiru jikin ta duk a sanyaye tana jin fad'uwar gaba a ranta,ta kalli umma muryar ta a sanyaye tace"inna fad'uwar gaba nake ji fa ina tsoron mahaifiyar sa da kmr in na koma akwai matsala"
Umma,tace"um um ki daina fad'ar haka babu matsala inshaa Allah,kuma ita da ma take can a rufe ki kwantar da hankalin ki kinji babu abunda zai faru sai alheri,amma idan har kina tsoro to ki riqa karanta wnn addu'ar a duk lokacinda kikaji tsoron nata yazo miki.
Addu'ar ita ce
_Allahumma ikfihim bima shi'ita._
To da yardar Allah,Allah zai kare ki daga gare ta ba abunda zai same ki kinji ko?
A hankli ta gyad'a mata kai.
Nan se ga saif ya shigo d'akin d'auke da sallama a bakin shi.
Umma ce ta amsa mishi sallamar yayinda yayi tsaye ba tare da ya iya qarasawa daga ciki ba se kallon zarah da yake tayi har baya son qiftawa,kan yanda ta mishi masifar kyau.
Yayinda ita kuma kanta ke qasa bata ko son su had'a ido,dmn kmr kar ya shigo taji fad'uwar gaban nata ya qaru sbd tasan yau kam ba me qwatar ta a hannun shi se yanda yayi da ita shiyasa ma duk take ta jin tsoron komawa.
Saif da ke ta faman kallon ta da qyar ya iya janye idon sa cikin sauke mufashi can qasa a hankli,snn ya qarasa ciki yana mai gaida umma,wacce ta amsa tare da kallon zarah tace to tashi kuje ko"
Jiki sa6ule zarah ta miqe suka fita.
Wacce har suna tafe cikin mota bata yarda sun had'a ido ba se shi dake ta faman kallonta riqe da lallausan hannun ta da ya kama,ya kasa sakin hannun se faman murza shi yake a hankli har suka isa gida.
*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»page«» 55*
Saif da shine ke jan motar da kanshi,bayan ya faka mota ya kalli zarah wacce duk qamshin ta ya cika motar,har yana ji kmr suyi zaman su a cikin motar dmn yayi ta shaqar qamshin nata.
Wanda ya kalle ta ne had'e da kai lallausan hannun sa zai d'ago fuskar ta,bata barshi ba taja gyalen ta a hankali ta rufe fuskar,yayi murmushi yana jin wani irin sonta a ranshi kmr ya had'iye ta kan yanda yake hango fuskar ta a cikin gyalen sai sheqi take cike da sha'awa.
A hankli ya matsa gab da ita bakin sa saitin kunnen ta muryar sa a natse can qasa
Yace"Amarsu ta ango yau ni ake rufewa fuska,to shikenan dai ki zauna yau angon naki da kanshi zai fita ya bud'e miki mota kinji.
Nan kawai bai jira me zata ce ba ya fita ya zagaya ya bud'e mata ganbu ya kama hannun ta ta fito ya maida ganbun ya rufe suka shiga ciki yayinda take manne a jikin sa har suka isa d'akin shi.
Numfashi taja a hankli can ciki sbd wani irin sanyi da dadda d'an qamshi da suka tarbe ta a lokaci d'aya,d'akin yasha gyara matuqa dashi kansa yasan dole babbar baquwa ce zata sauka a cikin sa musamman yanda aka shinfid'a qatuwar darduma a nn tsakiyar d'akin kusa da bed,snacks da naman kaji har da drinks jere akai wanda da gani kasan couples ne zasu cin wnn liyafar da akayita iya ta mutum biyu kad'ai,inda ba kowa ne yayi aikin ba face saif da kanshi su Nusaiba d'akin kawai suka gyara amma shi ya jera abinci ta yanda yasan dole zai qayatar da amaryar sa zarah,wacce duk da fuskar ta a rufe take amma tana ganin komai tsarin ya kuma birge ta sosai.
Nafila suka fara yi raka biyu suka godewa Allah da ya nuna musu wnn ranar snn suka zauna ma cin abinci ya bata ta bashi har saida