Showing 36001 words to 39000 words out of 145898 words

Chapter 13 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24728

Murmushi Nusaiba tayi dan zara ta birge ta duk yanda ta fad'a mata tsarin yanda zata riqa sa kaya su fito da ita bata yi kuskure ba haka take yi.
Cikin d'aga gira zarah tace da Nusaiba"kallon fa?
Nusaiba tace"wlh kyau kika yi sosai.
Zo muyi selfie.
Ta fad'a tare da kama hannun zarah ta zaunar da ita kusa da ita a nn kan sofa yayinda nadiya ke zaune d'ayan 6angaren,suka saka Nusaiba a tsaka wacce ta ciro wayar ta ta d'auke su selfie dukkan su kowannen su ya d'aura qafa d'aya kan d'aya se sukayi kyau sosai musamman yanda suka saki murmushi.
Take Nusaiba ta turawa kowaccen su hoton a wayar ta kmr yanda suka buqata,snn zarah tace"to ku tashi muje kitchen ku dafa abunda kuke so dan ni dai yanzu ba girki nakeyi ba tunda na fara zuwa school,da na dawo indomie kawai nake dafawa dan ta fimin sauqi.
Nadiya tace"Au shi yaya saif fa ko biye miki yake kuyi ta cin indomie d'in?
Kafin zarah tace"komai Nusaiba ta riga ta da cewa"Aa ae kinsan yaya saif ba ko yaushe abinci ya dame shi ba shiyasa take cin karanta ba babbaka.
Lallai yaya saif babba ne.
Nadiya ta fad'a wacce ta miqe tsaye tare da cire mayafin ta ta ajiye snn ta nufi bathroom dmn yin arwala sbd kiraye kirayen sllr zuhur da aka soma yi.
Bayan ta shige bathroom d'in ne Nusaiba ta kalli zarah tace"wae kinji wani qamshi dake fita a jikin ki mai dad'in gaske kodai.... Da sauri zarah ta harare ta tare da fad'in kodai me?
D'an murmushi Nusaiba tayi snn tace"maida wuqar ni bada wata manufa nake nufi ba ina nufin ko yaya ya gaya miki ra'ayin sa ne dan mutum ne mai son qamshi sosai.
Zarah ta ta6e baki tare da fad'in"hm Allah sauwaqe wlh ni yayanki sam baya a gabana bare har ya gaya min ra'ayin sa nabi kawai dai turarukkan da umma ta bani ne a kwana ki da naje tace na riqa amfani dasu kullum idan nayi wanka.
Nan Nusaiba ta jawo jakar ta da sauri tace"ae kin ma tuna min umma ta bani saqon wani turare tace na kawo miki da dare ake amfani dashi idan anyi wanka za'a kwanta se ki fesa a jiki.
Kana ta ciro turaren ta miqa mata,zara ta kar6i turaren tana dubawa se ganin hoton cartoon d'in mace da namiji tayi a jikin turaren rungume da juna se shinshinar qamshin jikinta yake tamkar ze had'iye ta.
Da sauri tasa tafukan hannayen ta ta rufe hoton snn kana ta maida tafukan hannayen nata ta rufe fuskar ta cikin jin kunya kmr umman na kusa.
Nusaiba dake kallonta d'auke da murmushi tace"lallai ma kunya su en cartoon d'in,to kar6i wnn ledar ki duba a kasuwa na siyo miki da umma ta aike ni.
Ta fad'i hakane tare da miqa mata wata leda snn ta tashi ta wuce zuwa bathroom sbd Nusaiba ta fito.
Zarah da ta bita da kallo ta d'auki ledar ta ware tana dubawa,kayan shiga swimming pool ne kala biyu,bra da d'an guntun skirt iya cinya me had'e da bomb short a jikin shi,sky blue in colour,se d'ayar klr kuma white yayinda bra d'in take d'auke da wani material lace like net da aka shinfid'a a gaban ta se tayi looking like half vest amma tsaf ake hango qoqannin bra,yayinda skirt d'in ya kasance shape d'in sa iri d'aya da tummy amma guntu ne sosai iya cinya kuma a ware yake ba'a d'inke ba d'aura shi ake kmr zani,da akwai en zareruwa guda biyu gefe da ake d'aurewa.
Hm zarah ta fad'a tare da maida kayan cikin leda se ga Nusaiba ta fito daga bathroom har ta d'auro arwala,suna had'a ido da zarah ta kashe mata ido d'aya tare da fad'in"ya kika ga kayan sunyi?
Zarah tace"inafa nikam bazan iya sa kayan nn ba kin sani gwanda kawai ki maida su inda kika siyo se a d'auko wa enda zan iya sawa yafi da ayi asara"
Nusaiba tace"kinga sis wa en nn fa kayan shiga swimming pool ne bawai wa enda zaki sa ki zauna bane.
Meye kuma haka?
Zarah ta tambaya.
"Zo kiga"
Nusaiba ta fad'a bayan ta kama hannun ta suka je gun window ta nuna mata swimming pool da suke hangowa.
Tace"amfanin kayan se idan zaki je gurin se kisa ki shiga kiyi wanka abunki"
Gwalo ido zarah tayi tana kallon ta tace"ga bayi se naje can nayi wanka awa wata mahaukaciya kowa na kallona"
Kafin Nusaiba tace komai se dariyar Nadiya suka ji wacce ta sallame sllh knn ta taso tazo gurin su ta dafa zarah tare da fad'in"kinga zarah ae wayewa ce wanka a gurin ba wanda zai d'aukeki mahaukaciya snn wanka ne na shan isk dmn kawai jin dad'i,ba kmr irin wankan da akeyi bayi bane snn kinga gurin a ke6ance yake har ki gama wankan ki ba me ganin ki,da akwai qofar da zaki bi ki wuce ba se kinbi qofar falo ba,kin fahimta?
Eh na fahimta
Zarah ta fad'a ba wai dan zata iya abunda suka ce ba ta fad'a ne kawai dan ta huta dasu.
Tace"yanzu dai ku gaya min me kuke so naje na dafa muku kafin yaya ma'aruf yace ku fito har de ke nadiya da zaku koma kaduna.
Nadiya tace"ai se gobe zamu koma ko kina so mu kwana a nn"
Tayi mgnr ne cikin tsokana.
Da sauri cikin marere ce fuska Zarah tace"eh wlh ina so dan Allah.
Hm um! rufa mana asiri da yaya saif haka ma umma baza ta bari ba cewar Nusaiba kafin nadiya ke cewa"lallai dai kam da dai baya nn.
Zarah tace"haba dai ko yana nn meye ruwan sa daku tunda ba'a kanshi zaku kwana ba,kuma inna nasan yanda zan bi da ita ta yarda kunji dan Allah"
Murmushi kawai sukayi ganin yanda duk ta wani marairai ce musu suka ce"shikenan kira umma muji idan zata yarda d'in to.
Um um tukun ni nafi so se na gama girka muku abinda zaku ci snn,kar yaya ma'aruf ya bar gidan nn bai ci komai ba.
Nadiya tace"cabd'i ina gimbiyar tasa zata yarda ta bar shi da yunwa ae ko ni er rakiyar sa a qoshe nake sbd albarkacin sa da na samu har ji nake kmr cikina ze fashe.
Nusaiba ta harare ta tare da fad'in me kk nufi.
Nadiya tace"ae kema kinsan gaskiya na fad'a dmn dani kad'ai ce zanzo baza kimin liyafar da kika mishi ba se dai idan nazo abunda na samu anyi a gidan shine zanci.
Kallon up and down Nusaiba ta mata tare da fad'in"ae kam kin san shi kad'ai keda wnn matsayin.
Daga haka bata jira me nadiya zata ce ba taje zuwa sllh.
Nadiya da ta bita da kallo tayi murmushi kawai haka ma zarah wacce taje bathroom ta d'auro arwala tayi sllh bayan ta idar,ta d'auki wayar ta dake kan bedside drawer ta kira umma.
Da qyar kmr zatayi kuka ta samu umma ta yarda ko shi se da sa bakin Abba dan suna tare shida umma shine yace ta barsu kawai su kwana tunda kwana d'aya ne.
Ae kuwa sosai Zarah taji dad'i haka ma su Nusaiba dan suna son kwana a gidan.
Har bayan la'asar ma'aruf na gidan be tafi ba suna can balcony shida saifuddeen kan resting chairs se fira suke tayi kmr wasu mata,dan haka suke suna jimawa basu had'u ba amma duk rnr da suka had'u tofa suna jimawa tare suna yin fira.
Se 5:30
Suka koma daga ciki kmr yanda ma'aruf ya buqata yana son zasu tafi dan shi sam bae san da zancen a nn gidan su nusaiba zasu kwana ba sbd basu gaya mishi ba se yanzu yake ji da suka zo suka same su a falo yace"su tashi su tafi Nusaiba kece mishi ae su a nn zasu kwana.
Kafin ma'aruf yace komai saifuddeen yace"what! uban me zakuyi a nn gidan idan kuka kwana"
Sis ce ta buqata ae.
Cewar Nusaiba da tayi kicin kicin da rai.
Saifuddeen da ya fahimci zarah take nufi ya kalli Zarah irin kallon kin raina ni ko.
Tayi qasa da idon ta kawai dan bata son ma'aruf da nadiya su fahimci wani abu.
Shi kuma saif ya maida duban sa gun Nusaiba zatayi magana knn ya mata wani kallo dako be fad'a ba tasan me yake nufi sum sum suka haura sama ita da Nadiya suka d'auko mayafin su da hand bags d'insu suka fita.
Nan Ma'aruf yayi sallama da saif shima ya fita.
Kmr jiran fitar sa yake da sauri cike da mugunta ya fizgo zarah cikin damqo gashin kanta ya riqe sosai har se da ta saki er qara tare da saurin kai hannayen ta kan nashi cike da son qwace kanta.
Bai barta ba se had'awa yayi da hannayen nata duk ya riqe guri d'aya tare da jelar gashin ta,with deep voice yace"kin raina ni ko munafuka wato so kike su san me yake going a gidan nn to bari kiji wlh duk naji wata magana ta fito wae ina kawo en mata a gidan nn ko se nayi gunduwa gunduwa dake naba kitty ta cinye wawiya kawai.
Ya tura ta da qarfi har sai da ta fad'i zaune yasa qafar sa yayi ball da ita snn ya wuce zuwa sama,Zarah da ta bishi da kallo qwallah tap a idonta ta mishi Allah ya isa yana jinta be juyo ba yayi tafiyar shi nn ta had'e kanta da guiwa ta shiga yin kuka.

_Thursday 22/02/2018_
[11:15AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Friday 23/02/2018_
*锘柯宦宦籗AIFUDDEEN!芦禄禄芦芦禄*






By
*Billy giro馃槉*




*芦禄Page芦禄 22&23*
Tuna cewa sun d'aura girki yasa ta sassauta kukan ta tashi cikin share qwallah ta nufi kitchen.
Ta samu ruwan zafin da suka d'aura dmn yin tuwon semo har sun tafasa ta kashe wutar gas cooker d'in ba tare da tayi tunanin tayi iya ko nata ba,har miyar agusi ma da suka d'aura duk ta kashe tayi ficewar ta zuwa d'aki ranta ba dad'i.
Washe gari da safe guraren qarfe goma ta fito kitchen riqe da cup d'in tea zata haura sama zuwa d'akin ta tana sanye da wani material me kyau turquoise green in clour d'inkin doguwar riga da tayi d'as a jikin ta,high neck me dogon hannu wacce ta baje sosai tun daga kan waist d'inta,snn tayi d'aurin d'ankwali simple iya yinta se yayi kyau ba laifi har de yanda ta jashi yayi baya kmr yanda taga Nusaiba nayi.
Sam bata ji motsin saukowar mutum daga staircase ba se ganin mutum tayi a gabanta,har se da ta d'an tsorata ta ja baya da sauri tare da kallon wacce tasha gaban ta wato d'aya daga cikin en matan saifuddeen,da ta fito zata tafi riqe da makullin motar ta saqale a d'an yatsan ta se jujjuya shi take tana fmn cin chewing gum.
Shaye da toka Zarah tace"lafiya meye haka?
Riqe waist d'inta tayi tare da sakar mata murmushi snn tace"yi haquri and idan baza ki damu ba plz ina son zamuyi wata magana ne game da mijinki saif.
Tsaki Zarah taja snn ta ra6a ta gefen ta zata wuce,da sauri ta tare mata hanya tace"Haba sis ki tsaya ki saurare ni mana magana ce fa mai mihimmanci".
Ke kika san wnn ni da Allah bani hanya na wuce.
Zarah ta fad'a tare da mangare ta gefe zata wuce.
Bata ji haushi ba ta riqo hannun ta a hankali cikin sanyin murya tace"yi haquri dan Allah ki saurare ni kinji sis"
Kallonta ta zarah tayi kmr baza tayi magana ba can ta kauda fuskar ta gefe tace"fad'i ina jinki kuma ni sauri nake idan baki tashi ba nayi tafiya ta.
Tace"to sis a tsaye d'in zamuyi magana da munje mun d'an zauna ko?
Mtsw zarah tayi d'an guntun tsaki snn ta yarda suka je suka zauna.
Yarinyar na kallon ta tace"am sorry bansan ya zaki d'auki maganar ba,gashi a gaskiya na kasa haquri bansan wa zan tunkara da zancen nn ba face ke dmn ke zaki fi sanin komai akan abunda nake son ji game da saif,so nake naji plz shin tunda kukayi aure da akwai wani abu da ya ta6a shiga a tsakanin ku na kwanciyar aure keda shi ko kuwa dama kinsan cewa baya da lafiya bazai iya amfanuwa da mace ba se dai kullum cikin wasa kawai.
Zarah dake kallonta cikin girgiza kai tace"Hm lallai iyayenki sunyi asara wlh,ta nuna ta tace to bari kiji in gaya miki ni ba asararriya bace irinki da har zaki zo ki tunkare ni da wnn banzan zancen naki.
Mtsw taja tsaki tare da tashi zata bar gurin,yarinyar ta riqo hannun ta da sauri tace"kinga sis matsalan nn fa har ke ta shafa gwanda ki tsaya mu san yanda zamu warware matsalar, ki daina jin haushi na ke kikayi sakaci ae da kika bar mijin naki yana kula en mata.
Zarah ta fizge hannunta cikin dalla mata harara tace"jaka kawai asararriya ki tafi can ki nemo sauran en matan nashi ku warware matsalar kuda yake gaban ku.
Daga haka ta wuce ba tare da ta jira me zata ce ba.
Yarinyar ta bita da kallo wacce duk a tunanin ta ta d'auka ko zarah sokuwa ce ganin kai kawon da take a gidan amma sam bata damu ba bayan tasan gurin mijinta take zowa har su kwana tare amma ko oho,ashe rashin so ne dan dai yanzu ta fahimci Zarah ba son saifuddeen take ba kmr yanda shima ta fahimci ba son zarah yake ba akayi auren.
Numfashi ta fitar a hankli tare da jinginawa a jikin kujerar da take zaune,ta lumshe ido tana tunanin tun lokacinda ta fara d'aura idonta akan saifuddeen ta kwad'aitu da son kasancewa tare dashi burin ta knn kullum amma duk tazo bai wuce yayi romancing d'inta ba yana jin kansa yanda yake so ze ture ta gefe ya hau baccin sa,kwanaki har camera tasa a d'akin nasa a 6oye dmn taga ya yake yi da sauran en matan nashi amma taga duk kanwar ja ce romancing d'insu kawai yake kmr dai yanda yake mata,kuma ta fahimci kowaccen su tana mamakin hakan amma kwarjinin sa yasa ba wacce ta iya masa magana,haka itama tasha yunqurin son ta tambaye shi wai lfy amma se ta kasa.
Qamshin turaren sa da taji ne yasa ta bud'e idanunta,fuskar sa a d'aure ya mata wani kallon me kuma kk yi zaune baki tafi ba.
Haquri ta bashi tare da saurin tashi ta fita.
Snn shima ya fita yaje ya samu jamil dashi ne dalilin fitowar shi.
Jamil dake jingine jikin motar sa yabi yarinyar da ido har taja motar ta ta fita,kana ya girgiza kansa ya kalli saifuddeen yace"haba saif is not gud wlh ba girman ka bane ace wai kana kawo en mata har gidan ka su kwana.
Cikin yanayin 6acin rai saifuddeen yace"dama wane girman ne dani to yanzu,ae tunda aka had'a aurena da wnn banzar yarinyar aka 6arar min da girma,kuma dan Allah ka daina sa ido akan abunda be shafe ka ba bana so.
Jamil yace"ae gwanda kaso dan gaskiya nake gaya maka in zaka daina ka daina.
Bazan daina ba jamil!kuma idan zaka fad'i abunda ya kawo ka ka fad'a kona tafi abuna dan nagaji da wnn banzan surutun naka da kake min.
Kallon sa kawai jamil yayi kmr bazai ce komai ba se can ya bud'e ganbun motar sa ya ciro wasu takardu ya miqa masa ba tare da yace masa komai ba ya shiga motar sa yayi tafiyar shi.
Saifuddeen da yasan takardun mene ne be damu da tafiyar sa ba se komawar sa yayi daga ciki yana me duba takardun da zeyi signing akai kan wani clinic da suka had'a hannu zasu bud'e shida jamil.
Koda zarah ta gama breakfast ta fito ta same shi zaune a falo ya gama signing d'in takardun yana waya da jamil.
Sau d'aya ta kalle sa ta wuce zuwa kitchen,ta fito zata koma sama se jin tayi ta fad'i ba shiri kan yanda saifuddeen ya jefo mata d'ayan takalmin shi daga can inda yake zaune,takalmin yayi super ya kad'e mata qafar ta da take shirin takawa ta fad'i har ta buga bakin ta kan stairs dan gab take da shirin hawa.
Ae kuwa ta saki qara tare da saurin ta6o bakin ta,se ga saifuddeen yazo ya zauna kan stairs tare da kai hannu ya tallabo fuskar ta yana kallon gefen bakinta dake fitar da jini yace"gud gobe ma idan kika sake zagina uban wnn zan miki wlh,er rainin hankali.....kai kuma mugu azzalumi Allah ya isa wlh!
Zarah ta fad'a tare da tofa mishi jinin da ya taru a bakin ta kan farar rigar sa.
Da saurin sa ya kalli rigar tashi snn cikin hanzari ya tashi ze damqo ta,amma kan kace me tuni ta zura aguje ta haura sama ta shige d'akin ta ta rufe.
Be bita ba se kallon rigar sa ya sake yi rai 6ace ya jinjina kansa tare da yin qwafa snn ya nufi d'akinsa ya cire rigar ya sauya wata.
Se da ta tabbatar ya bar gidan snn ta fito tayi zaune a falo tana waya dasu Nusaiba.
Washe gari da safe saifuddeen ya dawo daga masallaci be zarce koina ba se d'akin zarah ya same ta kwance wacce tana yin sllh ta koma kwanciya se bacci take ta rufa jikinta da blanket gabad'aya har fuskar ta ba'a gani duk ta rufe.
Yasa hannu ya yaye blanket d'in daga kan fuskar ta yana kallon bakinta da ya d'an kumbura kad'an ta gefe,kana ya maida duban sa gun gorar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login