Showing 75001 words to 78000 words out of 145898 words

Chapter 26 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24726

a gare ta,dan yasan duk aikin desire tablet d'inda ya bata ne,amma inshaa Allah wahalar tazo mata qarshe dan maganin da ya bata tasha yanzu me qarfi ne da yafi na farko wanda da zarar tayi bacci ta farka shikenan komai zai dawo mata normal.
Tun tana jurewa har ta soma yi mishi kuka tana rungume a jikin sa se rarrashin ta yake tayi har ya samu tayi bacci,hakan yasa ya sauke ajiyar zuciya a hankli snn ya kada mata seat ya kwantar da ita.
Kafin yake jan mota ya bar school d'in yana tafe duk rabin hankalin sa a kanta har suka isa gida.
_Sunday 18/03/2018_ *«»«»«»SAIFUDDEEN!«»«»«»*






By
*Billy giro😊*




*Dedicated to»»»Zarah gwandu*



*«»Page«» 38 & 39*
Suna qarasowa gida ya tsaya kawai yana ta kallon ta riqe da hannunta da ya kama yana d'an murza shi a hankli kmr me wani tunani a ranshi,can dai ya fita ya zagaya 6angaren da take,ya bud'e ganbu yasa hannuwan sa duka biyu ya d'auke ta snn ya tura ganbun da qafar shi ya rufe,ya shiga da ita ciki ya haura sama zuwa d'akin ta ya kwantar da ita kan bed,ya cire mata hijab,yaje d'akin shi ya had'o allura ya dawo.
A hankli ya bud'e zip d'in skirt d'in ta ya d'an d'aga pant d'in ta kad'an ya mata allura,byn ya gama d'an murza mata gurin ne snn ya rufe mata jikinta ya gyara mata kwanciyar ta ya fita daga d'akin.

Tun lokacin bacci Zarah keyi har sai qarfe uku snn ta farka,se ganin ta kawai tayi rungume a jikin saif,ta tashi da sauri hawaye na tserar saukowa daga kan kumatun ta,sbd lokaci d'aya abubuwan da suka faru da ita suka shiga dawo mata.
What's wrong zarah me kuma yake damunki?
Saifudden ya fad'a fuskar sa d'auke da damuwa yana qoqarin janyo ta jikin sa,zarah da bata ko iya kallon shi ta fashe da kuka cikin sauri ta sauka kan gadon zata fita daga d'akin dan ta ma rasa ina zata sa kanta da wnn abun kunyar da ya faru da ita kmr a mafarki.
Saif be bar ta fita d'akin ba ya taso da saurin shi yasha gabanta ya rungume ta yana fad'in"calm down zarah gaya min mene ne kinji daina kuka"
Komai zarah bata iya ce masa ba se kuka ta ci gaba dayi a jikin shi.
Nan ya tafi da ita kan bed suka zauna se rarrashin ta yake yana bata magana,dan ya fahimci dalilin kukan wanda dama yasan haka zata faru idan komai ya dawo mata normal,shine yake bata magana irin wacce zai samu ta sake ta maida komai ba komai ba.
Amma har ya qaraci maganganun shi zarah bata iya daina kukan da take yi ba,ya d'ago ta daga jikin sa yana kallon ta kanta qasa taqi yarda ta kalle shi gabad'aya kunyar sa take ji ita kam har bata jin zata iya sake had'a ido dashi,dan abunda ya faru da ita ya riga ya gama bashe ta,da ta rasa ta yanda akayi hakan ya faru da ita.
Saif dake kallon ta duk yaji damuwa a ranshi be san ta yaya zai fara gaya mata gskyr abunda ya faru cewa duk cin amanar sa ne.
Nan ya sake maida ta jikin sa muryar sa a hankli yana fad'in"kiyi haquri dan Allah zarah ki daina kukan nn haka kar ki janyo wa kanki ciwon kai kinji,a hankli ta gyad'a masa kai ba tare da ta iya kallon sa ba.
Yace"to tashi kiyi sllr azahar kinga har uku ta wuce kar sllr la'asar tazo ta same ki.
Nan ba musu ta tashi ta nufi bathroom koda ta fito saif baya nn ya fita,se bayan ta ida sallah da d'an jimawa snn ya dawo,riqe da plate d'in abinci a hannu shi white rice ce with stew wacce sosai taji naman kaji se qamshi ke tashi,ya ajiye mata a gabanta a nn inda tayi sallah still tana zaune gurin bata tashi ba.
Wacece bata kalle shi ba se abincin kawai ta kalla kafin tace komai saif dake kallonta yace"plz kar kice baza kici ba,bana siyarwa bane wnn a gurin umma naje na kar6o mana,bcos naga wancan lokacin da na ta6a siyowa miki abinci siyarwa baki ci ba,shiyasa nace may be ba kya son na siyarwa ne ko?
Bata bashi amsar abunda yake son ji ba se godiya da ta masa.
Ya kalle ta kawai snn ya tashi ya d'auko mata ruwa a fridge ya ajiye mata snn ya fita,shima yaje zuwa cin abinci dan tun tean da ta rage ya qarasa shanyewa be sake cin komai ba.

Har aka yi sati d'aya zarah bata iya had'a ido da saif,hakan yasa bata sake yarda ya kaita school ba kullum driver ne ke kaita ya kuma d'auko ta,amma hakan be hana saif kullum se yaje d'akin ta ba,dan so yake ko yaya ta sake ta manta komai amma ita kam ta kasa sakewa idan ma ta ganshi se taji komai ya sake dawo mata sabo duk abubuwan da suka faru suyi ta tariyo mata aka da har kullum ta kasa daina tunanin wae wane irin abu ne ya faru da ita awa mafarki da koda ace mafarkin ne yana d'aya daga cikin mummunan mafarkin da baza ta iya gayawa kowa ba.
Dan duk ta tuna abun ma se taji qwallah sun cika mata ido.
Yau ta kasance sunday guraren goma na dare ta fito daga d'akin ta,sanye da rigar bacci fara mai santsi er guntuwa wacce bata ko qarasa kai zuwa guiwar ta ba,ga hannayen ta en siriri kmr na vest,ta tufke gashin kanta da ribbon yayinda jellar gashin ta ke yawo a hankali sbd saukowar da take yi daga staircase zata je downstairs.
Tana qarasa saukowa kawai ta hango saif zaune a falo Tv kunne yana kallo,suna had'a ido tayi saurin janye idanunta ta juya zata koma,gashi ta fito ne da niyyar zuwa kitchen ta d'aura ruwan zafin tea tasa a flask dmn taje dashi d'aki sbd azumin da take son yi gobe Monday.
Tunda ta juya cikin tako d'aya bata qara wani ba ta tsaya cak sbd kiran da saifuddeen ya mata.
Ya taso ya qaraso gurin ta ya juyo da ita yana kallonta kanta qasa taqi yarda su had'a ido,se hawaye ya gani suna saukowa daga kumatun ta,a hankli cikin damuwa yace"oh Allah mene ne kuma zarah?
Ni bazan iya ci gaba da zama a gidan nn ba,ina son kaci ka min alqawari na dan Allah in tafi.
Zarah ta fad'a tana mai share hawayen da suka zubo mata.
Saif dake sauraren ta,shi kam gaban sa ne yaji ya fad'i,snn lokaci d'aya yaji duk jikin sa a sa6ule,be iya ce mata komai ba se kama hannun ta yayi ya tafi da ita kan kujera suka zauna yana kallonta da kulawa yace"No zarah indai akan wnn abun ne da duk kika sa kanki a damuwa ni bazan sake ki ba,idan zaki cire damuwar ki cire,abu ne fa wanda dan ya faru tsakanin miji da mata ba komai bane,ni sau nawa ina nuna miki tawa buqatar bansa kaina a damuwa ba se ke,yi haquri kinji ki daina zancen nn dan Allah,ki gaya min duk abunda kk so zan miki.
Duk yana mgnr ne cikin rarrashi.
Zarah da still kanta ke qasa tace"ni alqawari na kawai nake so ka cika min dan Allah.
Handkerchief ya ciro ya share zufar da yaji ta d'an tsastsafo mishi a goshi sbd maganar da tazo mishi da ita. Yace"meyasa zarah ko wanda kk so ne yake matsa miki?
Girgiza masa kai tayi tare da fad'in"um um ni ba wanda nake tare dashi fa,kawai dai ina buqatar ka cika min alqawari na ne,bana son abunda ya faru dani ya sake faruwa dani ina jin kunya.
Da saurin sa yace"No zarah nayi miki alqawarin bazai sake faruwa da ke ba"
Cikin muryar kuka tace"kmr ya abunda ya faru dani fa ni kaina bansan ya akayi ba"
Saif da duk ya daburce yace"to shikenan naji amma kinsan idan na sake ki yanzu Abba zai d'auka ko dan ya hana ni auren Sophie ne naji haushi na sake ki,kuma dama ae ce maki nayi se idan na samu auren Sophie snn ko zan cika maki alqawarin ki.
Se a lokacin ta kalle shi qwalla tap a idonta tace"to ai ni da kai fa ba me qaunar juna meyasa baza ka sake ni ba"
Yace"yanzu ke idan na sake ki me zaki cewa su umma? muryar ta a sanyaye tace"nima ban sani ba".
Yace"To kin gani nima bansan me zan gaya musu ba kuma haka kawai baza ayi saki ba,dan haka idan har kina so in sake ki to kije kiyi tunanin abunda kikasan su Abba baza su ga laifin ko d'ayan mu ba,ko kina da wata hujjar ne yanzu?
Ya fad'a cikin tsare ta da ido.
A hnkli ta girgiza masa kai alamar a'a.
Yaji wani dad'i a ranshi har yana sauke ajiyar zuciya.
Yace"to kije ko yaushe kika sami hujja kizo ki gaya min,amma fa daga yanzu bana son in sake ganin ki a cikin damuwa ki sake kamar ba wani abunda ya faru idan ba haka ba ko kin kawo min hujja bazan saurare ki ba bare har na rubuta miki saki.
Gyad'a masa kai tayi zata tashi ya riqo hannun ta yana kallon er fincikar rigar da ke jikinta ta mata kyau sosai,cikin wata irin murya qasa qasa yace"ina zaki tafi me kika fito yi?
Zan d'aura ruwan zafin tea ne nasa a flask sbd ina so zanyi azumi.
Azumin ranko?
Ya tambaya yana me kallonta.
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
Yace"to nima zanyi se kisa ruwan dani qarfe hud'u zan zo na tashe ki kinji"
Bata yi magana ba se gyad'a masa kai da tayi.
Snn ta tashi ta wuce ya bita da kallo har ta shige kitchen,ya sauke numfashi a hankli tare da jingina bayan sa a jikin kujerar da yake zaune,idanuwan sa a lumshe se wani irin qaunar zarah yake ji a ranshi,da ya d'auka ko birge shi ne kawai take.
Wanda yana zaune a gurin idanuwan sa a lumshe har se da zarah ta gama abunda takeyi a kitchen ta fito riqe da flask,snn ya bud'e idanun sa ya bita da kallo har ta 6acewa ganin sa snn ya iya tashi ya kashe Tv da hasken falon ya haura sama zuwa d'akin shi.
Qarfen hud'un asuba koda yazo tashin ta ya samu har ta tashi tana bathroom se yunqurin amanta yake jin yana fitowa a bathroom d'in,kae tsaye ya shiga bathroom d'in da sauri.
Ya same ta gun washbasin kan ta a duqe riqe da brush a hannun ta tana ci gaba da yunqurin amai.
Ya tallabo fuskar ta yana kallon ta yace"mene ne?
Ruwa tasa ta wanke bakin ta snn tace"ba komai brush kawai nakeyi.
Saif dake kallon ta yace"wane irin brush ne kk yi haka,ki riqa sa brush d'in a hankli kinji.
Gyad'a masa kai tayi tare da kunna famfo ta wanke brush d'in tasa a d'an wani cute case dake manne a jikin bangon bathroom d'in nasa brushes ta bud'e ta saka snn suka fito yana rungume da ita a jikin sa.
A nn d'akin sukayi sahur zaune kan rug suna fuskantar juna,yayinda saif shan tea kawai yake amma hankalin sa na gun zarah se kallonta yake tayi musamman yanayin zaman ta duk yafi tafiya da imanin shi,wacce tayi zaman ne cikin matse cinyoyinta kmr zamanta tahiya sbd yanayin rigar ta dole se tayi irin wnn zaman,en kyawawan fararen guiwoyin ta a bayyane,duk tabi ta tsauwala sbd ta lura da kallon da saif keta yi mata.
Wanda koda suka gama sahur ya bar d'akin duk a jiqe yake jin kansa shiyasa yana zuwa d'akin shi ya gaggauta yin wanka.

Washe gari shi yakai ta school ya kuma d'auko ta.
Da shigar ta d'aki ta tu6e ta fad'a bathroom tayi wanka byn ta shirya snn ta tafi kitchen dmn girka musu abunda zasu ci idan ansha ruwa.
Saif yazo yayi tsaye a bakin qofar kitchen d'in yana kallonta,zarah bata san dashi ba se qamshin turaren sa da taji,ta juyo ta kalli bakin qofar kitchen d'in ta ganshi sanye da qananun kaya ya cire suit da alama wanka yayi.
D'an murmushi ya sakar mata haka ita ma snn ya qarasa gurinta tare da riqo waist d'inta ya d'an tafi da ita jikin sa yana kallon,tarugu tattasai da albasa da ta yayyanka tana d'an soyawa sama sama had'e da qoda da tayiwa gutu gutu,ya kalle ta yace"me zaki dafa mana ne?
Zarah dake motsa abubuwan da take soyawa tace"taliya ce zan dafa had'e da wake naga lokaci ya tafi"
Yace"wow that's my best food but sauran abubuwan da kika d'aura mene ne?
Ya tambaya had'e da kai hannun sa ya bud'e d'ayar tukunya wanda da saurin sa ya saki marfin yana yarfi da hannu.
Zarah ta kalle sa d'auke da er dariya a fuskar ta.
Saif da har ransa yaji zafi yace"dariya ma kike min kinji zafin wae,ya d'aura mata en yatsun sa kan kunci,se kuwa taji yatsun nasa da zafi,a hnkli ta kama hannun nasa tana dubawa har ma ta sami kanta da hura masa en yatsun nasa da taga sunyi ja.
Kafin take kallon sa cikin yanayin murmushi tace"kai d'in ne da kaud'i in bashi ba me yakai namiji da bud'e tukunya.
Murmushi kawai yayi ya koma kai hannun sa ze bud'e tukunyar yana fad'in "so nake inga abunda yake ciki"
Tayi saurin riqe masa hannu tana fad'in"meye haka zaka sake qone kan ka fa"
Saif ya kalle ta wanda shi kam ae qonewar yake so ya sake yi dmn ta sake hura masa iskan bakinta da yaji wani irin sanyi da dad'i na ratsa hannun sa har be so ta daina ba ma.
Wanda a hankli ya lumshe idanun sa tare da ware su a kanta yace"to gaya min meye a ciki?
Tace"d'ayar tukunyar farfesun kaza ne d'ayar kuma wake nake tafasawa.
Tayi mgnr ne tare da bud'e masa kowace tukunya ya gani.
Ya kama hannun ta yana dubawa yaga ita kam ba abunda yatsun ta sukayi duk da irin laushin su kuwa dan har ma tafi shi laushin hannu.
Zarah da ta fahimci dalilin kallon hannun ta da yake,a hankli ta zare hannun nata da ya kama,d'auke da murmushi tana fad'in mu d'in ne na daban aikin mu ne mun riga mun saba ba abunda wuta zata mana.
Au haba ae kuwa yanzun nn zan gwada in gani,saif ya fad'a tare da rungumo ta ta baya snn ya kama hannun ta zai kai a wutar gas cooker.
Da sauri cikin maqe hannu Zarah tace"Wayyo!
Ya saki hannun had'e da lakato hancin ta yana murmushi yace"matsoraciya nida da wasa nake miki to"
Murmushi kawai tayi tana kallon sa har ya fita daga kitchen d'in,snn ta maida hankalin ta gun aikin da take yi.

Da aka sha ruwa bayan sunyi sallah,a nn falo sukayi zaune kan rug suna cin abinci a plate d'aya,abun se yayi musu kyau kmr dama can sun saba.
Wa enda suna cikin cin abincin ne aka soma danna doorbell,saif ya tashi yaje ya bud'e qofa.
Jamil ne,saif ya masa iso ya shigo ya zauna yana me amsa gaisuwar zarah.
Yayinda saif yaje ya zauna a gaban zarah suna fuskantar juna wato inda ya tashi.
Invitation a hannun sa yana dubawa,snn ya kalli jamil da shine ya bashi invitation d'in yace"this coming Saturday za'ayi auren knn?
Jamil yace"eh"
Allah kaimu
Cewar saif kafin jamil ke cewa amin.
Wanda duk yana yin maganar ne da qyar cikin danne kishi,ganin tare ne fa suke cin abinci har ma wani dukan uku uku yaji gaban sa nayi.
Can ya tsinkayo muryar saif yana cewa zarah taje ta kawo masa abinci,yace"A'a am ok"
Daga haka ya miqe tsaye ze fita,saif yace"plz to ka d'an jira ni mana mu kammala cin abinci da akwai mgnr da nake son zamuyi"
Jamil da baya jin zai iya kallon su suna cin abinci tare yace"ok zan d'an fita na dawo kafin ku kammala cin abincin.
Saif yace"ok to"
Snn jamil ya tashi ya fita.
Zarah ta kalli saif tace"katin d'aurin auren sa ne?
Saif ya kalle ta yace"tukuna ae shi wacce zai aura ba a ko sake ta ba tukun"
Wani iri zarah taji zancen tace"kmr ya ba'a saki wacce zai aura ba?
Saif ya d'anyi murmushi yace"da gaske nake gaya miki ba a saki wacce zai aura ba yana jiran a sake ta ne snn suyi aure"
Zarah tayi er dariya tace"uhm kaima dai da wasa kake se kace baya da aikin yi zai tsaya jiran wacce aka aura wae har se an sako ta,ae komai sonda yake mata gwanda kawai ya haqura tunda har yaga an riga shi ita.
Saif dake kallonta yace"dan baki san yanda abun yake bane shiyasa,ita yarinyar tun lokacinda ya fara ganin ta yaji yana sonta,amma ita bata sani ba dmn bai ta6a gaya mata ba,yana shirin shigar da kanshi,kwatsam yaji za'a aurawa abokin sa ita,gashi abokin nasa sam baya son ta auren dole ne za'a masa da shi har yarinyar duk ba mai son juna,shine da yaji duk yabi ya rud'e ya gayawa abokin nasa irin sonda yake mata har ma ya buqaci ya bar mishi ita ya aura tunda shi baya so,duk da abokin nasa yayi mamakin sonta da yake haka yayi fafutuka na ganin cewa auren ya koma kan jamil,dmn shi kuma ya samu a barshi ya auri wacce yake so,amma se hkn be samu ba,duk jamil yabi ya damu,abokin nasa yace kar ya damu ya masa alqawarin ko bayan anyi auren ze sake ta ya aure ta dmn shidai baya iya zama da ita,ko zaman da zeyi da ita na d'an wani lokaci dan ba yanda zeyi ne kawai an turasasa mishi,amma burin sa bai wuce ya auri wacce yake so ba.
Zarah tace"Hm lallai abu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login