Showing 135001 words to 138000 words out of 145898 words

Chapter 46 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24742

tana yin fushi dani.
Sophie?
Jamil ya tambaya yana mai kallon saif.
Kafin yake cewa kana waya da ita ne?
Inafa ae duk kiran da na gaya ma tana min ban ta6a yarda na d'aga ba,and ba sau d'aya ba basau biyu ba zarah tasha ganin kiran nata amma bata ta6a ce min komai ba abunda ya mata ciwo shine had'uwar da mukayi da ita Sophie d'in a England.
Nan ya gaya mishi yanda abun ya faru har ma fushin da zarah tayi dashi a can.
Snn yaci gaba da cewa shine fa da naga jikin nata yayi sauqi ina mata zancen mu koma gida ta dawo da yin fushin kuma,ba irin rarrashin ta da banyi ba amma taqi ta haqura,ta dake akan ita lallai jikinta ne nake so ba ita ba,bayan kuma ba haka bane jamil ina sonta wlh,wanda na fahimci haka ne sbd irin yanda nake jinta a raina fiye ma da yanda nayi jin Sophie a raina.
Jamil dake sauraren shi yace"zarah baza ta iya fahimtar hakan ba saif sbd tun farko tasan cewa ba qaunar ta kake yi ba,kuma a ganin ta kunci gaba da yin rayuwar aure ne dmn farin cikin Abba dan haka duk wasu abubuwa da zaka mata dmn nuna qauna a gare ta zata d'auka ko duk dan jikinta ne kawai,tunda ita kanta ta kasa fahimtar cewa tana sonka bare har ta iya gano sonda kake yi mata.
Cikin girgiza kai Saif yace"zarah bata sona jamil amma ni tun kafin a barni na maida ta na fahimci cewa sonta ne nake yi ba wai a dalilin farin cikin Abba kad'ai yasa nake so a barni na maida ta ba,amma ita har yanzu banga alamar ta fara sona ba ma,kawai tana biye min ne akan abubuwan da taga ina mata shine ita ma take min.
Jamil yayi murmushi yace"hm saif knn kana nufin kaima yanda zarah ta kasa fahimtar kana sonta,itama ka kasa fahimtar sonka take yi,to idan ba sonka take yi ba kan me zata damu dan kun had'u da Sophie har tayi fushi tayi tafiyar ta.
Saif yace"to ae jamil wnn dole ne taji haushi sbd yanda na barta tana ta jirana,ni kaina nasan ban kyauta ba wanda ba komai ne yasa na tafi da sophie muka ke6ance ba sai dan in kawo qarshen komai mu haqura da junan mu taje tayi auren ta kawai itama tunda tana da wanda yake sonta,shine fa da qyar na rarrashe ta na samu har ta haqura koshi ina ganin ma kmr fushi tayi dan tafiyar ta kawai tayi bata ce min komai ba.
Amma ita zarah sai ta d'auka ko wani abu ne,wacce ashe har ta lura da wayar hannun Sophie irin tawa ce da na saya mata irin ta itama shine ta cire sim card d'inta,ta bani wayar ta kuma had'a min hadda zoben diamond d'in da na saya mata da bata ko ga irin shi a hannun sophie ba,amma duk ta had'a ta bani bata so wae inje inyi ta kayan iri d'aya nida sophie ita in daina sako ta a cikin mu.
Jamil yace"to ai nn zaka qara tabbatar da cewa tana sonka dan wnn duk kishi ne.
No jamil wnn fushi ne kawai,da zarah na sona ya kamata taji ba dad'i a lokacinda take ta ganin shigowar kiran Sophie a wayata amma na lura ko kad'an ban ta6a ganin alamun kishi a fuskar ta ba sai dai ma in muna kwance ta qara gyara kwanciyar ta a jikina ta hau bancinta.
Jamil yayi shiru can yace"sai dai ko tana 6oye kishin ne a ranta,amma ba makawa zarah na sonka dan wnn fushin duk na sonka ne takeyi,barinta akan hanya tana ta jiranka ba zai sa tayi tayin fushi da kai har haka ba.
Saif da yayi shiru yace"to yanzu jamil ya kake ganin zan samu in shawo kanta wlh ina cikin damuwa ko kad'an bana jin dad'in wnn fushin da take yi dani.
Jamil yace"kawai kaje ka qara bata haquri tare da gaya mata dalilin da yasa ka tafi da Sophie kuka ke6ance duk dan kana son ka kawo qarshen komai ne ba wai da wata manufa ba,maybe jin hakan zai sa ta haqura.
Saif yace"hm jamil ae na gaya mata hakan tun a England amma taqi ta saurare ni,ganin take kmr ina fad'a ne kawai duk dan in shawo kanta wai in samu jikinta haka take gaya min,da tasan yanda kalmar take min ciwo a rai wlh da baza ta gaya min ba,shekaran jiya fa waya na siyo mana nida ita iri d'aya bcos still bata kar6i wancan d'in ba har ma da wani zoben diamond duk na qara siyo mata wani amma da na kai mata ko kallon su taqi tayi,hakan na koma da abuna yanzu haka suna nn d'aki a ajiye,na rasa wane irin fushi ne da zarah.
Jamil da duk yaji tausayin abokin nashi ya numfasa yace"kasan bafulatanin mutum zuciya ne dashi sosai,haka kuma wani cikin yana sa baqin rai da fushi,ka mata uzuri ba mamaki sune suka tara mata a lokaci d'aya,amma yanzu jeka d'in dai idan still taqi ta saurare ka se ka dawo da akwai shawarar da zan baka.
"Ok to"
Saif ya fad'a tare da kama hanya ya nufi ciki.
Ya sami su umma da Abba zaune a falo suna kallon labarai,yaje ya gaida su cike da ladabi snn ya wuce sama zuwa d'akin su Nusaiba.
Abba da ya bisa da kallo ya kalli umma yace"ya kamata yaran nn su koma gidan su haka tunda dai Alhmdlh jikin zarah se qara sauqi yake.
Umma tace"maganar da nake so in maka knn Alhj ince ya kamata su koma gidan su haka dmn na fahimci saifudeen duk yabi ya rame kmr wanda yake cikin damuwa,shine nake zargin wai anya tun farko ba yarinyar nn zarah ce tace masa bata tashi komawa ba se taji sauqi,dan nasan halinta zata iya yin hakan.
Abba dake kallonta yayi shiru can yace"to yanzu dai koma mene ne kije ki gaya mata ta shirya tabi mijinta su koma,idan har ma aikin gidan ne bata iya yi se a samar mata er aikin da zata riqa taya ta.
Nan umma ta tashi ta haura zuwa sama,wacce da isar ta bakin qofar d'akin kafin tayi knocking kawai ta soma jin muryar zarah cikin fad'a tana cewa saif dake ta lalla6ata.
"Wai ni kam dear nace bazan koma ba ka rabu dani dan Allah,jiki na ne kake yiwa ba kuma zaka sake samu ba na gaya ma kaje can kuci gaba da yi kaida wnn er iskar baturiyar taka da kuka saba......tas!
Taji saukar lafiyayen marin da yasa ta saki qara ba shiri,wato har umma ta shigo d'akin basu sani ba,wacce ita ce ta mare ta d'in ta kuma je a fusace ta ciro wayar caji tayo gun zarah cikin tsoratadda ita awa zata duke ta,ae kuwa a tsorace cikin kuka zarah ta tafi da gudu bayan saif ta rirriqe shi tana fad'in"wayyo! Allah inna dan Allah kiyi haquri wlh bazan sake ba"
Umma bata saurare ta ba sai qoqarin janyo ta take a bayan saif,da duk yabi ya rud'e yana fmn kare zarah cikin bawa umma haquri.
Nan sai ga Abba ya shigo d'akin da saurin sa yana fad'in"lafiya me yake faruwa?
Umma ta nuna zarah tace"ka ganta er rainin hankalin nn ashe kuwa duk itace tace bazata koma ba,very stupid! har yana lalla6a ki kina d'aga muryar ki akan tashi ko,oya duqa maza ki bashi haquri ko yanzun nn na zazzane ki wlh!
Da sauri cikin kuka zarah ta gurfana a gaban saif tana bashi haquri,kafin saif ya iya yin komai Abba ya tashe ta yana kallon gefen kuncen ta da duk yatsun umma sun kwanta akai gurin yayi ja har ma gefen bakinta ya fashe da jini,ransa a 6ace ya kalli umma yace"maman yusra wae marin yarinyar nn kikayi ashe har haka bayan kinsan ba ita kad'ai bace"
Umma da itama duk ran nata a 6ace yake tace"to Alhj dan tana da yaron ciki se a riqa barin ta tana yin duk iskancin da ta ga dama har tana d'aga muryar ta akan ta mijinta,ta nuna zarah tace"wlh bari kiji in gaya miki kar ki kuskura in dawo d'akin nn in same ki ki d'auki duk wani abu da kika san naki ne kibi mijinki yanzun nn"
Nan kawai ta fita daga d'akin Abba ya bita da kallo kawai kafin yake maida duban sa gun zarah muryar sa cikin rarrashi yace"ya isa haka kinji daina kuka amma daga yau kar ki sake d'aga muryar ki akan ta mijinki ba kyau duk da nasan laifin sa ne koh?
Da saurinta ta girgiza masa kai alamar a'a.
Fuskar sa a d'aure ya kalli saif da yaga yayi saurin kallon zarah,yace"gaya min gaskiya nasan haka kawai zarah baza ta ce baza ta koma ba har tana d'aga muryar ta akan taka,dole kaine babban mai laifin.
Kafin saif yace komai zarah tace"Aa Baffa ba laifin sa bane fa nawa ne amma kayi haquri bazan sake ba.
Tana mgnr ne kanta qasa tare da hawayen da ke sauka akan kumatun ta.
Abba dake kallonta yace"to shikenan Allah yayi miki albarka,se ki shirya ku tafi nayi magana da umman ki akan za'a samar miki mai aikinda zata riqa taya ki aikin gidan kinji"
A hankali ta gyad'a masa kai tare da yi mishi godiya snn ya fita daga d'akin.
Nan saif ya qarasa gurinta tare da kai lallausan hannun sa ya share mata jinin da ke gefen bakinta,ta d'ago idanunta ta cike tap da qwallah tana kallon nasa idanun da sukayi ja suka sauya kala sbd marinda umma ta mata sosai yaji abun har ranshi,bare kuma se ya qara jin tausayinta da qaunar ta a ranshi ganin yanda ta maida laifin gabad'aya a kanta,a hankali ya rungume ta yana mai shafa gefen kuncen nata cikin rarrashi da bata haquri,amma se wani sabo kuka yaji ta fashe mishi dashi tare da qara shigewa sosai a jikin shi tana ta bashi haquri itama,dan tasan ita kanta ya cancanci ta bashi haqurin,kan yanda fushi ya d'ibe ta tayi tayi mai rashin mutunci a matsayin sa na mijinta da bai kamata ace tayi mai hakan ba,da ba kowane d'a namiji ne zai yi ta faman haquri yana ci gaba rarrashin ta har haka ba.
Ta d'ago cikin kukan da takeyi tace"Dan Allah dear ka rabu da wnn baturiyar wlh bana son huld'ar ka da ita"
Saif da ya fara yarda tabbas zarah na son shi yaji wani dad'i a ranshi.
Muryar sa a natse cikin share mata hawaye yace"nayi miki alqawari cutie bazan sake kulata ba dama can dan in kawo qarshen komai nida ita ne yasa har nayi lokacinta amma bazan sake ba kinji 4give me"
A hankali ta koma kan qirjinsa muryar ta a sanyaye tana fad'in"nima ka yafe min dear bazan sake ba"
Sosai ya qara rungume ta a jikin shi yana mai shafa gadon bayanta alamar ba komai ya wuce.
Suka d'an d'auki lokaci a haka snn ya d'ago ta yace"bari mu shirya mu tafi koh"
Nan ta gyad'a masa kai tare da zamewa daga jikin shi,taje ta bud'e wardrobe ta ciro kayanta ya taya ta suka saka kayan a akwati,ta zira qaton hijab d'inta suka fito,da kai tsaye d'akin umma suka nufa dmn suyi mata sallama kafin su shiga sai gata ta fito daga d'akin Abba,fuskar ta ba yabo ba fallasa ta kalli saif tace"zaku tafin ne?
Yace"eh umma zamu wuce "
Tace"to Allah kaiku lafiya,amma bari kaji in gaya maka kar ka sake bari wnn yarinyar tana ma fitsara kayi maganin ta wlh er rainin hankali bansan a ina kika kwaso iye shegen nn ba nikam.
Tayi mgnr ne tana mai kallon zarah cikin dalla mata harara wacce da saurinta ta sadda kanta qasa qwallah na qoqarin cika mata ido.
Saifudeen kuwa se cewa yake ayi haquri umma bazata sake ba.
Nan kafin umma tace komai se ga kiran Abba ya shigo a wayar shi bai d'aga kiran ba sai d'akin Abba da ya nufa.
Umma da ta bishi da kallo ta maida dubanta gun zarah da still kanta yana qasa muryar ta a natse tace"dama ina so in tambaye ki har yanzu bai daina kula wnn baturiyar bane?
A hankali zarah ta d'ago cikin yanayin shagwa6a tace"Aa ita dai keyi ta fmn kiranshi amma baya d'agawa ban sani ba ko a bayan idona yana d'aga kiran nata,dan da mukaje England har had'uwa mukayi da ita,yaja ta suka tafi wani gun acewar wai na masa haquri yana son zasuyi magana ne,to shine ni kuma se banji dad'i ba har nakeyin fushi dashi.
Umma tayi murmushi snn tace"to ae zarah indai wnn ne ae har Alhj ya gayawa had'uwar da sukayi da sophie d'in akan yana son ya yafe mishi kulatan da yayi tunda kinsan ya hanashi har ma yace bai yafe masa ba idan har ya sake kulata to shine yaga ya zama dole ya nemi ya yafiyar shi har ma yayi mai bayanin baiyi hakan ba sai dan yana son ya kawo qarshen komai shida ita sbd ta dame shi da kira,snn ko kwanaki da ya tafi England ae a kanta ne ya kashe waya sbd awayar ta tana iya ganin inda yake,da sam ya manta koda yaje har ma tana qoqarin zuwa inda yake ne se ya ankara ya kashe wayar da bai sake kunna ta ba sai da ya dawo kin kuma sani"
Tace"eh umma amma bai gaya min dalili ba"
To ae dan baya son 6acin ranki ne zarah dan haka ki kiyaye harshen ki kar ki sake bari fushi ko 6acin rai yasa ki riqa gayawa mijinki maganganu haka marassa dad'in ji ba kyau kinji na gaya miki.
A hankali zarah ta gyad'a mata kai.
Nan sai ga saif ya fito daga d'akin Abba da ya d'auka ko fad'a ne ake tayi mata tun d'azu.
Cikin marairai ce fuska yace"plz umma dan Allah kiyi haquri haka baza ta sake ba.
Umma tayi murmushi tace"to ae ina ja mata kunne ne dan na fahimci har yanzu yarinta ke cinta bayan gashi har ana qoqarin samar min d'an jika.
Kunya zarah taji har ma da saurinta ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta.
Saif kuwa sai kallonta yayi cikin murmushi snn yace da umma"to a daiyi haquri umma mu zamu tafi.
Nan sukayi sallama da ita suka wuce,yayinda su Nusaiba basu ko san da zasu tafi ba suna can d'akin umma ita da yusra har ma sunyi bacci.
Su saif kuwa suna fita suka sami jamil still yana nn,bayan sun qarasa gurin shi zarah ta gaisa dashi ta koma can jikin motar saif ta tsaya dan motar ba'a bud'e take ba ko key ma bai d'auko ba.
Tana jin su se faman dariya suke jamil na tayiwa saif sheri.
Nan dai ba 6ata lokaci sukayi sallama jamil yaja motar shi ya tafi saif kuwa yaje 6angaren shi ya d'auko makullin motar sa suka wuce.

Bayan sun isa zarah takai akwatin ta a d'akinta snn suka wuce d'akin saif.
Sukayi zaune suna cin gasasshiyar kazar su da suka siyo kan hanya suka had'a da fresh milk,bayan sunci sunyi qat snn saif ya tashi ya fad'a wanka.
Yana fitowa itama zarah taje tayi wankan.
Da akwai kayan baccinta a d'akin,wacce koda ta gama shirin bacci ta samu saif har yayi bacci.
Ta hau kan gadon sai kallon sa take jikin ta duk a sanyaye tana shafa gefen fuskar sa a hankali,tasan dole yana buqatar ta amma meyasa zaiyi bacci bayan itama sosai take jin kewar shi a ranta.
Hakan dai ba yanda ta iya ta kashe wutar d'akin tare da shigewa jikin shi ta hau yin bacci,saif da ba duk bacci yayi ba ya bud'e idanun sa a hankali yana kallonta wanda ba kada'an ba yayi kewar daddad'ar zumar ta,amma kuma baya son taci gaba da mishi kallon jikinta kawai yake so ba ita ba,bare ma yaji jikin nata da d'an zafi zafi zai zama takurawa idan ya neme ta.
Hakan yasa dolen shi shima ya haqura da abunda yake ji ya hau yin bacci.
Wanda dashi har ita sun kasa baccin kirki se faman juye juye suke tayi har safe.
[4/30, 8:49 PM] Billy giro😊: _Monday 30/04/2018_
*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*



By
*Billy giro😊*




*Dedicated to»»»Zarah gwandu*

This pages is urs Sumee and Barira ina mugun yinku cos ku na daban ne.
Luv u so much dearests😍.

*«»page«» 65_66*
Bayan sunyi sllr asuba ya bata magunguna tasha sbd yanda jikin nata duk ya qara yin zafi da ba komai ne ya qara mata hakan ba se rashin samun bacci isasshe.
Wacce tana gama shan magungunan tayi baccinta rungume a jikin saif da yake ta faman yawo da hannun sa akan cikinta yana ji awa ace cikin yakai wata tara domin ya qagu yaga abunda za'a haifar mishi.
Koda ta tashi daga bacci se ganin kanta tayi kwance kan bed saif ya fita baya nn,nn ta tashi tayi wanka ta shirya cikin qananun kayanta da ya siyo mata a England da sukayi matuqar yin d'as a jikinta tayi kyau se qamshi take ta zubawa.
Ta nufi kitchen tayi tsaye tana tunanin abinda zata musu na breakfast dan yanzu har abinci tana iya ci.
Tana cikin tunanin ne kawai taji an rungume ta a hankli ta baya,ko ba'a fad'a ba dear d'inta ne ta sani dan qamshin turaren sa kad'ai ya shaida mata hakan.
Ta juyo d'auke da murmushi tana kallon sa da kai tsaye ta sami kanta dakai bakin ta a nashi ta had'e tare da sakar masa lallausan harshen ta a nashi ya cafka sukayi kissing d'in juna snn ta zare bakin nata d'auke da murmushi tana kallon shi had'e da yi mishi ina kwana.
Cikin murmushi ya amsa snn ya shafo gefen fuskar ta haka ma d'ayan hannun sa akan cikinta yana tambayar ya jikin nata da kuma lafiyar babyn shi.
Kmr da shagwa6a ta tafi jikin shi tana fad'in"duk lafiya qalau yunwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login