Showing 9001 words to 12000 words out of 145898 words
wani abokin nikam ina jin kunyar Abba rnr da asiri zai tonu bansan da wane ido zan kalle shi ba dan haka tun yanzu ba hannu na ba qafa ta.
Kallon sa saifuddeen yayi tare da ta6e bakin sa yace"and so what ae ba dole sai da kai za'a d'aura auren ba,da kaina zan nemo dattijawan da zasu zama waliyan mu.
Jamil yace"Allah taimaka,nidai a ina ka sami meat roll d'in nn se ci kake ka hana min"
Yace"rnr auren mu da Sophie zaka ci har ka ture in kaje amma,a gidana na G.R.A da zan siya can za'ayi party Sophie ta tare a can.
Da haka yasa qafa ze ficewar shi,jamil ya riqo shi da sauri yace"ina zaka je kabar ni da had'iyar yawu wae"
Murmushi saifuddeen yayi tare da janye hannun jamil daga riqon da ya mishi yace"je gun umma tana kitchen ka kar6o mana namu gabad'aya"
Yace"Aa muje tare dai"
Da mamaki saifudden yace"au kaji min gidan baqon ka ne,Allah idan bazaka je ba ni tafiya ta zanyi inada abun yi patients na jira na.
"Gud abun er rashin nasifa ce"jamil ya fad'a kana ya shiga ciki ya kar6o nashi kad'ai,ya fito yana ci ko gefen saifuddeen be kalla ba yaje ya shiga motar shi ya wuce.
Saifuddeen dake kallon sa yayi murmushi tare da girgiza kansa snn shima yaje ya shiga tashi motar ya wuce,dan wanda yaci ma ya ishe shi.
Su zarah kuwa a cikin mota kafin su isa,sosai Nusaiba ta bata haquri,hkn yasa koda suka isa gidan hajiya fuskar su wasai kmr ba abunda ya faru.
Wacce ake kira da hjy ta tarbe su da murna tana musu lale marhabin.
Nan take kuma se tasha toka tace"ae na manta fushi ma nakeyi dake Nusaiba tunda kika dawo kaduna nake ta sauraren zuwan ki inji labarin ya kika baro mutan kaduna amma shiru har aka share sati biyu.
Da sauri Nusaiba ta ajiye saqon da umma ta basu taje ta rungume hjy tana fad'in"haba dai hjy yi haquri kin san islamiyya muke zuwa shiyasa snn kinsan baquwa mukayi marmarinta akeyi kafin azo kanki"
"au lallai wnn baquwar ina take ne in ganta dame ta fini"
Hajiya ta fad'a tare da janye Nusaiba daga jikinta tana kallon zarah wacce tayi qasa da kanta d'auke da d'an murmushi a fuskarta tana wasa da en yatsun ta snn muryar ta a hnkli ta gaida ta cikin harshen fulatanci.
Hajiya ta amsa tare da kama hannun ta suka zauna kan doguwar kujera ta dafa kanta tana kallon ta d'auke da murmushi tace"zarahn inna,jonta ka inna muyi accinni amin ma,no inna 6andu mako dama ko?
Zarah tace"eh owad'i dama sosai "
Hjy tace"to Allah 6eddu dama"
Zarah tace"Amin"
Nusaiba dake kallon su tana jin abinda suke cewa amma maidawa ne kawai bata iyawa.
Yusra dai kam komai bata ji se kallon su kawai da take fuskar ta a shagwa6e ta tafi jikin hjy wai se ta gaya mata me suke cewa,dan haka take da umma ba halin umma tayi waya da fulatanci tana kusa se ta ajiye mata rigima ita se an fassara mata me aka ce.
Hjy ta d'auke ta ta d'aura kan qafafuwan ta tace"to zan fassara miki amma meye alhaki na tunda mamar taki taqi ta koya miki nima bazan koya miki a banza ba"
Yusra tace"kawai ki fad'a zan baki koma me kike so"
Hjy tayi murmushi snn tace"to abunda muka fad'a shine:-ce mata nayi zaran inna,yanzu dai inna ta haqura ta bar mana ke,to ya kika baro inna jikin nata yayi sauqi?
Se tace min"eh taji sauqi sosai"
Nace to Allah ya qara bata lafiya
Tace Amin.
Shine kawai abunda muka ce ba gulmar ki akayi ba.
Ta fad'i hakane tare da lakato hancin yusra,yusra tayi dariya tare da qara lafewa a jikinta.
Zarah da Nusaiba kuwa murmushi kawai sukayi nn Nusaiba ta bawa hjy saqon da umma ta basu,hjy ta kar6a washe da baki ta bud'e se sama umma albarka take dan har ranta tana jin dad'in yanda tayi sa'ar suruka kmr umma wacce ko yaushe cikin son kyautata mata take.
Se guraren 8pm snn suka dawo gida.
Sun samu saifuddeen zaune shi kad'ai a falo yana jiran fitowar umma daga kitchen da taje had'a mishi ruwan Lipton.
Sau d'aya da suka kalle shi suka kauda kai suka wuce ko gaida shi basu yi ba da zarah har Nusaiba wacce ke rungume da yusra kan kafad'ar ta tayi bacci.
Har suka shige saifuddeen kallon su yake yana mamakin wane irin klr raini ne su ganshi su wuce ba tare da sun gaida shi ba.
Ya kalli umma ransa a 6ace wacce isowar ta knn ta fito daga kitchen yace"umma wae ni yaran nn zasu raina su shigo su wuce ba tare da sun gaida ni ba kuma sun ganni ba wai basu ganni ba.
Umma dake kallon sa tace"suwa knn?
Yace"Nusaiba da wnn banzar yarinyar mana bansan gidan uban wa suka fito a wnn lokacin ba"
Zama umma tayi tare da ajiye mug d'inda ke hannunta tana kallon sa a natse tace"kayi haquri zan musu magana basu kyauta ba,amma kai d'in ne ka cika masu tsauri saifuddeen,ita Zarah kwata kwata ma baka amsa gaisuwar ta"
Saifuddeen yace"ko bana amsa gaisuwar ta shine dan tsabar raini zasu shigo su wuce ni ba tare da sun gaida ni ba kmr statue ne ni,har su kalle ni su kauda kae,to daga yau ko gaisuwar Nusaiba d'in bana so,tunda akan wnn banzar yarinyar zata d'auki yin fushi dani.
Daga haka ya d'auki mug d'inda umma ta ajiye masa ya tashi ya fita ransa a 6ace.
Umma da ta bisa da kallo ta girgiza kanta kana ta tashi ta nufi d'akin su Nusaiba.
Fuskarta a d'aure take kallon su kowannen su yana qoqarin cire kayan jikin sa tace"kan me zaku shigo ku wuce ba tare da kun gaida yayanku ba"
Dukkan su shiru sukayi.
Tace"daku nake magana ko bakwa jina ne kun min shiru"
Nusaiba fuskar ta a d'aure tace"hln da mutum ne a falo mu bamu ga kowa ba"
Umma tace"bana son shashan ci Nusaiba wnn ba tarbiyar da na baki bace tun wuri ki sauya dan bazan d'aukar miki wnn shashan cin ba.
Ke kuma zarah shine har da biye mata ko!?
Zarah da ko kad'an bata son fad'a kmr zatayi kuka tace"inna ko na gaida shi fa ba amsawa yake yi ba"
Umma tace"Amma zarah ae na gaya miki ko baya amsawa kici gaba da gaida shi da sannu zae riqa amsawa kinji yi haquri"
Zarah ta gyad'a kanta yayinda Nusaiba ke cewa"umma se kinji irin zaginta da yake yi a d'azun da zamu fita dan kawai sun tashi cin karo ita da shi har da cewa ta bar gidan nn tunda bana ubanta bane,dana masa magana kan ya daina hkn be dace ba se ya dawo kaina yana ta min masifa.
Umma ta numfasa a ranta tana fad'in"ya ta iya da halin saifuddeen tunda gado yayi abun se addu'a"
Snn a fili tace"Duk abun da yayi dai yayanku ne kuyi haquri kuci gaba da mishi biyaya kunji,zan mishi magana ya rage masifar nn da yake muku.
Dukkan su gyad'a mata kai sukayi alamar sunji snn ta fita daga d'akin.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Thursday/08/02/2018_ *芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄 Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 7*
Washe gari Friday Abba,saifuddeen,jamil dukkan su suna cikin tsadadden farin yadi an dawo daga sllr juma'a suna zaune kan dinning suna cin abinci su duka har su umma dasu Nusaiba wa enda sun ci kwalliya tamkar zasu je gurin biki dan haka rayuwar gidan take,rnr Friday kwalliya suke yi sosai a kuma yi abinci na gani na fad'a iri iri daban daban sbd daraja ta wnn rnr.
Ba kad'an ba hakan na matuqar birge jamil shiyasa duk rnr Friday a gidan yake yin lunch dan matar mahaifin shi kam sam ba ruwanta da wnn,tun rasuwar mahaifiyar shi tsawon shekaru biyu rabon da ayi abincin kirki a gidan kullum kusan abu d'aya ake yi wato jellof rice.
Cin abincin suke amma gabad'aya hankalin jamil na kan Zarah,se kallon ta yake tana cin abinci a natse haka duk wani motsi nata a natse take yin shi wacce tana yin hakane gudun kar tayi wani abun qauyanci,saifuddeen ya balbale ta da masifa dan ba qaramin aikin sa bane,shi kam jamil dake kallon ta se yaba irin natsuwar ta yake a ranshi yana fad'in ita dai komai nata a natse take yinshi,haqiqa irin klr macen da ya jima yana nema ce,duk da cewa baqauya ce amma tana da dama a cikin qauyawa sam baya ganin tana abubuwan qauyanci,ko dan yana sonta ne.....to koma dai yaya ne shidai yana sonta a haka,ba kuma zai yi sakaci ba garin kallon ruwa kwad'o ya masa qafa.
lallai yau idan suka kammala cin abincin nn zai yi qoqarin snr da ita abunda ke ranshi koma ya sami umma ya snr da ita,dmn shidai cikin sauri yake son ayi komai.
Sbd jamil mutum ne da Allah ya d'aura mishi lalurar son aure sosai amma rashin samun macen da ta dace dashi yasa beyi auren ba se yawaita azumi da yake gudun afkawa zina.
Amma yanzu ji yake a ranshi kmr matsalar shi ta kusa zowa qarshe dmn zarah 100% ce a tsarin macen da yake so ftr shi Allah yasa Zarah ta so shi.
Wayar sa ce ta soma ruri koda ya duba mahaifin sa ne,a mutunce ya d'aga kiran cike da ladabi kmr mahaifin nasa na kusa,dan jamil mutum ne mai girmama iyayen shi sosai.
Bayan ya gama wayar ne yake snr da su Abba ze tafi Abban shi yana son ganin shi.
Umma tace"ae da ka bari ka kammala cin abinci indai ba kiran gaggawa bane"
Yace"Kd zamu tafi yanzun jikin kaka ce ya tashi"
"Subhannallah ciwon sweetheart ya tashi yi sauri tashi muje"
Cewar saifuddeen wanda ya tashi da sauri riqe da tissue yana share bakin shi.
Yayinda umma da Abba cikin jimami suka mata fatar samun sauqi tare da musu addu'ar Allah kiyaye hanya snn suka fita.
Suna fita yusra tace"nidai mama tun yanzu idan kakar yaya jamil ta rasu zan biki kd gaisuwa"
Dukkan su ido suka saki suna kallon yusra mama kuwa da hanzarin ta buge mata baki tace"ba bakin ki ba yusra kin kuwa san me kike fad'a!
Kuka yusra ta fashe dashi ta sauka kan kujerar ta ta tafi jikin Abba.
Abba ya d'auke ta ya d'aura kan jikin shi yana kallon ta yace"yusra kin kuwa san meye mutuwa,idan mutum ya tafi fa baya dawowa shikenan idan muka je kd baza ki qara zuwa gurin ta ba,dan ko kinje ma baza ki ganta ba ta tafi knn.
Yusra tace"to ae kaka ta tsufa in ta mutu aljanna zata je,a islamiyya malamin mu ya gaya mana ba abinda yakai aljanna dad'i duk abinda kake so zaka samu a can.
Abba yace"to shi malamin naku ce maki yayi idan mutum ya tsufa in ya mutum aljanna zai je?
Aa yadai ce mana idan kana yawan alheri ma zaka shiga aljanna kuma kaka mai yawan alheri ce a kd in naje gidan ta duk abunda nake so baza ta hana min ba bani take kuma me yawa.
Abba dake kallon ta yace"to ae yusra ba'a yiwa mutum ftr mutuwa dan haka kar ki koma kinji"
Kai ta gyad'a masa alamar taji,yayinda umma tayi murmushi tare da girgiza kanta tace"su qurci dangin hauka wai ita fa ganin tayi duk akayi rasuwa se ince bazan je da ita gaisuwa ba shine yanzu tun wuri ta gaya min kar ma ince bazan je da ita ba.....ni daina kallona"
Umma ta fad'a tare da hararar yusra dake kallon ta.
Ae kuwa da sauri yusra ta 6oye fuskarta gabad'aya cikin jikin Abba.
Nusaiba da zarah kam murmushi kawai sukayi suna kallonta.
Abba kuwa lalla6ar ta yayi ta tashi ta koma kan kujerar ta suka ci gaba da cin abinci.
Bayan sun kammala ne Abba ya zari tissue yana share bakin sa yace da Nusaiba"Monday ne hutun ku ze qare ko Nusaiba?
Tace"eh Abba dama ina son in gaya ma da akwai abubuwan da nike so a siya min kafin Monday"
Kafin Abba yace komai umma tace"ke Nusaiba bana son iya yi,me zaki siya keda ba boarding school kike yi ba,sa'an nn ba hutun first term ba.
Ba abinda kk buqata u have everything,kwalin biro qwara biyar fa kawai kika ta6a a ciki,socks da akwai su sabbi dal har qafa uku,books ba kya ma da buqatar su,idan ma lokacin buqatar su yazo school ke baku to me kuma zaki siya.
A d'an shagwa6e tace"Allah umma da akwai,sweets,chocolate biscuit,juice duk inada buqatar na zuwa school,kuma naga karon nn ba'a siya ba har yanzu.
Umma tace"wnn ae yusra keda buqatar su ke kin wuce gurin baza a qara siya miki ba.
Kmr zatayi kuka tace"haba dai umma"
Kana ta kalli Abba alamar yace wani abu mana.
Nan Abba ya kalli umma d'auke da murmushi yace"Maman yusra ki barta kawai ta rubuto duk abunda take buqata har na yusra d'in duk se a siyo"
Umma tace"Alhj ka manta irin yanda Nusaiba ke fama da period pain,in ta fara abun ba sauqi kai da kanka ma kace na kula duk wani zaqi ta daina sha,3months knn da farawar ta amma still ba sauqi har tea ma hkn nn take shan sa ba sugar"
Shiru Abba yayi yana kallon umma snn ya kalli Nusaiba wacce tayi saurin sadda kanta qasa idon ta tap da qwallah ita bata so a hanata.
Yace"kinji ko er baba mamanki ta fimu gaskiya amma za'a siyo miki kad'an se kisan yanda zaki riqa d'auka kina ci not any time ba....promise?
Ya fad'a yana me kallonta,da sauri ta d'ago bakin ta a washe tace"eh Abba i promise u"
Ta fad'i hakane tare da kai d'an yatsan ta akan nashi suka qulla alqawari kmr yanda ya buqata.
Kana ya kalli zarah yace"kefa Zarah me kike so?
Kanta qasa muryar ta a hankli tace"ba komai Baffa.
Yace"da akwai mana tunda kin gama secondary ya kama ta kije high school mkrntr gaba da secondary,ko kinfi so mu wanke ki mu kaiki d'akin mijinki"
Da sauri ta rufe fuskar ta da tafukan hannyen ta tace"Aa baffa ni bana son a min aure karatu nake so nayi"
Yace"gud Zarah zakiyi karatu sosai kuwa tunda kina so,and u Nusaiba anjima da dare bayan sllr isha'i se ku shirya keda zarah da yusra muje kowa ya siyo abunda yake so.
Godiya sukayi umma tace"au ni kuma na zama er gadin gida knn?
Abba dake kallonta yayi murmushi snn yace"inafa na isa ganin nayi qwalama ce siyayyar yara amma idan zaki je se ki shirya muje mu dukan mu"
Umma tace"Aa ni bana da buqatar komai da wasa nake"
Murmushi Abba yayi snn ya fita acewar ze je gidan hjy suka mishi Allah kiyaye tare da miqa saqon gaisuwar su zuwa ga hajiya.
8:30pm saifuddeen ya dawo gidan be sami kowa a falo ba hakan yasa ya haura sama zuwa d'akin umma ya mata knocking ta fito wacce tana fitowa tace"Aa saifuddeen kaine kun dawo?
Yace"eh umma amma ni kad'ai na dawo"
Umma tace"subhanallah knn jikin sosai ya tashi"
Aa da sauqi sosai fa asthmar ta ce ta tashi kuma ta d'an kwanta mata.
Umma tace"to Allah ya qara sauqi"
Yace"amin"
Snn yace"umma abincin mutum biyu nake so za'a samu?
Yayi mgnr ne tare da d'an sosa bayan kanshi hakan yasa umma ta kalle shi da kyau snn tace"kaida waye?
Yace"nida wani baqo na ne"
Cikin kallon tuhuma tace"hm kaida Sophie dai ko?
Cikin fuskewa yace"haba umma wace Sophien kuma abokina dai.
Gaban rigar sa ta nuna tace"wnn abun fa a ina ka same shi ko abokin naka ne ya maka"
Kallon gaban rigar tashi yayi,kiss馃拫ne rand'am a jikin rigar wato fararen kayan shi da still yake sanye dasu bai sauya ba duk jan jan bakin Sophie ya 6ata su .
Ransa a d'an 6ace ya lumshe idon shi kana ya ware su akan umma yace"oh umma me kuma yakai idonki a can plz,Sophie ce ta min kuma bawai da wata manufa ba"
Rai 6ace Umma tace"in banda iskanci da wace manufar ma to zata maka kiss iye ita mtr ka ce ko me! ta nuna shi da yatsa tace bari kaji in gaya maka saifuddeen muddin kace zaka biyewa lalaci irin na turawa to wlh zamu sa qafar wando d'aya nida kai,sam bazan yarje maka wnn iskancin ba tun wuri ka sauya...karatu a England hauka ne ae ga jamil nan naga tare kukayi karatun amma shi sam baya iskancin da kakeyi.
Cikin yanayin damuwa Saifuddeen yace"oh Allah! umma wlh abinda kuke tunani bashi bane,nifa ba yaro bane nasan abunda nakeyi"
Umma tace"shikenan tunda kai ba yaro bane kaci gaba da yin abunda kake in dai dai ne,and 6ace in daina ganin ka a nn kafin Abban ka ya dawo ya ganka da wnn abun kunyar a rigar ka.
Kallon umma kawai saifuddeen yayi ba tare da yace komai ba ya wuce kmr yanda tace.
Tabi sa da kallo har ya fita a ranta se addu'a take mishi Allah ya shirye shi.
Tana jin lokacinda yaja motar sa ya fita daga gidan,ta girgiza kanta kawai snn ta koma daga ciki.
Washe gari da safe guraren qarfe goma da mintina su zarah suka dawo daga islamiyya sbd dama da safe 8 suke zuwa su dawo by 10.
Da shigar su d'aki Nusaiba ko hijab bata iya cirewa ba ta fad'a kan bed dafe da marar ta