Showing 84001 words to 87000 words out of 145898 words
ta sbd da gani baccin yana mata dad'i sosai.
Hakan dai ya shiga bubbuga pillown ta a hankli can zarah ta bud'e idanunta cike da jin bacci tana kallon shi fuskar ta a yamutse.
Saif dake kallonta yace"ki tashi Abba ne yake son magana dake a waya"
"Baffa"
Ta fad'a tare da miqewa zaune tana kallon shi,kafin take kallon agogon bangon d'akin snn ta maida duban ta gare shi tace"uku na dare ne fa yanzun me yake faruwa?
Saif da ya shiga kiran numbar Abba ya kalle ta yace"nima ban sani ba na tambaye shi yace min ba komai,but kar6i waya kiji maybe ze gaya miki ne"
Nan Zarah ta kar6i waya gaban ta se fad'uwa yake kaddai wani ne ba lfy ko ya rasu.
A natse tayi sallama cikin girmamawa kmr tana a gaban Abba,byn Abba ya amsa sallamar yace"kina lafiya zarah are u ok komai ba abunda yake damunki"
Tace"eh Baffa ina lafiya"
Yace"mashaa Allah,Allah ya qara tsare lfyr ku keda abunda kk tare dashi,idan zaki koma bacci kiyi addu'a kinji"
Tace"to Baffa Nagode"
Daga haka ta bawa saif waya kmr yanda Abba ya buqata.
"Ka kula da zarah kar ka barta ita kad'ai kasan ba ita kad'ai bace tana buqatar kulawa"
Abunda Abba ya gayawa saif knn a lokacin da saif ya kar6i waya,saif dake sauraren sa yace"to Abba inshaa Allah"
Nan suka tsinke wayar yana me kallon zarah da itama shi take kallo,yace"me Abba ya gaya miki?
Tace"ya tambaye ni ne ina lfy,nace mishi eh yace to idan zan kwanta nayi addu'a"
Shine kawai abunda ya gaya miki?
Girgiza masa kai tayi ta sadda kanta qasa tana wasa da en yatsun ta snn tace"ya min addu'a kan Allah ya qara tsare min lafiya ta nida abunda wae nake tare dashi.
Saif dake kallon ta ya numfasa yace"olryt ki kwanta kiyi bacci inaga Abba mafarki yayi shiyasa duk hankalin sa ya tashi.
Nima abunda nake tunani knn amma meyasa yake tunanin ciki ne dani.
Ta fad'a tana me kallon sa kmr me tuhumar shi.
D'auke da d'an murmushi saif yace"tun wnn murar da kikayi ne fa har kika kwana a gida ya d'auka ko ciki ne dake ashe har yanzu be ajiye wnn tunanin ba"
Cikin rashin jin dadi' tace"Eyyah gaskiya tun wuri kasan yanda zaka yi ka gaya masa gaskiyar cewar wnn murar duk muguntar ka ce ba wani abunda nake da nikam,Allah sauwaqe ma inyi ciki dakai.
Ta qarashe maganar fuskar ta a d'aure,snn ta kwanta,se ganin saif tayi shima ya kwanta gab da ita had'e da rungume ta a jikin sa,da saurin ta ta tashi zaune tana fad'in"wae malam ni kam lafiyar ka kaffa ka manta ba gwanar ka bace kake a gabanta ni d'in ce dai er qauye da ka tsana.
Sosai saif yayi murmushi cike da so yana kallon ta yace"baki ji abunda Abba ya gaya min bane,ce min yayi na kula da ke kar na barki sbd bake kad'ai bace kinada buqatar kulawa keda babyna"
Nan ya shafo cikinta.
Ta ture hannun sa cikin dalla mai harara tace"haqqin Baffa se ya kama ka wlh idan baka gaya mai gaskiya ba nidai ba ruwana.
Nan kawai ta kwanta had'e da juya mai baya.
Saif da still murmushi na kan fuskar shi ya kwanta gab da ita ya rungumota yana fad'in"zan gaya mae amma se idan tare dake zamuje mu wargaza masa farin cikin sa tunda kinfi son haka....da sauri ta juyo tace"Baffa bai haifen ba amma na tabbatar na fika son farin cikin sa.
Ta doka mai pillow snn ta sauka daga kan gadon taje kan sofa ta kwanta.
Komai saif bai ce da ita ba still se mumurshi kawai da yayi snn ya rungume pillown da ta doke shi dashi ya hau baccin sa.
Koda asuba tayi zarah se ganin kanta tayi kan bed rungume a jikin saif.
A maimakon taji haushi se murmushi tayi tana kallon shi har ma ta sami kanta da d'aura hannun ta a sajen fuskar shi tana shafa shi a hankli har zuwa lips d'in sa,nn kawai ya bud'e idanun sa ta janye hannun ta da sauri ta tashi zata sauka daga kan gadon.
Se jin tayi ya fizgo ta ta fad'a gabad'aya kan jikin sa tana kallon sa ya kama lallausan hannun ta ya d'aura kan sajen fuskar shi yace"ni mijinki ne ki shafa ni duk inda kike so,kmr yanda nima zan iya shafa koina a jikinki.
Da sauri ta ture hannun sa da yakai yana shafa mamanta snn ta qwace daga riqon da ya mata ta sauka kan gadon ta wuce zuwa bathroom,saif da ya bita da kallo yayi murmushi snn ya sauke numfashi a hankli ya tashi ya fita daga d'akin yaje d'akin sa yayi arwala ya wuce zuwa masallaci.
Tuni zarah ta jima da ida sallah ta tashi tana linke darduma,saif ya shigo d'akin yaje a natse ya kar6i dardumar da ke hannunta yasa a wardrobe snn ya kama hannun ta yace"muje Abba ne yazo yana son ganin mu"
Kallon sa tayi haka shima ya kalle ta basu ce komai ba dai har suka sauka downstairs a nn falo suka sami Abba zaune kan kujera.
Zarah da sam ta manta saif riqe yake da hannun ta,sai da taga Abba na kallon hannayen nasu d'auke da murmushi snn hankalin ta ya bata tayi saurin zare hannun ta daga na saif snn ta durqusa har qasa cike da ladabi tana gaida Abba.
Wanda d'auke da murmushin farin ciki ya amsa gaisuwar ta tare da kama hannun ta ya zaunar da ita akusa dashi snn ya dafa kanta yana fad'in"Allah yayi miki albarka zarah, ya kuma kare ki da dukkanin sharrin maqiya,haqiqa naji dad'in yanda nazo na same ki lfy,ba kmr yanda mafarki na ya nuna min ba,sosai na tsorata shiyasa nayi gaggawar rubuta miki wnn addu'ar,ya zaro wata farar takarda a cikin aljihun jallabiyar sa ya bata yace"ki riqa yinta duk dare idan zaki kwanta bacci da kuma bayan sllr asuba idan kin sallame sallah bayan kin gama addu'o'in ki se kiyi ta daga qarshe,kariya ce daga dukkanin sharrin mutum da aljan,nayi wani mafarki ne da ya bani tsoro amma inshaa Allah hakan bazai faru ba ki kwantar da hankalin ki kinji,sam kada kisa damuwa a ranki,ban fad'a miki ba sai dan ina so ki dage sosai kada kiyi wasa da addu'ar.
A natse zarah ta gyad'a masa kai had'e da mishi godiya.
Yace"ba komai jeki abin ki"
Bayan ta wuce ne Abba ya sauke numfashi yana kallon saif dake gurfane a gaban shi,ya zaro wata takarda ya bashi yace"wnn ma wata addu'ar ce a rubuce,ta farkon ita ce zaka karantawa zarah bayan tayi bacci,ta biyun kuma hannun ka na dama zaka dafa cikin ta dashi se ka karanta addu'ar sau uku yayinda sautin addu'ar ke sauka a hankli kan cikin ta snn ka tofa kana mai shafe cikin nata gabad'aya,ina fatar ka fahimce ni?
"Eh Abba saif"
ya fad'a wanda yayi shiru yana kallon addu'oin da ke rubuce a kan takardar da ya kar6a daga hannun Abba.
Nan Abba ya miqe yana fad'in"ni zan tafi,anjima da qarfe goma ka same ni a gida ina son zamuyi magana.
Saif yace"ok to"snn ya tashi ya raka Abba har sai da Abba ya shiga mota ya wuce snn ya dawo ya tafi d'akin zarah ya same ta zaune kan bed still da hijab d'in sllr ta a jikin ta har qasa tana duba takardar da Abba ya bata.
Be qarasa gurinta ba se kallon ta kawai ya tsaya yana yi,haka ita ma ta d'ago tana kallon shi,ba wanda yace da wani komai se juyawa yayi ya fita daga d'akin.
Yau be bar driver ya kaita school ba shi da kansa ya kaita,ya dawo zuwa 10 ya tafi gida kmr yanda Abba ya buqata.
Bayan sun zauna Abba yace da saif"saifuddeen tafiya zanyi zuwa abuja da akwai taron da zamuyi a can na manyan likitoci,ga wnn ya miqa masa wasu takardu snn yace"takardun kadodarin ka ne da na mallaka ma,ya miqa masa wasu yace"wnn kuma takardun asibiti na ne da na mallakawa abunda zarah zata haifa ina fatar Allah ya kawo shi duniya lafiya ya kuma kasance rayayye me albarka.
Saif da duk jikin sa yayi sanyi ya kar6i takardun had'e da mishi godiya.
Abba yace"ba komai kana iya ka tashi ka tafi.
Nan saif ya tashi jiki ba qwari yana jin kmr ya koma ya gaya wa Abba cewa zarah bata da komai amma kuma ya Abba zai ji a yanda yasa ransa sosai d'in nn haka.
Nan ya juya ya kalli Abba bai ce masa komai ba dai ya koma juyawa ya haura sama zuwa d'akin umma.
Ya same ta zaune kan bed riqe da takardu a hannun ta itama.
Yaje ya zauna a hankli kusa da ita ya kar6i takardun yana dubawa duk takardun kadarori ne suma wanda ya mallakawa umma,Nusaiba,yusra har ma da zarah ya bata wani gidan sa dake G.R.A.
Bayan saif ya gama dubawa ya kalli umma yace"umma me yake faruwa ne duk Abba ya rabe mana komai nashi bana tunanin da akwai wani abun kirki da ya bari a hannun shi se dai ko kud'ad'en banki da ya bari kawai,ki duba fa asibitin sa gabad'aya da yafi ji da ita ya mallakawa abunda zarah zata haifa.
Umma dake kallon sa ta numfasa tace"nima dai ban san me yasa yayi haka ba,amma ita zarah halan tana da ciki ne da gaske da har zai mallakawa abunda zata haifa gudan asibitin shi?
Saif da duk ya samu kansa da jin nauyin umma ya sadda kansa qasa yace"a gaskiya umma ban ta6a kusantar zarah ba bare tayi ciki,kawai dai tun lokacinda tayi fama da mura har ta kwana a nn gidan,shine ya d'auka ko ciki ne da ita,ban san ta yaya zan fuskance sa in gaya masa gaskiya ba umma,gashi bana so yayi tasa rai a kan abunda babu daga qarshe yazo yaji haushina idan ya gano gaskiyar komai,bazan so haka ba umma ina tsoron 6acin randa Abba zai shiga.
Duk yana mgnr ne cikin damuwa da macewar jiki.
Umma dake kallon sa tace"nima dai har kullum ina son in gaya masa gaskiyar abunda na fahimta zarah bata da ciki amma ganin yanda yasa cikin sosai a ranshi da har kullum muka zauna mgnr cikin yake hkn yasa na rasa ma ta yaya zan gaya masa.
Shiru saif yayi se ga Abba ya shigo d'akin d'auke da sallama a bakin shi yana fad'in"to ni zan tafi bana son 11 tayi bamu fara hanya ba"
Nan suka fito suka rako shi a bakin mota,wanda har zai shiga mota se kuma ya tafi da saif jikin sa ya rungume shi a hankli yana fad'in Allah yayi maka albarka saif,haqiqa nayi matuqar farin ciki da kayi biyaya a gareni har ya kasance zarah tana d'auke da juna biyu,ina fatar Allah ya biya maka dukkanin buqatun ka na duniya dana lafira ya kuma baka 'ya'ya masu yin biyaya a gare ka,snn ya d'ago shi yana riqe da hannyen sa duka biyu a cikin nashi yana kallon sa yace"abu na qarshe da zan gaya ma saif,ko bayan raina ka rabu da zarah zanyi baqin ciki,burina kayi rayuwa da zarah rayuwa ta har abdah,ka riqe ta amana duk rintsi kar ka bar wani abu ya raba ku kaji.
A sanyaye saif yace"Inshaa Allah Abba bazan rabu da zarah ba har abada.
Wani irin dad'i Abba yaji a ranshi har yana qara sawa saif albarka.
Jamil da ya d'an jima da zowa yana tsaye a gurin wata irin zufa ce duk ta lullu6e shi da jin zancen da Abba yayiwa saif da kuma jin irin amsar da saif ya bawa Abba,ya samu da qyar ya danne abunda yake ji ya d'an russuna cike da ladabi ya gaida umma da Abba.
Jiki sanyaye umma ta amsa mishi dan haka kawai taji duk ta tsinke da lamarin Abba,wanda shi kam da fara'ar sa ya amsa gaisuwar jamil har yana tambayar sa mutanen gida,jamil yace"mishi suna lafiya"
Yace"ka gayawa Abban naka nayi tafiya ban samu na kira shi ba se na dawo idan Allah yace"
Yace"to Abba Allah ya kiyaye hanya"
Abba yace"Amin"had'e da shiga mota"
Alu driver yaja motar suka wuce.
Sai da motar ta fita daga gate d'in gidan snn umma ta iya komawa daga ciki.
Jamil kuwa kallon saif kawai yake ya kasa ce masa komai se juya wa yayi ya bar gidan d'auke da zazza6in da yaji ya kama shi lokaci d'aya.
_Sunday 25/03/2018_
*«»«»«»SAIFUDDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«»43,44,45*
Kallo kawai saif ya bisa dashi be tsaida shi ba se juyawa yayi ya koma daga ciki ya d'auko takardun sa kawai ya fito ya shiga mota tare da bud'e drawar motar ya saka takardun a ciki ya rufe.
Snn yaja motar ya tafi se asibiti bai sami jamil a can ba,hakan yasa ya bar asibitin yaje gidan su jamil d'in.
Wanda kai tsaye 6angaren sa ya nufa.
Koda ya shiga d'akin nasa ya same shi lullu6e da blanket qudundune se kakarwa yake kmr me jin sanyi.
Da sauri saif ya qarasa gurin sa ya yaye blanket d'in yana fad'in"what happen jamil?
A hankli jamil ya tashi zaune lokaci d'aya idanuwan sa duk sunyi jajur ya dafe kansa dake masa masifar ciwo,muryar sa da qyar yace"sorry maganar bazata yiyu ba yanzun kaina yana min ciwo sosai kuma ina jin zazza6i,ko anjima ne idan naji sauqi zan same ka a gida mu tattauna maganar akan clinic d'in mu ne dama.
Saif da ya fahimci dalilin zazza6in nasa yayi shiru yana kallon sa,can ya tashi ya d'auko masa magani da ruwa ya bashi yasha,snn ya taimaka masa ya koma ya kwanta yasa blanket ya rufa masa jikin sa tare da fad'in"Allah sauwaqe"
Daga haka ya fita tunani fal a ranshi,wanda gabad'aya haka ya kasance asibiti jikin sa ba qwari se bayan yayi waya da Abba ne yaji cewa sun sauka lafiya snn ya rage jin abunda yake ji.
Da su zarah suka gama lectures yaje ya d'auko ta suka dawo gida.
Koda tayi wanka ta shirya ta fito zata je kitchen ta sami saif shima yayi wanka sanye cikin qananun kaya na shan isa yana kwance rigingine kan doguwar kujera 3seater idanuwan sa a lumshe kmr me yin bacci ya kara d'ayan hannun sa a goshin sa,snn ya d'aura d'ayar qafar sa kan d'aya.
Ta kalle sa kawai ta wuce zuwa kitchen wacce har ta gama girka abunda zata girka ta fito still yana nn yanda ta bar shi,hakan yasa ta qarasa a hankli inda yake ta ajiye plate d'in abincin kan rug itama ta zauna kan rug d'in,ta jingina gefen jikinta a jikin kujerar da yake kwance snn ta kama hannun sa a hankali dake ajiye kan cikin sa.
Nan saif ya bud'e idanun sa ya tashi a natse tare da kama hannun ta ya zaunar da ita a kusa dashi yana kallon ta da kulawa muryar sa a hankli yace"ya akayi ne zarah?
Zarah dake kallon sa muryar ta can qasa a hankli tace"ba komai kawai naga tun lokacinda na fito zanje kitchen na ganka a kwance har naje na kammala abunda nake na fito baka tashi ba,baka jin dad'i ne?
Girgiza mata kai kawai yayi alamar a'a lafiyar shi qalau.
Ta zuba mishi ido tayi shiru tana kallon shi sbd a lokacinda ta kama hannun sa taji jikin nasa da zafi kmr baya jin dad'i.
Saif kuwa dashi kansa bai san abunda ke damun sa ba,ya kalli abincin da ta ajiye kan rug snn ya maida duban sa gare ta yace"da yawa kikayi abincin in zauna muci yunwa nake ji"
Gyad'a masa kai tayi snn tace"eh da akwai wani a kitchen na zuba a kula.
Nan saif ya zame daga kan kujera ya zauna kan rug tare da lanqwashe qafafu yana kallon abincin jallof rice ce da taji kayan lambu da qoda tayi kyau sosai se qamshi ke tashi dan zarah duk da rayuwar qauye tayi amma a gidan su lafiyayyen girki suke sbd duk wata umma se ta aika musu kayan abinci dama duk wani abunda zasu buqata,wacce tunda sukayi aure da Abba shine ke bata isasshin kud'in da zata samu ta yiwa en uwan ta hidima.
Saif beci abincin ba se kallon sa yake tayi cike da sha'awa har sai da zarah taje kitchen ta d'auko wani spoon da abincin da tace ta zuba a kula ta kawo ta ajiye dan wanda ke cikin plate d'in na mutum d'aya ne bazai ishe su ba,byn ta d'auko musu ruwa da lemu a fridge snn ta zauna suka hau cin abincin.
8:30pm tuni zarah tayi sallar isha'i har ta tu6e tana d'aure da towel zata shiga wanka se ga saif ya shigo d'akin d'auke da sallama a bakin shi,fasa shiga bathroom tayi ta juyo had'e da amsa mishi sallama tana me kallon takardun da ke hannun sa har ya qaraso gurinta ya kama hannun ta ya tafi da ita kan sofa suka zauna,ya bata takardun yana kallon ta a natse yace"takardun asibitin Abba ne da ya mallakawa abunda zaki haifa".
Da sauri zarah ta kalle shi muryar ta na rawa tace"ba dai wnn hadaddiyar asibitin da kaje dani yau ba"
Cikin lumshe ido ya gyad'a mata kai alamar eh.
Da sauri ta girgiza kanta qwallah tap a idon ta tace"A'a dan Allah kaje ka gaya wa Abba gaskiya,kar mu barshi yana tunanin abunda bashi bane,byn kuma rabuwa zamuyi kaga ya zama cutuwa.
Saif dake kallonta a hankli ya kama kumatun ta yana kallon ta muryar sa a natse yace"zarah still kina nufin kina kan bakar mu rabu,ba kya so mu faranta mishi,tunanin sa ya zamo gaskiya?
Shiru zarah tayi tana kallon shi sosai tana son su farantawa Abba amma bata jin zata iya rayuwa