Showing 123001 words to 126000 words out of 145898 words
hasken d'akin tasa pillow da sauri ta rufe jikinta ya kalle ta kawai d'auke da murmushi snn ya miqe ya fita daga d'akin.
Yaje downstairs ya sami umma tare da baqon da yazo dashi wato mijin mom d'in shi da yazo basu haquri da kuma jajanta musu abunda ya faru,wanda bayan saif ya same su sosai yayi ta qara bashi haquri yana bashi magana kan yayi haquri da halin mahaifiyar tashi halinta se addu'a.
Nan yayi sallama dasu ya fita umma ta kalli saif da ya dawo daga rikan shi tace"mutumen nn fa ya nuna damuwar sa sosai inaga belin matar tashi yake son yi ko?
Da sauri saif ya kalli umma yace"haba umma beli fa ei sosai yaji haushin abunda ta akaita shiyasa ma da isowar mu garin nn ya nemi in kaisa gurin ta,muna zuwa ya miqa mata takardar sakin ta se kuka take tana roqon shi amma fir yaqi saurarrar ta.
Umma tace"to Allah ya kyauta amma kai kuwa ina ka had'u dashi?
Yaje dubin Abba ne a England da kuma jajantawa Abban kd abunda ya faru shine da zan zo yace yana son kema yazo ya jajanta miki.
Bawan Allah
Umma ta fad'a snn tace"to ya jikin Abban naka duk da Alhjn kd ya gaya min se qara samun sauqi yake koh.
Gaskiya kam Alhmdlh umma sai dai muce Allah ya tashi kafad'ar shi ya qara bashi lafiya.
Umma tace"Amin Amin,amma kai kuma meyasa ka kashe wayar ka ka kuma taso baka snr da mu ba?
Wlh umma dole ce tasa na kashe wayar sbd Sophie duk inda nake tana sani a wayar ta haka nima,amma ni sam na manta sai daga baya kawai na lura ta samu ganin ina England har ma tana zowa inda nake tana bin direction shine kawai na kashe phone d'in amma ayi haquri umma"
Umma tace"ba komai me kake son a dafa ma dan nasan baza ka ci abincin da mukayi ba yau tuwon qullu ne d'an marmari da miyar ku6ewa d'anya ko kana so a kawo ma?
Yace"no umma ni ruwan Lipton kawai sun ishe ni"
Nan umma ta wuce kitchen dmn had'o mishi ruwan Lipton.
Saif kuwa ya shiga qwalawa Nusaiba kira wacce tana zowa yace"je ki cewa cutie ta shirya mu wuce gida"
Nusaiba tace"to"
wacce ko ba'a fad'a ba tasan Zarah yake nufi da cutie,tace"kae lallai mutanen nn da gaske suke nuna soyayyar su a fili,dama haka nake so wlh Allah yasa kufi haka qaunar junan ku.
Tana maganar ne a cikin ranta cike da jin dad'i har tana ji kmr tayi ta tsallen murna.
Kana taje ta snr da zarah aiken da saif ya mata,koda zarah ta gama shiryawa shima saif ya kammala abunda yake sukayi sallama dasu umma snn suka bar gidan basu zarce ko ina ba sai asibitin Abba.
zarah ta kalli saif da ya gama faka mota tace"halan har yanzu ba'a sallami yaya jamil bane?
Saif yace"eh amma se mun fara zuwa duba Alu driver tukun shi zaki kaiwa fruits d'in da muka tsaya kan hanya muka siya"
Tace"to yaya jamil fah?
Saif da sam baya da niyyar zuwa da ita gun jamil sbd ganin yake kmr zuwanta qara masa wani ciwon ne da shiga damuwa.
yace"kar ki damu muje kawai.
Nan ba musu ta fita sukaje A&E ward,koda suka shiga d'akin da aka kwantar da Alu driver en uwan sa na tare dashi wanda Alhmdlh jikin nasa ya fara sauqi har ma yana cin abinci akasin daa da bai ko san inda yake ba.
Bayan sun gaisa da en uwan nashi har ma sun musu ya mai jiki suka ce Alhmdlh snn suka koma kan Alu driver bayan sun mai ya jiki saif ya duba jikin nashi har yana mai en tambayoyi sbd dama duk idan yana asibiti shine mai kula dashi.
Nan bayan ya gama duba shi ya rubuta masa wasu magungunan a takarda ya bawa en uwan Alu driver d'in yace gobe da safe a siyo mishi magungunan,suka kar6i takadar had'e da kud'in se godiya suke tayi mishi sbd kudi'n sun fi qarfin na siyan magani,da tun zuwan su asibitin sisin su bai ta6a ciwon kai ba haka ma abinci ko yaushe umma ke aiko musu.
Fita saif yayi yace da zarah yana zuwa,jim kad'an se gashi ya dawo yace ta taso su tafi nn ta bar fruits d'inda ta kawo musu ta tashi suka fita yayinda en uwan Alu driver da shi Alu drivern suka bisu da godiya.
Zarah dake tunanin gun jamil zasu je se ganin tayi sun tafi gun mota bayan har sun shiga motar ta kalli saif tace"Dear yaya jamil fa banga munje duba shi ba kuma gashi har mun fito zamu tafi?
Yace"eh naje na samu an sallame shi yanzu gidan su zamu je"
Tace"yaji sauqi knn?
Eh yaji sauqi ba kmr farko ba dan koda naje England har kirana yayi a waya ya tambaye ni ya jikin Abba.
Tace"Ayya Allah ya qara bashi lafiya saif yace amin.
Daga haka sukayi shiru,basu sake cewa komai ba har suka isa gidan su jamil.
Saif ya kalle ta yace"kiyi zaman ki a mota zan gaya masa kina masa ya jiki"
Tace"meyasa bayan gamu har qofar gidan su amma bazanje in gaida shi ba."
Yace"sbd kitty tana gidan nn kuma duk na shiga a haukace take zowa gurina,shiyasa bana son ta firgita min ke dan haka kiyi zaman ki kawai kinji"
Ya shafo gefen fuskar ta tare da d'aura mata kiss kan goshi.
D'auke da murmushi Zarah tace"to ina masa ya jiki"
Yace"zai ji"
Snn ya fita daga cikin motar.
Bai wani jima sosai ba ta hango shi ya fito gate rungume da kitty a hannun shi sosai tayi du6ul du6ul ta qara girma yayi tsayin shi bai qaraso ba se Zainab dake tare dashi ta qaraso gurinta suka gaisa snn taje ta kar6i kittyn ta koma daga ciki shi kuma saif yazo yaja motar suka wuce gida.
Da isar su gida yana gama faka mota ya bud'e boot ya fito ya ciro akwati zarah ta fito itama tana kallon akwatin tace"kaida naga baka je da komai ba a ina kuma ka had'u da akwati"
D'auke da murmushi ya kalle ta yace"har kya tambaya to tsaraban cutie na ce"
Cikin yin murmushi tace"uhm kaima dai da wasa kake kaida kaje duba Baffa me zai had'a ka da tsaraba ina ma kaga wnn lokacin wata qil dai saqon wani ne kawo in kama ma"
Yace"Aa bud'e bayan motar dai ki d'auko ledar da na ajiye.
Nan zarah ta d'auko ledar suka shiga daga ciki,da kai tsaye d'akin saif suka wuce.
Ya ajiye akwatin hannun shi kan bed snn ya kalli zarah yace"ki bud'e akwatin kiga ni zanje nayi wanka"
Daga haka ya wuce zuwa bathroom.
Zarah kuwa sai da ta ajiye ledar da ke hannun ta snn ta cire mayafi tare da zama kan bed ta bud'e akwatin da duk qananun kaya ne a cikinta masu kyau da tsada sai d'aukar su take d'ai d'ai tana dubawa.
Sharp sharp saif ya fito daga wanka d'aure da towel a qugunsa sa ya samu sai ci gaba da duba kayan zarah keyi yaje ta bayan ta ya zauna ya rungume ta tare da had'e gefen fuskokin su yana kallon kayan yace"ya kika ga kayan?
Tace"gaskiya kayan sunyi kyau na waye halan?
Cikin qara rungume ta yace"da wa kika ga sunyi kama?
D'auke da murmushi ta d'an juyo ta kalle shi tace"ina zan sani kawai dai kayan sun min kyau sosai wlh har ma sunfi na cikin kayan lefen da nake sawa"
Yace"kinsan mijinki ya iya za6en kayan da yasan zasu yiwa matar shi kyau ta fito tana d'aga mishi hankali har ma ya riqa ganin sauran mata a maza ita kad'ai yake gani mace.
D'auke da er dariya zarah tace haba dai dear da gaske knn kana nufin kaya na ne?
A hankli ya lumshe idanun sa tare da koma ware su akanta alamar eh.
Cikin nuna jin dad'i tace"kae amma nagode sosai dear but su Nusaiba da umma banga ka kawo musu komai ba.
Yace"cutie kinsan ba zuwan da zanje in yi ta kwaso tsraba bane da ke d'in ma kayan ne suka min kyau naga bazan iya barin su ba.
Tace"to amma duk da haka ka barni in d'ibarwa Nusaiba ko kala uku ne"
Yace"A'a wad'an nn wa ke kad'ai na siyo su ki bari idan munje duk wanda zakiyi yiwa tsaraba sai ki mai kinji,bare Nusaiba wa zai barta ta sa kayan nn"
Zarah ta kalli kayan taga lallai fa in ba aure Nusaiba tayi ba,ba kayan da zata sa a gida bane is too hot da miji kad'ai za'a sama su.
Ta kalle sa tace"hakane kam amma wae ni kam har yaushe ka sami lokacin yi min siyayya?
Yace"wani abokina ne ya gayyace ni inje inga sabon boutique d'insa da ya bud'e shine muna zuwa naga gabad'aya kayan dake suka dace nn kawai bansan lokacin da na shiga d'ibar kayan ba se dariya yake ta min wae in daina haka banyi lokacin sa ba sae da na gama d'ibar kayan yanda nake so snn na bashi kud'in shi.
Zarah dake kallon sa tayi murmushi tare da qara yi mishi godiya.
Snn ta d'aura masa kiss gefen kunce kmr yanda ya buqata,haka shima ya d'aura mata kiss d'in yana murmushi ya tashi ya nufi dressing mirror ita kuma ta maida kayan a akwati ta rufe ta kaita inda ta dace.
Yayinda Saif take duk ya cika d'akin da qamshin kalolin turarukkan da yake ta feshewa jikin sa.
Zarah dai sai kallon sa kawai take har ya gama ya nemi boxer short n singlet ya saka snn ya kama hannun ta suka zauna ma cin kazar su da suka tsaya kan hanya suka siyo suna korawa da hollandia yoghurt mae sanyi,har sai da sukayi qat snn suka je bathroom sukayi brush.
Koda zarah ta gama shirin bacci tuni saif na kan bed ita kad'ai yake jira duk ya qagu dan tun d'azun jurewa kawai yake gabad'aya ya riga ya tayar wa kanshi sha'awar abun tun a gidan su umma.
Ae kuwa zarah na hawa gadon ya tafi da ita jikinsa tare da sanya hannun sa a cikin rigar ta ya kama abunda suka fi rikita shi wato na fulanin ta snn yakai bakin sa a nata ya had'e.
Kan kace minti goma tuni sunyi fatali da kayan jikin su se qoqarin faranta ran juna da suke musamman saif da yake yin komai cike da qwarewa har yana qara d'aura zarah akan wasu wasanni da take jin kanta awa jin nice d'in zai shid'ar da ita haka shima ihu ne kawai bai mata ba dan sosai tabi dashi yanda yake so.
Koda suka je ga babban aiki abun ba'a cewa komai dan zarah da kanta tasan cewa tabbas mijinta gwarzon gaske ne,yayinda shi kuma yake jin kmr kaf cikin maza shi yafi kowa sa'ar mace duk da ana cewa farar mace bata da wata n'ima to shi kam ya qaryata abun dan kuwa yau har second round sai da yayi.
Ae kuwa washe gari bacci sukayi sosai har sai da ya ishe su snn suka tashi.
Bayan sunyi wanka sun shirya saif da kanshi ya shiga kitchen kmr yanda ya buqata iyakar zarah ta nuna mishi abunda zai sa da haka har suka kammala breakfast d'in suka zo sukayi zaune kan rug suna ciyadda junan su kmr wasu luv birds.
Lol.
_Thursday 19/04/2018_
*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»page«» 60*
Suna kammala cin abincin zarah ta d'auko handouts d'inta tana karatu saif na qara fahimtar da ita.
Haka da dare bayan sunyi wanka sun gama cin grilled meat with soft drink,ta hau yin karatun ta har sai guraren sha biyu bacci yayi awon gaba da ita bata ko sani ba.
Saif dake can zaune kan bed yana wani aiki a laptop ya gama ya rufe snn ya taso yazo gun zarah dake kwance kan rug,yana d'aga ta a hnkli da niyyar zai maida ta kan bed,kawai ta farka ta tashi zaune a hankali ta tafi jikin shi tana fad'in"wae dear bacci nayi?
Yace"eh tashi muje kan bed"
Ta janyo handout d'inta had'e da fad'in"um um karatu zanci gaba da yi"
Ya kar6e handout d'in yana fad'in"no cutie karatun ya isa haka kinji"
Tace"um um dear wlh tun tafiyar ka ba abunda na karanta fa gashi gobe ne kad'ai baxa mu fara exam ba"
Yace"to amma cutie tun yaushe kike ta fmn yin karatun nn yi haquri muje kiyi bacci kinji gobe kyaci gaba.
Idanun ta rufe bata ko iya bud'e su sosai sbd bacci tace"um um dear ka banni result d'ina nake so yayi kyau in fi kowa"
Murmushi kawai yayi dan yaga abun nata kmr gigin bacci ne,ya kama hannun ta suka je kan bed suka kwanta ta wani shige qirjinsa kmr wata er baby mai shirin shan mamma wacce nn take ta koma yin bacci kafin shima yake biye mata.
Washe gari da asuba saif na bathroom zarah kuwa na kwance se sharar bacci take bai riga ya tashe ta ba tukun.
Se wayar sa dake ajiye kan bedside drawer ce ta soma tashin ta sbd qarar da ta shiga yi.
Da qyar ta iya bud'e idonta cike da jin bacci ta kalli gefen da wayar ke ajiye kafin take maida duban ta gun agogon bangon d'akin taga lokacin asuba yayi hakan yasa ta tashi zaune taja jikinta zuwa qarshen gadon tare da had'e kanta da guiwa tana son baccin ya d'an sake ta kafin saif ya fito daga bathroom dan taji alamun yana bathroom d'in bare kuma baya ko wucewa masallaci ba tare da ya tashe ba.
Jin kiran da ake mishi ya tsinke an kuma sake kira yasa ta d'ago ta kalli wayar ganin mae kiran yasa taji wani abu a ranta wato Sophie,kafin ta iya yin komai se ga saif ya fito da kai tsaye gun wayar tashi yazo yana ganin mae kiran ya kalli zarah da itama ta kalle shi kawai snn ta sauka kan bed d'in ta wuce zuwa bathroom.
Shi kuma bai d'aga kiran ba sai wayar ya saka silent ya bud'e bedside drawer ya sakata a ciki snn yayi shirin masallaci ya fita.
Koda ya dawo daga masallaci ita ma zarah ta ida sallah amma bata riga ta tashi daga kan darduma ba tana karatun qur'ani se bayan ta idar snn ta tashi da kae tsaye ko hijab d'in jikinta bata cire ba taje ta samu saif da ya kwanta kan bed ta kwanta a jikin shi had'e da yi mishi ina kwana.
A natse ya shafo gadon bayanta had'e da amsa mata gaisuwar snn yace"ina fatar cutie na itama ta tashi lfy?
Tace"lfy qalau na tashi se bacci da nake ji gashi kuma ina so inyi karatu"
Yace"cutie brain na son hutu fa ki bari idan kinyi bacci kin tashi snn.
Tace"Dear amma kasan karatu yafi shiga irin lokacin nn"
Haka ne amma baccin da kk ji bazai bar ki iya fahimtar komai ba gwanda kawai kiyi baccin.
Shiru tayi sbd sosai kam take jin bacci ko riqa handout d'in tayi ba lalle ne ta iya karanta abun kirki ba,da gabad'aya bata ganin da akwai wani abun da bata iya ba sai dai ta qara daddaqawa kawai.
Jin shirun yayi yawa yasa ya kira sunan ta snn ya kalli fuskar ta yaga ashe ma har baccin yayi awon gaba da ita,nan ya cire mata hijab d'in jikinta snn a hankali ya miqa hannun sa ya ciro wayar sa da ya saka cikin bedside drawer koda ya duba missed calls d'in Sophie sun fi a qirga yayi d'an guntun tsaki tare da cillar da wayar gefe,snn yayi shiru yana kallon silin kmr mai tunani.
Ranar Monday wato rnr da su zarah zasu fara exam tun wuri ta kammala komai ta shirya saif ya kaita school zata fita mota ya d'aura mata kiss kan goshi tare da mata fatar nasara,d'auke da murmushi tace masa amin had'e da d'aura masa kiss shima snn ta fita tana mai kiran frnds d'inta a waya taji ko sun shigo.
Saif da ya bita da kallo bashi yaja motar sa ba har sai da ya daina ganin ta snn ya wuce kmr dai kullum.
Koda suka gama exams d'in rnr saif sosai aiki ya masa yawa a asibiti be samu yaje d'aukar ta ba se drivern ta da ya tura mata.
Bayan ta dawo har tayi wanka ta girka musu abunda zasu ci,tana kwance kan bed ruf da ciki,as usual handout a gabanta tana karantawa daga ita sai er half vest a jikinta da d'an bum short na jeans,ta tufke gashin kanta da ribbon kmr wata baby doll yanda fakin d'in yayi sama,se wasa take da en qafafuwan ta a hankali tana ta yawo dasu.
Saif da ya shigo d'akin nata bata sani ba yayi tsaye se kallonta yake tayi can ya sauke numfashi snn ya qarasa gurinta a hankli ya d'an rankwafa tare da lotsa en yatsun sa kan arse dimples d'in ta.
Da sauri ta juyo tana ganin shine ta saki murmushi had'e da miqewa tsaye ta rungume shi a hankali tana mishi sannu da zuwa.
Ya amsa yana mai shafa gefen fuskar ta yace"ya exams?
Tace"wlh Alhmdlh sosai tayi sauqi ba kad'an ba se murna nake tayi ina roqon Allah yasa har mu gama exam d'in haka zamuyi ta jin su.
Amin my cutie Allah yasa,ya fad'a d'auke da murmushi har yana jan karan hancin ta.
Snn ya zauna cikin sauke numfashi dan duk agajiye yake,nn zarah taje ta kawo mishi ruwa masu sanyi yasha snn ta taya shi ya rage kayan jikinsa.
Ya kalle ta yace"je kitchen da akwai fruits na ajiye a leda ki gyara mana kisa a fridge suyi sanyi idan nayi wanka mukaci abinci se musha koh.
Ta gyad'a masa kai d'auke da murmushi snn ta tashi ta fita shi kuma ya tashi ya fad'a bathroom.
Koda ya fito ya samu har ta