Showing 60001 words to 63000 words out of 145898 words

Chapter 21 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24729

a ranta ganin yanda zarah take ta qara kyau da ko ba'a fad'a ba tana cikin qoshin lfy.
Se yamma snn su Nusaiba suka tafi ita da yusra.
Rnr lahadi saif yayi ta bud'an idon ganin zarah ta dawo amma shiru har ya kwanta bacci bata ba alamar ta gashi a gaban shi umma ta tura Alu driver yaje ya d'auko ta amma har washe gari shiru.
Bayan ya shirya zai tafi asibiti ya biya gida a tunanin sa ko ta dawo dare yayi shine bata sami komawa gidan nashi ba dan da shigar shi gidan ya sami motar da aka tura Alu driver yaje ya d'auko ta da ita.
Amma da ya shiga ciki babu alamar zarah d'in ta dawo dan bayan yaje d'akin umma ya gaishe ta yana fitowa ya tafi d'akin su Nusaiba be sami kowa ba su Nusaiba basa nn sun tafi school ya bud'e har bathroom wai ko zarah na ciki amma be ganta a ciki ba,jiki sa6ule ya bar gidan ba tare da ya iya tambayar umma ina zarah d'in take ba.
_Wednesday 07/03/2018_
*«»»««»SAIFUDDEEN!«»»««»*






By
*Billy giro😊*



*Dedicated to»»»Zarah gwandu*



*«»Page«» 31*
Tun yana ganin abun wasa wasa har aka share kusan sati bata dawo ba,duk ya shiga damuwar rashin dawowar ta da shi kan sa bai san dalilin hakan ba.
Wanda tunda umma tace mishi babu nasara akan yaudarar Abba da yake son ci gaba dayi se duk yaji bazai sake yin hakan ba,zai dai yi wani tunanin akai kmr yanda umma tace mishi,shiyasa yake mamakin to meyasa duk ya damu da rashin dawowar zarah da kullum se ya duba laptop yana kallon previous video d'in ta da be zauna ya gani ba.
Wani abun se ta bashi sha'awa wani abun kuma haushin kansa da tausayin ta yake ji dmn kmr kar yaga lokacinda ya bar mata kitty irin wahalar da tasha da qoqarin ganin cewa ta kula da ita,amma yana dawowa jin ta 6ata da kuma 6acin ran ganin tasha kashin ruwan sama be bar ya tsaya wani bincike ba kawai ya yanke mata hukunci,hukuncin da duk yaji ashe be kyauta ba,da ya duba abubuwan da suka faru a wnn lokacin da bazai yanke mata wnn hukuncin ba amma 6acin rai be bar yayi tunanin dubawa ba ma.
A hankali ya sauke numfashi tare da rufe laptop d'in da ke gaban shi wanda yanzu gabad'aya ya gama duba previous video d'in ta ba wani next abunda ze gani kuma.
Ya na rufe laptop d'in ya kwanta a natse tare da lumshe idanun sa,duk yabi ya rame kan damuwar da ke ranshi na tunanin mafitar samun auren Sophie da ya shiga yi kuma,wacce kullum cikin karanta saqonin da ta turo mishi a wayar jamil yake har kullum tana cikin damuwa da tambayar ya ake ciki dmn a tunanin ta amincewar da tayi zata musulunta shikenan ta kawadda duk wata matsala,take Abba ze amince ya bar su suyi aure se gashi taji shiru har kiran jamil take tayi a waya amma kullum abu d'aya ne,haquri kawai yake bata kan ta kwantar da hanklin ta,ta kasa samun ainihin abunda take son ji.
Gashi sosai take gudun sake causing d'in wata matsalar,daa saifuddeen zata kira taji komai daga bakin shi amma sanin irin kashe din da Abba ya mishi kmr yanda jamil ya mata bayani can farko yasa take tsoron ta kira shi,wacce ko texts d'in da take turowa a wayar jamil iya kan saif ya karanta yace duk abunda jamil ya bata replay is ok,dan sosai yake gudun furcin da Abba ya mishi kan duk ya sake kula ta be yafe mishi ba,shiyasa wani lokacin har numbar ta ze zauna yayi ta kallo yana jin kmr ya kira ta amma tuna wnn furcin kesa dole ya fasa.
Kana ya tashi ya sauka daga kan bed yana yawo a cikin d'akin wanda yanzu abunda yafi damun shi a gaba shine rashin dawowar zarah wacce rashin ta a gidan se yaji wani iri ba dad'i kmr dama can wani shiri sukeyi.
A ranshi yana tunanin dole ne yanzu yaje gida yayi magana da umma baya jin zai iya ta zuba ido haka kawai duk da dai ya kasa fahimtar abunda yasa duk ya damu da rashin dawowar ta amma yafi yarda cewa tausayin ta ne ya fara kamashi snn yana son yaga cewa ta dawo taci gaba da zuwa school.
Nan ba 6ata lokaci ya d'auki makullin motar sa ya tafi gida gun su umma.
Da shigar sa falon ya sami umma da Abba zaune kan rug sun jingina bayan su da jikin kujera 3seater,fruit bowl ajiye a tsakiyar su an yanyanka fruit d'in sunyi sanyi se fira suke suna shan fruit d'in cike da nishid'i.
Bayan ya gaida su yaje ya zauna a kusa da umma yana neman shigewa a jikin ta kmr wani qaramin yaro muryar sa a hankali yace"umma wai meyasa har yanzu yarinyar nn bata dawo ba bayan a gabana naga kin tura driver yaje ya d'auko ta.
Kafin umma tace komai Abba yace"Au ikon Allah wai umman taka bata gaya maka yanda akayi ba,ae da Alu driver yaje se ya samu zarah bata jin dad'i baza ta iya dawowa ba a rnr shine ya dawo ba ita.
Saif da yanayin damuwa ya d'an bayyana a fuskar shi yace"Amma Abba is gud ta dawo nn zata fi samun kulawa ina ne qauyen ni a gaya min inje"
kar ka damu ae idan taji sauqi zata dawo inna na kula da ita sosai.
Cewar umma wacce tasan zarah lafiyar ta qalau ba wani ciwo dake damunta,ta fad'i hakane kawai dan ta samu ta zauna kuma umma se bata matsa mata ba ta barta.
Saif yace"No umma idan har qauyen yana wahalar ganewa ne plz a had'a ni da Alu driver se muje is gud ta dawo ko dan school d'in ta.
Umma da ta d'auka yana yi ne dmn yaudarar Abba ta kalle sa kawai kafin Abba ke cewa shikenan ae Alu yana can tare da gateman suna fira se kaje ka mishi magana.
Nan saif ya tashi ya fita se qwalawa Alu driver kira yake wanda yazo da saurin shi yace"gani yalla6ai"
Kai tsaye saif ya jefa masa key d'in motar shi snn yace"oya muje ka kaini wnn qauyen inda ka kai wnn yarinyar amma mu fara zuwa gidan su jamil tukun dmn tare nake son zamu je dashi.
Alu driver da ya fahimci zarah yake nufi yace"to"
Snn ya tafi da sauri ya budewa saif ganbun mota na baya,saif d'in ya shiga ya zauna yana me waya da jamil.
Abba kuwa saif na fita ya kalli umma wacce tabi saif da kallo yace"kema kin lura da yanda yaron nn ya rame sosai ko?
Ae dole ne ya rame Alhj sbd yana cikin damuwar auren Sophie da ka hana mishi.
Abba ya kalle ta yace"ina fa ya isa yasa damuwa akan abunda yasan ba samun sa zai yi ba ae shi kansa yasan idan yasa damuwa akan hakan wahala kawai zai yi,ni nafi yarda cewa bai san sun shaqu da zarah sosai ba ne har se da tayi tafiyar nn yasan muhimmacin ta a kusa da shi gashi kina gani ma da kanshi yace ze je qauye ya d'auko ta wanda nn gaba se kinji ya daina zancen wnn baturiyar kwata kwata.
"Uhm Allah taimaka"
Cewar umma wacce daga haka bata sake cewa komai ba se shan fruit d'in ta taci gaba dayi haka shima Abba.
Su saif kuwa koda suka isa rimin dako kawun zarah suka samu a nn qofar gida qarqashin bishiya gishingid'e kan tabarmar kaba yana shan iska riqe da radio a hannun sa ya kara a kunnen sa yana sauraro.
Suka je cike da girgimawa suka gaida shi wanda se da ya kashe radio snn ya tashi zaune cikin sakin fuska yana amsa musu gaisuwar har yana tambayar su ya hanya ya kuma suka baro su Abba.
Jamil ne ya iya bashi amsa saif kuwa se kallon yanayin gurin yake da ma qofar gidan yayi mishi kama kmr ya ta6a zowa amma bazai iya tuna yaushe ne ba.
Wanda sam beyi mamakin nuna musu sani da kawun zarah yayi ba har yana tambayar su yasu Abba ya ajiye akan kawai Alu driver ya sani.
Bai san cewa kawun zarah ya san shi ba tun yana yaro amma se bayan Abba ya auri umma ne take zowa dashi ko shi sau biyu kacal,dan saif d'in ne tun yana yaro tsanar qauye yake a cikin ranshi shiyasa duk umma zata zo se yace mata baya zuwa be sake yarda ya biyo ta ba se dai duk lokacin da zata zo ta kai shi gidan hajiya da haka ba a wani jima ba aka tura shi waje karatu shine fa tun lokacin be sake dawowa qauyen ba se yau,wanda ko kawun zarah ba tun sanin yarin ta ne yasa ya gane shi ba,zuwa d'aurin auren da sukayi ne.
Nan suna gama gaisawa ya tafi dasu cikin gida.
Sun samu su zarah suma suna zaune a qarqashin bishiya innan dije ta sata a gaba tana mata kalaba,wacce duk ta kasa zama guri d'aya se motsi take tayi tana jin kmr ta fashe da kuka dan ko kad'an bata son kitso mugun ciwon sa take ji,ko yanzu dan an tursasa mata kan dole ne yasa ta zauna wacce tana jin dije ta ta6a mata kai ta juyo da sauri ta kai mata duka.
Dije ta fashe da wata irin dariya har tana duqawa,nn zarah ta miqe tsaye a fusace idon ta tap da qwalla tana kallon innan dije tace"mama wlh ki mata magana ta daina ta6a min kai"
Innan dije tace" fad'ima ae ni nace ta kama min ayi a qarasa miki naga se ciwo kk ji duk kin gaji amma yi haquri zauna baza ta qara ta6a miki kai ba ni kad'ai zan qarasa miki.
Kallon dije Zarah tayi wacce still bata daina mata dariya ba,ta dalla mata harara had'e da yin qwafa snn tasa ribbon ta dunqule kanta tace"ki barshi kawai mama nagode zan qarasa da kaina"
Daga haka tasa takalmi zata bar gurin se kici6us tayi dasu saif wacce sam bata san da zuwan nasu ba se ganin su kawai da tayi.
Ae kuwa ta tsaya cak tana kallon saif da shima ita yake kallo,wanda sosai ramar sa ta bayyana da lokaci d'aya ta fahimci haka,amma ba tayi tunanin me ya kawo masa ramar ba dan tasan damuwar da yake ciki,kawai dai tayi mamakin me ya kawo su dmn sam bata kawo wae saif yazo ne dmn ya koma da ita ba duk da dai ta ganshi tare da jamil,wanda kansa qasa ya tsiri danne danne a wayar shi sbd baya iya kallon zarah dake sanye cikin kayan fulani riga da zani yayinda rigar a d'age take ana ganin lafaffen cikin ta a bayyane bata saka rigar da ake sawa a ciki ba sbd zafin da ake,da sam ta manta da yanayin dressing d'in nata sai da ta kama saif yana kalla mata ciki snn ta tuna,ta bar gurin da sauri ba tare da iya ce musu komai ba ta shigewar ta d'akin inna.
Kawun ta dake tare da su a tunanin sa ko kunya ce irin tasu ta fulani yasa zarah ta kasa ce musu komai ta wuce,yayi murmushi tare da cewa"dije d'auko musu tabarma ki shimfid'a musu a nn qaraqashin bishiya baza su iya zama ciki ba zafi.
"To"
Dije tace wacce sai da ta gaida su snn taje ta d'auko sabuwar tabarma ta shimfid'a musu suka zauna snn ta kawo musu ruwa ta wuce yayinda ita ma innan dije tuni ta bar gurin bayan sun gama gaisawa da ita.
Bayan wucewar ta ne inna ta fito tare da kawun zarah da yaje ya snr da ita tazo gasu saifuddeen mijin zarah,wacce washe da baki cikin fara'a sosai take musu maraba ya hanya suka ce"Alhmdlh mun same ku lafiya?
Tace"lafiya qalau"
Yayinda lokaci d'aya saif na kallon ta ya fahimci ita ce wacce ya gani rnr sunje ita da wani har yace da gateman kar ya sake barin su su shigo mai gida.
Wacce se yanzu yake ganin yanda sukayi kama sosai da zarah har ya shiga tunanin ko mahaifiyar zarah ce duk da dai ya ganta tsofuwa.
Nan dai ya basar da zancen ya shiga snr dasu cewa sun zo zasu tafi da zarah ne da fatar taji sauqi.
Inna tace"sosai kuwa taji sauqi bari naje na snr da ita ta shirya.
Nan bata jira me zasu ce ba ta tashi ta tafi zuwa d'aki.
Kawun zarah kuwa ya shiga qwalawa dije kira kan taje ta kaiwa driver ruwa shima yana a waje,nn ba 6ata lokaci dije ta fito taje ta kai mishi.
Yayinda it kuma inna tana shiga d'aki ta snr da zarah abunda ke tafe da su saif.
Zarah tayi shiru tana kallonta a ranta tana tunanin baza ta gaya musu cewa tazo dmn niyyar kashe auren ta ba ne,zata yarda d'in ta koma,ba mamaki komawar ta zata fi samun damar yin abunda take tunani akan saif.
Nan kawai ta hau shirya kayan ta.
Snn bayan ta gama ta cire kayan fulanin da ke jikin ta ta shirya cikin atamfa.
Da zasu tafi dije ta riqa mata kayan ta ta raka ta har mota su inna da suma duk sun fito rakiya se Allah kiyaye hanya suke musu had'e da musu godiya akan alherin da su saif suka musu.
Alu driver da jamil sune a gaban mota zarah da saif su ne a baya.
Yayinda zarah tunda Alu driver ya tashi mota bayan tayi addu'a ta bud'o qur'ani a wayar ta ta soma karantawa a hankali cikin ranta,saif se kallon ta yake amma ita koda kuskure taqi yarda ta kalli ko gefen da yake,har suka isa garin kano kuwa bata yarda ta kalle shi ba se karatun qur'anin ta take tayi.
Da shigar su garin kano kae tsaye Jamil aka fara saukewa a gidan su,snn aka sauke su a gida.
Saif ya kar6i makullin motar shi had'e da ciro 5k ya bawa Alu driver ya kar6a yayi godiya ya tafi snn su kuma suka shiga daga ciki.
Zarah ta wuce d'akin ta shima haka wanda da shigar shi ya d'auro arwala ya fito ya tafi zuwa masallaci dmn yin sllr magrib da ake tayin kiraye kiraye.
Wanda bashi ya dawo gidan ba se 8:30,kai tsaye ya wuce d'akin zarah ga mamakin sa ya samu har tayi bacci,jiki sa6ule ya kalli takeaway d'in da ya siyo mata,ya qarasa gun bedside drawer ya ajiye takeaway d'in snn ya zauna a hankali kan bed tare da d'aura idon sa akan kalabar kanta da tayi kyau sosai wacce suna dawowa bayan tayi sllr magarib tayi zaune ta qarasa abunta dan kad'an yayi sauri.
Mamakin ganin an qarasa kalabar ne yasa saif ya d'aura hannu sa a hankli yana duba kalabar se ganin yayi ta bud'e idanunta tana kallon shi.
[10:31PM, 3/10/2018] ‪+234 816 253 8316‬: _Thursday 08/03/2018_
*«»»««»SAIFUDDEEN!«»»««»*






By
*Billy giro😊*



*Dedicated to»»»Zarah gwandu*



*«»Page«» 32*
Ya kauda fuskar sa tare da janye hannun sa a kan ta a hankali snn ya d'auko ledar takeaway da ya ajiye kan bedside drawer yace"tashi ga abinci kici"
Kallon sa kawai zarah tayi bata ce masa komai ba se blanket taja ta tafi dashi zuwa qirjinta ta rufe dan rigar baccin da ke jikinta santsi ne da ita sosai tsaf ake ganin yanayin qirjinta.
Saif kuwa ganin ba alamar tashi zata yi ta kar6a ba ya maida ya ajiye ya tashi ya fita daga d'akin,nan Zarah ta gyara kwanciyar ta dmn ci gaba da baccinta se kuma ta tuna abinci ba abun wulaqantawa bane gwanda ta saka shi a fridge in yaso da safe tayi warming ta bawa mai gadi dan dai bata da buqatar shi ita kam.
Nan ta sauka daga kan gadon ta d'auki takeaway d'in taje tasa a fridge ta dawo ta kwanta.
Saif dake d'akin shi yana kallon ta a laptop ya tsinci kanshi da rashin jin dad'in qin cin abincin da tayi,gashi ita kad'ai ya siyo ma abinci shi bai ko yi tunanin ya siyo ma kanshi ba duk da irin yunwar da yake ji kuwa.
Nan ya rufe laptop d'in yaje bathroom yayi wanka bayan ya fito yasha fresh milk snn yayi shirin bacci ya kwanta.
Washe gari koda yaje d'akin ta da niyyar tashin ta tayi sallah ya samu har ta tashi amma be ganta ba ta shiga bathroom.
Nan ya fita ya wuce zuwa masallaci.
Zarah kuwa bayan ta ida sallah,ta d'auko hand bag d'in ta ta ciro wayar ta wacce tun lokacinda suka iso tasa ta a ciki shine se yanzu ta ciro ta ae kuwa ta sami missed calls d'in umma har da na nusaiba sbd wayar a silent take shiyasa bata ji lokacinda suke kiran nata ba ga missed calls d'in ma tun jiya suke,ba kati a wayar ta se flashing da ta musu.
Ba 6ata lokaci se ga kiran su d'aya bayan d'aya wa enda ba wani abu bane so kawai suke suji ko sun iso lfy.
Byn ta gama waya dasu ne ta tashi ta hau share sharen gidan dmn idan ba kan lokaci tayi aikin ba,zata yi lattin zuwa school shiyasa take yin aikinta da wuri.
Kmr kullum idan ta shirya ta fita ta kan samu driver har yazo yana jiran ta amma akasin yau da taga wayam bashi ba alamar shi,wacce kafin tayi komai se ganin saif tayi ya fito riqe da makullin motar shi yazo ya kama hannunta se kallon sa kawai take har ya tafi da ita gun mota ya bud'e mata gidan gaba byn ta shiga ya rufe mata ganbun snn ya zagaya 6angaren driver ya shiga yaja motar bai zarce koina ba se school d'in su ya sauke ta snn ya dawo to 10 ya shirya ya wuce aikin shi.
Zarah kuwa bayan sun gama lectures taje ta siya kati ta kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login