Showing 6001 words to 9000 words out of 145898 words
ga wacce nake son in aura,bare idan yaji cewa ta gudo ne bada izinin iyayen ta ba matsalar zata fi yawa shiyasa kawai nake ce masa tukuna"
Shiru jamil yayi a ransa yana jin kmr ya bawa Saifuddeen shawara ya haqura da Sophie kawai ya za6i d'aya daga cikin en matan da ke rubibi akan shi tunda dukkan su musulmai ne kuma suna da kyau dede gwargwado.
Amma kuma sanin irin yanda suke qaunar juna da kuma sanin halin abokin nasa yasa dole zai bar shawarar a ranshi dmn fitar da ita wani babban abune da zai sa suyi fad'a.
Yace"is she still at d hotel ko ka samar mata gida?
Inafa ae bata so ka sani ita se nn d'in take so tazo ta zauna tare dani sam ta kasa fahimtar cewa mu da su ba d'aya bane,se da qyar na samu ta yarda zata ci gaba da zama a hotel d'in kafin na samar mana mafita,shine kullum se damuna take taji shiru wae ko dai tazo muje tare mu sami Abba.
Ya qarashe mgnr ne d'auke da murmushi a fuskar sa sbd zancen Sophie wacce da ta san halin Abba da koda kuskure bazata fad'i haka ba.
Shima dai Jamil murmushi yayi dan dukkan su sun san waye Abba snn qasar Hausa ne nn ba kmr qasar turawa ba,da akwai banbancin al'ada dama komai.
Nan ya jingina bayan sa a jikin sofar da suke zaune ya lumshe ido a ransa yana jin dad'i shi kam Alhmdlh yasan inshaa Allah Zarah bazata masa wahalar samu ba.
Bayan mako Biyu da faruwar haka ne Nusaiba ta shigo d'akin umma wacce dawowar su daga islamiyya knn.
Ta sami umma zaune kan bed tana qoqarin buga waya,taje ta zauna kusa da ita cikin yanayin damuwa.
Umma dake kallonta tace"lafiya Nusaiba me ya faru?
Cikin yanayin damuwar da take d'auke dashi tace"umma wae meyasa yaya saif kwata kwata baya amsa gaisuwar zarah,ko yaushe cikin mata kallon tsana ko ta mishi wani laifin ne?
Umma tace"ba laifin da ta mishi kin san halin yayanki se shi,tunda tazo gidan nn haka kawai ya d'auki karan tsana ya d'aura mata"
Tace"umma halan baki gaya masa cewa Zarah er uwar mu bace"
Umma tace"Abbanku ya gaya mishi se dai bana jin ya yarda ganin yake kmr er aiki ce,Abbanku ya fad'a ne kawai dan ya 6ata masa rai.
Nusaiba tace"umma to shine kika barshi yana ta kallon ta a er aiki"
Umma tace"Aa na gaya mishi ba er aiki bace kawai dai ra'ayin ta ne baya yi ya ganta baqauya"
Tace"gaskiya umma yaya ya canja halin shi beyi ba,ni bana jin dad'in abunda yake mata, ae ko ba er uwar mu bace ya kamata a matsayin ta na musulma ya riqa amsa gaisuwar ta shikenan dan tana baqauya ya wani d'auki karan tsana ya d'aura mata se kace bada qauye akayi birni ba.
Umma tace"to yayanki dai ne kisan irin mgnr da zaki fad'a akanshi"
Cikin turo baki tace"to umma kuma meye laifina a nn ae gaskiya na fad'a"
Bance ba gaskiya kika fad'a ba,kawai abinda nafi so dake shine ki tayani mu taya yayan naki da addu'a Allah ya sauya masa halin shi ya daina halayen sa da basu dace ba.
Nusaiba tace "amin"
Kafin umma ke cewa"snn abu na biyu da nake so da ke shine duk wani abu da zarah tayi na qauyan ci wato a yanayin saka suturar ta,kwalliyar ta ko mgnr ta duk ki riqa lura cikin hikima da dabara kina gyara mata ta yanda zata fahimci abun ta riqa gyarawa da kanta.
Nusaiba tace"Ae umma sosai zarah ke son ta zama er birni dan da kanta ma tace na riqa koya mata kwalliya gashi kuwa har ta fara iyawa,cikin ma muna zuwa islamiyya bama samun isasshen lakaci.
Umma tace"yayi kyau amma kar ki ga wae ke ke koya mata abubuwa kizo ki rainata bayan kuwa yayarki ce ta girme ki har da shekara biyu.
Nusaiba tace"haba umma ae kinsan bana da wnn halin"
Umma tace hakane na nasani Allah ya miki albarka,idan kinje d'akin naku ki turo min yusra tazo inji me aka musu yau"
Nusaiba tace"to"
snn ta tashi ta fita.
Da dare Abba ne zaune a falo shida umma dasu Nusaiba,zarah ce kawai bata gurin.
Se fira suke tayi abinsu suna kallo,se can Abba ya lura cewa Zarah bata gurin,a nn ya kalli nusaiba yace"wae Nucy ina zarah ne?
Nusaiba tace"Abba ae Zarah kunya take ji idan kana zaune a falo bata fitowa ta zauna ayi fira da ita.
Abba yace"ikon Allah ai ni se yanzu na fahimci duk zaman da mukeyi falo bana ganin ta,je kira min ita tazo maza"
Nan Nusaiba ta tashi da hanzarin ta taje d'akin su ta sami zarah zaune kan rug kusa da gefen gado ta lanqwashe qafafuwan ta tana duba littafan ta na islamiyya.
Taje kai tsaye ta kama hannunta tare da fad'in"zo muje Abba ne ke kiranki"
Da sauri zarah ta kalle ta tare da d'an ware idanuwan ta na alamar ni?
Nusaiba tace"of course tashi muje"
Nan zarah ta tashi suka tafi wacce suna isa falo ta durqusa cike da ladabi ta gaida Abba.
Cikin sakin fuska ya amsa snn yace"Zarah meyasa kowa na falo amma ke kin shige d'aki ke kad'ai baki fito anyi fira tare da ke ba?
Cikin yanayin jin kunya tace"ba komai Baffa"
Abba yace"ba wani ae Nusaiba ta gaya min wai kunya ta kikeji shiyasa ba kya zowo ayi fira dake ko"
A hankli zarah ta d'ago idanun ta ta kalli nusaiba se kuma tayi saurin sauke idanun nata qasa ganin iskancin da nusaiba ta mata na kashe mata ido d'aya tana son sata dariya"
Abba dake kallon zarah yace"ki sani ni Abbanki ne kuma nn gidan ku ne ki saki jiki ki zama er gida kinji na gaya miki"
A hankli zarah ta gyad'a masa kae yace"yauwa inace dai kina jin dad'in zaman gidan nn ba me takura ki?
Nan ma gyad'a masa kai tayi alamar ba me takura ta.
Yace"gud to tashi ku tafi kuyi shirin bacci dare yayi,Nusaiba d'auki yusra ku tafi"
Nusaiba ta d'auki yusra da tayi bacci kan qafafun umma suka wuce.
Nan Abba ya kalli umma yace"Zarah tace bamai takurata alhali kuma na fahimci duk lokacinda muke cin abinci saifuddeen baya son kallon inda zarah take kuma koda kuskure suka had'a ido se ya mata wani irin kallo na harara da saurin ta take d'auke idonta akan shi da alama tsoron sa ma take ji"
Umma tace"nima haka na fahimta amma kar kace masa komai musa musu ido kawai dmn da haka da hakane se kaga abun ya juye sun fara shiri da junan su har soyayya tazo ta shiga tsakanin su.
Abba yayi murmushi tare da fad'in"da nafi kowa farin ciki idan soyayya ta shiga tsakanin su dmn ina son Zarah ta kasance mtr saifuddeen Allah de ya yarda"
umma tace"Amin"
Kafin suke tashi suka bar falon.
Su Zarah kuwa suna zuwa d'akin su Nusaiba ta shimfid'e yusra kan bed d'inta.
Snn ta kalli zarah dake duqe tana tattara littafanta na islamiyya,bata bar ta qarasa ba taje ta kama hannun ta suka zauna kan bed tana kallon ta tace"Zarah meyasa baki gayawa Abba cewa yaya saif ko gaisuwar ki baya amsa ba se ma kallon banza da yake miki idan kika gaida shi.
Murmushi kawai zarah tayi tare da fad'in ba abinda zan gaya ma Abba bane wnn nida kaina zanyi maganin abun.
Daga haka ta tashi taje ta qarasa tattara littafan ta ta saka a cikin jakar islamiyyar ta snn takai jakar inda ya dace.
Nusaiba kuwa tun d'azu ta bita da kallo da d'an murmushi a fuskar ta kmr me son cewa wani abu se kuma bata ce komai ba ta tashi ta cire kayan jikinta ta fad'a bathroom.
Bayan ta fito ne itama zarah taje tayi wanka.
Da ta fito tayi shirin bacci cikin riga da wando soft silk,milk in colour snn ta saka hular baccin ta black ta net ta tura gashinta gabad'aya ciki kmr yanda taga Nusaiba nayi,dan Nusaiba ce ma ta bata hular sbd sun manta da suka je kasuwa basu siyo ba.
Bed ta hau zata kwanta Nusaiba dake kishingid'e kan bed d'in riqe da littafin addu'o'i tace"zaki kwanta gashi kin manta baki sa abu d'aya ba"
Nan Zarah ta shiga kallon jikinta tana son tuno mene ne taga dai har safa bata manta ba suna sanye a qafar ta,dan haka taga nusaiba nayi duk zata kwanta se ta saka socks a qafafuwan ta shine itama tace tana so Nusaiba ta bata,kuma sune ta cika mantawa dasu.
Nan ta nuna ma Nusaiba qafafuwan ta tace"kin gani ban manta ba yau"
Nusaiba tace"um um basu bane"
Zarah tayi shiru d'an yatsan ta kan lips d'inta tana kallon silin tana son tuna me ne ne.
Can ta kalli Nusaiba da sauri tace"brush ne kuma da naje wanka nayi ban manta ba"
Girgiza kanta nusaiba tayi alamar a'a snn ta dunqule en yatsunta na right hand tana moving da babban yatsan ta kan sauran tana zuwa da hannun nata a jikinta kmr me fesa turare.
Zarah dake kallonta tayi rolling eyes d'inta tare da d'an buga kanta a hankli,snn ta tashi taje ta saka turaren ta dawo ta kwanta,a ranta tana mamakin su birni in za'a kwanta bacci wai har da turare ake sawa,hm lalle sudai komai nasu na daban ne shiyasa suke ganin mutumen qauye wani iri wanda ko fita anguwa ze yi ba lalle bane ma ya saka turaren.
Ranar Thursday ta kasance basa zuwa islamiyya.
Guraren 11 suka shirya zasu je granny house,acan acan dasu sunyi kyau kayan su iri d'aya swiss less ne sky blue n baby pink yana cikin kayan sllr bara da Abba ya musu,sbd duk shekara tare yake musu d'inki iri d'aya.
Zarah hijab ta saka iya guiwa klr wanda ya dace da kayanta kmr yanda Nusaiba ta za6ar mata dan kaf cikin kayanta bata da gyale ko d'aya.
Nusaiba kam tafi ra'ayi da gyale shiyasa duk kayanta gyale sunfi yawa ko yanzu gyale ne ta yafa a jikinta,fuskar nn tata taci kwalliya kmr wacce zata je gasar kyau,haka ma zarah tayi er kwalliyar ta ta en birni da ta d'an fara iyawa kuma ba laifi tayi kyau dan Nusaiba ta d'an gyaggyara mata.
Tare zasu je da yusra wacce ke sanye cikin riga da wando en kati masu kyau se d'an qaramin veil dai dai ita da aka yafa mata aka.
Umma na Kitchen tana suyar meat roll wacce tana yin shi ne sbd a kaiwa hjy sbd tana son shi sosai.
Suka je suka same ta acewar zasu tafi,umma ta saki baki tana kallon en matan nata se yaba kwalliyar tasu take,kana ta miqa musu meat roll d'inda ta d'ibarwa hjy a d'an wani small midi tray da akayi wrapping ta basu tace"to gashi ku kaiwa hjy ina gaida ta,a dawo lfy"
suka ce to kafin suke barin kitchen d'in.
Sunzo zasu fita falo se ga saifuddeen ya shigo kad'an suci karo da zarah da sauri ta d'an ja baya snn a hankli ta sadda kanta qasa tana gaida shi.
Harara ya dalla mata tare da kallon d'an space d'inda ta bashi,ya daka mata tsawa yace"ke dan kin raina ni wnn d'an space d'in ne ze ishe ni na wuce!da Allah ni matsa min er iska!ae ko zan ra6i mace in shafi jikinta ba irinki kucaka ba,an saba iskanci a qauye shine aka zo nn birni ma anayi.
Ya nuna ta da yatsa yace"to bari kiji in gaya miki koda kuskure kika qara min irin haka marin ki kawai zanyi wlh! and u better leave this house tunda bana ubanki bane,very stupid!
Zarah wacce tunda ya soma masifar shi tayi saurin matsa mishi snn da daga baya ta fita sum sum janye da hannun yusra qwallah tap a idonta dan sosai taji zafin kiran ta da yayi er iska,ita sam bata lura gurin da ta bashi baya isar shi wucewa ba,kai bare masifa ce kawai irin tashi ze wuce tsaf ba tare da ya shafe ta ba ma.
Saifuddeen kuwa yana kai qarshen zancen shi yasa qafa ze fice Nusaiba tayi saurin tare shi tana kallon sa cikin marere ce fuska tace"haba yaya abunda kake yi be kamata ba Zarah fa er uwar.....da saurin sa ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu ransa a 6ace yace"keep ur mouth shut!wlh kar in koma jin kinyi gigin alaqanta ni da ita and 6ace in daina ganin ki a nn very stupid!
Qwallah ne suka ciko a idon Nusaiba jikinta a sanyaye ta ra6a ta gefen sa ta wuce.
Saifuddeen ya bita da kallo yana fad'in"dan kin rainani ni zaki zo kisa a gaba kina gaya min abunda ya dace akan wata banza can wacce ba mamaki compassion ne kawai irin nasu Abba suka tsinto ta wani gun suka kawo a wani ce munada relative da ita.
Mtsw yaja tsaki ya nufi hanyar kitchen sbd kiran da yaji umma ta mishi tana tambayar sa shida waye.
Sai da ya shiga kitchen d'in snn yake gaya mata shida Nusaiba ce dake son 6ata mishi rai kan wnn banzan yarinyar.
Murmushi kawai umma tayi tare da girgiza kanta,a ranta tana addu'a Allah ya sauya mishi halin shi.
Saifuddeen kuwa yace"wow meet roll kike yi umma"
Kafin tace komai yasa hannu a cikin matsamin deep frayer ya d'auki d'aya dan shima yana son shi sosai.
Ba shiri ya saki yana yarfi da hannu kmr qaramin yaro ya kalli umma yace"umma kice min it's very hot"
Murmushi umma tayi snn ta zari tissue ta saka mishi a ciki tana fad'in ae punishing d'inka ne nayi ka kami er qanwar ka se fad'a kake mata"
Saifuddeen da ya kar6a yace"umma Nusaiban ce ta cika katsalandan ai banso na mata fad'a ba,bata ji ne to"
Nan yakai meat roll d'in a bakin sa yaci yace"uym umma yayi dad'i sosai a ajiye mana nida jamil kinsan shima yana son shi"
Tace"to"
kafin yake tambayar ta ina Abba ya kira sa ne yace yana son ganin shi.
Tace mishi yana d'akin sa.
Nn ya bar kitchen d'in ya tafi sama zuwa d'akin Abba.
[11:13AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Wednesday/07/02/2018_
*芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 6*
Nusaiba kuwa tana fita ta hango jamil ya tsaida zarah yana tambayar ta me aka mata take yin kuka.
Ae kuwa se ta had'iye nata kukan snn ta qarasa gurin su ta d'an saki fuska ta gaida shi.
Jamil kam be iya amsa gaisuwar ba se tambayar ta yayi me aka ma zarah take yin kuka dan yaga zaran taqi tace dashi komai.
Nusaiba tace"ba komai cin karo ta tashi yi ita da yaya saif shine ya mata fad'a bayan kuma bada gangan bane"
Tsaki yayi cike da damuwa snn yace"na rasa me yake damun saifuddeen wlh hatta baquwa ma baya raga ma wane irin abu ne wnn mtsw....
Plz Zarah kiyi haquri kinji"
Ya fad'a cikin muryar rarrashi yana me kallonta,
a hankli ta gyad'a masa kai alamar ba komai.
Ya kalli Nusaiba yace"ina zaku je ne?
Tace"Granny house zamu je"
Yace"muje na sauke ku to"
Tace"Aa wlh da ka barshi driver ze kaimu ka ganshi har ya fitar da mota mu kad'ai yake jira tun d'azu "
Ta qarashe mgnr ne d'auke da d'an murmushi a fuskarta,shima jamil yayi murmushi yace"to a gaida hajiya"
Tace"to zata ji"kafin suke wucewa"
Ya bisu da kallo har sai da suka shiga mota suka wuce,snn ya sauke numfashi a hankali tare da ciro wayar sa a aljihu ya kira saifuddeen,bai d'aga kiran ba se qatse kiran da yayi hakan ya bashi cewa yana tareda Abba ne.
Nan yaje ya jingina a jikin motar sa yana jiran fitowar sa.
Jim kad'an se gashi ya fito yana cin meat roll har ya cinye wancan ya sake kar6o wasu biyu a gurin umma.
Ya qaraso gun jamil yana fad'in"ae na d'auka office kaje baka same ni ba ashe nn kazo"
Jamil yace"ae kam office naje ban same ka ba nasan kana nn gida shine na biyoka"
"To da ka biyo ni me zan maka?
Ya fad'a yana ci gaba da cin meat roll d'inshi.
Jamil yace" Sophie ce ta same ni office tana kuka wai jiya kunyi fad'a na baka haquri"
D'an ta6e bakin sa yayi yace"Sophie ta kasa fahimta ne jamil,ita lallai fa se munje mun sami Abba snn ta gaji da zaman hotel gurina zata dawo da zama a nn gidan,kullum se ta dame ni da zancen nn tun ina lalla6ar ta har jiya ta ban haushi na mata fad'a.
Jamil yace"saifuddeen dole ne ta dame ka ta fa bar iyayen ta cikin tashin hankli ta gudo ta bar su sbd kai"
Yace"to ae nima cikin tashin hankali nake ban san ta ya zan tunkari Abba da zancen ba kullum cikin tunanin neman mafita nike ta bar ni inji da abu d'aya mana haba,ae tunda nace zan aure ta zan aure ta ko a 6oye ne.
Jamil dake kallon sa yace"ko a 6oye ne?
Of course dan na tabbatar ko na gayawa Abba bazai barni na aure ta ba gwanda kawai na aure ta a 6oye,se ka shirya next coming week zamu je a d'aura mana aure nida ita.
Jamil yace"hum amma dai da wasa kake ko?
Hararar sa saifuddeen yayi yace"na ta6a maka wasa irin wnn"
Jamil yace"baka ta6a ba amma baka gudun Abba yaji"
Sai dai in kaine munafikin.
Saifuddeen ya fad'a.
Jamil yayi shiru yana me kallon saifuddeen yasan tabbas tunda ya fad'a ze aikata d'in yace"to bada ni ba ka nemi