Showing 54001 words to 57000 words out of 145898 words

Chapter 19 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24734

rug,Abba yace"A'a zo nn zarah ki zauna inji ya jikin naki yake"
Yayi mgnr ne tare da nuna mata kusa dashi kanta qasa ko kallon su bata iya yi taje ta zauna a kusa da shi d'in,ya dafa goshin ta se kuwa yaji zafi kmr da gaske d'in bata da lafiya haka ma kukan da tasha ya nuna fuskar ta kmr wata mara lafiya.
Sannu ya mata tare da kallon saif yace"tana yin amai sosai ne?
Yace"A'a bata amai zafin jiki kawai ne kuma da zarar tasha magani tayi bacci koda zata tashi komai ze dawo mata normal.
Abba yace"to shikenan zo maida ta ta samu tayi baccin mu zamu koma Allah ya sauwaqe"
Kmr da gaske yaje da kulawa ya kamata umma da Nusaiba se sannu suke mata,snn ya haura da ita sama su kuma suka fita.
[8:18PM, 3/5/2018] ‪+234 806 812 5769‬: _Friday 02/03/2018_
*«»»««»SAIFUDDEEN!«»»««»*






By
*Billy giro😊*



*Dedicated to»»»Zarah gwandu*



*«»Page«» 28*
Suna isa d'aki ya tunkud'e ta daga jikin shi yana kallon ta fuskar sa a d'aure yace"cika ni kin wani liqe min a jiki matsoraciya kawai next time ba qazamin baqon naki ze dawo ba ko uban sa ne se na koya miki hankali,in gidan ku ba'a koya miki yanda zaki fiddowa babba magana ba ni nn zan koya miki.
Yayi qwafa tare da zuwa gun wardrobe ya miqa hannun sa ya d'auko makullin bathroom snn yazo ya zare na qofa ya fita dasu.
Binsa kawai zarah tayi da kallo snn taje jiki sa6ule ta kwanta a hankli kan gadon tana jin kanta kmr wata marar lafiya,duk ta qarar da d'an qarfin ta a gurin kokawar qwatar kanta daga saif,numfashi ta sauke a hankli cike da godewa Allah da ya ku6utar da ita yasa On d'in nn ya sake dawo mata duk da dai silar dawowar shi tsoran da taji ne,and tana ji a jikin ta kmr ta ku6uta daga muguntar saif knn,indai har Allah yasa On d'in be d'auke mata ba har lokacinda zata tafi rimin dako.
Tana nn a nn kwance gurin bata sani ba bacci yayi awon gaba da ita.
Ba ita ta farka ba se 11 ta samu da qyar ta miqe zaune dan jin jikin nata take kmr wacce aka yiwa duka,ta kafe idanunta tana kallon jikinta a ranta tana tunanin ya akayi bacci ya d'auke ta bata shirya kanta ba gashi duk jikinta ya lallace,fuskar ta a yamutse kmr me qyamar kanta ta tashi tare da cire bedsheet d'in gadon ta nufi bathroom bata fito ba sai da tayi wanka,tana d'aure da towel taje ta bud'e wardrobe ta ciro kayan bacci ta saka,taje da niyyar zata kwanta se jin take jiri na d'an d'ibar ta dan yunwa take ji sosai tun fresh milk d'inda tasha da safe ta bar gidan bata sake sa komai a cikin ta ba sam tama manta se yanzu take tunawa kan yanda cikin ta ke faman qugi ba sauqi.
A hankali ta shafi cikin ta yanda take jin yunwar nn abu me d'an nauyi ya kama taci amma bata jin zata iya fita ta girka wani abu a cikin daren nn,da akwai Freshmilk a fridge taje ta bud'e ta tsiyaya a cup tasha me isar ta snn taje ta kwanta se bacci.
Washe gari guraren goma saif ya fito cikin shirin sa na suit chocolate brown,ta cikin ce kawai milk amma tun daga ta sama,wando belt har takalmin duk chocolate brown ne,yayi kyau sosai se zuba amshi yake.
Yana riqe da makullin motar shi ya fita,se hango drivern da ke kai zarah school yayi tare da gateman suna zaune guri d'aya se fira suke tayi.
Drivern na hango shi ya taso da sauri yazo gurin shi cike da girmamawa ya d'an russunar da kanshi ya gaida shi,saif be amsa gaisuwar ba se cewa yayi"me ya faru ko ka sake tafka min wani shirmen ne kuma?
Yace"yalla6ai tun kafin takwas nazo amma bata fito ba har yanzu kuma wayar ta a kashe,dana kira taka wayar kuma se ba'a d'aga ba.
Saif da be ga kiran nashi ba ya ciro wayar shi ya duba yaga missed call lokacin yana bacci kuma mostly silent yake saka wayar shi idan ze kwanta.
Ya kalle sa kawai ba tare da yace masa komai ba ya koma daga ciki ya haura sama zuwa d'akin zarah.
Koda ya shiga ya same ta kwance ruf da ciki ta rungume pillown da take kwance akai se sharar bacci take kanta ba hula duk gashin kanta ya baje a saman pillow snn qafafuwan ta a hard'e d'ayan kan d'aya.
Da har ya kalli fridge da niyyar d'auko ruwan gora masu sanyi dmn ya kwara mata ta tashi se kuma ya fasa ya kafe idon sa kawai yana ta kallon ta ya rasa meyasa yaga ta mishi kyau har yana jin wani abu na fizgar shi bayan ba wasu kaya masu sha'awa ne a jikin ta ba face riga da wando na bacci,kawai dai wandon a iya guiwa ya tsaya haka kayan d'as suke a jikin ta masu laushi da hoton katun katun a jiki.
Tsintar kanshi yayi da zama saman gadon a hankli kmr wanda baya son ya tashe ta snn kmr da tsoro yakai hannun sa kan sumar kanta dake barbaje kan pillow,har ransa wani abu yake ji idan yaga sumar ta tamkar be ta6a ganin suma me tsawo ba a rayuwar shi wani irin kyau take mishi se yaga kmr ba nata bane dan sosai sumar keda santsi da laushi kmr baby hair da aka haifa yau yau d'in nn,gashi baqi sosai abun sha'awa,se jin yake kmr kar ya daina ta6awa amma dolen shi ya janye hannun sa da sauri sbd motsin da tayi ta gyara kwanciyar ta tare da sauke nannuyan ajiyar zuciya kmr me mafarkin an kama ta ta kufce.
Yana nn zaune idon shi akan ta har se da baccin ta ya koma yin nauyi snn yakai hannun sa a hankli ya yaye mata sumar kanta da ta zubo ta rufe mata fuska,nn hannun sa ya d'an shafi gefen fuskar ta se yaji jikin ta da zafi kmn garwashi musamman saman goshin ta dan a hankali ya tafi da hannun sa yana ta6a jikinta har zuwa wuyan ta duk jikin nata zafi koina.
Nan kawai ya d'aga ta cak kmr wata er baby ya zaunar da ita,da sauri zarah ta bud'e idanunta a d'an tsorace tana kallon shi,fuskar sa a d'aure yace"ya kin bar driver tun d'azu yazo yana ta fmn jiranki?
Muryar ta can ciki ta marasa lafiya tace"bana jin dad'i ne bazan iya zuwa school ba"
Me yake maki ciwo?
Ya tambaya fuskar sa ba yabo ba fallasa.
Tace"kaina ne...
Se tayi shiru amma da alamar bashi kad'ai bane but she can't tell him.
Saif da ke kallon ta yace"and what?
"Ba komai"
Ta fad'a zata sauka kan gadon ya riqo ta se bin jikinta yake da kallo har ya sauke idon sa akan qirjinta yana kallon yanayin boobs d'in ta sunyi luhu luhu a jikin rigar snn nipples d'in ta sun bayyana a jikin rigar sosai.
Ko bata fad'a ba ya fahimci suna d'aya daga cikin abunda ke mata ciwo dan muguntar da ya mata a kan su yasan dole ne zasu mata ciwo.
Sam zarah bata lura da inda yake kallo ba sbd in seconds ne ya mata kallon,shiyasa kai tsaye se jin tayi hannun sa dumu dumu a cikin rigar ta yana ta6a mata boobs snn ya kama rigar ta da d'ayan hannun sa ze yaye ya gani,ranta a 6ace ta riqe rigar tare da saurin riqo hannun shi zata fitar daga cikin rigar ta,bata sami damar hakan ba se kuka ta fashe dashi sbd matse boobs d'inta da yayi.
Yana kallonta hankalin shi a kwance yace"da zafi?
Da sauri ta gyad'a mishi kai yayinda hawaye ke sauka a hankali kan kumatun ta.
Nan kawai ya zare hannun sa a hankli daga cikin rigar ta ya shiga share mata hawayen yana fad'in"amma shine na samu kin kwanta akai"
Shiru ta mishi dan ita bata ma san ta kwanta akai ba kawai dai a lokacin da ta gyara kwanciyar ta taji kmr an zare mata qaya.
Bai damu da shirun da ta mishi ba se koma kai hannun sa yayi ze yaye rigar ta dmn yaga yanda mamman ta sukayi bcos da akwai maganin da yake son kawo mata but yafi son se yaga yanda maman sukayi tukun,amma se ta riqe rigar sosai taqi barin shi,ya girgiza kansa tare da ta6e bakin sa yace"wane dare ne kuma jemage be gani ba,ke kika sani idan suka ru6e ae se a yanke a yar kin ma huta da kayan nauyi.
Zarah da duk haushin sa take ji ta kalle sa shaye da toka tace"ko na huta da muguntar ba,dan gwanda su ru6e akan kaci gaba da ta6a min.
Tayi tsaki tare da tashi ta shiga bathroom ta banko ganbun qofar da qarfi ta rufe.
Saifuddeen da yayi mgnr ne dan kawai ta barshi ya gani,yayi murmushi kawai snn ya tashi ya bar d'akin.
Ya fita had'e da kiran jamil a waya,jamil na d'agawa yace"plz jamil idan zainab na free ka turowa mutuniyar ka ita bata jin dad'i naso na duba ta sbd ta raina ni taqi ta bari"
Jamil yace"yawan masifar ka da muguntar ka yau da gobe ai dole yasa ta raina ka sbd sanin kanka ne farko ba haka take ba kai ka janyo wa kanka rainin"
Saif yace"kaga jamil ba wnn na tambaye ka ba,ka turo mata zainab nace"
Yayi tsaki tare da tsinke wayar ba tare da ya jira me jamil d'in zai ce ba,ya nufi motar shi zai shiga knn se ga drivern zarah yazo da saurin shi yace"yalla6ai na ci gaba da jiran ta ne zata fito?
"Aa"
Ya fad'a a taqaice snn ya shiga mota yaja ya fita daga gidan.

Kafin sllr juma'a ya dawo yayi wankan juma'a ya shirya cikin farin yadi ya fita.
Se bayan ya dawo snn ya tafi d'akin zarah,ya same ta ta ida sllh,qur'ani a hannunta tana karatun suratul kahfi,wacce a bayyane take karantawa cikin zazzaqar muryar ta me dad'in sauraro,har saif ya sami kansa da tsayuwa yana ta sauraren ta,har se da ta kammala karantawa zata rufe qur'ani kawai ta ganshi yazo gabanta tare da rage tsawon shi suka rufe qur'anin tare snn ya kar6i qur'anin ya ajiye a hnkli gefe kan dardumar da take zaune akai.
Wani irin fad'uwar gaba ta samu kanta da shi idanun ta qasa taqi yarda su had'a ido wacce ko kad'an bata so ya kama ta dumu dumu haka ba.
Saif dake kallonta ya d'ago fuskar ta ga mamakin sa hawaye ya gani cike tap a idonta har suna tserar sauka akan kumatun ta.
Ya riga yasan dalilin kukan muryar sa a natse yace"ki cire tsoro a ranki zan barki bazan sake takuraki ba amma se idan zaki min abu d'aya"
Da saurin ta ta kalle shi muryar ta a sanyaye tace"koma mene ne zan maka fad'i ina jinka"
Se da ya d'an d'au lokaci snn yace"Ina son gobe naje dake gurin Abba ki nuna masa cewa da yardar ki nake son zan auri Sophie idan kika min haka har na sami auren ta ni kuma na miki alqawarin zan sake ki kije ki auri duk wanda kike son ki aura.
Har ranta taji wani irin dad'i ta share hawayen fuskar ta tare da fad'in"shikenan gobe da yaushe zamu je dan tafiya zanyi bana so inyi dare"
Kumatun ta ya kama a hankli yana me qara share mata hawaye yace"kar ki damu akan lokaci zamu tafi har ki samu kiyi tafiyar ki in time"
Ya qarashe mgnr ne cikin sakar mata murmushi.
Nan ita ma ta tsinci kanta da sakar mishi murmushi snn ta bisa da kallo har ya tashi ya fita daga d'akin.
[9:27AM, 3/6/2018] ‪+227 90 04 34 04‬: _Sunday 04/03/2018_
*«»»««»SAIFUDDEEN!«»»««»*






By
*Billy giro😊*



*Dedicated to»»»Zarah gwandu*



*«»Page«» 29*
Saif da ya fita har ya kai qofar d'akin shi ze mird'a handle,se yayi tsaye yana dawo da hoton fuskar zarah a lokacinda ta sakar mishi murmushi,se duk yaji yana son sake ganin murmushin nata har dei yanda dimples d'inta suka lotsa yafi matuqar birge shi.
Nan kawai ya fasa shiga d'akin nashi ya juya zuwa d'akin ta,da shigar shi ya samu ta miqe tsaye daga kan darduma a tsorace cikin fasa ihu ta nufo shi se nuna mishi spider take da ya fito under bed tana fad'in"ka ganshi ko gashi nn har yau be fita daga d'akin nn ba dan Allah ka fitar min dashi kar ya ta6a ni ina jin tsoro.
Kallonta kawai saif ya tsaya yana yi,yanayin jin tsoron ta ma abun sha'awa da son kayi ta kallo,shi se yanzu ma ya fara fahimtar son ta da jamil keyi,lallai kuwa idan ya sake ta ze yi qoqarin ganin cewa jamil d'in ne ya aure ta ba wani ba.
Ihun da ta saki ne tare da fita aguje daga d'akin ya farkar dashi shagaltar da yayi yana kallon ta,ya tafi da sauri kan dressing mirror ya d'auko insect killer ya fesa mishi take ya mutu,yasa faka da sweeper ya fitar mata dashi.
Zarah dake tsaye bakin qofa ta mishi godiya snn ta koma daga ciki,ta d'auke qur'ani takai shi inda ya dace snn ta linke darduma tasa a wardrobe had'e da hijabin sallar ta da ta cire shima ta linke.
Nan se ga saif ya dawo d'akin wanda kae tsaye corner of bathroom ya tafi ya ajiye faka n sweeper a mazaunin su.
Da har zai fita daga d'akin se kuma ya tsaya yana tambayar ta ko zainab tazo ta duba ki?
Zarah tace"eh tazo ta min allura ta kuma bani wasu magunguna nasha"
Yace"muga magungunan,ba musu ta d'auko mishi ta kawo mishi byn ya duba magungunan ya kalle ta yace"baki gaya mata qirjin ki na maki ciwo bane?
Shan toka tayi kafin take sadda kanta qasa snn ta girgiza masa kai alamar a'a.
Saif da ke kallon ta be ce mata komai ba se miqa mata magungunan yayi ya fita daga d'akin.
Ta maida magungunan knn ta soma jin doorbell nn ta fita ta sauka zuwa downstair ta bud'e qofa,se ganin Nusaiba tayi riqe da er wata doguwar silver food flask a hannun ta 5pieces amma ba wani tsayi ne da ita ba sbd cute pieces of bowls d'in qananu ne basu da girma sosai.
Zarah ta d'an yi far da idanun ta d'auke da murmushi na alamar kece.
Nusaiba tace"eh surprise,nazo duba ki ne ya jikin naki?
Alhmdlh naji sauqi zarah ta fad'a had'e da kar6ar food flask d'in da ke hannu Nusaiba suka shiga daga ciki,Zarah na mai tambayar ta yusra fa jiya da kuka zo ban ganta ba yauma gashi kin zo min ba ita.
Nusaiba da har sun qarasa cikin d'aki ta zauna kan sofa tare da yaye gyalen ta ta ajiye snn tace"yusra ae satin nn kaf a gidan hajiya tayi shi daga sunan zuwa weekend fa tace ita bata tashi dawowa ba,shine umma ta tattara mata tufafin ta har ma da uniform d'inta ta aika mata se idan za'a kaini school a biya a d'auke ta mu tafi.
D'auke da murmushi zarah tace"ina ma nn tazo na samu me tayani zama da safe se muyi shirin mu,mu fita tare a sauke kowa a school d'in su.
Cabd'i ae school d'in su da taku ba kusa ba kwata kwata ma basu had'a hanya ba.
To ae duk a cikin gari d'aya ne,kawai dai zamu shirya kan lokaci ta yanda za'a kai kowa akan lokaci.
Hmm duk da haka dai zaman ta a gidan nn bazai yiyu ba dan naga yaya saif ya fara tsunduma a sonki,se ma kinji wani dad'i da naji a raina a lokacinda ya fito dake manne a jikin sa yana wani nan nan dake,da gani ya damu sosai akan rashin lafiyar.
Zarah dake kallon ta ta ta6e baki snn d'auke da murmushi tace"hm Nusaiba knn nida yama alqawarin gobe idan munje.....
Se tayi shiru taqi qarasa zancen dan se taga kmr ba mgnr da ya kamata ta snr da Nusaiba bace.
Nusaiba tace"alqawarin me ya miki gobe,ko tare zaku je rimin dako?
A'a ae ko me za'a bashi nasan bazai je wnn qauyen ba bare ni bana ma son yaje...me kika kawo min a kula?
Zarah ta fad'a cikin basar da waccan mgnr.
Nusaiba da har taso tayi wata magana se kuma tace"Bud'e kiga umma ce ta bayar a kawo miki.
Zarah dake zaune kusa da Nusaiba a hankali ta shiga 6alle bowls d'in d'aya bayan d'aya tana duba abubuwan da ke ciki.
Abincin marmari ne irin wanda masu ciki keso.
Bowl d'in farko da ta bud'e alala ce yayinda na biyu ta sami sauce d'in qoda wanda zata had'a taci da alalar,na uku kuma d'an wake ne with cucumber salad da dafaffen qwai a gefe,and the 4th one mai da yaji ne a ciki na had'in d'an wanken,then d last one danbun shinkafa wanda yayi kyau har ya gaji se qamshi ke tashi.
Murmushi zarah tayi me d'auke da nuna jin dad'i snn tace"wlh kmr inna tasan banyi abinci ba gashi yunwa nakeji na kasa zuwa na girka.
Nusaiba tace"lallai ma so kike ki kashe mana baby"
Cikin jin zancen wani iri zarah tace wane babyn.
Ta6e baki Nusaiba tayi tare da mata wani kallon up & down kafin take cewa"hmm kinji ki 6ter ae ko zaki 6oyewa kowa banda ni,bare tunda naga umma na miki wnn had'e had'en kalolin abincin nasan cewa ciki ne da ke.
Dam kawai zarah taji gaban ta ya fad'i wacce da saurinta ta kai ma Nusaiba duka cikin dalla mata harara tace"Allah sauwaqe ni wlh banda komai"
Dariya Nusaiba tayi tace"karki maida ni qaramar yarinya mana ko kin manta jiya da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login