Showing 102001 words to 105000 words out of 145898 words
yau ba sei gobe"
Yace"no umma i cnt wait har gobe ina so in ganta yau plz"
Aa kayi haquri har gobe yanzu dare yayi kuma gashi naji jikin naka da zafi sosai da alama yinin yau baka ci komai ba ko?
Eh umma amma zan iya....se kuma yayi shiru yana tuna yau gabad'aya in banda sllr asuba ba sllr da yayi.
Nan kawai ya miqe tsaye da sauri,umma ta kalle shi tace"lafiya?
Yace"zanje inyi sallalon da ake bina ne umma gabad'aya yau in banda sallar asuba ba sllr da nayi"
Umma tace"subhanallah bansan kana wasa da sallah ba ya akayi ka manta?
Saif da bai san mom d'insa ce ta qara yi masa wata allurar ba bayan wacce jamil ya masa yace"Ba mantawa nayi ba umma allurar da jamil ya min ce tasa ni yin bacci sosai shine koda na farka na samu har dare yayi.
Umma ta miqe tsaye tace"to bari na kawo ma abinci kaci dmn kaji qarfin yin sallolin ko"
Yace"no umma ni bazan iya cin abinci ba idan ba sallolin nn nayi ba"
Har zai fita se kum ya tsaya yace"plz umma kafin na dawo asa ko Nusaiba ce ta dafa min indomie ita nake jin zan iya ci.
Umma tace"kar ka damu da kaina ma zan dafa maka amma za'a soya maka qwai ne ko a dafa maka?
Yace"Aa zarah dafawa take yi nima dafaffen nake so"
Tace"to shikenan jeka kayi sallolin to.
Nan saif ya fita umma ta bisa da kallo a ranta tana tunanin kmr son zarah ne fa saif ya farayi nn take kuma se ta basar ta wuce zuwa kitchen dmn dafa mishi indomie d'in.
Da shigar ta kitchen ruwan Lipton ta fara had'a mishi tasa a mug ta rufe snn ta dafa mishi qwai guda uku,kafin take fara had'a mishi indomie sbd tafi so koda zai dawo indomie d'in bata huce ba da zafin ta dai dai yanda zai fi jin dad'in cinta.
Ae kuwa da ya dawo sosai yaci indomie d'in dan ba kad'an ba yunwa yake ji dan koda yaje yana yin sallah har wani jiri yake ji,amma hakan ya jure ya samu natsuwar yin su duka.
Wanda yana gama cin indomie se ga jamil ya shigo sbd kiran sa umma tayi ta gaya masa saif ya dawo shine yazo dmn ya kwana tare da saif d'in dan tsoron yake kar mom d'in saif ta sake dawowa ta bar garin dashi gabad'aya,gashi shi kuma jin saif d'in yake kmr wani d'an uwan sa da baya son ganin ranar da zasu rabu.
Saif na ganin sa ya miqe yana fad'in"yauwa jamil muje ka rakani kd"
Kafin jamil yace komai umma da dama tana nn zaune a falo tace"saif ba nace kbr tafiyar har gobe ba"
A d'an shagwa6e ya kalli ta yace"umma am ok now zan iya zuwa kuma kinga ga jamil ko a can ne zamu iya kwana se gobe da safe mu dawo abunda kawai nake so shine inga zarah.
Jiki sanyaye cikin fad'uwar gaba jamil ya kalle shi,umma tace"A'a just kabar tafiyar nn har gobe hankalina yafi kwanciya"
Ba yanda ya iya a hnkli ya gyad'a mata kai alamar yaji,kana suka mata se da safe suka wuce part d'in saif.
Plz Jamil kana da numbar zarah ina so nayi waya da ita inji ko ta daina kuka,bcos umma tace min kukan da takeyi ne yasa aka wuce da ita kd.
Saif ya tambayi jamil bayan sun isa 6angaren nashi.
Jamil ya kalle sa kawai tare da girgiza masa kai alamar bashi da.
Komai saif bai sake ce masa ba har suka kwanta bacci inda jamil har safe bai iya yin baccin kirki ba se juyi kawai da yake cike da tunanin zarah a ranshi da kullum qara jin sonta yake a ran shi musamman abubuwan nn da suka faru sei duk ya shiga tausayin rayuwar ta.
Washe gari bayan sunyi wanka har sunyi breakfast suka kama hanyar kd.
Basu jima da wucewa bane umma na d'aki ta soma jin qarar door bell dan rufe qofar tayi sbd wani lokacin se ayi ta sallama basu ji ba suna ciki.
Koda taje ta bud'e qofa mom d'in saif ta gani wacce kae tsaye ba gaisuwa ba sallama tace"ina d'ana?
D'anki kin bani ajiyar sa ne?
Umma ta fad'a tana kallonta fuskar ta a d'aure.
Cikin isa da gadara Mom d'in saif tace"ban baki ajiyar sa ba amma inada tabbacin kinsan inda yaje,dan naje 6angaren sa ban same shi ba kuma driver ya tabbatar min jiya har nn gida ya sauke shi.
Umma tace"ae sai kije ki neme shi tunda shi yaron goye ne da zaki kama faman bibiyar sa duk inda yaje.
Nan kawai ta rufe qofar ba tare da jira me mom d'in saif d'in zata ce ba.
Koda ta juya se ganin Nusaiba tayi tsaye a bayan ta wacce jin qarar door bell ne yasa ta fito ta kama hannunta kawai suka wuce zuwa sama.
Mom d'in saif kuwa tana ganin umma ta rufe mata qofa duk ranta a 6ace ta juya had'e da kiran wanda tasa yana kula mata shiga da fita na saif,suna gama waya dashi taje ta shiga mota tace da driver suje kd.
Nan driver yaja mota suka hau hanya.
Su saif kuwa a lokacin sun d'anyi nisa akan hanya yayinda jamil yana jan motar ne kawai amma jin kansa yake kmr wani marar lafiya a hakan har suka isa.
Abban kd baya nn ya fita se umman kd suka samu,bayan sun gama gaisawa da ita dukkan su sukayi shiru basu sake cewa komai ba kmr wasu baqin kunya.
Umman kd dake kallon su tace"ya akayi ne saif ko na kira Alhj yazo zakuyi magana ne?
Saif da kansa ke qasa yace"Eh umma amma ina so dan Allah zanga zarah tukun"
Shiru umman kd tayi na d'an wani lokaci tana kallon sa can tace"Tana a d'akin su Nadiya zaka iya zuwa ka same ta.
Wani sanyi saif yaji a ranshi kmr har ya ga zarah d'in ya tashi a natse ya haura sama zuwa d'akin su Nadiya yayi knocking,Nadiya ta bud'e mishi qofa ta gaida shi tare da bashi hanya ya shiga ita kuma ta fita.
Damuwa ce ta bayyana a fuskar sa ganin Zarah kwance kan bed ana mata qarin ruwa,ya qarasa da saurin sa se kuma ya zauna a hankli kan gadon ganin kmr bacci take,wanda a natse ya d'aura tafin hannun sa a hankali kan goshin ta yaji jikin nata duk zafi bai janye hannun nasa ba kawai yaga ta shiga bud'e idanunta a hankli ta ware su a kan shi se kallon sa kawai take tayi,haka shima ya kafe idanun sa akan ta se kallon ta yake,snn a hankli ya kira sunan ta tare da kama ta ya tafi da ita jikinsa ya kwantar da kanta a kafad'ar shi,yana shafa gadon bayan ta a hankli,zarah wacce ganinsa yasa taji wani sanyi a ranta ta qara lafewa sosai a jikin sa ta sauke ajiyar zuciya a hankali can ciki.
_Thursday 05/04/2018_
*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»page«» 52*
Saif dake shafa bayanta muryar sa a hankali yace"jikin ki yayi zafi sosai zarah,meyasa kikayi tayin kuka har zazza6i ya kama ki haka plz indai akan wnn mtr ne ki cire damuwa a ranki komai zai daidaita kinji"
Zarah dake manne a jikin sa a hankli ta gyad'a masa kai,yace"kinci abinci?
Ta girgiza masa kai,ya kalli abincin da aka ajiye mata nn kusa da gefen gado cikin plate an rufe da d'ayan plate fresh milk da cup ajiye a kusa yace"bari to na d'auko maki abincin kici"
Muryar ta can qasa ta marasa lfy tace"um um bana iya ci bakina baya min dad'i,kawai cire min wnn qarin ruwan da ake min ni na gaji dashi.
Tayi maganar ne had'e da miqa masa hannun ta da aka d'aura mata ruwa akai.
Saif ya kama hannun nata a hankali zai cire mata,se ganin sukayi an tizge mata cannula d'in da qarfin tsiya har sai da jini ya fito aguje ba shiri,zarah ta fasa ihu cike da jin zafi wacce kafin ta iya ganin wanda ya tizge mata cannula d'in se jin tayi an kuma fizge ta daga jikin saif had'e da kai mata lafiyayyen mari har sai da ta fad'i kanta ya daki beside drawer,ta fasa ihu tare da dafe gefen kan ta,a rikice saif yaje da sauri ya kamata tuni gefen kanta ya fashe jini na fita nn saif ya d'ago idanun sa da duk sukayi jajur lokaci d'aya,cikin tsananin 6acin rai yake kallon mom d'in sa da duk ita ce tayi aikin,sosai ya jimqe hannun sa jikin sa na wani irin rawa yana jin kmr yaje ya doke ta amma be iya yin hakan ba se qwalla da suka taru a idon shi,ya kalli zarah da sai kuka take zai tafi da ita jikin sa dmn ya rarrashe ta,ta tafi da gudu jikin Umman kd da shigowar ta knn d'akin ita da Nadiya kan jin ihun zarah da yasa su zowa da sauri sbd duk basu san da shigowar mom d'in saif ba dmn saif na barin falon bayan ta kira Abban kd a waya ita ma ta tashi ta nufi kitchen a niyyar zata kawo musu lemu a can Nadiya ta same ta dan koda ta sauka bata ga kowa a falon ba,bcos umman kd na barin falon jamil ya tashi ya fita yaje cikin mota ya zauna sbd kansa dake masa masifar ciwo ya had'e kan nasa da sitarin mota shiyasa har mom d'in saif ta shiga cikin gida baiga wucewar ta ba.
Ae kuwa da mamaki umman kd ke kallon mom d'in saif snn ranta a 6ace tace"masifaffiya masifar taki kuma kika zo zakiyi ta a nn ko kuma kinzo zaki kashe tan ne iye! ta kama hannun zarah ta kai mata ita tace"gata ki kashe ta in san cewa ke cikakkiyar marar hankali ce me lasisi.
Mom d'in saif dake kallon ta tace"Kome zaki kirani indai akan d'ana ne ni bazan damu ba,amma ina son in gaya miki idan har na sake ganin ta a karo na uku tare da d'ana sai dai ku nemi wata er wlh babu kuma abunda zaku iya yi,idan kuma kinyi gardama mu zuba nida ku shege ka fasa.
Daga haka ta fita daga d'akin duk ranta a 6ace ta wuce Abban kd da isowar sa knn qofar d'akin zai shiga ya bita da kallo kana ya qarasa daga ciki yana kallon su umma yace"lafiya me kuma ya kawo ta a gidan nn"
"D'anta ta biyo mana"
Umman kd ta bashi amsa tare da kama hannun zarah dake ta kuka suka fita daga d'akin har Nadiya.
Abban kd ya bisu da kallo kana ya juya gun saif yayi tsaye yana kallon saif da ya zauna kan bed tare da dafe kanshi irin cikin damuwa d'in nn,nn ya qarasa kusa dashi ya zauna ya dafa shi a hankali,saif ya d'ago idanun sa da suke jajur kuma cike tap da qwallah muryar sa na rawa sbd 6acin rai da kukan da yake ji yace"Abba ni kam wace irin uwa ce wnn na had'u da ita dan Allah kasa a d'aure ta dmn wlh na fahimci ba hankali ne da ita ba zata iya kashe zarah da gaske.
Abban kd yace"tabbas kuwa amma kaine kasa hankalin nata ya gushe,kuma kaine zaka iya dawo mata da hankalin nata.
Da kamar mamaki Saif yace"kmr ya Abba na bita kake nufi ko kuma na rabu da zarah wanne kake nufi ciki?
Abban kd yace"ae dama ita zarah kun rabu....da sauri yace no Abba zarah she is still my wife wlh a bisa kuskure na rubuta mata saki kuma....is ok basai ka sake maimaita min bayani ba naji komai na kuma fahimci iya inda kake da laifi,but still zarah baza ta koma maka ba sbd a cikin bayanin da aka min da akwai inda na fahimci lallai ba son zarah kakeyi ba wata qil shaquwar zaman da kukayi ne yasa duk kabi ka damu da rabuwar auren ko kuma ince jin ita wace ce a gun umman ka yasa duk kaji idan kuka rabu baka kyauta ba shiyasa kake son a mayarda auren ko?
A sanyaye saif yace"ba haka bane Abba"
To yaya ne?
Ina son cikawa Abba burin sa ne.
Ya fad'a cikin marairaicewa.
Abban kd yace"ka gaya min gaskiya rasuwar sa ce tasa kake son cika masa burin sa ko tun kafin ya rasu ne kake son ganin ka cika masa burin nasa?
Saif yace"eh tun kafin ya rasu"
Abba dake kallon sa yace"meyasa zaka min qarya saif bayan kafin na tambaye ka sai da nace ka gaya min gaskiya"
Saif yace"Abba gaskiya na gaya maka wlh"
Abba ya girgiza kansa yace"wnn rayuwar da ka d'aukowa kanka sam bata dace da kai ba saif,idan har gaskiya ka gaya min meyasa to har Abban naka ya rasu ba abunda ya ta6a shiga tsakanin ka da zarah.
Da sauri saif ya kalli Abban kd se kuma ya sadda kansa qasa yayi shiru bai ce masa komai ba.
Abban kd yace"ko kuma ba haka bane da akwai?
A hankli saif ya girgiza kansa yace"babu"
Abban kd yayi shiru yana kallon sa can ya jinjina kansa yace"hm saifuddeen knn a hkn ne to kake da burin samarwa Abban ka farin cikin sa har kana fad'in zaka maida auren ka da zarah bayan kulata ma baka iyayi,but shikenan dai yanzu abunda nake so dakai daga yau ka d'auke qafar ka da zowa gurin zarah dmn babu zancen maida auren ka da ita,kabar jamil dake sonta yaci gaba da zowa gurin ta har Allah yasa su sasanta tsakanin su suyi aure.
A rikice saifudeen ya kalli Abba da yaji zancen nasa kmr saukar guduma,muryar sa na rawa yace"Abba meyasa,dan Allah kayi haquri zaman da mukayi a baya sam ba irin shi zamuyi ba yanzu wlh cike nake da burin samarwa Abba farin cikin sa.
Abban kd yace"na gama fahimtar ka saifuddeen dan haka ka daina cutuwar kanka kana fad'ar abunda fad'a kawai kake ko an barka baza ka iya aikatawa ba,abunda kawai nake so dakai shine ko kad'an kada kayi wasa da yiwa Abbanka addu'a dmn abunda yafi buqata knn a gurin ka yanzu.
Mahaifiyar ka kuma ina son kayi haquri ka cire komai a ranka ka mata biyaya dmn sam ban gaya maka halinta dan ka tsane ta ba sai dan ina tsoron kar wata manufa ce yasa tazo zata tafi dakai shiyasa na gaya maka dmn koda ta tafi da kai d'in zaka iya kare kanka daga sharrin ta,amma a yanda na fahimce ta bada nufin cutuwa ta dawo gare ka ba qauna ce,wacce idan ba binta kayi ba hankalinta bazai ta6a kwanciya ba haka muma da kai karan kanka,dan haka kawai kayi haquri ka bita duk lokacinda ka buqaci ganin mu kai namiji ne zaka iya zowa ka kawo mana ziyara akoyaushe amma idan zakayi aure kasan irin macen da zaka aura kar kayi irin kuskuren da Abban ka yayi da farko,da kuskuren ne yazo yana ta bamu matsala a yanzu,Allah de ya kyauta.
Saifudeen dake jin kuka da qyar ya iya had'iye kukan yace"Abba ni gaskiya bazan iya bin wnn matar ba,burin ta fa taga cewa ta rabani da ku kwata kwata.
Abba yace"ka ta6a ganin inda aka raba mutum da iyayen shi ae wnn sai dai mutuwa"
Yace"to ba gashi ba Abba se biye mata kukeyi har kuna cewa zarah baza ta koma min ba"
Cikin d'aure fuska Abba ya kalle sa yace"we are all educated dan haka kar ka sake yunqurin maida mu shashashai,abunda kawai nake son ji shine gaya min ita mahaifiyar taka a ina take nufin ka bita a can gidan ta na kano da naji ance ta kaika ka ko kuwa Maiduguri?
Saif dake jin wani qololon baqin ciki ya danne abun yace"Nima ban sani ba kawai dai tace min ko kano d'in nake son inci gaba da zama zata yarda amma kune bata so inci gaba da kulawa wai.
Abba yace"fad'a kawai take ita kanta tasan bazata ta6a iya rabamu dakai ba,haukar son ganin ka koma gare ta ne kawai ke d'ibar ta,dan haka ka daina tunanin wae zata iya raba mu dakai mutuwa ce kad'ai ta isa tayi hakan,snn ko barin ka da zamuyi ka koma gurin ta dan ita mahaifiyar ka ce da ta haifeka hkn yasa zamu barka ba dan masifar ta ko wani abu ba ka fahimce ni?
Saif da duk haushi yake ji a ransa ya gyad'a masa kai kawai.
Nan Abban kd ya tashi ya fita daga d'akin,saif da ya bisa da kallo shima ya tashi ya fita duk ransa a 6ace ya tafi sai d'akin umman kd,se ganin Abban kd yayi a can yaje duba zarah da har an mata dressing kan inda taji ciwo haka ma hannunta a samu jinin ya tsaya.
Suna had'a ido da Abban kd ya sadda kansa qasa fuskar nn tasa ba annuri yana gudun kar Abban kd d'in yace mai me yazo yi gun zarah kuma,Abban kd kuwa shi a tunanin sa ma ko yazo yiwa umman kd sallama ne zasu wuce,wanda har ya nufi qofa ze fita se kuma ya tsaya yace da saif kafin ku wuce kace da jamil yazo ina son zamuyi magana nida shi.
Bansan taya ma zan misalta muku abunda saif yaji ba dan ko magana ma kasa yiwa Abban kd yayi,wanda yana gama fad'a ya fita ba tare da ya jira me saif d'in zai ce ba.
Nan umman kd da Nadiya suma suka fita daga d'akin sbd sun fahimci saif da zarah yake son zai yi magana,wacce tana ganin sun fita ta tashi da sauri itama zata fita,saif ya rigata isa bakin qofar d'akin yasa key ya rufe snn ya kama hannun ta a fusace ya tafi da ita ya manna ta a jikin bango yana kallon ta idanun sa jajur cike da qwallah with deep voice yace"ke wace irin yarinya ce mai fallasa sirrin aure da har