Showing 90001 words to 93000 words out of 145898 words
ya rasu ba.
Wa enda suna shiga falon hankalin su yayi matuqar qara tashi,ganin gawa ajiye a tsakar falon rufe da farin qyalle duk jini,ga su umma,Hajiya, Nusaiba,yusra,se kuka suke tayi ba mai kama wani,Abban Kd ne ya d'an fisu dama amma shima ya sadda kansa qasa se kukan zucci yake da yafi na fili ciwo.
Cikin tsakanin tashin hankli saif ya gurfana a gaban gawar tare da zarah da yake riqe da hannunta,ya saki hannun nata jikin sa na wani irin rawa ya bud'e fuskar gawar da qyar.
Kmr shed'ar sa zata d'auke yace"Inalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Se kawai ya fasa wani irin kuka me tsuma zuciya ya fad'a jikin gawar yana jijjiga ta yana kiran sunan Abba.
zarah dake kallon fuskar Abba yau gashi kwance ba rai hawaye ne suka fito aguje kan kumatun ta,ta fashe da kuka snn ta tafi da gudu ta fad'a jikin umma wacce itama nn wani sabon kuka ya qwace mata ta had'a su su duka uku,Nusaiba,zarah yusra,duk ta rungume su se kuka suke tayi.
_Tuesday 27/03/2018_
*«»«»«»SAIFUDDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«»46*
Sosai Abban kd ya shiga basu magana,har ya samu suka d'an sassauta kukan da suke snn a kafaice ya share hawayen da suka zubo mishi dan kuwa saif still yana rungume da gawar Abba se kuka yake sosai bai daina ba,yaje ya samu da qyar ya 6an6are shi daga jikin gawar,ya rungume shi a jikin sa yana ta rarrashin sa yana bashi magana.
Daga haka akayiwa Abba komai da akeyiwa mamaci aka kaishi makwancin sa.
Ae kuwa kuka ya dawo musu sabo yayinda shi kuma aka baro shi can shi kad'ai a cikin kabarin sa,Allah sarki mutuwa knn Allah yaji qanka Abba,duk burin sa na son ganin en jikokin sa ashe bazai samu gani ba mutuwa knn mai yankan qauna,kana naka Allah na nashi,dmn kuwa duk burin uwa na son ganin abunda ta haifa tana ji zata haifu amma se Allah ya kar6i ranta ba tare da taga abunda ta haifa d'in ba,Allah knn mai iko kuma sarkin saraku nan da babu kamar shi.
Bayan kwana uku da rasuwar Abba ne,zarah na zaune a d'akin su Nusaiba ta ida sllr isha'i,qur'ani a hannun ta tana karantawa a hankli cikin ranta,su Nadiya da dije ma sllr suka ida,suna zaune kan dardumar da suka ida sallah kowaccen su zugum shiru cazbi a hannun su suna ja.
Nusaiba kuwa da alama ta riga su ida sllr tana kwance ruf da ciki kan bed sanye da qaton hijab me kai mata har qasa,wayar ta riqe a hannun ta se kallon futunan su take da sukayi da Abba,hawaye na faman zarya a idon ta.
Umman kd ce ta shigo d'akin ta zauna a hankli kusa da ita tana kallonta tace"Ajiye wayar nn haka Nusaiba addu'a ya kama ta ki masa ba ki zauna kina ta kallon hoton shi kina kuka ba yi haquri tashi daina kuka kinji.
Cikin kuka Nusaiba ta taso tazo jikinta tana fad'in"umma na kasa yarda Abba ya rasu a kullum gani nake kmr ze dawo.
Ta qarashe mgnr sosai cikin kuka tana kallon hoton Abba dake jikin wayar ta yana murmushi kmr ya motsa yayi magana.
Umma ta kar6i wayar snn ta share mata hawaye cikin muryar rarrashi tace"ya isa haka daina kuka je ma'aruf yana falo zasu koma kd ne"
Nan Nusaiba ta tashi jiki sanyaye ta fita daga d'akin.
Kafin umman kd ke cewa da zarah"idan kin kai aya zarah kije jamil yana a waje yana kiranki.
Ba musu zarah nakai aya ta rufe qur'ani ta ajiye a hankli kan darduma snn ta fita.
Koda ta sauka downstairs ta sami Nusaiba tasa ma'aruf a gaba tana mishi kuka shi kuma yayi shiru se kallonta kawai yake cike da jin tausayin ta ya kasa ce mata komai,sbd ko ya rarrashe ta ba shiru zatayi ba dmn tun da Abba ya rasu haka take bata awa1 bata fasa wani sabon kuka ba kuma in ta fara se ta gaji dan kanta snn take yin shiru.
Zarah dake kallonta qwalla ne taji sun ciko mata ido tayi saurin fita daga falon taje ta sami jamil a waje,suka gaisa har yana mata ya qarin haquri,tace"mun gode Allah,snn a natse yace"saif ne dama still har yau bai ci komai ba ruwan drip ne kawai da na d'aura mishi ke amfani a jikin shi nayi nayi dashi ko ruwan Lipton ne yasha amma yaqi.
"Za'a gayawa umma ne?
Zarah ta tambaya a sanyaye tana mai kallon shi.
Yace"A'a zaki je ki duba shi ne ki samu ko kad'an ne yaci abinci dmn idan ya sake kwana baici komai ba zazza6in zai qara masa yawa"
Tace"to bari naje na d'ebo masa abinci"
Yace"Aa ankai mana abinci yanzun,jeki kawai ki d'ibar masa a can.
Tace"to snn ta wuce zuwa 6angaren saif Jamil ya bita da kallo har sai da ya daina ganin ta,snn ya d'auki motar sa ya fita daga gidan.
Zarah kuwa tana isa 6angaren saif a hankli ta bud'e qofa ta shiga had'e da sallama a bakin ta.
Taje ta zauna kan bed kusa da saif dake kwance idanuwan sa a rufe kmr meyin bacci da ko shigowar ta ma bai ji ba,sai da ta d'aura tafin hannun ta a hankli kan goshin sa ne snn ya bud'e idanun sa yana kallonta.
Ya kira sunan ta a hnkli cikin muryar sa can ciki da bata ko fita sosai,snn ya yunqura zai tashi ta taimaka mishi ya tashi zaune,ya d'aura kan sa a kafad'ar ta,hannun sa kan waist d'inta ya zagayo dashi kan cikinta yana shafa cikin nata cikin muryar kuka yace"zarah Abba ya tafi ba tare da mun samar masa farin cikin sa ba"
Shiru zarah tayi bata iya ce masa komai ba se hawaye da suka silalo a hankli kan kumatun ta,ta share hawayen snn ta kalli saif da shima hawayen ne suka silalo kan kumatun sa tasa lallausan hannun ta ta share mishi,snn ta kama kumatun sa tana kallon sa muryar ta a hankli tace"jikin ka yayi zafi sosai dan Allah kayi haquri kaci abinci kaji"
Komawa yayi kan kafad'ar ta ya kwanta yana fad'in"i cnt eat zarah bazan iya cin komai ba"
Um um kayi haquri dan Allah zaka iya.
Nan ta janye shi a hankli kan kafad'ar ta ya koma ya kwanta zata tashi ta d'ibar masa abinci ya riqo hannun ta yace"no zarah bazan iya ci ba fa ko kin d'ibar min is just wasted.
Zarah dake kallon sa cikin damuwa ta shafo cikin sa tace"kwanan ka uku baka ci komai ba fa,gaskiya yau in baka ci ba zanyi kuka"
Saif dake kallonta hawaye ya gani kuwa har sun cika mata ido.
Ya girgiza kansa alamar kar tayi kukan zaici.
Da taimakon ta ya tashi zaune,dan ba wani qarfi a jikin sa,har sai da ma tasa masa pillow ya jingina bayan sa.
Da akwai ruwan Lipton a mug ta tsiyaya mishi a cup ta bashi yasha kmr yanda ya buqata snn ta d'ibar mishi abinci d'an dai dai da tasan ze iya cinyewa,ta shiga bashi abincin da kanta har sai da yace ya ishe shi snn ta ajiye,ta bashi ruwa yasha snn tasa tissue ta share masa bakin sa.
Ta miqe tsaye da niyyar zata gyara masa pillow ya kwanta,yace"Aa zanyi wanka ne je bathroom ki had'a min ruwa"
Nan zarah ta cire hijab d'in jikinta ta ajiye sbd babba ne har qasa baza ta ji dad'in shiga bathroom dashi ba.
Bayan ta wuce yakai hannun sa a hankli ya cire drip d'inda aka d'aura mishi snn ya cire kayan jikin sa ya bar d'an guntun wando kawai a jikin sa ya tafi bathroom,nn zarah ta fito ta bashi guri dan har ta gama had'a mishi ruwan se kayan bacci ta fidda mishi snn ta maida hijab d'in ta a jikin ta da niyyar zata tafi se kuma tayi zaune kan bed tana jiran fitowar shi gudun kar se ta tafi da akwai abunda yake buqata kuma.
Se 10 jamil ya dawo gidan sbd a nn yake kwana tun lokacinda akayi rasuwar shine ke kula da saif.
A mamakin sa koda yazo d'akin saif se ganin zarah yayi a d'akin ashe bata tafi ba,tana kwance kan faffad'an qirjin saif ya rungume ta suna bacci abinsu,da alama baccin ya kwashe su ne basu sani ba dan still zarah na sanye da qaton hijab d'inta mai hannu da ya rufe mata jikin ta gabad'aya se en kyawawan qafafuwan ta dake waje kawai.
Jamil dake kallon su a hankli ya juya ze fita daga d'akin se jin yayi saif ya kira sunan shi cikin muryar bacci.
Sai da jamil ya share en guntayen hawayen da suka fito mishi,snn ya juya yana kallon yanda saif ke shafa bayan zarah a hankli yana kiran sunan ta,ta tashi a natse tare da sauke idanun ta akan agogon bangon d'akin ta bud'e ido cikin mamaki tana kallon saif tace"qarfe goma har da en mintina yaushe mukayi bacci har haka,nn kawai bata jira me saif zai ce ba ta tashi da sauri tana fad'in"zan tafi sai da safe.
Kallo kawai Saif ya bita da dashi,ita kuma ganin jamil yasa ta sadda kanta qasa cikin jin kunya ta fita,jamil ya kalli saif da ya gyara kwanciyar sa ze ci gaba da bacci yace"baza ka iya raka ta bane dare fa yayi ba kowa a harabar gidan nn zata iya jin tsoro.
A hankali saif ya lalla6a ya tashi ya fita,jamil ya bisa da kallo qwallah tap a idon sa,har suna qoqarin zubowa bai bar hawayen sun zubo ba ya samu da qyar ya had'iye kukan da yake ya tafi bathroom dmn watsa ruwa.
Saif kuwa koda ya fita ya samu zarah se sauri take har tayi nisa.
Ya kirata ta tsaya ya qarasa gurinta tare da kama hannun ta yana kallon ta yace muje na rakaki ko"
Duk da tasan jikin nasa bai yi wani qarfi ba bata musa mishi ba dan tsoro take ji shiyasa ma take ta sauri.
Har qofar falo yakai ta se bayan ta shiga snn ya koma.
Umma na zaune a falon kan kujera riqe da qaton photon su dake manne a falon ta ciro tana kallo,su duka ne gabad'aya,ita da Abba,saif,Nusaiba da yusra dukkan su suna murmushi amma fuskar Abba kawai take kallo qwalla tap a idonta,har ma hawayen suka soma saukowa a hankli,jin motsi yasa tayi saurin share hawayen,snn ta ajiye photon a can d'ayar kujera ta juyar da fuskar photon.
Snn ta miqe tsaye tana mai kallon zarah da ta shigo, muryar ta a hankali mai cike da damuwar rasuwar Abba tace"zarah a ina kika fito yanzun qarfe goma fa har da mintina"
Zarah bata iya ce mata komai ba sai sadda kanta tayi qasa.
Kafin umma ta sake tambayar ta se ga umman kd ta sauko tana fad'in"Gurin saif ta fito kinsan baya jin dad'i tun shekaran jiya har yau bai ci komai ba,shine jamil yace taje ko zata shawo kan saif d'in yaci abinci,ina fatar yaci abincin dai ko?
Umman kd ta tambayi zarah,zarah tace"eh"
Umma tace"To ya jikin nasa?
Zarah tace"yaji sauqi"
Tace"to Allah qara sauqi jeki kwanta"
Umman kd tace"A'a bari tasha ko fura ce kafin ta kwanta,dan nasan koda ta fita bata ci komai ba ko kinci abinci a can?
A hankali Zarah ta girgiza kanta alamar a'a.
Umma ta kalle ta kawai ba tare da tace komai ba ta wuce,se umman kd ce ta kama hannun ta ta zaunar da ita kan kujera snn da kanta taje ta d'ebo mata fura a fridge ta sata a gaba har sai da ta shanye snn ta barta ta tafi,dan haka take fama dasu,tunda akayi rasuwar nn basa iya cin abinci se idan ta sa su a gaba har umma kuwa se tayi da gaske snn take cin abinci koshi kad'an.
Bayan zarah ta wuce ta d'auki photon da umma ta ajiye tana kallon photon cike da tausayin umma a ranta karo na biyu knn da ta rasa uban 'ya'yan ta,duk sun tafi sun bar ta da 'ya'ya marayu,ita kuma jarrabawar ta knn.
"Allah sarki"
Umman kd ta fad'a a fili snn ta share en guntayen hawayen da suka fito mata ta wuce riqe da photon a hannunta dan ta san idan ba 6oye photon aka yi ba,umma bazata daina zowa duk dare tana kallon photon ba,wanda in banda damuwa ba abunda yake qara mata.
Washe gari da safe zarah ta fito riqe da basket d'in abinci a hannun ta zata kaiwa su saif breakfast d'in su,ta tsaya tana kallon wata irin dakakkiyar mota da aka bud'ewa gate tana kunnowa a hankali cikin gidan,inda motar na fakawa da sauri driver ya fito agurguje yaje ya bud'e gidan baya,se ga wata mata fara tas da ita ta fito cike da qasaita wacce kallo d'aya zakayi mata kasan cewa kud'i sun bala'in zauna mata,ko daga yanayin tsadaddar suturar ta kad'ai in ka kalla zaka ka san hakan.
Tana fitowa mota idon ta ya sauka akan zarah wacce taji lokaci d'aya duk ta shiga ranta,hakan yasa ta d'anyi murmushi tare da yafuto zarah alamar tazo.
Ba musu zarah ta ajiye basket d'in da ke hannunta ta qarasa gurinta tare da gaida ta,matar wacce still mumurshi na kan fuskar ta tace"lafiya qalau ya sunan ki en mata?
Zarah wacce taji ita ma lokaci d'aya taji son matar a ranta,fuskar ta ba yabo ba fallasa tace"suna na zarah"
Zarah!
Matar ta fad'a tare da zare eyeglass d'inda ke sanye a idon ta,ta mugun d'aure fuska tana yiwa zarah wani irin kallon tsana,da har yasa zarah taji tsoro taja baya tana kallon yanda matar ke masifar kama da saif,da saida ta cire eyeglass d'inta ne snn zarah ta fahimci hakan.
_Thursday 29/03/2018_
*«»«»«»SAIFUDDEEN!«»«»«»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
_Sorry my fans kuyi haquri typing is not easy wlh._
*«»Page«»47*
Tana kallo matar ta kar6i pistol a hannun drivern ta,ta shiga matsowa a kusa da ita hakan ya mugun qara tsorata zarah,da sauri taje ta d'auki basket d'in abincin da ta ajiye ta wuce 6angaren su saif ba tare da ta tsaya yin knocking ko sallama ba ta fad'a kawai,dai dai saif ya miqe tsaye a hankli ze lalla6a yaje yayi wanka,jamil kuwa shi har yayi wankan yana d'aure da towel a qugun sa,ta saki basket ta tafi jikin saif duk a rud'e,ya kamata yana fad'in"what happen zarah lfy?
Idanunta tap da qwallah ta kalle shi tace"inaga mahaifiyar ka ce tazo gata nn ta biyoni da bindiga ban san me na mata ba"
Saif da yaji abun wani iri banbarakwai yace"mahaifiya ta ta biyo ki da bindiga kmr ya bangane ba,me ya same ki zarah are u ok?.....kafin zarah tace wani abu se jin yayi an fincike zarah daga jikin sa an tunkud'e ta da qarfi zata fad'i jamil yayi saurin kamata.
Mahaifiyar saif da ita ce ta tukud'e tan rai 6ace ta nuna ta da pistol d'in da ke hannun ta tace"I will kill u idan na koma ganin ki a kusa da d'ana se na kashe ki er matsiyata kawai get out! in daina ganin ki a nn!
Kuka zarah ta saki ta fita aguje jikin ta na rawa.
Saif da jamil kuwa mamaki ne qarara a fuskar su.
Yayinda mahaifiyar tashi ta miqawa drivern ta pistol snn ta nufi saif cike da murmushi zata rungume shi,da saurin sa yaja baya awa yaga abun tsoro zuciyar sa na halbawa kan irin kamar da yaga suna yi wanda da qyar muryar sa na qiqqilewa yace"wa..ce...ce..ke?
Mom d'in shi da ta tsaya tana kallon shi d'auke da murmushi tace"my Son am ur real mother baka gani a fuska ba...da sauri yace"what! Allah sauwaqe ni umma ce kad'ai mahaifiyata.
Shu'umin murmushi ta saki tare da kallon su umma da suka shigo d'akin sbd yanda zarah taje a rud'e ta gaya musu abunda yake faruwa.
Ta nuna umma fuskar ta a yatsine tace"ka dai ce Allah sauwaqe wannan matsiyaciyar ta zamo mahaifiyar ka,nice nn mahaifiyar ka ta asali da nayi kayan cikin ka tsawon wata tara na haifeka,mahaifin ka mara tausayi ya rabani da kai tun kana d'an yaron ka wata shida,shine dan ka taso a hannun wnn banzar zaka d'auka ko ita ce mahaifiyar ka bayan babu wata alaqa a tsakanin ku.
Saif da duk ransa ya gama 6aci ya nuna ta yace"ya ishe ki haka wlh is enough ki tsaya a matsayin ki in ke er uwa ce amma ba kizo kina gayawa iyayena baqar magana ba akan su zan iya yin komai wlh.
"Ya salam"
mom d'in tashi ta fad'a,tana mai kallon sa kafin take kallon umma tace"kin gani kin 6ata min yaro kina gani a gabanki ya nuna min yatsa yana gaya min magana son ranshi a matsayina na mahaifiyar shi,wnn wace irin tarbiya ce ni kam kuka bashi,koda yake banga laifin sa ba sbd zalunci ku be bar kun gaya masa cewa yana da real mother ba,shiyasa kika yi shiru kin kasa cewa komai dan baki ma san taya zaki fara masa zancen ba,to wlh bari ki dake har uban nashi zaluncin ku bazai ta6a yin tasiri ba.
Umman kd tace mata"kinga dakata kubra ya isa haka ki san irin mgnr da zaki fad'a,mahaifin saif fa ya rasu yau duka duka kwana hud'u dan haka ki daina sako shi a cikin zancen ki,ki barshi ya huta yaji dad'i a cikin kabarin shi.
Wani irin murmushi mom d'in saif tayi irin murmushin da ya bayyana alamar ta ma riga su sanin rasuwar Abba kafin su,tace"ae nasan ya rasu ba se kin gaya min ba,shiyasa nazo yau da nasan cewa kun gama zaman makoki zan d'auki d'ana in tafi dashi dmn bazan barshi yaci gaba da zama da matsiyatan mutane irin ku ba.....wlh ya ishe ki fa!
Saif ya fad'a cikin nuna ta yana wani irin huci.
Umma ta janyo shi qwalla tap a idon ta tace"ya isa haka saif