Showing 93001 words to 96000 words out of 145898 words

Chapter 32 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24740

mahaifiyar ka ce fa.....ina zai sani kun zalunci yaro kunqi gaya mishi gaskiya.
Mom d'in shi ta fad'a dan shi saif d'in ya ma kasa cewa komai se kallon umma da ya tsaya yana yi,wacce ta kalli jamil tace"plz jamil sa tufafin ka kaje gidan Hjy ka gaya mata abinda ake ciki kuzo tare kaji.
Jamil wanda rud'u da mamaki ya mantar da shi yanda yake ya sadda kansa qasa tare da gyad'a mata kai alamar "to"
Snn ta kalli mom d'in saif tace"kiyi haquri muje falo mu jira zuwan hajiya se ayi magana ko.
Ta6e baki tayi tace"Allah kawo ta lafiya tazo taji abunda nazo dashi d'ana ne ba wanda ya isa ya hana min in tafi dashi.
Ba dai wanda yace da ita komai,suka tafi falo su duka har su Nusaiba,zarah ce kawai bata gurin tana can sama d'akin su Nusaiba tana faman kuka.
Saif kuwa still jin al'amarin yake wani iri gabad'aya kansa ya d'aure yana kallon umma cike da son ya mata magana,ta kama hannun sa had'e da girgiza masa kai alamar yayi haquri har Hjy tazo,dolen shi yayi shiru ba dan yaso ba wanda sam ya kasa yarda da abunda mom d'inshi tazo dashi wae shi d'anta ne,jin abun yake awa almara.

Da zaman su falon ne Umman kd ta kira Abban kd a waya da niyyar snr da shi abunda ake ciki,sai jin qarar wayar sa tayi a bakin qofar falon,bai d'aga kiran nata ba se sallama yayi musu suka amsa mishi snn ya shigo ya shiga rarraba idanun sa yana kallon su gannin yanda duk sukayi zazzaune a falo sbd shi sam baisan abunda ke faruwa ba isowar shi knn daga kd,dmn kullum da dare komawa yake da safe se ya dawo.
Sosai yayi mamaki da ganin mom d'in saif amma kuma sanin abunda ya faru yasa ya 6oye mamakin dan a tunanin sa ko gaisuwa tazo musu.
Kallon sa take har ya zauna snn tace"Alhj Hassan ya kuka ji da haquri"
Yace"haquri Alhmdlh "
Tace"To Allah yaji qansa amma asali ni ba gaisuwar ta kawo ni ba nazo ne ku bani d'ana in tafi dashi......
Wani iri Abban kd yaji abun d'auke da mamaki ya kalle ta yace"wane d'an!...banni da ita cewar Hjy wacce shigowar ta knn daga falon,ta nuna mom d'in saif tace"bari kiji in gaya miki kinyi kad'an kice zaki tafi da saifudeen,dan kin raina mana hankali tun yana d'an wata shida da kika tafi ko sau d'aya baki ta6a zowa kin ganshi ba haka ma kaf en uwanki ba wanda yazo se yanzu da kika ji mahaifin sa ya rasu shine kika d'auko qafa kikazo wae zaki tafi da d'anki sbd gado ko to kinyi kad'an baki isa ba"
Miqewa mom d'in saif tayi tana kallon hajiya tace"Gado fa kika ce Hjy kalle ni sama da qasa kinga alamun talauci a tare dani ne bare har tsiyar abunda d'anki ya bari ta dame ni,Allah sauwaqe wlh,gadon ma saifudeen baya so ku d'auka duka ya bar muku rabon shi dmn kune matsiyata da gado yashawa kai....tas! Abban kd ya wanke ta da lafiyayyen mari ransa a mugun 6ace ya nuna ta cikin kakkausar murya yace"wlh mind ur tongue kar ki sake dubin Hjy ta ki gaya mata maganar banza,fitsararriya kawai mara tarbiya da baqin cikin ki ne ya kashe mahaifiyar ki wnn kam kinyi kad'an,kuma saifuddeen ba inda zaki je dashi!matsiyatan da kike kira mana ai daga tsatson namu ya fito me zakiyi dashi ki tafi can ki nemi d'a dai dai da irinki ba wnn ba.
Mom d'in saif dake dafe da kuncen ta kan jin zafin marin,rai 6ace ta janye hannun ta akan kuncen nata tace"koma me zaka fad'a ka fad'a amma d'ana ba wanda ya isa ya hana min in tafi dashi,ya gama zama a gurin ku yanzu lokaci ne da ni kuma zanje dashi inji dad'in d'a nima.
Umman kd tace"Hm Kubra knn ko kunya ma baki ji ba har kina fad'in kiji dad'in d'a kema,bayan da kika samu cikin sa ba yanda bakiyi ba na ganin kin zubar amma Allah besa kinyi nasara ba,da kika haife shi kuma kwata kwata baki ta6a nuna masa qaunar da uwa ke nuna ma d'anta ba kika banzar tar dashi a hannun masu aiki su kawai ke hidima dashi,breast feeding d'in shi ma se kin ga dama se yanzu zaki zo mana da wani banzan zance,dan kinga ya girma ya zama mutum.
Tace"Eh koma me zaki ce dai yanzu naji ina buqatar kasancewa da d'ana kuma dole a bani in tafi dashi,dmn cikin ku ba wacce ta tayani renon cikin sa ni kad'ai nasha fama da abuna har na haife shi dan haka zancen kuce zaku hana min in tafi dashi ma bata taso ba,idan kuma kunce da ja to lallai kuwa kotu ce zata raba mu....kin dad'e baki je kinsa qara ba sha sha sha.
Cewar Hjy.
Abban kd yace"No Hjy plz samu guri ki zauna kar ki sake ce mata komai ku bar ni da ita kawai.
Nan ya kalli Saif wanda duk zancen nasu ya rud'ar dashi muryar sa na rawa yace"Abba shin wane irin zance nake ji ana yi haka ban gane ba kun min bayani dan Allah"
Cikin jin tausayin sa Abban kd ke kallon shi ya dafa shi yace"kayi haquri saif gaskiyar magana maman yusra ba ita ce ta haife ka ba,ya nuna mom d'in saif yace"wnn da kake gani ita ce mahaifiyar ka da ta haife ka,amma rashin qaunar da ta nuna maka tun kana cikin ciki har ka fito yasa ko kad'an Abban ka baya so a gaya ma labarin ta kwata kwata dmn ba uwa bace da d'a zai so yaji labarin ta baqin ciki ne kawai,sam bata da mutunci bata kuma ganin girman kowa har shi mahaifin naka wanda auren so ne sukayi bana qiyaya ba amma bai ta6a jin dad'in zama da ita ba har ya gaji ya sake ta,inda a lokacin kana d'an wata shida wacce tun lokacin da ta tafi ko sau d'aya bata ta6a zowa ganin ka ba bare wani nata,dan haka ne yasa muka ce bazata ta tafi da kai ba,amma idan kana ra'ayin binta baza mu hana ka ba u are free.
Saif da duk jijiyoyin kansa suka taso idanuwan sa kuma sukayi jajur suka ciko tap da qwallah ya tafi jikin umma cikin kuka yana fad'in"wnn wace irin rana ce umma da nake ji wai ba kece kika haife ni ba,ni kam har yanzu kece uwata umma banida wata uwa bayan ke,har abada bazan bi uwar da bata sona ba nima bana sonta na tsane ta bazan bita ba kawai ta fita ma in daina ganin ta i dnt wnt see her any more!
Duk yana mgnr ne cikin kuka
Umma dake rungume dashi qwallah cike a idon ta tace"A'a saif ban baka wnn tarbiyar ba, mahaifiya,mahaifiya ce ka daina gaya mata kalamai irin haka.
Ya d'ago yace"umma ae d'a ma d'a ne amma meyasa ni ta jefar dani bata d'auke ni d'aba ta nuna min tsana tamkar bata hanyar halal aka same ni ba why!?
Kafin umma tace komai mom d'in shi ta qaraso cikin marairaice fuska tace"kayi haquri my son wlh nayi nadamar abunda na aikata maka a baya yanzu ina qaunar ka fiye da yanda kake tunani dmn banida wani d'a da nake da duk duniyar nn bayan ka.
Wani irin kallon tsana saif keyi mata snn cikin murya mai cike da jin baqin ciki har tana wani rawar kuka yace"ok shiyasa kika dawo gare ni knn sbd ni kad'ai ne d'anki da kina da wasu 'ya'yan fa?
Da sauri tace"Wlh zan dawo gare ka kaifa d'ana ne da nake matuqar so.
zata janyo shi jikin ta yaja baya da sauri baya son ta ta6a shi.
Ta kalli Abban kd duk ranta a 6ace tace"munafuki shine ka gaya mai har abubuwan da bai kamata ya sani ba dan kawai ya tsane ni ko,to bari kaji baza ka ta6a yin nasara ba wlh.
Nan ta juya gun saif tace"plz my son naji komai laifina ne amma kayi haquri kazo mu tafi kaji wlh ina qaunar ka duk duniyar nn banida abunda yafi min kai"
Kauda fuskar sa kawai saif yayi daga kallon ta ya kalli Abban kd cikin muryar kuka irin mai cike da jin takaici sosai d'in nn yace"Dan Allah Abba ku taimaka min matar nn ta bar gidan nn in daina ganin ta.
Kafin Abban kd yace komai umma ta janyo shi cikin rarrashi tace"Saifudeen tunda har tayi nadama ta kuma baka haquri,i beg u kayi haquri ka bita kaji ae kai namiji ne idan kayi kewar mu zaka iya zowa ganin mu ako yaushe.
Cikin mamaki yace"haba umma ya zaki ce in bi matar da bata nuna min qauna ba a lokacinda nafi buqatar qaunar ta se yanzu da rashin 'ya'ya ne yasa ta dawo gareni....no my son wlh ba haka bane trust me.....i will never trust u,ni bazan ta6a yarda dake ba dan haka ki fita kawai kije ki nemi wani d'an bani ba,ki kuma shafe ni a rayuwar ki cewar babu ni kmr yanda babu ke a gurina umma ce kad'ai uwata.....cikin daka tsawa tace"is enough my Son ya isa!
Ta nuna umma snn tace"kar ka sake kiran wnn banzar matsiyaciyar matar da mahaifiyar ka Allah tsare ka,nice mahaifiyar ka har abadah ba kuma zaka ta6a iya canza ni ba,ina lalla6a ka ne sbd kai d'ana ne da nake qauna amma ita ba wata qauna da take maka tana lalla6a ka ne kawai sbd matsiyaciyar er ta da kake aure.
Saifudeen wanda har ransa yake jin ciwon zagin da mom d'insa keyiwa umma,amma mamakin jin zarah er ta ce bai bar ya iya cewa komai ba se saurin kallon umma da yayi cike da mamaki yace"what! umma wai zarah er ki ce?
Shiru kawai umma tayi bata ce masa komai ba.
Ta6e da baki Mom d'in saif tace"er tace kuma agola ba,dmn ta auri Abban ka ne bayan mutuwar mijinta da shima liqa masa ita ne akayi ba auren so ba,kmr yanda aka so da farko a liqawa Abbanka ita yaqi amma sbd kwad'ayayyu ne su marasa zuciya suka sake liqewa Abban naka har sai da ya aure ta wanda na tabbatar ba a banza suka barshi ba.
Ta kalli umma tace"to bari kiji yanda kika liqewa uban sa har sai da kika yi nasarar ya aure ki kika hau yin wadaqa da dukiya ni kam kunyi kad'an daram zaku bar min d'ana duk baqin tsafin ku baza ku ta6a yin nasara akan shi ba,dan haka idan har wae tunanin kike ko da ita zamu tafi shine kike wani lalla6a shi ya yarda ya bini to kiyi gaggawar janyewa,d'ana ko a qafa bazai ja wnn matsiyaciyar er taki ba sakin ta zai yi yaje ya aure dai dai dashi wacce yake qauna ba wacce aka tursasa mishi kan dole ba ehe.
Umma da tun d'azun haquri kawai take tana danne zuciyar ta wnn karon kam ta kasa,ta kalli mom d'in saif fuskar ta a d'aure tace"bari kiji Kubra kk ko mene ne,ni bazan biye miki ba sbd dama can ke marar mutunci ce da ko tsofaffinki ma ba ragawa kika yi ba bare wani,shiyasa tun farko banso auren ba sbd nasan dole wnn rnr zata zo,kuma kmr yanda kike fad'in dole akayiwa saif haka ma zarah ba son auren take yi ba,Alhj ne kawai ke son auren wanda yanzu Allah yayi mishi rasuwa sai dai muce Allah yaji qansa ya masa rahama.
Nan ta share qwallar da suka zubo mata snn ta kalli saif tace"Saifudeen ina son ka rabutuwa zarah takardar sakin ta yanzun dmn bazan iya jure wnn rashin mutuncin ba.
A rud'e ya kalli umma muryar sa na rawa yace"umma kinsan me kk fad'a kuwa dan Allah kiyi haquri wlh bazan iya ba"
Ya qarashe mgnr ne qwallah tap a idon sa.
Umma tace"saboda me saifudeen baka son zarah fa haka itama bata son ka....haba umma ki daina wnn mgnr,kin manta maganar da mukayi da Abba rnr sa ta qarshe da zai bar gidan nn,cewa fa yayi ko bayan ransa na rabu da zarah zeyi baqin ciki,har na masa alqawarin bazan rabu da zarah ba har abadah,kan me zaki biyewa wnn mtr har kice in saki zarah.
Umma tace"ba ina biye mata bane,hakan shine mafi a'ala da kaima na tabbatar kafi son hakan wanda ko alqawarin da kace kayiwa Abbanka kayi masa ne kawai ba wai har cikin ranka ba dmn da bakin ka ka gaya min cewa duk wani abu da kake yi a gaban Abban ka na kmr kuna zaman lfy da zarah kana yi ne kawai sbd ka samu ya barka ka auri Sophie....da sauri cikin rud'u saif ya girgiza kansa yace"no umma tuni na janye wnn manufar wlh duk abunda na gaya masa a rnr da gaske ne har cikin raina babu wata manufa a raina irin inga na faranta mishi,dan haka ki taimaka min dan Allah umma ki janye zancen in saki zarah wlh bazan iya ba.....dole zaka iya dan haka maza wlh rubuta mata sakin ta yanzun!
Mom d'in sa ta fad'a wacce sosai cikin 6acin rai tayi maganar dan maganganun da umma ta gaya mata sun 6ata mata rai ba kad'an ba.
Shi saif mamaki ma ta bashi ya kalle ta kawai irin kallon hm lallai ma.
Ta jinjina kanta tace"hm kamin komai ma bazan ga laifin ka ba,ta nuna umma tace"wnn azzalumar duk ita ce ta lalata min kai taqi baka tarbiyar ganin girman na gaba da kai,dan haka bari kiji in gaya miki wlh ko ki tilasta shi ya rubutawa er ki saki ko kuma.....cin mutuncin ya ishe ki haka!
Cewar zarah wacce ke saukowa daga staircase,dmn duk abunda yake faruwa tana ji a kunnen ta shiyasa ma ta kasa jurewa ta fito,wacce idon kowa ya koma kanta suna kallonta har ta sauko riqe da dunqulalliyar takarda a hannun ta tazo tayi tsaye a gaban saif tana kallon shi qwallah tap a idon ta haka ma muryar ta cike da son yin kuka tace"kayi haquri ba ina ina nufin in qara saka ka a cikin damuwa bane,abun ne naji ba dad'i,yau kwana hud'u kacal da rasuwar baffa amma abubuwa sun zo suna faruwa haka marar dad'i a cikin gidan shi,ba'a barmu da zafin mutuwar shi ba se wani zafin ake son d'aura mana,dan haka ni kam na kasa jurewa bazan iya ci gaba da jin abunda yake faruwa ba,zan kawo qarshen abun.
Nan kawai ta miqawa umma takardar da ke hannun ta.
Umma ta walwale takardar ta duba bayan ta karanta tace"meye haka zarah wa ya gaya miki kina iya rubutawa kanki saki"
Zarah da duk kuka take ji kanta qasa tace"Aa inna ba ni na rubuta ba shine da kansa ya rubuta min"
Ta qarashe maganar ne had'e da kallon saif wanda hankali tashe hannun sa na rawa ya kar6i takadar a hannun umma ya duba yaga tabbas kuwa takardar sakin da ya rubuta mata ce wacce be bata ba ya fasa ya yar.
_Saturday 31/03/2018_
*«»«»«»SAIFUDDEEN!«»«»«»*





By
*Billy giro😊*



*Dedicated to»»»Zarah gwandu*



*«»Page«»48*
Kafin ya iya yin komai Abban kd yazo ya kar6i takardar ya duba ya kalli saif d'in snn ya kalli zarah yace"yaushe ne ya rubuta miki sakin?
Kafin tace komai sai da ta kalli saif wanda da saurin sa ya girgiza mata kai cikin yanayin begging baya so ta fad'a.
Zarah da ba yanda zatayi ta janye idanunta kawai kanta qasa tace da Abban kd yau kwana hud'u knn da ya rubuta min.
Abban kd dake kallonta yace"kina nufin rnr da Abban sa ya rasu?
A hankli ta gyad'a masa kai alamar eh.
Nan Hjy ta hau yin salati,umman kd da su Nusaiba kuwa duk haka suka ji abun ba dad'i,kmr dai
Abban kd wanda cikin wani yanayi ya jinjina kansa yana kallon saif da duk ya marairaice fuska yace"Abb....Abban kd bai barshi ba yayi saurin d'aga mai hannu alamar baya son ji.
Da saurin sa ya koma kan Zarah yace"Plz zarah ki mai bayani dan Allah jefar da takadar nayi fa ba baki nayi ba kin tsince ta ne kawai ki gaya masa kinji.
Kallon sa kawai zarah tayi bata iya ce masa komai ba se kuka da taji yana son qwace mata nn kawai ta bar gurin da sauri ta haura zuwa sama.
Mom d'in saif da sosai taji wani irin dad'i a ranta ta6e da baki tabi zarah da kallo kana ta kalli saif wanda yaje gaban Abban kd jiki sa6ule ya gurfana kan guiyoyin sa snn sosai cikin marairaice wa yana kallon sa yace"wlh Abba tsinta tayi bani na bata ba"
Abban kd yace"kai dai ka rubuta sakin ko?
Eh Abba amma....amma me ae tunda har ka rubuta ta gani shikenan bana son jin wata magana ka tashi kawai kabi uwarka ku tafi,dmn baka da wani amfani a gare mu tunda har Abban naka ma baka amfana mishi da komai ba,bayan bijire masa da kayi ka watsa masa qasa a ido,mutumen da duk muka had'u baya da wata magana sai taka ya kasa 6oye farin cikin sa duk a tunanin sa lafiya lau kuke zaune da zarah ashe kana nuna masa ne kawai sbd wata banzar manufar ka.
Kwallah cike a idon saif muryar sa na rawar kuka yace"wlh kuskure ne Abba bada niyya nayi sakin ba,tuni na janye waccan manufar yanzu da gaske nake son in faranta mishi shiyasa ma ban bata sakin ba na fasa.....to yanzu da ta gani ya zaunu babu aure tsakanin ka da zarah,kaje ka auri wnn baturiyar da kake so babu wanda zai hanaka tunda dama can bamu isa da kai ba,sha sha sha kawai fitsararre har ni zaka rainawa hankali wae kayi saki a kuskure,bayan qaryar da ka gama shirga mana yanzu har kana rantsuwa wae da gaske ne har cikin ranka ka masa alqawarin baza ka rabu da ita ba har abadah,ashe dan iskanci ka ma rubuta mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login