Showing 132001 words to 135000 words out of 145898 words

Chapter 45 - SAIFUDEEN COMPLETE BY ESHAAAT

EYSHAAT   

12 Jul 2024

24727

shayin dan sai taji zaqin shayin na kama bakin ta taji wani iri ba dad'i,ga sugar d'in is normal ba yawa tayi ba amma zaqin ne dai taji bai mata dad'i a baki ba,se ma hautsinar mata da zuciya ya qara yi,da har ma taji ko shayin bata son gani ta had'e kanta da guiwa tana cewa saif dake gurfane a kusa da ita ya fitar da shayin bata son ganin shi.
Ba musu saif ya fitar da shayin,byn ya dawo yasa tissue yana goge wanda ta tofar.
Nan Umma ta shigo d'akin ta kalle sa tace"wani aman kuma ta sake yi ne?
Saif yace"no umma tean ne dai har tasha se kuma ta tofar bata so"
Umma tace"Ayya shifa laulayi haka yake ba kowa keson abu mai zaqi ba,bari naje to na d'aura miki ko kunu ne ko kinfi buqatar kici abinci na kawo miki?
Zarah da still kanta na had'e da guiwa a hankli ta girgiza kanta alamar bata son abinci.
Umma tace"to shikenan bari naje nayi miki kunun se kar asa sugar.
Ta fita saif shi kuma ya kama zarah a hankali suka koma kan bed sai sannu yake mata yana jin awa ya maida ciwon a jikin shi dan lokaci guda duk jikinta ya saki ba qarfi ta zama kmr wacce tayi sati tana fama da rashin lfy,ga jikin nata da yayi wani irin zafi kuma.
Yayi shiru se kallon ta yake tayi da duk wani motsi tayi sai ya mata sannu,har umma tayo kunun ta kawo,saif da ya kar6i kunun a natse ya shiga ba zarah wacce bata wani sha sosai ba tace ya isheta,ya 6alla mata magungunan da ya siyo ya bata tasha ta kwanta se bacci daga ita sai d'an towel d'in da take d'aure dashi asalima bata ko samu tayi sllr isha dake kanta ba.
Se can cikin dare ta farka ta ganta sanye da kayan bacci a jikinta da tasan ba kowa ne zai mata aikin ba face saif.
Nan ta tashi a hankali cikin lalla6awa ta nufi bathroom ta d'auro arwala tayi sallah,tana idarwa a nn kan darduma taci gaba da yin baccin ta sbd tashin ma wuya yake mata bare har ta iya komawa kan bed.
Washe gari haka ta yini kwance ba abunda take iya ci sae kunu koshi kad'an se yawan bacci da take tayi,yayinda saif keta faman safa da marwa yana duba ta wanda ji yake kmr ma ya maida ta 6angaren shi,dan ganin yake kmr zaifi jin dad'in bata kulawa yanda ya kamata duk da dai da zarar ya shiga d'akin duk wanda ke ciki fita yake ya bashi guri koda kuwa bacci takeyi ba kuma za'a koma ba har sai ya fita,shiyasa yau da dare ma da kanshi ya taimaka mata tayi wanka dama komai na shirin bacci snn ya lalla6a ta ta d'an sha kunu ya bata magunguna tasha,wacce tana rungume a jikin sa har tayi bacci ya maida ta kan bed tare da rufa mata blanket snn ya fita.

Yana saukowa downstairs ya sami Abba da umma zaune a falo sai fira suke tayi abinsu cike da nishad'i yayinda yusra ke kan qafafun umma tayi bacci,Nusaiba kuwa tana can d'akin umma tana karatun exam.
Cike da ladabi ya musu sai da safe snn ya fita wanda kafin ya fita sai da Abba ya tambaye sa ya jikin zarah d'in yace"Alhmdlh.

Bayan 3dayz da faruwar haka ne Abba na d'akin su Nusaiba yaje duba zarah da kullum sai ya shiga duba ta amma yau sai yaga kmr ma tafi jin jiki kan yanda jikin nata ya nuna dan duk ta fad'a tayi wani haske kmr wacce jini ya qare ma,sauqin ta kawai yawan baccin da takeyi da ko yanzu baccin ne take tayi.
Abba dake kallon ta cikin sauke numfashi ya janye hannun sa akan goshin ta da yaji duk zafi,ya kalli umma cikin damuwa yace"maman yusra a gaskiya ya kamata ki riqa tasa zarah gaba cikin lalla6awa ta d'an riqa cin abinci ko yaya ne kunu fa ba wani riqon ciki ne dashi ba ki dubi yanda duk tabi ta qare cikin en kwanaki,kullum kunu ko kunun ma kince ba wani sha takeyi ba ae dole jiri ya hana mata sukuni tunda kince ko bathroom ma se an taimaka mata take iya zuwa.
Umma tace"To Alhj ya zanyi abincin ne ko son ganin shi ba tayi ana d'aukowa yanzu zata hau yin amai duk tabi ta amayar da d'an kunun da tasha da wani lokacin ma se an lalla6a ta da qyar snn ake samu tasha,shiyasa nake binta a haka kasan laulayi ba iya mishi ake ba se idan kuma Allah ne ya kawo ma sauqin shi.
Abba dake kallon ta a sanyaye ya maida duban sa gun zarah da duk yake jin tausayin ta a ranshi.
Yace"hakane Allah ya sauqaqa miki zarah,kana ya kalli umma yace"ni zan d'an fita in qara dubo jikin Alu driver.
Umma tace"to a dawo lafiya.
Ya fita ita kuma taje ta zauna a kusa da zarah ta d'auki ruwa da farin handkerchief d'in da ta ajiye ta hau daddanna mata jikin ta da kullum take jin kmr ma qara zafi yake.
Nan se ga saif ya shigo d'akin d'auke da sallama a bakin shi,umma ta amsa tana mai kallon sa har ya qaraso ya zauna kan bedside drawer yana kallon zarah da ake d'an daddana mata jikinta wato ana rage mata zafin jikin nata.
Kana ya kalli umma yace"sannu da aiki umma bari na qarasa mata naga kmr baqi sun shigo nn gidan basu riga sun shigo falo ba tukun dai.
Umma dake kallon sa tace"to bari naje inaga mutanen da ke zowa gaida abbanku ne"
Nan kafin ma ta tashi se ga Nusaiba ta shigo tana snr da ita cewa ga baqi nn sunxo umma ta tashi tana fad'in"to gani zuwa ae yanzun nn yayanki yake gaya min muje ki had'awa baqin ruwa da lemu kafin na kira Abbanku ko zai iya juyowa su gaisa dan yanzun ne fitar sa ba nisa yayi ba.
Nan suka fita,saif kuwa kafin yaci gaba da daddana ma zarah jikinta sai da ya cire mata rigar jikinta ya barta da half vest snn yaci gaba da daddana mata jikin nata har zuwa d'an lafaffen cikinta da yake ta kallo d'auke da murmushi yana shafa cikin wae babyn sa na a ciki.
Kana ya kalli fuskar zarah cike da jin qaunar ta a ranshi yakai lips d'insa a hankali kan goshin ta ya d'aura mata kiss,snn ya d'ago yana shafa gefen fuskar ta muryar sa a natse yana roqa mata sauqi a gun ubangiji,kafin yake ci gaba da mata wacce a hankali cikin sauke numfashi take gyara kwanciyar ta sbd yanda taji jikin nata ya d'an mata dad'i zafin jikin ya rage iska mai dad'i na sanyin split na ratsa jikinta.

Da dare koda yazo bai sami kowa a d'akin ba se Zarah kad'ai tana zaune kan bed ta had'e kanta da guiwa,wacce tana jin an bud'e qofa ta d'ago kanta a hankali idanunta cike da qwalla.
Nan saif ya qarasa gurinta da saurin sa,ya zauna a gaban ta tare da kama kumatun ta da kulawa yana tambayar me aka mata.
Komai bata ce masa ba se matsowa tayi ta shige jikin shi kmr wata er baby ta sakar masa kuka.
Ai fa se duk ya qara shiga damuwa ya d'ago ta yana fad'in"plz cutie gaya min kinji wani abu kk so umma ta hana miki ne?
A hankali ta girgiza masa kai tana kallon sa cikin kukan da takeyi tace"uhm dear ni na gaji bazan iya ba"
Cikin rashin fahimta yace"Mene ne?
Nan kawai ta nuna mai cikin ta tace"Dan Allah ka cire min ina jin wahala sosai inaga ma bazan iya haifuwa ba nayi qanqanta.
Saif ya saki ido tare da saurin rufe mata baki muryar sa can qasa kmr me tsoron wani ya jiyo yace"haba dai cutie kinsan me kk fad'a kuwa"
A shagwa6e ta janye masa hannu qwallah tap a idon ta cikin marairaice fuska tace"Dan Allah dear ka taimaka min wlh wahala nake ji sosai kana gani fa ko abinci bana iya ci,yanzu haka ma yunwa nake ji kmr zan mutu,kuma ni bazan iya shan kunu ba na gaji wlh.
Ta qarashe mgnr cikin kuka.
saif ya qara rungume ta sosai a jikin sa cikin rarrashi yace"to yi haquri kinji gaya min me kk son ci?
Ta d'ago fuskar ta sha6e sha6e da hawaye tace"wnn abun nake so d'an wake"
D'an wake?
Saif ya tambaya dan shi baisan meye haka ba.
Zarah kuwa se gyad'a masa kai tayi alamar eh"
Bai tambaye ta meye shi ba se lallausan hannun sa yakai ya share mata hawaye yana fad'in"to shikenan bari naje na gaya ma umma"
Nan ya janye jikin sa a hankali daga nata tare da janyo mata pillow ta kwanta dan ya fahimci kwanciyar take son yi.
Koda yaje ya gaya wa umma akayi d'an waken aka kawo sai kallon d'an waken yake,snn ya kalli umma yace"umma wnn abun kuwa bazai 6ata mata ciki ba"
Tace"A'a baya 6ata ciki ai da kanwa akeyin shi yanda ciki bazai lallace ba.
Shiru kawai yayi yana kallon d'an waken ya kanyi kyau da haske awa ba kanwa a cikin sa but still yana shakku tunda ba saba ganin sa yayi ba,zarah da itama kallon d'an waken take tayi duk ya biya a ranta,ta kalli saif cikin marairaice fuskar tace"plz dear ka barni inci ina so"
Da kulawa ya kalle ta yace"ae bazan hana miki ba cutie tunda kina so bari naci dai naji tukun kinji"
Nan ya d'auki d'aya ya had'o shi tare da abubuwan da ya gani akai wato dafaffen qwai da akayi slicing d'in shi da kusan yawan sa d'aya shida d'an waken da source d'in qoda da aka zuba akai hadda cabbage.
Had'e da bismillah yasa a bakin shi yaci,ae fa se yaji yawun sa sun tsinke kan dad'i dan umma kam ba dai girki ba sosai ta iya girki ba kad'an ba,musamman d'an wake abu ne da take so shiyasa ko yaushe bata rasa garin shi a ajiye.
Cikin lumshe ido yake cin d'an waken kafin yake ware idanun sa akan umma yace"wow ummana ashe haka abun yake da dad'i"
D'auke da murmushi umma tace"ai fa dama kallon ka kawai nake har se kaci tukun.
Yayi murmushi tare da sake kaiwa a bakin sa yana fad'in"gaskiya kam umma wnn abun ae ba cutie kad'ai zata ci ba hadda ni,ina Nusaiba taje ta sake yi mana wani dan ina son cutie taci har sai ta qoshi.
Umma dake ta fmn yin murmushi tace"da akwai saura ma a kitchen bari na bawa Nusaiba d'in ta kawo muku dan wnn kam bazai ishe ku ba.
Nan ta fita yayinda saif ya shiga bawa zarah d'an waken sai ci take tana bashi a baki shima,duk suka cinye har wanda Nusaiba ta qaro musu.
Saif sae dad'i yake taji ganin yanda taci d'an waken sosai bata yi amai ba ya bata magunguna tasha,tana kallo yaje ya sakawa d'akin key dan duk zai taya ta wanka haka yakeyi,duk da cewa d'an waken nn da taci ta d'anji qarfi a jikinta amma haka ta barshi da kanshi ma ya cire mata kaya ya bata towel ta d'aura suka wuce bathroom.
Koda akayi sati Alhmdlh jikin nata yayi sauqi da kullum d'an wake ne ta maida abincin ta da suke cin abinsu tare ita da saif.
Wanda ganin jikin nata yayi sauqi ya yanke shawarar zasu koma yau har ma yana batun ya gayawa su umma se gashi sun riga shi tunkarar sa da zancen.
Bayan sllr isha'i ya shirya abun sa tsaf se qamshi yake ta zubawa yaje ya sami zarah a d'akin su Nusaiba ta fito daga wanka knn d'aure da towel a jikinta tana jikin wardrobe zata ciro kayan bacci,se jin tayi an rungume ta wacce kafin ma ta juyo tasan waye sbd qamshin turaren sa da taji.
Ta juyo d'auke da murmushi tana kallon sa sosai taga ya mata kyau cikin shafo gefen fuskar sa tace"dear ka min kyau sosai ina zuwa haka da wnn dressing awa ango?
A hankli yaja karan hancinta yana murmushi yace"ae kam ango ne da yazo d'aukar amaryar sa cutie se ki shirya yanzun zamu koma gidan mu kinga se inji dad'in bawa babyna kulawa sosai da sosai koh.
Ya qarashe mgnr ne yana mai shafar cikinta,da still ya kasa daina murmushin da yake yi,zarah kam na jin zancen sa lokaci guda tasha mishi toka har tana ture hannun sa daga kan cikin ta,tare da juya mishi baya ta ciro kayan baccinta zata je tasa ya riqo ta cikin rarrashi yana tambayar ta me ya faru ko rashin gaya mata da baiyi bane se yanzun,yaso surprising d'inta ne dama amma tayi haquri.
Zarah bata saurare shi ba se janye jikinta kawai tayi taje tasa kayan baccinta ta kwanta hadda kashe wutar d'akin,ya bita sai rarrashin ta yake yana ta bata haquri har ma ta gaji da sauraren shi,ta miqe zaune tace"kaga dear dan Allah ka rabu dani,jikina ne kakeyiwa ba kuma zaka sake samun sa ba na gaya ma.
Cikin marairaice fuska yace"haba cutie meye kuma na dawo da abun da ya riga ya wuce plz i beg u kiyi haquri kinji wlh ni ke nake so ba wai jikin ki kad'ai ba trust me"
Zarah dake jin zancen nasa a yaudara ta6e da baki ta kalle sa kawai ta koma ta kwanta ba tare da tace da shi komai ba.
Saif yayi shiru kawai yana kallonta can ya tashi ya fita daga d'akin ransa ba dad'i.
Wanda da fitar sa d'akin ne Nusaiba dake bathroom tana wanka ta fito d'aure da towel,wacce da fitowar ta ta tsaya cak ganin ba haske se kawai tayi murmushi tana kallon zarah cikin zolaya tace"Aa 6ter yau kuma da wuri haka aka kashe mana light kaddai duk laulayin ne,da kuwa babyn nn nawa d'an gata ne mai son hutawa.
Zarah na jinta amma tayi banza da ita dan ko magana ma bata son yi,se kwanciyar ta da ta gyara.
Nusaiba da tasan tabbas ta jita ta kalle ta cikin murmushi da son sake yin wata magana se kuma ta fasa dan yanayin zarah kad'ai ya nuna bata cikin mood,kasancewar d'akin ba wani duhu ne dashi sosai ba shiyasa har ma ana iya ganin yanayin mutum.
Inda haka Nusaiba ta bud'e wardobe ta d'auki abunda ya fito da ita wato pad snn ta koma bathroom dmn qarasa yin wankanta

Saif kuwa yana sauka downstairs ya sami umma da Abba zaune suna kallon labarai ya qarasa gurin su tare da russunawa a hankali cike da tunanin abunda zai ce dasu,nn kafin yace komai Abba ya kalle sa d'auke da murmushi yace"ya akayi ne saifuddeen har zaku tafi knn to ina zarah da ka barta baku fito tare ba bayan kasan jikin nata ba wani qwari yayi sosai ba har yanzu tana fama da jin jiri.
Saif dake tunanin abun cewa yace"Abba ae ganin ma jikin nata baiyi qwari ba yasa na yanke shawarar da munci gaba da zaman mu a nn kawai har idan jikin nata yayi qwari tukun,kasancewar idan mun koma can ba kowa da zai kula da ita idan bana nn.
Abba dake kallon sa se da ya d'anyi shiru kafin yake cewa"haka ne kayi magana amma ita zarah d'in ta amince da haka ko kai kad'ai ne ka yanke wnn shawarar?
Kansa qasa yace"A'a ta amince ai har ma ta kwanta bacci"
Yace"to shikenan jeka Allah yayi maka albarka ya qara maka tausayin iyalin naka.
"Amin"
Umma ta fad'a,saif kuwa bai iya cewa komai ba se tashi yayi ya fita.
Wanda har aka share sati gabad'aya a cikin damuwa ya kasance sbd sam zarah taqi ta saurare shi se fushi take tayi dashi,da har idan ya shiga d'akin fita take ta barshi,ga su umma duk basu san abunda ke faruwa ba dan da ita har shi basu bar aka fahimta ba.


Sorry 4 kept u waiting ban zauna bane wlh,and ko yanzu ma ba a nn naso in tsaya ba but inshaa Allah gobe zanyi qoqari inga cewa na turo muku wani page.
Luv u all❤
[4/28, 8:47 PM] Billy giro😊: _Saturday 28/04/2018_ *«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*



By
*Billy giro😊*




*Dedicated to»»»Zarah gwandu*

_Am very sorry my Fans nayi muku alqawari kuma se ban samu cikawa ba kuyi haquri dan Allah abubuwan ne se a hankali wlh._


*«»page«» 64*
Guraren 9pm saif ya fito daga 6angaren shi zai je 6angaren su umma gun zarah da kullum baya gajiya da zuwa bata haquri.
Kafin ya qarasa isa 6angaren ne se ga jamil ya kunno motar sa a cikin gidan.
Nan ya qarasa gun jamil d'in wanda ya faka motar sa ya fito suka gaisa,snn cike da nishad'i yace"kasan tun rnr na ce ma da akwai labari to shine....se yayi shiru yana kallon saif da ya fahimci duk ya fad'a ya rame ga kuma damuwar da ya gani a tattare dashi.
Kafin ya iya ce masa komai saif d'in yace"what happen ka fara magana kuma kayi shiru?
Jamil dake kallon sa yace"dole nayi shiru saif sbd yanayin ka ya nuna gabad'aya kana cikin damuwa me yake faruwa ne?
Shiru Saif yayi kmr bazai ce komai ba can ya numfasa a hankali snn yace"haqiqa jamil bazan iya 6oye maka ba ina cikin damuwa sosai,kaf satin nn da ya wuce zarah fushi take yi dani nayi nayi ta haqura taqi ko saurarata ma bata son yi.
Jamil da ke kallon sa yace"subhanallah me yayi zafi haka kaddai halinka ne har yanzu baka daina ba saif?
Saif yace"haba jamil nafa gaya ma duk iskancina ni ba wani abu ne fa nakeyi da mace ba,bare tuni na ajiye wnn yanzu ba wata macen da nake kulawa,a dalilin Sophie ne dai har tazo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login