Showing 12001 words to 15000 words out of 145898 words
dake mata masifar ciwo tana kuka.
Se sannu Zarah ke mata wacce ta ajiye jakar islamiyyar ta snn ta cire hijab ta linke tasa a wardrobe da niyyar zata je ta snr da umma halin da nusaiba ke ciki se ga umma ta shigo d'akin.
Kafin tace komai idonta ya sauka kan Nusaiba dake kwance kan bed tana juyi a hnkli sautin kukan ta na fita kad'an kad'an.
Sai da ta girgiza kanta snn taje ta zauna kusa da ita tana kallonta tace"jiya da kuka dawo shopping kinsha alawa da yawa ko,alqawarin da kikayiwa Abbanki knn?
Cikin muryar kuka tace"Allah umma ni kwata kwata bansha ba pringles kawai naci ki tamvayi zarah ma kiji.
Umma tace"to naji tashi kisha magani ki kuma yi gaggawar kimtsa kanki kinsan yanda abun ke zo maki.
Ba musu ta tashi zaune tare da cire hijab d'in jikinta,umma ta bud'e bedside drawer ta ciro magani,da kwai ruwa ajiye cikin jug kan bedside drawer d'in ta 6alle mata maganin tare da tsiyaya mata ruwa a cup ta bata tasha snn ta miqe da qyar tana tafiya sannu a hankli har ta shiga bathroom.
Umma da ta bita da ido ta maida duban ta gun Zarah tace mata"ina ce dai ke kam al'adan ki baya baki wahala kmr haka ko?
Sai da Zarah ta sadda kanta qasa snn tace"yana min amma ba sosai ba kad'an kad'an"
Umma tace"to Allah sauwaqe muje ki kaiwa yayanku breakfast tun d'azu nayi jiran shigowar sa ko ze shigo amma naji shiru gashi jiya yace min yana da baqo.
Nan suka fita suka bar yusra na cire uniform d'in jikinta.
Koda Zarah ta tafi 6angaren Saifuddeen se sallama take tayi har da knocking amma shiru ba amsa se kid'an music dake fitowa a hnkli.
Kmr ta juya se kuma ta kae hannun ta kmr da tsoro ta 6ird'a handle d'in qofar,se gambun ya bud'e a hnkli ta shiga had'e da sallama a bakinta"
Bata qarasa sallamar ba da sauri tasa hannu ta rufe bakinta,ta kuma bud'e ido a tsorace ganin Sophie hakan nn ba komai a jikinta daga ita se d'an pant sun fito daga bathroom ita da Saifuddeen tana rungume a jikin shi,yana sanye da d'an guntun wandon da da ya manne sosai a jikin shi hannun Sophie gabad'aya akan wandon nashi tana shafa shi,yayinda shi kuma hannun sa ke kan qirjin ta yana shafata snn bakin su a had'e gam suna kissing d'in juna.
Zarah da tayi mugun gani ihu ta saki tare da sake breakfast d'in da umma ta aiko ta dashi dake cikin basket ta fita aguje.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Friday/09/02/2018_ *芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 8*
Umma na falo zata haura sama se ganin Zarah tayi aguje tazo duk a tsorace jikinta se rawa yake.
Da sauri umma ta riqo ta tace"lafiya Zarah me yake faruwa?
Komai zarah bata iya ce ma umma ba,se janye jikinta tayi da sauri zata haura sama zuwa d'akin su se ga Abba ya sauko da saurin sa wanda ya fito knn daga d'akin sa ya hango lokacin da zarah ta shigo aguje.
Bai bar ta wuce ba yace"mene ne zarah lafiya a ina kika fito haka?
Kuka kawai ta fashe masa dashi snn ta tafi aguje zuwa d'akin su.
Abba ya kalli umma yace"a ina ta fito?
Umma tace"6angaren Saifuddeen na aike ta ta kai masa breakfast shine ta dawo haka.
6angaren Saifuddeen?Abba ya tambaya.
Se dai kafin ma umma ta bashi amsa tuni ya fita da saurin sa ya nufi 6angaren Saifuddeen.
Shigar sa d'akin yayi dai dai da lokacinda Saifuddeen ya rufawa Sophie white bedsheets a jikinta yana ce mata tayi sauri taje ta 6uya a bathroom.
Cak Abba ya tsaya cike da tsananin mamaki yana kallon su wanda duk a tunanin sa ko Saifuddeen ya balbali zarah da masifar sa ne dan an aiko ta 6angaren shi se ya samu abunda be ta6a tsammani ba.
Ransa a mugun 6ace ya nufo su,Sophie ta fice da sauri jikinta na rawa ta shige bathroom ta rufe.
Tas!tas!!taji saukar marikan da Abba ya yiwa Saifuddeen wanda har sai da yayi taga taga kmr ze fad'i.
Abba ya nuna shi jikinsa na wani irin rawa sbd tsananin 6acin rai yace"maza ka sameni a falo yanzun nn!
Yana gama fad'ar haka ya fita.
Sophie na jin fitar sa ta fito da sauri tazo gun Saifuddeen idanuwan ta tap da qwallah take shafa kumatun sa da sukayi jajur duk yatsun Abba sun kwanta akai.
A fusace Saifuddeen ya ture ta daga jikinsa ya nufi wardrobe ta biyo shi da sauri,ya dakar mata tsawa kan kar ta kuskura ta ta6a shi.
Kuka Sophie ta fashe dashi ta zube qasa tana ta bashi haquri be kulata ba har ya ciro tufafin sa ya saka,zai fita har yakai bakin qofa ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba yace"u better leave this house b4 i came back.
Daga haka ya fita ba tare da ya jira me zata ce ba.
Koda yaje 6angaren su umma be sami Abba a falo ba kai tsaye ya haura sama zuwa d'akin su Nusaiba,Nusaiba ta fito daga bathroom knn se saukar gigitaccen mari taji a fuskarta,ba shiri ta dafe kuncen ta,ta saki ido cikin mugun tsorata tana dubin a ina marin ya fito,se ganin Saifuddeen tayi a gabanta wanda shine ya mare ta d'in,ransa a 6ace yace"uban me yakai ki 6angare na da har zaki shigar min d'aki without permission iye!
Da sauri ta girgiza kanta cikin kuka tace"wlh Allah bani bace ni ko lafiya ma bana da"
Yace"wat! bake bace u mean wnn banzan yarinyar ce taje 6angarena ta kuma shigar min d'aki haka kawai,lallai yau zanyi maganin ta wlh!
Ina take gaya min!?
Ya tambayi Nusaiba tace"ni ban sani ba"
Ya tambayi yusra tace mishi umma tazo ta tafi da ita.
Fuuu! ya fita a fusace ya nufi d'akin umma.
Da shigar sa ya sami Abba a d'akin yana snr da umma abin baqin cikin da ya gane ma idon sa.
kallon da Abba ya mai yasa yayi saurin sadda kansa qasa,snn cikin kakkausar murya Abba yace"falo nace kaje ka same ni dan uwar ka ba a nn ba very stupid get out! in daina ganin ka a nn shasha sha kawai mara kunya fitsararre.
Sum sum Saifuddeen ya fita gabad'aya ransa a dagule ko kad'an baiji dad'in faruwar hakan ba wanda yanzu bai san wane iri hukunci ne Abba zai yanke akanshi ba.
A hnkli yake tafiya har Abba yazo ya wuce shi yaje ya zauna kan doguwar kujera,kana Saifuddeen ya qarasa ya zauna qasa wanda gabad'aya jikinsa a sa6ule yake,tsoron sa d'aya kar Abba ya masa iyaka da Sophie.
Kansa qasa yana sauraren me Abba zai ce dashi,Abba be ce dashi komai ba har se da umma ta qaraso ta zauna.
A hnkli Saifuddeen ya d'ago ya kalle ta ya d'an marairaice fuskar sa alamar ta taimaka ta bawa Abba haquri plz.
Shaye da toka umma ta dallah mai uwar harara ae kuwa yayi qasa da kanshi muryar sa a hnkli yace"Abba dan Allah kayi haquri"
Muryar Abba daji kasan sosai ransa a 6ace yake yace"bari kaji in gaya maka Saifuddeen wlh kaji na rantse kar in sake ganin ka da wnn yarinyar har abada,a waya ko a bayan idona ka sake kula ta bazan ta6a yafe maka ba!.
Take Saifuddeen ya runtse idanun sa gam lokaci d'aya jijiyoyin kansa duk suka taso yana jin kansa cikin wani irin yanayin dashi kansa be san ma yazai fisalta ba dmn ko mutuwar Sophie yaji baya jin ze sami kansa a yanayin da ya tsinci kansa a yanzu.
Kana ya bud'e idanun sa tare da had'e tafukan hannayen sa yana kallon Abba muryar sa na rawa yace"Abba dan girman Allah kayi haquri ka janye min wlh bazan iya ba"
Abba ya kalle sa da kmr mamaki yace"baza ka iya ba!to kasani wnn d'in ko zaka iya ko baza ka iya ba dole se ka kar6e shi umarni ne,sati mai zuwa rnr juma'a zan d'aura auren ka da zarah!.
Kamar saukar guduma Saifuddeen yaji mgnr ya miqe zumbur yana kallon Abba wanda yana gama fad'ar mgnr ya ficewar shi ya haura sama.
A rud'e ya rarrafa gurin umma dake qoqarin tashi ya kama hannayen ta yace"umma na shiga uku wace ce kuma zarah!?
Umma tace"Zarah dai da ka sani baquwar gidan nn"
Saifuddeen da sam bai kawo ita Abba ke nufi ba,ba shiri ya saki hannun umma tare da girgiza kansa snn cikin wata irin murya da shi kansa bai san yana da ita ba yace"never!wlh nasan Abba ya fad'a ne kawai sbd 6acin randa na saka shi a ciki"
ya tashi a kid'ime kmr wani zautacce yace"umma bari naje na same shi na bashi haquri,na amince zanyi rayuwa ba Sophie kmr yanda yake so bazan sake kulata ba har se da izinin shi.
Tashi umma tayi tare da riqo hannun sa tana kallon sa lokaci d'aya duk ya haukace.
Tace"Saifuddeen sam 6acin randa kasa Abban ka a ciki ba shine dalilin da yasa yace zai had'a auren ka da zarah ba,asalin zuwan Zarah a gidan nn dmn ya had'a auren ku ne amma a niyar sa se tayi karatu,wanda yanzu ya janyo auren kusa ne sbd ya fahimci kana neman ka kunyata mu ne a idon duniya!.
Da sauri ya girgiza kansa lips d'insa na rawa cike da son yace wani abu,umma tayi saurin dakatar da shi ta hanyar d'aga masa hannu tace"bazan saurare ka ba Saifuddeen,kasan halin Abbanka sarai idan ya fad'i magana bazai ta6a canzawa ba.
Tana gama fad'ar haka ta wuce,ya bita da kallo idanuwan sa sunyi jajur a ransa yana fad'in"wnn karon zai canza dmn bazai ta6a yiyu na aure ta ba wlh"
Daga haka ya bar 6angaren bai zarce koina ba se 6angaren shi,be sami Sophie a 6angaren ba ta tafi kmr yanda yace dmn sosai tana gudun zuciyar shi shi kansa ya sani shiyasa yake matuqar sonta.
Sakwaf yaje ya zauna kan bed ya sauke idon sa akan wata farar kyanwa wacce ba d'igon komai a jikinta ko inan ta duk fari ne du6u du6ul da ita er qarama ta dunqule guri d'aya se bacci take tayi abunta.
Kyanwar Sophie ce wacce take matuqar ji da ita idan tana bacci sam bata son wani abun da zai tashe ta shiyasa bata je da ita ba ta barta.
Saifudddeen dake kallonta ya maida duban sa gun hoton su dake ajiye kan bedside drawer yana kallon fuskar Sophie gabad'aya yau ta mugun 6ata mishi rai dan kusan duk ita taja komai,dmn sam ba'a son ranshi yazo da ita gidan ba se dan matsa mishin da tayi kan lallai ita se tazo ta mishi ko kwana d'aya ne,yanzu ga abunda kwana d'ayan yaja musu,take kuma takaicin sa ya koma kan zarah a lokacinda ya maida duban sa gun basket d'inda ta 6arar,ba kad'an ba yaso ya samu damar damqar ta ya mata hukuncin da ko a mafarki baza ta sake fatar ta ganta a gidan nn ba bare hanyar 6angaren shi.
Kana yayi wani irin murmushi me ciwon gaske wai shi Abba ze had'a auren sa da ita,mummunan mafarki knn dan muddin Abba yace dagaske yake zai had'a auren sa da ita se dai a nemi yarinyar a rasa.
Hm Kaiyh! it's better ya gaggauta zuwa ya samu Abban Kd dmn ya bawa Abba haquri.
Abban Kd
cewa da Abokin tawaicin Abba wato en biyu ne shida Abba,Shine Hassan Abba kuma Hussain.
Nan ba 6ata lokaci Saifuddeen ya d'auki makullin motar sa ya tafi se zuwa kd.
Umma kuma koda ta koma d'akin ta ta sami Abba zaune kan sofa zarah na zaune qasa a gaban shi ta sadda kanta qasa yana snr da ita auren su da yake son zai had'a ita da Saifuddeen wanda yana magana ne cikin natsuwa da kuma neman amincewar ta.
Ganin bata iya ce masa komai ba ya kalli umma yace"kiyi magana da ita idan ta amince to idan kuma bata amince ba kar ki mata dole"
Nan ya tashi ya fita umma ta zauna kan sofa d'in tana kallon zarah da still kanta a qasa
tace"Zarah meyasa Alhj na maki magana kikayi shiru ko ba kya son auren ne?
Da sauri zarah ta d'ago idanun ta dake cike tap da qwallah tace"eh inna"
"Oh my God!"
Umma ta fad'a snn a hnkli ta kama hannun Zarah ta zaunar da ita kusa da ita tana kallon ta muryar ta a hankli tace"meyasa zarah?
Zarah tace"inna ni gaskiya bazan iya auren me irin halin shi ba"
Umma dake kallon ta,ta numfasa tace"Zarah kiyi haquri ki amince da buqatar Alhj sanin kanki ne bai cancanci kice masa a'a ba"
Zarah ta kalli umma cikin muryar kuka tace"na sani inna shiyasa ma na kasa ce masa komai amma a gaskiya bana son auren haka shima nasan baya so komai zai iya faruwa idan aka had'a aure na dashi.
Umma tace"ba abinda zai faru se alheri Zarah"
Hawaye ne suka silalo akan kumatun zarah dake kallon umma tace"nidai inna dan Allah a'a,tare fa na gansu shida wata meyasa baza a had'a shi da ita ba"
Umma tace"Zarah Saifuddeen da wnn baturiyar sam auren su bazai ta6a yiyu ba,ke Alhj ke son Saifuddeen ya aura asali ma shine ya tura ni musamman rimin dako naje nazo dake garin nn sbd yana son had'a auren ku,kinga kuwa idan baki amince ba bazai ji dad'i ba, haka nima bazan ji dad'i ba,inna ma baza taji dad'i ba sbd tasan da zancen tun rnr da naje nazo dake.
Shiru zarah tayi tana kallon umma d'auke da hawayen da ke kan fuskar ta bata share ba,tayi qasa da idanun ta snn tace"inna d'an iska ne fa bashi da hali nagari me yasa kuke so na aure shi"
Da kulawa umma ta kalle ta snn tace"Zarah kiyi haquri idan kika aure sa kmr kinyi jahadi ne,inshaa Allah zai rabu da duk wasu banzan d'abi'un da yakeyi kinji"
A hnkli zarah ta gyad'a mata kai tare da saurin share hawayen da suka zubo mata.
Umma taja ta zuwa jikinta se qara rarrashin ta take cike da tunani fal a ranta,haqiqa ita kanta ba son auren take ba sbd wani dalili da yasa ta hango abubuwa da dama a cikin auren amma tunda Abba yana so ba yanda zatayi.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Saturday/10/02/2018_
*芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN!芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 9*
Yusra ce ta shigo d'akin bata qarasa gurin su ba se tsaye kawai tayi tana kallon su kmr yanda umma ke kallonta,zarah dake rungume jikin umma taji alamun shigowar mutum se dai bata san waye ba nn ta janye jikinta a hankli daga jikin umma,ta juyo ta kalli yusra bata ce mata komai ba se tashi tayi ta fita daga d'akin,yusra ta bita da kallo har ta fita snn ta qarasa gun umma tace"umma halan me Anti zarah da anty nucy suka ma yaya da ya dake su?
Umma tace"ya dake su?
Yusra tace"Eh a gabana ya mari anti nucy gata can ma se kuka take tayi.
"oh Allah me kuma Nusaiba ta mishi da zai mare ta muje in ganta"
Umma ta fad'a tare da jan hannun yusra suka je d'akin su Nusaiba.
Kan bed ta zauna tana kallon Nusaiba dake kwance kan bed tana kuka kuncen ta duk yatsun saif ne da suka kwanta.
A hnkli umma ta shafi kuncen nata tace"laifin me kika masa?
Cikin kuka Nusaiba tace"ba abinda na mishi,wai ya d'auka ko nice naje 6angaren shi shine ina fitowa daga bathroom se jin saukar mari nayi bansan hawa ba bansan sauka ba.
Umma da tayi shiru tana kallonta tace"Ayya sorry kinji k'yale shi,kana takai hannun ta a hankli tana share mata hawaye.
Saifuddeen kuwa yana isa kd kai tsaye gidan Abban kd ya nufa ginin gidan sak irin nasu dake kano komai iri d'aya.
Zaune yake a falo yana jiran fitowar hjyr gidan da ya aika mai akin gidan ta kira mishi ita.
Jim kad'an se gata ta fito wacce kallo d'aya zaka mata kasan cewa jini d'aya ce da umma wato yayar umma ce uwar su d'aya uban su d'aya.
A natse Saifuddeen ya gaida ta ta amsa tare da zama kusa dashi tana kallon sa da kulawa ganin irin yanda yake cikin damuwa sosai,
tace"saifudddeen lafiya me yake faruwa?
Kallonta yayi d'auke da idanuwan sa da still suke jajur yace"sosai ina cikin damuwa umma,Abba nake son gani ko yana nn?
Cikin yanayin damuwa ta numfasa snn tace"eh yana nn bari na kira maka shi"
Nan ta tashi jiki sa6ule ta haura sama zuwa d'akin shi.
Ba 6ata lokaci se gashi ya fito,Saifuddeen ya zame qasa ya zauna tare da gaida shi.
Abban kd da sak kmr sa d'aya da Abba tamkar an tsaga kara,ya zauna a natse tare da amsa gaisuwar da Saifuddeen ya mishi,snn da kulawa yace"ina jinka Saifuddeen gaya min meye damuwar ka Maman Salma ta gaya min kana cikin damuwa"
Saifuddeen kansa qasa yace"eh Abba wlh nayiwa Abba laifi ne ya yanke min tsastsauran hukunci shine nake son dan Allah ka taimaka min ka bashi haquri ya janye min nayi alqawarin zan kiyaye bazan sake aikata abunda na aikata ba.
Abban kd dake kallon shi ya numfasa snn yace"me ka mishi tukun inji?
Saifuddeen bai 6oye mishi komai ba ya gaya mishi duk abinda ya faru.
Abban kd ya jinjina kansa yace"cabd'i lallai Saifuddeen karatun da ka koyo a England knn,to ka sani sam baka kyauta ba ka kuma d'auko abunda kaf dangin mu ba wanda ya ta6a aikata hakan,kuma hukuncin da Abbanka ya yanke maka shine