Showing 66001 words to 69000 words out of 145898 words
sa ta nuna cikin kasa dannewa yace"kamar yanda nima kika san har abada bazan ta6a qaunar ki ba,shiyasa ma nake gab da cika maki alqawarin ki in huta da ganin ki a gidana.
"Kodai ni na huta da muguntar ka ba"
Ta fad'a tare da kauda fuskar ta gefe duk ranta a 6ace.
Saif ya kalle ta wanda se a lokacin yaga ashe jiya ya ji mata ciwo a gefen lips d'inta gurin yayi kwancin jini na alamar cizo snn kuma ya d'an kumbura kad'an.
Da kulawa yakai babban yatsan sa yana shafa gurin a hankali,zarah ta ture hannu nashi da sauri cikin dalla mishi harara.
Yayi murmushi tare da maida hanklin sa kan tuqi,wanda har ya sauke ta school bata sake yarda ta kalli ko gefen shi ba,dan sosai taji haushin maganganun sa.
Da yamma liqis har magrib na qoqarin gabatowa,still zarah na school zaune cikin class,bata kira driver ba kuma bata da niyyar kiran shi dan har yanzu driver take kira amma saif ke zowa,but ba wnn ne damuwar ta ba irin Assignments d'in da ke gaban ta,da ta kasa yin ko d'aya a cikin uku,bcos ba easy bane kuma bata nn koda aka bada Assignments d'in tana Rimin daako har gashi gobe da safe za'ayi submit,wanda basuyi ba suna nn a cikin class d'in suma seyi suke tayi amma ita ta kasa yi duk haushi ya cika ta tana kallon takardun da ke gaban ta kmr ta fashe da kuka.
Qamshin turaren saif da taji ne yasa ta d'ago fuskar ta a hankli taga shi d'in ne,d'auke da mamaki take kallon shi wanda yasa hannu ya shiga tattara takardun da ke gabanta ya saka a jakar ta,nn se ga wani yazo gun zarah riqe da duka assignments d'in sa da yayi yace"wato qanwa ba kya nn koda akayi lecture akan topics d'in nn shiyasa abun ya maki wahala,gashi kuma lokaci ya qure bare na zauna na fahimtar dake,shiyasa nace bari kawai na kawo miki nawa Assignments d'in kije da su gida kiyi gobe da safe idan mun had'u se ki bani ko.
Kafin zarah tace"komai saif ya masa wani mugun kallon da yasa guy d'in ya bar gurin sum sum,shi kuma ya kama hannun zarah ransa a 6ace suka fita daga class d'in.
_Monday 12/03/2018_
*«»»««»SAIFUDDEEN!«»»««»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«» 34*
Zarah na biye dashi se kallon sa kawai da take har ya tafi da ita suka shiga mota,amma har suka iso gida in banda sharara gudu da yake faman yi da mota ba abunda yace da ita,kawai dai suna isowa gida kamar yanda yasa ta a mota ran sa a 6ace haka ya bud'e ganbun motar ransa a 6ace ya fizgo hannun ta ya fito da ita.
zarah ta shiga qoqarin qwace hannun ta tana fad'in"wai meye haka dan Allah ni ka sake ni!
Be kula ta ba har sai da suka shigo falo dai dai ta samu ta fizge hannun ta,shi kuma a fusace ya had'a bayan ta da jikin qofar fallon ya manne har sai da qofar ta rufe da qarfi.
Da sauri zarah ta qara kamewa a jikin qofar kan yanda ya doka hannayen sa da qarfi a jikin ganbu yasa ta a tsakiyar shi yana kallon ta cike da 6acin rai,snn with deep voice yace"gaya min waye wnn d'an iskan yaron da yazo ya same ki har inda kk zaune?.
Wani iri taji abun banbarakwai tace"Ikon Allah kai kuwa meye ruwan ka dashi ka ji min"
Ubanki ne ruwana dashi very stupid zaki gaya min waye shi ko se nayi gunduwa gunduwa dake a nn gurin"
Ni ban san waye shi ba ta fad'a had'e da qoqarin ture shi dmn ta wuce"
Ba shiri ta fasa ihu sbd qafar sa da yasa ya daki qafar ta da qarfi snn ya fizgo ta cikin riqo kafad'un ta yace"waye shi nace ki gaya min!
Kuka zarah ta fashe dashi tare da fad'in"ni ban san shi ba kawai dai na san d'an course d'in mu ne"
Shine to har ze kira ki qanwa wai kuma har yana fad'in da akwai lokaci da ya zauna ya miki bayani dan uban shi,to bari kiji in gaya miki wlh duk iskancin da zakiyi ki bari idan na kwance igiyar aure na akanki,ki tafi can kiyi tayi da duk uban da zakiyi amma bawai kina gidana ba.
Wawiya kawai wacce bata san darajar aure ba.
Yayi tsaki tare da ture ta gefe har se da ta fad'i zaune snn ya wuce fuuu!ya haura sama zuwa d'akin shi.
Zarah kuwa bata tashi ba se kuka taci gaba dayi a gurin riqe da qafar ta se can byn tayi me isar ta snn ta tashi ta tafi d'aki.
Guraren 11 saif ya fito sanye da kayan bacci ya nufi d'akin ta,wanda a tunanin sa zai samu tayi bacci amma se ya same ta zaune kan bed ta had'e qirjinta da cinyoyinta idanun ta cike tap da qwallah tana kallon takardun assignments d'in ta ajiye a gaban ta.
Ya qarasa a hankli ya zauna ze d'auki takardun dmn ya duba,da saurin ta ta riga shi d'auke takardun tare da sauka kan gadon.
Beyi yunqurin riqo ta ba se binta kawai yayi da kallo har ta fita daga d'akin,taje downstairs ta kwanta ruf da ciki kan doguwar kujera 3saeter ta saki kuka a hankali.
Saif da ya fito yana kallon ta duk da ya fahimci kuka take be qarasa downstairs d'in ba yayi tafiyar shi zuwa d'aki.
Har sai guraren 12:30 ya kwatanci cewa tayi bacci snn ya fito.
Ya same ta still tana nn kwance ruf da ciki tayi bacci gashin kanta duk ya rufe mata fuska,a hankali ya gurfana kan guiwar shi yayinda ya jigina d'ayar guiwar a jikin kujera gab da ita yakai hannun sa ya yaye mata sumar kanta da ta rufe mata fuska wanda se a lokacin yake tuna cewa kalaba ce fa a kanta duka duka yaushe ne a kayi ta,just 2dayz har ta tsefe,ya d'an ta6e bakin sa cikin ko in kula dan shi sam baya ra'ayin kitso duk da kalabar da aka mata ta mishi kyau,amma dai yafi son ganin gashi yasha gyara yana sheqi qamshi na fita akan a kitse.
Wanda a hankli ya shiga shafa sumar kan nata amma idon sa na kan eyelashes d'in ta dake d'auke da sanyin hawaye,bata jima da yin bacci ba knn dan har en guntayen hawaye ya gani a gefen idon ta har sun gifta kan karan hancin ta,ya tafi da babban yatsan sa sannu a hankli ya share mata hawayen,snn ya karkatar da kansa a hankli yana bin karan hancin nata da kallo da ya kasa d'auke yatsan sa akai,se ma tafiyan tsutsa ya shiga yi da yatsan nasa akan karan hancin nata ya tafi har zuwa lips d'in ta yana shafawa.
Wata kasala ce ta saukar mishi kan yanda yake jin laushin lips d'in ta akan d'an yatsan shi wanda hakan yasa ya lumshe idanun sa a hankli kafin yake ware su akan cheeks d'inta ya tafi da yatsan sa a gurin yana shafa dai dai inda dimples d'in ta ke lotsawa idan tayi dariya,ba akanta ya fara ganin dimples ba amma sosai yafi ganin kyawon nata but Why?
Ya tambayi kanshi.
Be iya ba kanshi amsa ba se dire idanun sa yayi akan rigar baccin da ke jikin ta,fara ce me santsi sosai yayinda hannun rigar ya kasance d'an siriri kamar na vest,snn tsayin ta zai kai zuwa rabin k'aurin ta,wacce tsaf ta fito mata da kyawon surar jikin ta,nn saif ya shagala se kallon surar jikin nata yake,shape d'in hips d'inta masu kyau kmr na Sophien shi,kawai dai tafi Sophie bumbum,dmn na Sophie basu da wani cikowa da zaka kalla kayi sha'awa kmr irin wad'anan da yake kallo har yana jin abu na fizgar shi da yasa ya kauda idanun sa da sauri.
Snn a hankli ya matsa ya kama lallausar qafar ta yana duba saman qafar wato kan inda ya daka mata qafar shi d'azun,gurin yayi ja abinda yayi tunani knn dan yasan takalmin sa masifar ciwo ne dasu.
Samun kansa yayi yana me murza mata gurin a hankali......
Nan qarar wayar sa da ya ajiye kan rug ya katse shi,koda ya d'auki wayar ya duba jamil ne me kiran amma kafin ya d'aga se kiran ya tsinke da kmr network problem dan kiran be isa tsinkewa ba.
Duba lokaci ya fara yi tukun"
"qarfe d'aya"
Ya fad'a d'auke da mamaki kan fuskar sa yana kallon agogon bangon falon yaga shima haka ne.
Kallon zarah yayi yana mamakin wane shagala ne yayi a kanta har 30 mnt be sani ba shida yake ganin kmr ma just 2mnt yayi a gurin.
Yayi kasaqe yana kallon ta,kana ya shiga dialling numbar jamil d'auke da tunanin meyasa jamil zai kira shi wnn lokaci.
Amma se bai sami jamil d'in ba har kusan sau uku bata shiga,nn kawai ya haqura da kiran,ya zauna kan rug yana me lanqwashe qafafun sa sannu a hankli kan tsamin da sukayi,snn daga nn ya d'auki assignments d'in zarah ya hau yi mata.
Washe gari tun da asuba qarar wayar zarah ta tashe ta sbd alarm d'in da saif ya sa mata,ta tashi da qyar se miqa take wacce a tunanin ta ko kira ne dan sam bata fahimci ba ringing d'in da take amfani da shi bane sai da ta duba taga alarm ne snn hankalin ta ya bata,amma se ta shiga tunanin ita da bata ma ta6a sa alarm ba ya akayi yau kawai ya tashe ta....se kuma da sauri ta katse kanta da wnn tunanin,tana kallon inda take ta yaya itada ke falo ta dawo d'aki har gata a kan bed.
"Na shiga uku"
Ta fad'a cikin jin tsoro idan ba gamo tayi da aljanu ba suka maido ta d'aki.
Se kuma tayi shiru hankalin ta yana d'an dawo mata,tana tuna jiya fa kmr a mafarki taji saif ya maida ta d'aki wanda sam bata ta6a kawo cewa ba mafarki take yi ba se yanzu da ta ganta a d'aki.
Hm ikon Allah duniyan cin sa me yawa ne abunda take ganin ana yiwa indiyawa a TV a d'auke su cak kmr wata er tsana shine ya kawo kanta dan dai jiya kusan kmr haka ta gani a cikin baccinta.
Nan bata gama mamakin abun ba ta hango Assignments d'in ta da ya mata ajiye kan bedside drawer,da saurin ta ta matsa ta d'auko tana dubawa taga kuwa duka ba wanda beyi mata ba.
Nan tayi murmushi me nuna alamar jin dad'i,duk da jiya ya 6ata mata rai amma zata masa godiya dan dai ya mata abunda ta kasa yi,duk da cewa ba kad'an ba taso ace ita tayiwa kanta Assignments d'in akan fahimtar ta,wanda hakan yasa taqi tambayar abokanan ta su ara mata se questions kawai da ta amsa a hannun su.
A hankali ta sauke numfashi ta tashi riqe da Assignments d'in taje ta saka a cikin jakar ta da take zuwa school da ita,snn ta fad'a bathroom ta d'auro arwala tazo tayi sallah.
Bayan ta idar ne tayi duk wani aiki da takeyi a gidan,tayi breakfast snn tayi wanka ta shirya ta fito,a niyyar ta ta jira fitowar saif dan duk ta fito haka kawai take ganin shima ya fito,amma akasin yau da ta samu har drivern da ke kaita school yazo yana jiran ta.
Taje ta shiga mota tana mai kallon gurin da saif ke ajiye motar shi taga motar bata nn,wata qil kiran gaggawa aka masa asibiti.
Abunda take tunani knn a ranta kafin driver ke jan mota suka bar gidan.
Wacce har satin ya qare driver ke kaita ya d'auko ta,ga alama saif tafiya yayi dan bata qara ganin shi ba har kwana uku yau saturday,ita kad'ai ke rayuwar a gidan bata san inda yaje ba bata kuma nemi ta sani ba.
Washe gari sunday da safe bayan ta gama share sharen gidan har ma tayi wanka tana kitchen ta jiyo knn riqe da tea a hannun ta zata fito se kawai taci karo da saif,taja baya da sauri gudun kar tean ya zuba a jikin shi,bata ankara ba se jin tayi tean ya zuba a hannun ta,ta saki qara tare da sake kofin snn taje aguje gun sink cikin yarfi da hannu zata bud'e famfo dmn ta sakarwa hannun nata ruwa,saif ya kama hannun da sauri yana dubawa.
Rai 6ace ta qwace hannun nata zata fita,ya riqo ta yana fad'in"sorry is not intentionally bada sani na bane"
Kallon shi kawai tayi still ranta a 6ace,ta ra6a ta gefen sa ta wuce,wacce ita bama tean da ya zuba a hannun ta ne yasa taji haushin sa ba,haka kawai taji ta sami kanta da jin haushin sa da ita kanta bata san dalili ba.
D'aki taje ta kasa zama se yawo take tana faman hura hannun ta dan sosai tean keda zafi,har ma gurin yayi ja.
Nan se ga saif ya shigo d'akin wanda kae tsaye ya kama hannun ta ya tafi da ita suka zauna kan bed snn ya kama hannun ta da tea ya zuba akai,da akwai d'an tube cream da ya shigo riqe dashi a hannun shi,ya matsa kad'an yana shafa mata a hankali.
Wani sanyi taji a cream d'in da ya ratsa hannun ta taji abun har cikin zuciyar ta,wanda hakan yasa ta lumshe idanun ta a hankali,saif yayi quri da idanun sa yana kallon fuskar ta har ma zuwa dressing d'in ta ba kad'an ba gown d'in da ke jikinta ta mata kyau.
Amma hankalin sa duk yafi karkata akan fuskar ta da ya sake maida duban sa akai,nn zarah ta ware idanunta a hankali sukayi 4 eyes,inda a natse saif yace"sorry lalura tasa nayi tafiya ban gaya miki ba,kakar jamil dake KD ce Allah yayi mata rasuwa shine naje se yau na samu dawowa.
Zarah dake kallon sa take se ta soma jin haushin sa da take ji yana tafiya a hankali,ta sadda idanunta qasa muryar ta a sanyaye tace"Allah yaji qanta yasa ta huta"
Yace"Amin,anjima da yamma se ki shirya mu tafi gidan su jamil ki masa gaisuwa.
A hankli ta gyad'a masa kai alamar taji.
Yayinda shi kuma ya tashi ya nufi fridge ya tsiyayo mata fresh milk a cup ya kawo mata,wacce dama tunanin ta knn ta nemi fresh milk tasha dan bata jin zata iya koma had'a wani tea,shiyasa bata musa masa ba ta kar6a tare da masa godiya snn ta bisa da kallo har ya fita daga d'akin.
Kana ta kauda fuskar ta tana tunanin meyasa Nusaiba da inna basu gaya mata rasuwar kakar yaya jamil ba,gashi kusan kullum se tayi waya dasu koda yake basa ma tunanin bata ji ba.
Nan kawai ta kai cup a bakin ta,ta hau shan fresh milk d'in saif ya kawo mata.
Da yamma guraren qarfe biyar suka tafi gidan su jamil,suna gab da qarasawa qofar shiga falo ne,se ga baqar kyanwa ta fito aguje daga cikin flowers,cikin mugun tsorata zara taje zuwa fasa ihu saif yasa hannun sa ya rufe bakin ta da sauri,tare da kai d'ayan hannu sa kan waist d'inta ya matso da ita sosai zuwa jikin shi yana kallon yanda duk idanunta suka ciko tap da qwallah snn jikinta na wani irin rawa,saif dake kallonta ya janye hannun sa kan bakinta tare da rungume ta a hankali zuwa jikin shi dan ya fahimci ta tsorata sosai fiye da yanda yake ganin tana tsorata idan taga kitty.
Wani irin abu jamil yaji kmr zuciyar sa zata faso qirjin sa ta fito wanda fitowar shi knn daga 6angaren shi ya gan su a haka.
_Tuesday 13/03/2018_
*«»»««»SAIFUDDEEN!«»»««»*
By
*Billy giro😊*
*Dedicated to»»»Zarah gwandu*
*«»Page«» 35*
Ji yayi kmr ya juya ko zai fi samun sa'ida amma hakan ya jure da qyar ya danne abunda yake ji ya qarasa gurin su cikin yin gyaran murya,hakan yasa zarah ta d'ago da sauri cikin share qwalla.
Kafin take sadda kanta qasa muryar ta a sanyaye ta gaida shi.
Fuskar sa ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar yana kallon ta snn ya kalli saif yace"what's wrong naga kmr kuka zarah keyi,and yanayin ta kmr she is not okay.
Saif ya kalli zarah kafin yake maida duban sa gun jamil yace"eh wlh ta tsorata ne sosai kan wata baqar kyanwa da ta fito aguje cikin flowers d'in nn ta fita.
Jamil da ya d'anji sauqin abunda yake ji a ranshi har yana sauke numfashi,yayi d'an guntun tsaki snn yace"kyanwar gate man ce wlh bansan a ina ya samo ta ba,but am sorry zarah kiyi haquri kinji"
Bata iya ce masa komai ba se gyad'a masa kae da tayi.
Snn suka shiga daga ciki,sun sami mtr mahaifin shi da kuma qanwar shi zainab a nn zaune falo,byn sun gaisa snn zarah ta musu gaisuwa,daga haka basu wani jima ba suka fito dan saif ya fahimci tsoron da zarah taji still be sake ta,ta jure ne kawai,dan da zasu fita gate suna kawowa ta gurin d'akin gateman,ta riqe hannun saif sosai dan ganin take kmr fitowa kyanwar zatayi,yayinda saif da kulawa ya qara riqe ta a jikin shi har sai da suka fita snn.
Jamil da ya raka su se a lokacin ya fahimci knn zarah tsoron kyanwa take,ba fitowar ta aguje kad'ai ne ya firgitata ba.
"Amma kuma shine saif ya bar kitty a gidan shi".
Ya fad'a tare da juyawa yana kallon saif da ya tashi mota suka wuce.
Yayinda a ranshi yake tunanin dole zai san abun yi kitty ta bar wnn gidan,dan ko wnn kyanwar ba barin ta zai yi ba yanzun nn zai yiwa gateman magana yayi gaba da ita baya son sake ganin ta a gidan.
Nan ya koma daga cikin gidan ya kalli mai gadi dake zaune kan bench a kusa da d'akin shi yace"kana ji na Audu ka d'auke wnn kyanwar daga gidan nn dan Allah bana son sake ganin ta dmn tana