Showing 129001 words to 132000 words out of 157890 words
uwa ta yi wa Ɗanta rowa ai ba kanta." Sumayya ba haka ta so ba don ta so maganar da ta faɗa ta ɓata wa Raihan rai amma sam bata lura da haka ba." A wani food flask Raihan ta zuba wa Sumayya ta miƙa mata sannan ta fice, jin ƙamshin na bugarta ya sa tun a hanya ta ɓuɗe ta damƙi loma ɗaya ta ci tana lumshe ido. Tun bayan fitar Sumayya jikin Raihan sanyi ya yi, ƙwallah ta ciko mata ido don a yanzu ta yadda da zarginta Sumayya wani cikin gare ta, hawaye ne ya zubo mata da ta kalli yadda ta shirga kwanukan Al'amin ta ƙarewa kanta kallo sannan ta tuno yau kusan watansu huɗu da aure amma babu wani abu da ya taɓa shiga tsakaninta da shi. Jiki a sanyaye ta ƙarasa aikinta ta koma Falo ta zauna tana ɗan danne-danne a wayarta. Har aka yi sallar magriba Al'amin bai dawo ba sai gabannin isha'i ta ji alamun shigowarsa, tana nan zaune ya shigo ƙamshin turarenta ya doki hancinsa har sai da lumshe ido, kallonta ya yi tana sanye da riga da sike na leshi ba ƙaramin kyau suka yi mata ba. Murmushi ta yi masa ta ƙarasa ta karɓi jakarsa, wannan karon ta yi mamaki da har ya mayar mata da martanin murmushi. Al'amin ji yake kamar ta rungume ta saboda yadda ya ga ta yi masa kyau, ita kanta Raihan ta lura da irin kallon da yake yi mata don haka take cikin farinciki haɗe da fatan ta samu babban matsayi a zuciyarsa. Sai da ya yi wanka a ɓangare Sumayya ya sako ƙananan kaya ya fita sallar isha'i ya dawo sannan ya ci abinci, yana cin dambu yana lumshe ido don ba ƙaramin daɗi ya yi ba, ita kuwa Sumayya a daddafe ta yi sallar Isha'i kasancewar wannan laulayin nata shi ma ba ƙaramin bacci yake saka ta ba. Lura da yanayinta da Al'amin ya yi kama ya sa idan ya dawo ko ranar girkinta ne idan ya ga tana bacci baya tashinta, don haka a wannan lokacin ma Al'amin ya ke ta kallon Raihan yana jin wani baƙon yanayi a tattare da ita. A zuciyarsa ya ƙudurce a ranar sai ya sauke mata nauyinta da yake kansa don ba ƙaramin nadama ya yi ba saboda tuna hukuncin da Ubangiji ya hukunta akansa, tausayi ta bashi da ya tuna tsawon watannin da suka ɗauka ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, har zuciyarsa ta fara ayyana masa da a ce ba mai tsoron Allah ba ce tuni ta nemar wa kanta mafita.
Bayan ya gama cin abinci Laptop ɗin sa ya ɗauko saboda wasu aikace-aikace da yake da su, Raihan na gajiya da zama ta wuce ɗakinta ta cire kayan jikinta ta saka wata doguwar riga mai shara-shara. Fitilar ɗakin ta kashe ta yi addu'a ta haye gado ta yi kwanciyarta, sai kusan goman dare Al'amin ya gama aikin da yake yi don haka ya miƙe ya fita daga gidan don ya tuna kayan tea ɗin su ya ƙare gashi washegari da wurwuri zai fita. Fitarsa ke da wuya Sumayya ta fito daga ɗakinta don wata irin azababbiyar yunwa ce ta tashe ta. Tana zuwa falo ta ga wani matashin saurayi ya fito daga sashen Raihan a furgice yana gyara tazugensa, tsoro ne ya kama Sumayya don a tunaninta Al'amin ne ya ji motsinta ya fito don haka a firgice ta furta, "Hubby me nake gani haka dama amanata kake ci ban sani ba?" Sai da ya gama ɗaure tazugensa sosai ya juyo ya kalli Sumayya ya ce, "Na miki kama da mijinki? Ni ma wurin masoyiyata na zo kuma na gama biyan buƙatata." Zaro ido Sumayya ta yi kafin ta yi magana ya fice daga ɗakin, a hargitse Sumayya ta riƙa ƙwalawa Al'amin kira jin shirun ya yi yawa ya sa ta faɗa ɗakinta ta rufe don tsoro ne ya kamata. Wayarta ta ɗauka jiki na rawa ta lalubo lambarsa ta fara kira, katse wa ta ga an yi babu jimawa ta ji kiransa ya shigo. Hannu na rawa ta ɗauka tana faɗin, "Kana ina Hubby?" Jin yadda take magana ya faɗar masa da gaba don haka ya furta, "Na ɗan fita amma ina hanyar dawowa." Sumayya ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "To wallahi yanzu na ga kwarto ya fito daga sashen Raihan ni dai ka yi sauri wallahi tsoro nake ji." Ras! Gaban Al'amin ya faɗi, har sai da ya yi parking ɗin motarsa a gefe jiki a sanyaye ya ce, "Gani nan ki rufe ƙofarki In sha Allah babu abin da zai faru." Bai jira cewarta ba ya katse wayar. A gaggauce ya lalubo lambar da aka kira shi babu jimawa, sake karanta sakon ya yi yana jin kansa na wani irin sara masa. "Ka na tare da Raihan ne ba don kamai ba amma ni saurayinta muna jone ni da ita, Raihan tsohuwar budurwata ce kuma ta gaya min duk irin zaman da kuke yi hasalima babu abin da ya shiga tsakaninku. Wannan dalilin ya sa take gayyatata a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, a yanzu haka ina can gidanka ina ɓarje shagalina don tun bayan fitarka ta kira ni a waya, idan kana musu ka buɗe Whatsapp ɗinka za ka tabbatar da abin da nake gaya maka. Na gaya maka ne domin ka sakar min abar ƙaunata idan ba haka ba kuwa mu ci gaba da shan shagalinmu a cikin gidanka ko kuma ta riƙa biyoni har mahallina kamar yadda ta saba zuwa da farko." Jikin Al'amin na rawa ya sake buɗe Whatsapp ɗin sa ya kuma duba waɗansu irin munanan hotunan Raihan maƙale da wani saurayi da lambar ta turo masa sai dai kiran duniya ya yi wa lambar ta ƙi shiga. Da wani irin gudu ya take motarsa ya nufi gida zuciyarsa na wata irin suya da raɗaɗi, a hargitse ya yi parking ya nufi cikin gidan kai tsaye ya wuce ɗakin Raihan. Tana kwace ta yi ɗaiɗai da alama ta ji daɗin baccin da take yi, cikin bacci ta ji an yi mata wata irin daƙuma. A firgice ta wartse idanunta suka sauka akan Al'amin, ganin yanayinsa ba ƙaramin tsoratata ya yi ba. Tana shirin yin magana ta riski muryarsa yana faɗin, "Ke munafuka ce annamimiya maci amana ashe duk wannan ladabi da biyayyar da kike yi min a munafurci ne?" Hawaye ne ya fara wanke fuskar Raihan don irin zagin da yake yi mata tun da ta zo duniya ba a taɓa yi mata irinsa ba, kasa buɗe baki ta yi balle ta yi masa magana sai ji ta yi ya wurgar da ita kan gado. Wayarta ya hango a gefen fulonta don haka ya ɗauka ya fice daga ɗakin, kan kujerar falo ya koma ya zauna ya haɗa kai da gwiwa maganansa suna sake tarayo masa munanan hotunan da aka tura masa. Ɗakin Sumayya ya ƙwanƙwasa sai da ji muryarsa sannan ta buɗe masa ƙofar, yana shiga ta faɗa jikinsa tana fashewa da kukan kissa ta ce, "Na rantse da Allah ban yi wa Raihan ƙarya ba da idona na ga kwarto ya fito daga sashenta." Jinjina kai ya yi cikin ɓacin rai ya furta, "Na ga komai kuma dole na ɗauki mataki akai." Daɗi ne ya kama Sumayya don ta san shi kenan ƙarshen zaman Raihan ya zo a cikin gidan, musamman da ta san halin Al'amin mutum zmai tsananin kishi. A daren ranar kusan kwana Al'amin ya yi yana jin wani irin kishinta don haka ya ji zuciyarsa na ɗaci duk da ba zai ce yana ƙaunar Raihan ba amma kishinta ya gama mamaye zuciyarsa. Yadda Al'amin ya riƙa juyi haka Raihan da bata san hawa ba balle sauka aka hau ta da faɗa ta riƙa juyi tana hawaye, ta maimaita maganganun Al'amin ya fi a irga. Daga ƙarshe ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah tana miƙa wa Allah lamuranta.
Tafiya suke cikin tsananin zafin rana a galabaita don kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da suna cikin wani irin mawuyacin hali, Hatsabibiya ce ta yanke jiki ta faɗi tana sauke numfashi da ƙyar. Ta ɗago jemammun idanunta tana kallon Abar bauta ta ce, "Wannan tafiyar da muke yi tana yi min kamanceceniya da dajin ƙare kukanka saboda ɗaya bayan ɗaya muna ta rasa rayuwarmu." Kuka ne ya ci ƙarfinta ya yin da ta tuna baƙar kurar da ta laƙume gawar mijinta, ta share ƙwallarta tana ci gaba da cewa, "Na yi babban rashi na maigidana wanda har abada ba zan taɓa manta mummunar mutuwar da ya yi ba, mun rasa Barira matar Alhaji Bala. Mun rasa Aljani Burdudu wakilin zuƙe jini shin kina ga za mu samu wanda zai maye gurbinsa? Mun rasa Alhaji Gali kasuwar kwari shi ma yana taimakawa Ƙungiya ta fannin shayar da ita jini, anya kina ga sannu a hankali ba za mu ƙare ba kafin mu ƙarasa tsibirin Jabbul-ƙasi?" Abar bauta da ita ma ta gama galabaita ta numfasa da ƙyar ta furta, "Ba za mu mutu mu duka ba kamar yadda Jabbul-ƙasi ya furta amma ni kaina ina jin tsoron wannan baƙar rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki. Ni kaina na fara sarewa duk da sarewa ba halina ba ne, amma ina yi mana fatan zuwanmu lafiya tun da tafiyar da ke gabanmu ko ta sa'a uku bata kai ba." Babu wanda ya sake tankawa ɗan uwansa suka ci gaba da tafiya a galabaice tafiyar da suke cin karo da munanan halittu masu firgitarwa, sai da suka shafe awa biyu da rabi suna tafiya sannan suka fara hango wani dogon tsauni wanda kallonsa kaɗai zai iya rikitar da idanu, daɗi suka ji har cikin zuciyarsu a lokacin saura su goma sha uku waɗanda suke rayayyu. Da sauri suka ci gaba da tafiya suna gabda shi ga tsibirin wata irin guguwa ta taso ta turbuɗe su haɗe da fara wurgi su tana maka su da ƙasa, sai da ta jima sannan ta fara sararawa, a hankali suka fara dawowa hayyacinsu lura suka yi da sun gabda ƙofar shiga tsibirin don haka suka miƙe a hankali, daga can nesa da su suka hango ragowar gawarwakin abokan tafiyar ta su, ba su damu ba don sun tabbatar da sun kawo tudun tsira tun da har ga su a ƙofar tsibirin Jabbul-ƙasi. Waɗansu gajerun baƙaƙen aljanu ne suka zo suka yi musu rakiya ta wata siririyar hanyar, suna tafe suna ƙare wa hanyar kallo, tafiya suka yi ta kusan minti goma sannan suka ɓulla a wani ƙaton fili mai ɗauke da wani irin haske tamkar hasken rana. Sai dai wurin a rufe yake ruf babu wata ƙofa da hasken rana za ta shigo, aljanun da suka yi musu wannan rakiyar ne suka dube su sannan suka furta, "A nan za mu dakata akwai wakilai na gaba." Suna rufe baki suka nutse ta ƙarƙashin ƙasa. Suna nan tsaye a daga bangon arewa suka hango wata mace ɗaure da wata saƙar baƙin ƙarfe, jin alamunsa ya sa ta ɗago a galabaice ta cikin ɗimuwa ta furta, "Ku yi min rai ku kawo min agaji wahala za ta kashe ni." Idan ba gizo idon Hatsabibiya yake yi ba gani take tamkar Mugaza, da hannu ta yafito Abar bauta ta yi mata maganar a hankali. Ware idanu ta yi karaf suka sauka akann Mugaza da ta jeme ta bushe ta lalace, jikinsu ne ya yi sanyi wata irin nadama ta shige su don haka suke ganin babbar wautar da suka tafka. Suna cikin wannan yanayin wasu dogayen Aljanu suka zo suka wuce da su zuwa ƙofa ta gaba, haka aka riƙa shiga da su ƙofofi har ƙofa saba'in da bakwai sannan suka ƙarasa wani babban fili, kallon wurin kaɗai ya isa kaɗa hantar cikin bil'adam idan bai aro jarumta ba ya haɗiyi zuciya ya mutu. Jinsin jinnu kuwa suna iya razana su shiga firgici don haka zuwansu Hatsabibiya ya saka su firgicewa har suna niyyar zubawa a guje suka ji wata irin razanannitar tsawa. Lokaci ɗaya suka tsaya ƙyam wuri ɗaya jikinsu na karkarwa daga bangon kudu suka hangi wata irin kujerar farin dutse na hudowa daga cikin ƙarƙashin ƙasa, mamalallakinta Jabbul-ƙasi na zaune akai hannunsa ɗauke da wani zabgegen takobin farin dutse. Wani irin yawu suka haɗiya wanda saura kaɗan su tafi da maƙogaronsu, suna shirin yin magana suka hango Huzaifa ya hudo ta bangon Kudu yana ƙyaƙyacewa da wata shu'umar dariya.
Jin hayaniya ta fara yawa ya sa Nurses suka taho wurin da sauri, suna ganin abubuwan da Kabiru yake yi da sauri suka kira security don ya fita da shi, amma bugu ɗaya Kabiru ya yi masa har sai da ya bugu da bango sannan ya faɗi ƙasa yana ƙwalla ƙara. Nan take suka fita da gudu suna kuruwa don lamarin ba ƙaramin tsoro ya ba su ba, Maryama ce ta farka daga bacci tana ƙarewa wurin kallo ganin Kabiru a tsaye ya sa ta saki murmushi ko da tana jin nauyin Inna wuro amma ta ji daɗin ganinsa don ta yi kewar mijinta. Inna wuro ce ta ƙarasa wurin Kabiru cikin kuka ta furta, "Ka dubi girman Allah Ibrahim ka yi haƙuri." Shiru Kabiru ya yi adaidai lokacin su Baffa suka ƙaraso cikin asibitin, tun ba su ƙarasa cikin ɗakin ba Inna wuro ta nufe su cikin tashin hankali cikin kuka tana faɗin, "Baffa ku zo ku gane min halin da yaron nan yake ciki, yana ganin jaririn Maryama shi kenan Ibrahima ya ziyarce shi." Da hanzari su Baffa suka ƙarasa gaban Kabiru Baffa ya dubi Kabiru sannan ya furta, "Ibrahim ka dubi girman Allah ka kama gabanka indai har yadda ka faɗa gaskiya ne Kabiru aboki kuma ɗan uwanka ne." Baffa ya dubi Inno wuro da ke sharɓar kuka sannan ya ci gaba da cewa, "Ka na ganin yadda mahaifiyar Kabiru take zubda ƙwallah shin jin daɗinka ne ko kuwa za ka so abin da zai musgana ran mahaifiyar amininka? Don Allah ka tashi mu wuce can gida amma a nan za ka tara mana jama'a ne." Kamar raƙumi da akala haka Kabiru ya bi bayan su Baffa suka wuce gida. Tun da suka tafi uffan Kabiru bai sake tankawa ba don haka babu wanda zai kalli Kabiru ya yi tsammanin baya cikin hayyacinsa. A haka har Maryama ta shafe kwana uku tana karɓar kulawa daga wurin likitoci, a kwanansu na huɗu aka sallame ta ita da jaririnta. Sai dai tun ranar da Kabiru ya tafi gida har ranar da aka sallami Maryama uffan bai sake tanka musu ba, wannan lamarin ba ƙaramin sake ɗaga hankalin su Inna wuro ya yi ba don komai ka cewa Kabiru sai dai ya bika da ido. Sai dai ya ci abinci ya yi sallah ya shiga banɗaki amma babu wani abu da yake yi bayan wannan, don haka koda lokacin suna ya zagayo babu wani taro da aka yi kasancewar shi kansa jaririn ba lafiyayye bane ga kuma shi ma Kabiru halin da yake ciki Kullin cikin yi masa turare da jiƙe-jiƙen magunguna suke.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
47
Ibrahim Alƙasim Bn Muhammad Mustafa shi ne ainihin sunan aljanin da ke jikin Kabiru, asalin haɗuwarsu sun haɗu ne a tsangaya tun suna ƙanana. A lokacin da aka kai Kabiru karatu ne suka ƙulla abota da Ibrahim da ke ɗauke da siffar mutane don ko kaɗan babu wanda ya san Ibrahim ba mutum ba ne sai Malaminsu, dalilin da ya sa ta su ta zo ɗaya kasancewar kusan shekarunsu ɗaya, kuma lokacin da aka kai Kabiru almajiranci ya daɗe idan ya tuno su Inno wuro yana kuka. Idan yana kuka shi ma sai Ibrahim ya zo kusa da shi ya zauna ya fara kuka sakamakon tuno na shi mahaifan da ya yi. Haka za su zauna su ci gaba da koke-koke idan suka gama su share hawayensu su tafi yawon bara. Kamar yadda Baffajo yake ziyartar Kabiru shi ma haka Mahaifinsa yake kai masa ziyara bayan wani lokaci, a haka suka taso cikin soyayya da shaƙuwar junansu saboda duk inda aka ga Ibrahim za a ga Kabiru, a wannan rayuwar suka girma har suka yi saukar Alƙur'ani. A lokacin Kabiru na shekara ashirin daidai haka shi ma Ibrahim, tun da lokacin saukarsu ta ƙarato idan suka tuna lokacin rabuwa ya zo kowannensu yana jin babu daɗi hasali wani lokacin har ƙwalla Kabiru yake yi. Saura sati guda su Kabiru su tafi wata rana suna zaune suna hira Ibrahim ya dubi Kabiru ya ce, "Kabiru ga shi lokacin rabuwarmu ta zo amma daga ni har kai babu wanda ya san garin kowa." Cikin damuwa Kabiru ya ce, "Wallahi kuwa Ibrahim amma mai zai hana na fara zuwa garinku idan ya so in Baffa zai zo tafiya da ni ba sai ka bi mu ni ma ka gano ƙauyenmu ba." Ibrahim bai damu ba ya ce, "Shi kenan babu damuwa amma ba za ka ji tsoron mutanen garinmu ba kuwa?" Cikin halin ko'inkula Kabiru ya ce, "Sai ka ce wasu dodanni zan ji tsoronsu. Allah ya kaimu kawai mu tsayar da lokaci." Nan take suka tsayar da ranar tafiya sai dai tun da aka tsayar da lokacin tafiya Ibrahim yake cikin damuwa, fargabarsa ɗaya kada ya bayannawa Kabiru kansa ya zo ya guje shi a ɓangare ɗaya kuma yana tsoron kada ya kai shi duniyarsu wani abu ya faru Kabiru ya razana abotarsu ta zo ƙarshe duk da ya san babu wani abin cutarwa da ahalinsa za su yi masa. A haka har suka samu Malaminsu da maganar, da farko ya so ya hana su tafiyar amma a wani dare sai Ibrahim ya samu Malam ya roƙ shi akan ya bar shi su tafi. Ba don ya so ba ya amince musu Kabiru ya ɗebi kayansa kala biyu suka ɗauki hanya, sai da suka ɗan yi tafiya ta ƙasa mai nisa har sun fara shiga cikin daji Kabiru ya dubi Ibrahim ya ce, "Kai Abokina wannan wacce irin tafiya ce