Showing 105001 words to 108000 words out of 157890 words
jin abin da Al'amin yake faɗa ba ya katse wayar, ba a ɗauki lokaci ba Malam ya ƙarasa asibitin. Daga harabar asibitin ya kira Al'amin yana tambayar ɓangaren da suke, Malam na shiga ya sauke idonsa akan Raihan yana faɗin, "Garin yaya hatsarin ya faru..." Sauran maganarsa ce ta maƙale jiki na rawa ya ƙarasa bakin gadon yana faɗin, "Raihan!" Police ɗin da Al'amin suka juya da sauri suna kallonsa, cikin tsananin mamaki Al'amin ya ce, "Daddy ka santa ne?" Malam ya sake matsa wa gaban gadon da Raihan take bacci saboda allurara baccin da aka yi mata ya yi, ya juyo wurin yana kallon Al'amin ya ce, "Raihan ita ce yarinyar da ta ɓace ranar daren aurenta." Da sauri Al'amin ya ƙarasa gaban gadon yana ƙare mata kallo, sai a lokacin ya tabbatar da kammaninta. Police ɗin da ke gefe ya ƙarasa yana faɗin, "Wallahi Alhaji tun gani na da ita nake wasu-wasi idanuna suke gane min kamar ita ce amma sai na yi tunanin wannan ko masu rangwamen hankali ce." Malam na gama jin sa ya sauke ajiyar zuciya haɗe da zaro waya ya furta, "Ai ta kwana gidan sauƙi. Kai Alhamdulillah Allah shi ne abin godiya." Wayar Daddy ya kira bata daɗe tana shiga ba ya ji an ɗauka, ko ƙwaƙƙwarar gaisuwa ba su yi ba Malam ya ce, "Alhaji don Allah ka ƙaraso yanzu ina Health Care Clinic na kan titin sharaɗa." Cikin sauri Daddy ya ce, "Malam Allah ya sa an dace ko an ganta ne." Malam ya yi murmushi mara sauti ya ce, "A'a ba haka ba ne amma ka dai ƙaraso yanzu." Katse wayar Daddy ya yi cikin sauri ya shiga mota kamar Yadda Malam ya gaya masa sunan asibitin sai ga shi bai ɗauki lokaci ba ya ƙaraso, kiran Malam ya yi ya sanar da shi yana harabar asibiti nan take Malam ya tura Al'amin ya taho da shi, sai da Al'amin ya gaishe da Daddy cikin girmamawa sannan ya yi gaba Daddy na biye da shi zuciyarsa sai buga wa take yi. Shigarsa ɗakin ya kusa daskarar da numfashinsa, murza idonsa ya yi ya sake ware su akan Raihan da ke kwance a kan gadon cikin wani irin yanayi, duk wanda ya ganta a wannan lokacin ba zai taɓa tsammanin mai cikakkkiyar lafiya ba ce, kana ganinta za ka yi tunanin ko mahaukaciya ce sabon kamu. Da sauri Daddy matsa gaban gadon sai kawai ya rungumeta haɗe da ruƙo hannunta tsam kamar wani zai ƙwace ta, Malam ne ya riƙo hannunsa ya ɗago Daddy ya nuna masa kujera sannan ya ce, "Godiya za mu yi wa Allah da ya bayyana mana ita, komai ka ga ya faru da bawa yana daga cikin jarrabawarsa don haka sai mutum ya sa hannu bibbiyu ya rugumeta a yadda ta zo masa, kuma ya gode wa Allah." Jinjina kai Daddy ya yi ya ce, "Wannan haka yake sai dai mu ce Alhamdulillah." Nan take Malam ya zayyana wa Daddy duk abin da ya faru, jim Daddy ya yi ya furta: "Shi Huzaifa ba a gan shi ba kenan? Ya Rabbi! Ubangiji ka bayyana wannan yaron cikin ƙoshin lafiya." Gabaɗaya suka amsa da amin. Daddy ne ya ciro waya ya kira Mommy ya sanar mata halin da ake ciki, a take ta miƙe ta ce ta warke don duk yadda Likitoci suka so dakatar da ita ƙi ta yi. Ita da Mama Hafsa suka ƙarasa asibitin Mommy na shiga ta saka kuka haɗe da faɗa wa jikin Raihan, a hankali Raihan ta buɗe idonta tana ƙare wa mutanen da ke ɗakin kallo. Karaf idanunta suka sauka akan Al'amin da yake danna waya yana sakin murmushi. Yunƙura wa ta yi za ta tashi zaune Mama Hafsa ta taimaka mata, kallon su Daddy ta fara sai kawai ta saka musu kuka. Duk yadda Daddy ya kai da yin dauriya sai da hawaye ya zubo masa. Ganin haka ya sa Malam ya miƙe yana shirin yi wa Al'amin magana Raihan ta nuna Al'amin ta ce, "Mommy kin gan shi, don Allah kema kina ganinsa." Sai a lokacin Mommy ta kai idonta wurin Al'amin da ya ɗago suka haɗa ido. Ita kanta mommy ta yi mamakin ganinsa tana shirin yin magana Malam ya ce, "Raihan wa kike gani Al'amin ko wani ne daban?" Ya yi mata wannan tambayar ne don ya tabbatar da ba buɗe mata ido suka yi ba. Raihan ta sake nuna Al'amin ta ce, "Abba wannan fa mai baƙaƙen kayan nan wallahi a Harami na taɓa ganinsa." Malam ya yi murmushi ya ce, "Yayanki ne, ai yarona ne sunansa Al'amin." Mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Raihan da jin Al'amin ɗan gidan Malam ne amma ta shafe shakaru tana dakon soyayyarsa, ba su yi aune ba sai gani suka yi murmushi ya kuɓuce mata. Ta koma ta kwanta haɗe da lumshe ido, Malam da Al'amin sallama suka yi wa Daddy suka tafi tare da cewar zai turo wa Raihan waɗansu magunguna a riƙa bata da na turarawa.
Inna wuro na yin sallama da Kabiru ta wuce gida shi kuma Kabiru ya ci gana da kula da Baffajo duk da ciwon nasa sai dai a ce da sauƙin musulunci. Washegarin ranar da Kabiru ya je garin a ranar ne Allah ya yi wa Baffajo rasuwa, mutane da dama sun ji mutuwarsa musamman da jinyar Baffajo ta zama sananniya ce a cikin garinsu Kabiru, kafin wani lokaci tuni aka karaɗe cikin rugar da sanarwar mutuwar tare da cewar za a yi jana'izarsa bayan sallar Azahar. Duk da kasancewar Kabiru namiji ne amma hakan bai hana shi zubar da ƙwallah ba, kafin a yi jana'izar Baffajo ya kira Daddy ya sanar da shi a nan kuma shi ma yake jin daddaɗan labari na dawowar Raihan, Daddy ya ce masa za su shiryo washegari su zo gaisuwa. Farinciki ya yi sosai ya yi wa Allah godiya sannan suka yi sallam, kamar yadda aka shelanta ana idar da sallar Azahar aka yi wa Baffajo sallah sannan aka kai shi gidansa na gaskiya. Da yammacin ranar Kabiru ya shiga cikin gari ya siyo kayan abinci masu yawan gaske, saboda masu zaman makoki, a rumbun hatsi ya ce a riƙa shiga da kayan abincin ana buɗe wa suka ga ya yi tsalle ya fito tsidik sai ga shi a gaban Kabiru. Ras ƙirjin Kabiru ya buga ya kalli hagu da dama yana shirin yin wani yunƙuri ya ji Talatuwa na cewa, "Hai ga mari babban kifi ya fito." Da hannu ya riƙa kai wa yaran duka yama zaro harshe waje. Ganin bai kalli ƙurar Kabiru ba duk da sun haɗa ido ya harzuƙa shi, don gani yake rainin wayon Huzaifa har ya yi yawa. Afusace ya sha gaban Huzaifa ya tattakura ya ɗauke shi da mari, kafin ya an kara Kabiru ya sake ɗauke shi da wani marin jikinsa na rawa ya shaƙi wuyan Huzaifa yana faɗin, "Me ya sa ka wahalar da ƴar mutane bayan ka san ba ƙaunarta kake ba? Ka fito ka gaya mana wanene kai?" Huzaifa ya dafe kunci yana kallon Kabiru a tsorace sai kawai ya fashe da kuka. Da sauri Jume da fasa ihu tana kiran maza su zo su taimaka Kabiru yana dukan ɗan tsintuwa, kafin wani lokaci tuni wurin ya ɗinke da mutane kowa yana bawa idonsa abinci. Da ƙyar su Baffa Giɗaɗo suka kwaci Huzaifa suka rufe Kabiru da faɗa, duk yadda Kabiru ya so fahimtar da su wani abu game da Huzaifa fir suka ƙi sauraronsa. Kaiwa da kawowa ya fara yi a cikin gidan jikinsa na rawa, da sauri ya fice daga gidan ya wuce can bayan gari. Sai da ya yi nesa da jama'a sannan ya kira lambar Daddy ya sanar masa da abin da yake faruwa, wannan labari ba ƙaramin faranta ran su Daddy ya yi ba, nan take ya kira iyayen Huzaifa da jami'an tsaro ya sanar musu da abin da yake faruwa. Tun a ranar Jami'an tsaron da ke kula da shiyyar jahar Kano suka kira wasu daga cikin jami'an tsaron da ke garin Shanono, suka sanar musu duk abin da yake faruwa. Duk wani shirye-shirye game da zuwan su Daddy da iyayen Huzaifa garinsu Kabiri a ranar suka yi shi. Saboda Kabiru ya sanar musu da babu yanda bai yi don su saurare shi amma sun ƙi. A washegarin Ranar Daddy da Mahaifin Huzaifa sai yayansa suka shirya zuwa garinsu Kabiru, da yake Daddy ya san garin ba su sha wahalar kwatance ba. A headquarter hukumar ƴan sanda suka fara sauka kasancewar tare da su za su ƙarasa garin, da yake dama an san da zuwan su Daddy ba su ɓata lokaci ba suka wuce cikin rugarsu Kabiru. Tun da suka shiga yara suke bin su da kallo, tsararu daga cikinsu suna biye a bayan motar suna kurma ihu don abin mamaki da tsoro ne a wurinsu, sakamakon sun jima ba tare da sun ga motar ƴan sanda a cikin rugar ba.
Kabiru na jin dirar motocin ya fito ya yi wa su Daddy barka da zuwa, sai da Daddy ya yi masa gaisu sannan suka ƙarasa ya nemi ƴan uwan Baffajo ya yi musu gaisuwa. Har cikin gida ya shiga ya gaida Inna wuro ita ma ya yi mata gaisuwa sannan ya sa Kabiru ya buɗe booth ɗin mota ya riƙa shiga da kayan abinci. Bayan sun gama gaisuwa Baffa Sama'ila ya dubi Daddy ya ce, "Hai Alhaji da mun san wannan lamarin har da hukuma a ciki da tuni mun sallama wa Kabiru ya kawo maka yaron nan har gida." Daddy ya yi murmushi ganin yadda duk suka firgice lokaci ɗaya, ya juya ya nuna Baba sannan ya ce, "Ga mahaifin yaron nan, kuma Alhaji Sama'ila don hukuma ta shiga cikin maganar ai ba wani abu ba ne." Baffa Sama'ila ya nuna ɗakin da Huzaifa ya ke ciki a ɗaure ya ce, "Kai Kabiru shi ga ka fito da shi, su tafi da shi ko hankalinmu ya kwanta." Da sauri Kabiru ya buɗe ya fito da Huzaifa sai dai wannan lokacin bai da kuzari sai kallon mutane yake a tsorace. Baba na ganin Huzaifa ya rungume shi ya fara kuka shi kuwa ban da yaƙe baki babu abin da yake yi. Cike da mamaki Daddy ya ce, "To wai yaushe Huzaifa ya zo garin nan Kabiru?" Inna wuro na daga gefen dokin ƙofa ta ce:
"Yaron nan Huzaifa yau kusan watansa biyu cir a garin nan yara sun tafi kiwo suka dawo da shi sun tsinto shi a kogi suka ɗoro shi akan jaki ya sha ruwa ya ƙoshi don ma Allah ya sa da kwanansa a gaba, tun da ya farko yake a wannan halin don ga dukkan alamu makarai sun shafa masa kai." Inna Wuro na rufe baki Huzaifa ya zubara ya fusgo wani dokin kara da yake hannun wata yarinya, ya ɗare kai yana faɗin, "Mu je ka kaini gaban Mai shari'a." Da sauri Baba da sauran mutane suka yi kan Huzaifa suka rirriƙe shi. Ganin yananyin Huzaifa ya sa aka ɗaɗɗaure shi sannan suka ci gaba da tattaunawa. Daga ƙarshe aka damƙa Huzaifa a hannu su Daddy suka saka shi a mota, sannan suka yi sallama da su Baffa Sama'ila suka wuce tare da yarjewar jami'an tsaro. Har su Daddy suka tafi Kabiru gani yake kamar Basaja Huzaifa yake yi don shi bai yarda da ciwon haukan da yake yi ba, ya so ace an bar su da shi ya lillisa shi ko ba komai zai yi magana idan ya ji wahala. Sai da su Daddy suka ɗauki hanya sai kuma tsoro ya dira a zuciyar Daddy, zuciya ta raya masa kar suna cikin tafiya suma ya ɓace da su kamar yadda ya faru da Raihan, duk da har lokacin yana wasu-wasi game da lamarin Huzaifa da Huzaifa. Ba shiri ya kunna karatu a cikin motarsa sannan suka ci gaba da tafiya, suna shiga garin Kano kai tsaye Daddy ya bayar da shawara akan su wuce da Huzaifa Waraka Islamic Chemist, idan aka gwada aka ga ba na islamic chemist ba ne sai a yi ci gaba da na asibiti. Malam ya yi murna sosai da bayyanar Huzaifa sai da bai ji daɗin ganin halin da yake ciki ba. Tun daga jin jawabin da suka yi masa ya saki murmushi don ya fahimci wannan Huzaifa shi ne na ainihi wancen nunke su kawai ya yi ya samu ya tafi da Raihan.
Sannu a hankali raunikan da ke jikin Raiha suka riƙa warke wa tana samun sauƙi, kwananta biyu a asibitin aka sallame ta sakamakon ba wasu munanan raunuka ta samu masu yawa ba, lokacin da su Inno suka samu labarin dawowar Raihan, har da kukansu don a ranar sai da Daddy ya kai su asibitin suka ganta sannan hankalinsu ya kwanta. Tun a asibiti Raihan ta riƙa ba su labarin rayuwar da ta yi tare da Huzaifa, har zuwan su Mama Hafsa da Daddy duk sai ta gaya musu, saboda tausayi haka suka riƙa yi mata hawaye daga baya kuma wani abin ya ba su dariya.
Malam Usman dama abin da ya yi tsammani shi ne ya tabbata, lokacin da ya fara yi wa Huzaifa ruƙiyya nan take Huzaifa aljani ya fara magana cikin izza, taƙama da girman kai. "Malam Usman ka na yawon son shiga gonata da yawa, a kodayaushe ina jaddada maka wahainiyarka ta kiyayi ramata. Wai ma me ya sa ka addabi rayuwata? Me na tsare maka da za ka riƙa bibiyar sahuna?" Malam Usman ya bashi amsa, "Abin da ya kai ka jikin bayin Allah shi ne silar dalilin bibiyarka. Idan har ita Raihan birgeka ta yi har ka aure ta shi kuma wannan bawan Allahn me ya yi maka da za ka nemi salwantar da rayuwarsa." Huzaifa ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya sannan ya ce, "Ba sai an yi wa Huzaifa wani abu ba yake shiga rayuwar bil'adam ba. Hasalima wannan Huzaifan babu abin da ya yi min kwangilar aikinsa kawai aka bawa Kakana Jabbul-ƙasi a yayin da nake durƙushe a wurin neman tawa buƙatar, babban abokinsa kuma amininsa na wurin aikinsu wato Abubakar shi ne ya kai wa Boka Naziru aikinsa, akan yana son a ɓatar da shi ta kowanne hali domin ya jima baya ƙaunar ganinsa a bakin aikinsu, sakamakon yana yawan samun ci gaba tun da ƙwararre kuma gogagge ne abakin aiki.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
40
Da farko na yi niyyar kashe shi faraɗ ɗaya amma sai na fasa don na san idan na kashe shi lokaci ɗaya mutuwarsa za ta zo masa da sauƙi, ni kuma wanda ya bayar da kwangilar cewa ya yi a kashe shi da kisa mai muni. Kakana ya so hana ni ɗaukan wannan aikin a tunaninsa na shiga halwar soyayya ba zan iya taɓuka komai ba, amma sai na nuna masa sam ba haka ba ne hasalima na yi amfani da surarsa don cimma tawa buƙatar, ranar da na fara zuwa gidansu Raihan har a raina na tsorota don na yi tsammanim Mahaifinta zai zargi wani abu har ya hana ni aurenta, amma sai da na ci galaba akansu suka amince min suka ba ni aurenta. Ba zan daina faɗa ba babu maccen da nake so a duk duniya kamar Raihan, don haka da na aureta na ajiyeta a ƙasaitaccen gidana da na fi ji da shi sai dai ko kaɗa ban samu nasarar kusantarta ba, daga ƙarshe a ranar da na so yin galaba akanta na wayi gari da matsanciyar gobara hatta ni kaina ban tsira daga kaidin wannan gobarar ba, kuma na tabbata ba komai ya haddasa min haka ba face kaidin addu'o'in da kuke yi tare da wanda ita kanta Raihan take yi ba dare ba rana. Shi kuma wannan Huzaifan lokacin da na tashi yaudararsa a siffa budurwa na je masa saboda na san ya ƙware wurin neman mata, a ranar na je wurinsa ban sha wata wahala ba don ina yi masa tayin kaina muka jone, muna shiga ɗakin da suka saba aikata baɗalarsu na ɓace da shi ban sauke shi a ko ina ba sai a tsakiyar kogin wani ƙauye, na danna shi can ƙasan ruwa na yi tafiya saboda na tabbata ko awa guda ba zai ƙara ba zai baƙunci lahira, tun a wannan kogin Aljana 'yar Dugwal take ita kuma bata da aiki sai zuƙe jinin bil'adama idan ta gama da shi ta turo gawarsa sama. Hasalima duk wani kogi da kuka sani mai cin mutane zuri'ar 'yar Dugwal ne a ciki domin ita tana daga cikin jinsin jinnu masu zuƙe jinanen mutane. Dalilin da ya sa kuka ga su Daddy sun ɗauko Huzaifa lafiya, sun kawo shi ba tare da wani abu ya faru da su ba saboda ina matuƙar daraja soyayya. Daddy ya nuna min ƙauna matuƙa kafin daga baya ya fara ƙyamatarka, ni kuma ina daraja shi ne saboda soyayya ita ce abu na farko da ya fara nuna min ba ƙiyayya ba domih sai da ya san wanene ni yake ƙi na. Shi kuma wannan yaron zan isar da saƙo ku gaya masa hawainiyarsa ta kiyayi ramata domin na lura yana son tsalla gonar da ba tashi ba, to ahir kabewar kan kabari tafi ƙarfin taushe idan kuma taurin kansa ya kai shi zan nuna masa shayi ba ruwa ba ne don sai na nuna masa ba a ja da ni a soyayya. Yaron da nake nufi ba kowa ba ne face Kabiru idan kuma ya yi gaddama zan bambamce masa tsakanin tsaba da tsakuwa. " Malam Usman ya ja kujera ya zauna sannan ya ce, "Tabbas Huzaifa ya cika gawurtaccen hatsabibi." Huzaifa na jin haka ya bushe da dariya yana faɗin, "A cikin hatsabibancina ba na jin na tsakuro maka cikin cokoli, ni kaina na san ba ni da kyau hatta ni kaina tsoron kaina nake yi." Malam Usman ya kafe Huzaifa da ido ya furta, "Don na faɗi haka ba ina nufin ka gagare ni ba, Huzaifa ba za