Showing 81001 words to 84000 words out of 157890 words
masa rasuwa nan muka shiga tashin hankali, Mahaifinmu shi ne komai namu kuma ya rasu dama duk abin da yake yi mana ƙarfin hali ne. A kan dole muka shiga gwagwarmayar rayuwa don dangin mahaifinmu ba sa taimaka mana da komai. Kwatsam bayan wasu watanni aka yi wa Mahaifiyata shawarar tafiya saudiya yin aikatau, don haka muka shirya mahaifiyarmu ta sayar da duk wani abu da ta mallaka muka tafi ni da ita. Zuwanmu ƙasar babu wuya sai Allah ya haɗa ni sa Salman, shi ma asalinsa ɗan Najeriya ne amma shi da iyayensa duk mazauna saudiya ne. A ganina ya yi min nisa saboda shi ɗan masu kuɗi ne amma ya nuna ni yake so don haka zai iya rayuwa da ni, yanzu haka shekararmu biyu da rabi da aure kuma yaranmu uku ga su, Salma, Salim Suhaima. Haihuwar fari na haife su ƴan uku yanzu haka jiya muka zo ƙasar nan jibi za mu wuce Spain." Intisar ta ƙarasa bayaninta tana kallon Raihan.
Salman cikin yanayin tausayi ya dubi Mommy ya ce, "Dama haka rayuwa take Allah ya gafartawa Salim, na so ace yana raye da na ga wannan mai tsananin kama da ni." Raihan ta goge hawayen idonta har lokacin tana karanta hailala acikin zuciyarta, wata irin nutsuwa ce ta zo mata. Ta dubi Salman tana murmushin ƙarfin hali ta ce, "Don Allah ka yi haƙuri Salman da abin da ya faru, wallahi a duk lokacin da wani abu na Salim ya zo gare ni ina kasa riƙe kaina tabbas mutuwa gaskiya babu wanda zai mutu ya taɓa dawowa." Intisar ta karɓi lambar Raihan tana tambayar mommy address ɗin hotel ɗin da suka sauka. Sunan hotel ɗin mommy ta gaya mata Intisar ta ce su shiga mota su sauke su idan ya so sa je su ga hotel ɗin. Babu musu su Raihan suka shiga motar sai dai wani irin ɗaci Raihan take ji a zuciyarta. A hankali ta lumshe idonta tana jin wani iri a zuciyarta. A daidai bakin hotel ɗin Salman ya sauke su Raihan, mommy ta yi musu godiya sannan suka yi sallama Raihan ta sumbaci yaran Intisar tana jin kamar kar ta rabu da su. Su Intisar sai da suka ga shigewar su Mommy sannan suka ja mota suka yi gaba, Salman ne ya waiga wurin Intisar ya ce: "A cikin hatsabiban aljanu ma ke ta daban ce, a gidan uwar wa muka haɗu a saudiyya?" Intisar ta bushe da dariyar ƙeta sannan ta ce, "A da'irar abar bauta. ke kin ga yadda ta susuce lokaci ɗaya mahaukaciyar banza, ni na ɗauka ciwon haukan nata zai tashi ma." Hatsabibiya da ke ɗauke da siffar Salim ta ce, "Ai na gaya miki ta warke garau wannan karan dama dole mu sauya salo idan ba haka ba waɗannan ƴan iskan iyayen nata su gama da mu." Intisar ta waiga wurin su Suhaima ta ce, "To garda'u har yanzu kana kan sunanka na Suhaiman ne?" Kusan lokaci ɗaya su Salma suka sake bushewa da dariya suka ce, "Wa ya ga Suhaima." Salma ta rikiɗe zuwa wani mummunan tsuntsu ta ce, "Ni fa ban so ta sauke ni daga jikinta ba don wallahi jikinta wani irin taushi na ji an ya ba zan maye gurbin Huzaifa ba." Mugaza ta saka wata irin dariya mai ɗauke da ma'anar ka kusa kai kanka halaka ta ce, "In dai Huzaifa ne ga fili ga mai doki." Daga haka suka ɓace daga titin Ba su yada zango a ko'ina ba sai a cikin tsibirin ƙungiyarsu. Abar bauta na ganinsu ta bushe da dariya saboda duk abin da yake faruwa tana ganin komai, kallon Intisar ta yi tana yage manyan bakunanta ta ce, "Kin burge ni da wannan shawarar da kika kawo matuƙa, yanzu haka na san tana nan cikin wasu-wasi kuma haka za mu ci gaba da jefa mata wasu-wasi kala-kala har sai mun mayar da ita ruwa mun cimma burinmu a kanta. Wannan karon ba za mu dogara da Huzaifa ba domin shi ma kansa yaje yi wa yaƙi, da mu da shi kowa ya yaƙi abin da yake niyyar cimma buri idan ya so kowa tashi ta fisshe shi." Lokaci ɗaya suka ɗauki soya da wani irin ihu mara daɗin sauraro saboda farincikin samun mafita.
Su Mommy na shiga ɗakin su Inno suka same su duk sun yi jigum-jigum da alamun suna cikin damuwa, mommy ta yi musu barka da hutawa kamar dai ba za ta tanka musu game da yanayinsu ba sai kuma ta ce, "Inno lafiya na ganku duk wani iri?" Inno kamar me jira ta ɗago hijabinta ta ce, "Don Allah me ye wannan Zainabu?" Mommy ta ce, "Hijabi ne Inno." Inno ta ce, "Wallahi yanzu nake shirin fita na bi jikata. Ina dalili ce mana kuka yi kanti za ku je siyayya, ya ilahi kanti da yake cikin unguwa. Tsorona Allah kar yarinyar nan Raihane ta ɓace miki a hanya na shiga uku." Raihan na daga gefe ta ja guntun tsaki ta ce, "Da yake kuma kowa irinku ne ko Inno?" Mommy ta yi mata daƙuwa, Raihan ta turo baki gaba. Goggo da ke gefe ta ce, "Ni abu ɗaya ne ya hana ni fita, ina tsoron kar na shiga cikin larabawa na ɓace don Allah Zainabu ko hasken fitilun ƙasar nan ba su isa kashe min ƙawayar ido ba?" Mommy ta yi murmushi tana cewa, "Ai shi ya sa muka ce ba za ku fita ba sai ranar da za mu tafi saboda kar a wahalar da ku." Inno ta kalli window ta ce, "Zo ki ga Zainabu ni kam waɗannan dogayen gine-ginen an ya ace laburorine suke ginawa? Kai gaskiya akwai ayar tambaya don mutanen nan da alama hatsabibai ne." Goggo ta karɓe zancen da cewar, "Zainabu ba don kar nace idona gizo yake min ba Allah da sai na ce Sha'aban mai aski mijin Safare na hango a wancan wurin a tsaye." Mommy ta riƙe baki ta ce, "Sha'aban Goggo kuma? Me kika ga yana yi?" Goggo ta washe baki ta ce, "A tsaye dai na hango shi." Raihan ta girgiza kai cike da ɗoki ta ce, "Inno yau dai na ga Intisar har da ƴaƴanta sai kuma..." Raihan ta katse maganarta da cewar, "Wallahi baki ga yaran ba gwanin sha'awa. Su Inno suka yamutsa fuska Goggo ta ce, "Wace kuma mai wannan sunan?" Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Ƙawar nan tawa fa." Ganin ba su gane ta ba ya sa Raihan ta tuno musu da Intisar nan take suka gane ta. Nan Raihan ta ci gaba da ba su labarin yadda ta ga Intisar da ƴaƴanta. Sai dai ko kaɗan bata gaya musu ta ga mai kama da Salim ba, don tun a lokacin da ta bawa Kamal haƙuri ta ci burin ba za ta sake yin zancen Salim ba saboda ta lura tana aikata abubuwa da dama cikin rashin nutsuwa. Mommy ta ji daɗi sosai ganin hankalin Raihan bai ta shi ba sai dai yanayinta kaɗai zai nuna maka tana ɗan cikin damuwa. Ko da Mommy ta ƙarasa ɗakin da suke ita da Daddy tas ta bashi labarin abin da ya faru, shi kansa ya yi mamaki matuƙa mommy ta nuna masa ba abin mamaki ba ne a cikin lamarin ubangiji tun da haka na iya kasancewa baka san mutum ba bai sanka ba ka ga yana yi maka kama da wani ko kuma kai kanka. Daga haka suka ci gaba da hirar yadda kasuwanci Raihan zai kasance da irin kayan da zai saya mata, da bayan sun koma Nigeria har zuwa yadda za ta ci gaba da sarrafa dukiyar da kanta. Raihan a ranar kusan kwana ta yi tana tunani daga ƙarshe da ta ga abin ya yi mata yawa sai kawai ta miƙe ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar nafila raka'a biyu ta kai wa Allah kukanta akan ya yaye mata damuwar da take ciki.
Satin su Raihan ɗaya suka ɗunguma zuwa ƙasa mai tsarki, kafin tafiyarsu Daddy sai da ya gama yi wa Raihan komai ya yi mata awon kayanta sannan suka wuce ƙasar Saudiya. Su Inno baki ya ƙi rufuwa dukda wannan zuwan nasu ba shi ne na farko ba amma farincikin kasancewarsu a ƙasar ya sa murna ta cika su. Mommy sosai ta duƙufa wurin yi wa Raihan addu'ar Allah ya cire mata damuwar da take ciki, ya kuma mantar da ita Salim daga zuciyarta. Ta yi mata addu'a sosai akan Allah ya fito mata da miji nagari. Ita kanta Raihan ta yi wa kanta addu'a sosai a harami, ta kuma yi wa Salim addu'a mai yawan da neman Allah ya zaɓa mata abin da ya fi alheri a rayuwarta. Ana gobe za su dawo Nigeria da daddare sun dawo daga sallar Tarawi za su tsallaka don zuwa hotel ɗin da suka sauka. Kamar a mafarki ta hango mutum a bakin titi zai tsallaka, wani ni'imtaccen murmushi ne ya suɓucewa Raihan ta dubi Mommy ta ce, "Mommy kin ga mutumin nan da nake baki labari." Gaban mommy ne ya faɗi don tana tsoron kar Raihan ta sake gano mata mai kama da Salim, kallon wurin ta yi ta hango wani matashin saurayi da yake tsaye da baƙar jallabiya a jikinta. Da ganin yanayinsa shi ma baƙar fata ne don haka cikin rashin fahimta Mommy ta ce, "Waye wancen ɗin?" Raihan ta ce, "Wanda na taɓa baki labari na bige shi yana mashin ina cikin mota. Don Allah mommy na je na yi masa magana." Haɗe fuska Mommy ta yi ta ce, "Ba na son sakarci me kike yi haka? Raihan ko kin manta ke mace ce ne? Idan kin yi masa magana ki ce masa me?" Raihan gabanta na ci gaba da faɗuwa ta ce, "Wallahi ba wani abu zan yi ba Mommy haƙuri kawai zan bashi." Tsaki Mommy ta yi ta ce, "Da can baki bashi haƙuri ba sai yanzu." Idon Raihan ya ciko da ƙwallah ta ce, "Don Allah mommy." Mommy ta sake ɗaure fuska ta ce, "Maza ki je yanzu ki dawo ina jiranki." Daɗi ne ya kama Raihan har a fili sai da ta murmusa. A hankali ta fara takawa tana gabda ƙarasawa wurinsa ya fara haramar tsallakawa, da sauri ta furta: "Bawan Allah ɗan tsaya!" A hankali Al'amin ya tsaya juyo jin muryar bahaushiya na yi masa magana, takawa ya fara yi wurinta sannan ya nuna ƙirjinsa ya ce, "Da ni kike?" Raihan kai ta gyaɗa masa ta ce, "Am dama haƙuri na zo in baka." Da mamaki ya ɗan zaro ido ya ce, "Haƙuri kuma me kika yi min?" Raihan ta ɗan sosa kai a kunyace ta ce, "A nigeria ne dama na taɓa yi maka laifi." Wannan karonma zaro ido ya sake yi don rabonsa da Nigeria ya haure shekara biyu. Raihan tana cikin nazari ta riski muryarsa ya ce, "Duk irin laifin da kika min na yafe miki." Murmushi ta yi masa tana son sake yi masa magana ta ji ya ce, "Idan babu damuwa zan tsallaka wani Bro ɗina yana jirana." Raihan na son karɓar lambar wayarsa amma sai ta rasa me za ta ce masa kunya ta kama shi, don haka ta yi masa godiya suka yi sallama Al'amin ya tsalla ita kuma ta koma wurin Mommy sannan ita ma suka tsallaka suka yi ɓangaren wurin da Hotel ɗin su yake.
Wani irin farinciki Raihan take ji har sai da mommy ta fahimci halin da take ciki, mommy murmushi ta yi don ta fahimci Raihan na matuƙar ƙaunar bawan Allahn tun kafin wannan ranar. Abin da ya sa bata ba ta goyon baya bata san ya halin yaron yake ba tun da a wannan lokacin da ake ciki namiji ya nuna shi yake sonka ma ya gari ya waya balle a ce mace ita ta kai kanta. Abin da Mommy ta ƙudurtawa kanta komai rubutacce ne a wurin Ubangiji Idan Allah ya yi mijinta ne babu makawa sai ta aure shi, idan kuma ba mijinta ba ne duk yadda ta ƙaunace shi ba za ta taɓa aurensa ba. Don haka take ci gaba da yi wa Raihan addu'a da fatan alheri akan dukkan lamuranta. Su Raihan sai da suka shafe sati biyu a ƙasa mai tsarki sannan suka dawo gida Nigeria, tun daga ranar da Raihan ta ga Al'amin kullin suka fita ta rinƙa baza idanu ko za ta ƙara ganinsa amma ko mai kama da shi ba ta gani ba, ta ciza yatsa sosai don ta yi dana-sanin rashin amsar lambarsa hasalima ko sunansa bata sani ba balle ta san wani abu game da shi. Har addu'a ta riƙa yi Allah ya sa ta gan shi ko a hanya ne kamar wancen karon amma ko walƙiyarsa bata gani ba, ranar da za su tafi ƙuncin duniya ya rufe ta don ko kaɗan ba haka ta so ba. Tun tana fushinta a ɓoye har ya fito fili, a nan Daddy yake tambayarta abin da yake damunta don ya san Raihan ba ma'abociyar fushi bace. Bata ɓoye masa komai ba tun daga lokacin da ta ga Al'amin har lokacin tafiyarsu, shi kansa ya ji babu daɗi amma sai ya ƙarfafeta ta hanyar yi mata nasiha akan abin da ya dace da wanda bai kamata ba. Tare da nusar da ita illar abin da take shirin aikatawa dukda ba haramin ba ne a musulunci mace ta furta soyayya ga namiji, har ya nuna mata da ace ya san yaron yana iya yi masa tayin auren Raihan ba wai don ta gaza ko bata da masoyi ba. Ko ba komai Raihan ta ji daɗi don haka ta ci gaba da harkokinta.
Suna Airport gabda za su shiga jirgi suna zaune su Inno sai kalle-kalle suke yi, idan suka hango wani abin da bai yi musu ba sai dai Mommy ta ji suna ƙusƙus abin su. Idan kuma wani abin ne ya ba su dariya sai dai su ji su Inno sun tuntsire da dariya, Raihan ce ta shiga yi musu hotuna da Videos ba tare da sun sani ba sai da ta gama yi musu sannan kuma suka ɗaɗɗauki hotuna gabaɗayansu. Daddy na daga zaune ya hango Malam Usman da wata mace a tare da shi, kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da iyalinsa ce. Fara ce matar mai ɗan jiki yanayinta zai tabbatar maka da babarbariya ce duba da yanayin shigarta da tsagun fuskarta, Malam Usman bai ga Daddy ba sai Daddy ne ya yi masa magana haɗe da ƙarasawa wurinsa. Cikin mutumci suka gaisa Daddy ya ce, "Malam Usman kar dai jirginku ne ya sauka." Matar Malam Usman suka gaisa da Daddy a daidai lokacin Mommy ta ƙaraso, Malam Usman na hango su Inno ya ƙarasa ya tsugunna har ƙasa ya gaishe su sanna ya dubi Daddy ya ce, "Wallahi zuwanmu kenan hala duk jirgi ɗaya muka hau?" Daddy ya yi murmushi ya ce, "A'a mu ai yau za my wuce." Raihan ce ta gaida Malam Usman ya amsa har yana tambayarta sauƙin jikinta ta amsa masa. Adaidai lokacin jirgin su Daddy ya fara shela, Malam Usman ya ce, "To Alhaji sai mun taho. Ni ma na jima a nan ɗan wurina nake jira Al'amin tun ɗazu bai ƙaraso ba." Daddy da suke haramar wuce wa ya ce, "Kasan yaran nan da shiririta ta yuwu wani abu ne ya tsayar da shi." Daga haka suka yi sallama suka wuce ɓangaren da za su shiga ya sada su da jirgin da za su hau. Barin wurinsu ke da wuya Al'amin ya ƙaraso cike da zolaya ya ce wa Mahaifinsa, "Ahlan wasahlam ya Abiey." Malam Usman ya ce, "Balaraben Sudan ka shanya mu da yawa, tun ba wannan tsohuwar taka ba yau ina jin sai ta yi wa ƙafafuwanta ruwan zafi." Murmushi ya yi sannan ya yi musu barka da zuwa babu jimawa suka wuce masaukinsa.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
31
Raihan har suka dawo gida Nigeria bata da tunani sama da na Al'amin, ita kaɗai take sakin murmushi lokaci-lokaci idan ta tuna lokacin da suke tattauna wa ita da shi. Saboda yanayin daɗewar da suka yi basa gida ya sa kafin komawarsa Mommy ta yi wa Mama Hafsa magana ta turo wasu maƙonta da byake ba su da ƙarfi kuma ana ɗan basu wankau da sirfau, sai ta haɗo su da su Safna suka zo suka gyara gidansu Raihan. Don tun daga kan Mama Uwani su Mommy suka ce sun yaye ɗaukan kowacce mai aiki, ana gobe su Raihan za su dawo tuni an gyaran gidan komai ya yi tsaf don haka suna dawo wa suka samu komai tsaf gwanin sha'awa. A gajiye Raihan ta faɗa ɗakinta sai da ta ajiye jakar hannunta sannan ta ta fara rage kayan jikinta, a gajiya ta shiga banɗaki ta watsa ruwa. Kan katifarta ta kwanta ta lumshe ido tana hakaito fuskar Al'amin a lokacin da yake yi mata murmushi. A hankali ta tashi zaune ta furta, "Sau biyu kaɗai na taɓa ganinsa amma soyayyarsa na neman malale birnin zuciyata. Allah ka bayyana min shi a matsayin masoyi idan da alheri a tarrayata da shi" Hannunta ta kai saitin ƙirjinta a daidai lokacin bugun zuciyarta ya ƙaru, ta janyo fulo ta rungume haɗe da ɗora kanta a kan fulon ta furta, "Bayan Salim ban taɓa jin mutumin da ya ƙawata birnin zuciyata ba sai wannan gwarzon mazajen." Tana zaune tana zancen zuci har ta ji bacci na neman lulluɓe idonta ta, a hankali ta ja blanket ta kwanta, babu jima wa bacci ya yi awon gaba da ita.
Kwance take daga ita sai ƴar ƙaramar riga iya cikinta, ɗan gajeren wandonta ko gwiwa bai ƙarasa ba. Mama Uwani ce ta shigo ɗakin ta zauna a gefenta haɗe ta tallafo ta jikinta tana shafata ta ce, "Uwar ɗakina hutawa kike yi." Raihan ta ɗago ta ce, "Huta wa nake Mama Uwani ya aiki?" Mama Uwani ta kai hannu ta ci gaba shafa saman cinyoyin Raihan