Showing 126001 words to 129000 words out of 157890 words

Chapter 43 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

176

ta hango Al'amin rungume da Sumayya, ajiyar zuciya ta sauke ta kawar da idonta haɗe da miƙe wa tsaye. Sai da ta gaishe shi ya amsa sama-sama sannan ta ce, "Dama magana nake son yi da kai." Haɗe fuska ya yi ya ce, "Sai da kika ga na shirya za ki ɓata min lokaci." Sumayya ta sake maƙale shi tana zira ƙafafuwanta don ta sauka ta ce, "Haba Hubby ka saurareta mana." Al'amin ya dubi Raihan ya ce, "Ina jin ki." Jiki a sanyaye Raihan ta ce, "Mu je ɗaki." Dariyar ƙeta ce ta ƙwace wa Sumayya sai ta maze ta ce, "Hubby bari na shiga ciki don gyaran ɗaki zan yi." Tsaki Al'amin ya yi ya wuce ɗakin Raihan, Sumayya na ganin haka ta faɗa ɗaki tana tsallen murna da sauri ta ɗauki waya ta kira Mami, tana jin ta ɗauka ta yi ƙasa da murya ta ce: "Mami buƙata ta biya lamari na ta ɗaukan zafi fa." Amsa mata Mami ta yi cikin farinciki sannan Sumayya ta ci gaba da yi mata bayanin irin zama da Raihan take yi da Al'amin, cikin jindaɗi Mami ta sake ɗora Sumayya akan miyagun shawarwarinta.

Al'amin na shiga ya dubi Raihan cikin kallon tsana ya furta, "Sauri nake ina jin ki." Ƙwalla ce ta ciko idon Raihan murya na rawa ta ce, "Yau kimanin kusan wata biyu da wani abu kenan da aurenmu amma..." Da sauri Al'amin ya katse ta da cewar, "Dakata don Allah, wai ni da bakina na je gidanku na ce ina sonki ne? Na san maganar da kike shirin yi wato can mazajen da kika aure sun koya miki jaraba da rashin haƙuri har ta kai saboda ina bawa matata kulawa kina baƙinciki ko? Don Allah matsa karki ɓata min lokaci." Fuuuu Al'amin ya saka kai ya fice ya bar Raihan sake da baki, don bata yi tsamanin lamarin Al'amin haka yake ba. Durƙushewa ta yi a wurin tana wani irin kuka mai ban tausayi, ta jima tana abinta sannan ta koma kan gado ta yi kwanciyarta don zuciyarta wani irin turiri take yi mata. Tana cikin wannan yanayin ta ji wayarta na ringing lambar Mama Hafsa ta gani, sai da ta goge hawayenta ta ɗauka amma kalma ɗaya za ta furta ka fahimci yanayin da take ciki ba mai daɗi bane. Sai da suka gama gaisawa Mama hafsa ta tambayeta abin da yake damunta don ta fahimci muryarta, Raihan dama zuciyarta cunkushe take da baƙinciki don haka tana jin tambayar Mama Hafsa ta fashe da kuka, lallashinta Mama Hafsa ta yi sannan Raihan ta sanar da ita gutsire daga cikin irin zaman da suke yi, duk da Raihan bata sanar da ita babu wani abu da ya taɓa shiga tsakaminta da Al'amin ba ta fahimci duk maganganun Raihan, don haka ta ce mata za ta ƙaraso gidan. Raihan ta ji daɗi sosai ko ba komai ta san Mama Hafsa za ta zo ta tausheta ko zuciyarta za ta yi sanyi. Kamar yadda Mama Hafsa ta faɗa ko awa ɗaya da rabi bata yi ba ta ƙaraso gidan, a lokacin Sumayya na zaune a falo. Cikin mutumci suka gaisa da ita sannan ta wuce ɓangaren Raihan. Haka kawai Sumayya ta ji zuciyarta bata yarda da zuwan Mama Hafsa ba don ta yi zargin Raihan ce ta yi mata waya ta gaya mata wata maganar. Tana shiga ta samu Raihan zaune akan gado ta zabga uban tagumi, murmush Raihan ta yi mata sannan ta ɗebo kayan marmari da ruwan sha ta ajiye mata, ruwa kawai Mama Hafsa ta sha sannan ta dubi Raihan ya furta, "Kin ba ni mamaki Raihan." Gaban Raihan ne ya faɗi don haka ta fara ayyana wataƙila wani faɗan za ta yi mata haka ne ya sa koda wasa bata taɓa gayawa kowa halin da take ciki ba, tana cikin nazari ta riski muryar Mama Hafsa na ci gaba da cewa, "Yanzu kamar ba wayayya wacce take da ilimi ba za ki zauna kina shaƙar takaici da baƙinciki? yaron nan fa mijinki ne kamar yadda take a wurinsa kema haka. Ki riƙe tsafta kwalliya da dressing kala-kala, kuma ki daina cusa kanki wurinsa don wani lokacin namiji da gayya yake wulaƙanta mace musamman idan ya ga ta mutu akansa, duk abin da ya saki ki yi masa biyayya matuƙar ba saɓon Allah ba ne, komai ya yi zafi maganinsa Allah ki riƙe sallar dare kina kaiwa Allah kukanki, sannan ki dage da Azkar babu wanda zai ga kukanki da ikon Allah, kuma karki mayar da kanki sakarai kishiyarki ta rainaki ki ja ajinki da matsayinki." Jinjina kai Raihan ta yi a hankali ta furta, "Na gode Aunty insha Allah zan rinƙa yi." Mama Hafsa ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta ta ce, "Dole ki cire kunya ki ƙwaci kanki don kunyar mara kunya asara ce, ni yanzu zan wuce don wallahi ban yi niyyar zuwa gidanki yanzu ba, kar na zama uwar banza niyyata sai baɗi idan Allah ya sauke ki lafiya." Kunya ce ta kama Raihan har da rufe fuska sannan suka fito ta raka Mama Hafsa, a lokacin da suka fita Sumayya bata falon don haka Mama Hafsa ta wuce.

Tun bayan auren Raihan sai gidan ya yi wa Kabiru wani iri, duk da gabannin bikinta ba wani yawan hira suke ba amma kaɗaicinta bai dame shi kamar bata gidan ba. Ranar da aka kaita gidan mijinta kusan kwana ya yi yana juyi don tuni zuciyarsa ta riƙa yi masa tunane-tunane kala-kala, so da ƙaunar Raihan suka ci gaba da nuƙurƙusarsa a haka har gari ya waye. Haka ya ci gaba da danne soyayyarta kullin sai ya yi addu'ar Allah ya yaye masa sonta don ya gama tabbatar da cewar ya rasa Raihan har abada, tun da ga shi ta shafe wasu kwanaki a gidan mijinta lami lafiya. Lokaci-lokaci tana kiransa su yi waya har ta tambayi jikin Maryama don ta san tana ɗauke da juna biyu, ko a waya idan ta kira shi ta rinƙa yi masa tsiyar tun da ta yi aure bai zo gidanta ba. Kabiru sai dai ya yi murmushi ya ce mata zai zo amma gani yake ba zai taɓa iya zuwa gidanta ba, har ya ganta da wani namijin a matsayin mijinta, saboda shi kaɗai ya san irin kishin Raihan da yake ɗawainiya da shi a birnin zuciyarsa. Watanta biyu da aure wata ranar Asabar su Inno wuro suka kira Kabiru hankali a tashe Maryama na naƙuda amma ta shafe wuni guda idan haihuwa ta zo gadan-gadan sai ta koma, hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya yi ba don haka nan take ya turawa Baffansa kuɗi ya ce su tafi babban asibitin garinsu kafin ya ƙaraso. A lokacin ya kira Daddy ya sanar masa da halin da ake ciki, kasancewar wata ya yi nisa ba a yi albashi ba Daddy ya ɗebi kuɗi masu yawa ya bashi, ya ja kunnensa akan su tabbata sun kai Maryama asibiti. Bayan wasu mintuna Inno wuro ta kira shi take sanar masa sun je asibiti amma an tabbbatar musu da CS za a yi mata saboda ta gama galabaita ba za ta iya yunƙurin haihuwa da kanta ba. Tun Inna wuro bata gama maganar bata Kabiru ya amsa mata, don ya fi son Maryama ta rabu da cikin jikinta lafiya saboda a ƴan kwananin nan kullin sai ya yi mummunan mafarkinta. Lokacin da Kabiri ya isa garin an yi wa Maryama aiki lafiya, Inno wuro ta dubi Kabiru a lokacin likitoco sun tafi da Jaririn Maryama don duba lafiyarsa ta ce, "Kabiri hai sai dai mu yi haƙuri da abin da Allah ya ba mu..." Zaro ido Kabiru ya yi ya ce, "Inno ba dai Jaririn ya mutu ba?" Jiki a sanyaye Inno wuro ta ce, "Yana da Rai sai dai ba daidai yake ba." Kabiru na shirin magana wata Nurse ta shigo da Jaririn naɗe cikin showel, Inno ta miƙa wa sannan ta fice daga ɗakin. Kabiru ne ya miƙa hannu ya karɓi jaririn sai dai nauyisa tamkar ƴaƴa biyu aka haɗa a wuri ɗaya, yana ido biyu da jaririn zumbur! Ya miƙe sakamakon tozali da ya yi da jaririn mai ɗauke da wata irin hallita. Kan jaririn ya kusa na jarirai huɗu ga idanunsa a warƙale, hannuwansa da ƙafafuwansa duk a juye. Jikinsa ne ya fara wata irin karkarwa, kansa ya sara masa wata irin juwa za ta ɗebe shi. Nan take fasalin Kabiru ya sauya muryarsa ta canja daga fasalin harshen fulani zuwa ta tsurar bahaushe. Dangwarar da jaririn ya yi akan gado cikin wata irin murya ya furta, "Tabbas Abokantaka ita ma Ƴan uwantaka ce, wannan ba jaririn Aminina ba ne an taɓa masa shi. Haƙiƙa Jikan Jabbul-ƙasi ka taɓo wa kanka tsuliyar dodo domin a wannan karon na rantse da zatin Ubangiji ba za ka sha daga hannuna ba. A baya ma saboda ba hurumin abokina ka shiga ba da na nuna maka iyakarka, kuma na yi nisan zango sai daga baya na samu labari amma a wannan karon zan nuna maka ina girmama aminantaka." Hankalin Inno Wuro ba ƙaramin tashi ya yi ba muryarta na rawa ta furta, "Ibrahim ka dubi girman Allah ka yi haƙuri wannan Ɗa da kake gani haka Allah yake son ganinsa." Kallon Inno Wuro ya yi sannan ya kai hannu ya cakumi wuyan jaririn ya furta, "Wannan ba jinin Abokina Kabiru ba ne wannan wani bawan Aljanin Jabbul-ƙasi ne kuma a yau ba sai gobe zai tabbatar da ni ba kanwar lasa bane."

Eheeem 🤭 Nace ba. Kun tuna wanda ya taɓa tare Kabiru lokacin da aka tsorata shi zai bar aikin gidansu Raihan, idan baku manta ba a take ya yi masa nasiha kuma ya ɓace.🌚 Wanene Ibrahim ya aka yi Inno wuro ta san da zamansa? Shin ya za ta kaya tsakanin Ibrahim da Huzaifa? Ina labarin gidansu Raihan za ta ƙwato mijinta ko yaya?🫣

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

46


Tun bayan tafiyar Mama Hafsa Raihan take saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa lamarin dangane da shawarwarin da ta bata, gani take kamar ba za ta iya wasu abubuwan ba don sai ta ga kamar kunyar Al'amin za ta ji. Amma da wata zuciyar ta sake tuno mata da irin shawarwarin da Mama Hafsa ta bata sai ta ayyana za ta fara gwada wasu ko babu komai ta fahimci yanayin yadda zai karɓi abin. Sai da yamma ta ƙarato ta fesa wanka ta ɗauko wani ƙananan kaya riga da wando, farar riga ce kar da jan wando sai kuma wata jar hula da ta saka mai baƙaƙen duwatsu. Har ta saka ta sai kuma ta cire ta dubo wani ƙaramin jan mayafinta saboda tunowa ta yi da yadda gashinta yake ɗauke masa hankali. Ɗaura shi ta yi ta bazo gashin ta baya sannan ta fara gwada irin tafiyar da za ta yi idan Al'amin ya dawo. Tuwon shinkafa miyar agushi ta dafa musu sai lemon abarba da ta yi mai daɗi ta saka shi a firji, tun da ta shirya bata fita waje ba don ta ci alwashin Al'amin ne zai fara ganin wankan da ta yi ba Sumayya ba, saboda ta fahimci wani abun tana kwakwaiyarta. Tana zaune a ɗaki ta ji muryar Al'amin da alama dawowarsa kenan, don haka ta tura ƙofar a hankali wani irin ƙamshinta ya doki hancinsa, a hankali ya ɗago yana kallon wurinta ta yi kamar bata gan shi ba saɓanin lokacin baya da idan ta gan shi jikinta na rawa take zuwa tana yi masa sannu da zuwa. Kai tsaye firji ta wuce ta ɗauko lemon da ta yi sai da ta zo gabansa ta tsiyaya ta miƙa masa sannan ta furta, "Barka da dawowa." Tun da ta shiga falon yake bin ta kallo don haka bai san lokacin da ta yi masa barka da zuwa ba sai da ta sake maimaitawa, a kunyace Al'amin ya sosa kai haɗe da faɗin, "Yauwa barka." Kan kujera Raihan ta koma ta zauna ta ɗauki wayarta tana dannawa ɗaiɗai kamar ba ta san yana falon ba. Cikin takun isa Sumayya ta turo ƙofa tana tafe ƙamshi na biye da ita, doguwar rigar shadda ta saka ta ɗaura ɗankwalinta ita ma ba ƙaramin kyau ta yi ba. Tana ganin Raihan ta haɗe girar sama da ƙada, da gayya ta ƙarasa wurin Al'amin ta zaune haɗe da cewar, "Barka da zuwa Husbee." Murmushi ya yi ya amsa mata da cewar, "Barka dai Wifey ya gida." Wani ɗaci Raihan ta ji a ranta amma sai ta ci gaba da taunar cingam ɗinta tana karkaɗa ƙafa tana danna waya, harara Sumayya ta wurga mata sannan ta furta, "Hubby an kawo maka ruwan wankin hannu da abinci kuwa?" Sumayya ta faɗi haka ne don ta san Al'amin zai sake aiken Raihan kuma ta san ba zai yi mata daɗi ba. Tana tsaka da tunanin ta riski muryar Al'amin yana faɗin, "Ke! Tashi ki miƙo min abinci." Shiru Raihan ta yi tana kallon waya, yana rufe baki ta kishingiɗa ta ci gaba da abin da take yi. Kallonta ya sake ya furta, "Ke Raihan ba magana nake yi miki ba." Murmushi Raihan ta sakar masa sannan ta furta, "Ban yi tsammanin da ni kake ba na ji kana kiran matarka da ke Daz why ban kawo da ni kake ba." Daga Al'amin har Sumayya ido suka bi Raihan da shi don tun da ta zo gidan wannan ce doguwar maganar da ta yi. Cikin wani irin taku ta miƙe ta nufi kitchen ta ɗebo ruwa ta dawo ta ajiye ta sake komawa ta ɗaukon abincinsa sannan ta koma kwanta, sannu a hankali Sumayya ta lura da irin satar kallon da Al'amin yake yi wa Raihan. Cike da ɓacin rai ta dubi Al'amin tana cewa, "Hubby mu wuce ɗaki mu ci a can." Sam ba shi da sha'awar tafiya don ko babu komai Raihan ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, musamman gashinta da yake ta sheƙi da ya zubo har baya. Abincin hannunsa ya cinye sannan ya furta, "Am comportable a nan, bayan na gama cin abinci ma ina da aikin da zan yi." Ganin babu wasa a fuskar Al'amin ya sa Sumayya ta yi shiru sai dai gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi saboda babban tashin hankalinta kar Al'amin ya faɗa ƙaunar Raihan don kallon da yake yi mata mai ɗauke da ma'anoni ne. Wurgawa Raihan mugun kallo ta fara yi cike da jin haushi ta tashi fuuuu ta shige ɗaki. Zuciyar Raihan fes don har sai da ta murmusa ta ci gaba da danna wayarta, a lokacin Al'amin ya samu damar more wa Raihan kallo haka kawai ya ji tana birge shi uwa-uba ga girkin da ta dafa ba ƙarmin daɗi ya yi masa ba, kasancewar ba zai tantance girkin Sumayya ba don tun da suka yi aure bai fi sau uku ta yi girki ba, yau ta ce nan na ciwo gobe ta ce can. Don haka Raihan ta karɓi ragamar gyaran gidan gabaɗaya, sai dai koyaushe idan ta tuna bata da wata fada a wurin mijinsu abin yana yi mata ciwo. Bayan Al'amin ya gama cin abinci Raihan ce ta kwashe kayan gabaɗaya tana yin aikin idon Al'amin na kanta, tana sane da shi don haka ta riƙa taku ɗaiɗai har ta gama kwashewa gabaɗaya. Tana gamawa ta wuce ɗakinta bakinta ɗauke da dariya don ta lura da yadda yake shan magani a duk lokacin da ta ɗago suka haɗa ido da shi, kwanciya ta yi tana murmushin farinciki don ko babu komai ta san yau rana ɗaya ya yi mata kallon ƴa mace saɓanin lokacin baya da baya ɗaukanta a komai. Bai gaji da kallonta ba don haka kai tsaye ya nufi ɗakin Raihan sai da ya je bakin ƙofa sai kuma ya ja guntun tsaki don bai san abin da zai ce ya zo yi ɗakin ba. Ɗakin Sumayya ya shiga don ya lura sarai haushinsa ta ji din haka ta wuce ɗakinta a fusace, yana zuwa ya same ta tana ƙwallah nan ya shiga rarrashinta daga ƙarshe ta sauko suka dawo falo. Zaman Raihan da Al'amin haka ya fara ɗaukan sabon salo, don yanzu ta rage rawar jiki akansa sosai dukda a koyaushe tana jin soyayyarsa da kewarsa a zuciyarta. Girki kuwa tuni Sumayya ta karɓi abinta don tuni Mahaifiyarta ta yi mata faɗa akan wannan wautar da ta yi, don haka suke girkin kwana bibbiyyu amma duk ranar Raihan bata da kwana sakamakon duk ranar girkinta tun magriba take kwanciya wani irin bacci mai nauyi ba ita za ta farka ba sai bayan sallar asuba, lamarin wannan bacci nata ba ƙaramin damunta ya yi ba akwai ranar da ta zauna a falo tana jiran dawowar Al'amin ana yin sallar Isha'i bacci ya yi awon gaba da ita ba ita ta farka ba sai da ana kiran sallar asuba. Tun abin bai ɗaga hankalin Raihan ba har ya fara damunta don haka ta dage da nafilfili tana kaiwa Allah kukanta. Sai da ta shafe sati biyu cikin wannan yanayin sannan Allah ya yaye mata, ana cikin haka har ranar girkinta ta zagayo tun ana gobe za ta karɓi girki ta sa Al'amin ya yi mata cefanen dambu, tun bayan azahar ta shiga kitchen ta fara haɗa kayan dambu wurin bayan sallar la'asar ta gama dambun shinkafarta ban da ƙamshi babu abin da yake yi. Tun lokacin da Dambun ya turaro Sumayya ta kasa zaune ta kasa tsaye, yawunta ba ƙaramin tsinkewa ya yi ba amma faɗin rai ya hanata zuwa ɓangaren Raihan. Ganin ta kasa daurewa ya sa ta taka har ɓangarenta fuska ɗauke da murmushi ta ce, "Aunty Raihan na zo cin dambu wallahi Ɗan baba nake ji kamar zai fito." Ras gaban Raihan ya faɗi don saboda a ƴan kwanakin nan ta lura da sauye-sauyen da take gani a tattare da Sumayya, murmushin ta yi mata sannan ta ce, "Dama yanzu nake shirin kai miki don gaskiya karki haifo min Ɗa da rowa, na zo na ji kunya ace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login