Showing 54001 words to 57000 words out of 157890 words
har wani irin baƙi ta yi ko ruwan kirki bata iya sha, wasu daga cikin mutane har sun fara tunanin Inno na da ƙaramin ciki a lokacin, sai daga baya kowa ya fahimci tsantsar damuwa ce. Bayan sadakar Bakwai aka tara su Inno a ɗaki tashin farko da Alhaji Ƙasim ya sanarwa da Inno zai ɗauke ƴaƴan ɗan uwansa, Daddy da Mama Hasiya zuwa ƙasar Ingila. Inno na jin haka ta rushe da kuka nan take mutuwar mai gidanta ta sake dawowa mata sabuwa, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce sam bata ƴarda ba. Sai da aka kai ruwa rana sannan Alhaji Ƙasim ya amince zai barwa Inno Hasiya, don acewarsa babu yadda za a yi ta tafi da ƴaƴan ƙaninsa ƙauye. Ita kuma a lokacin Mahaifinta ya ce sam ba za ta zauna ita kaɗai daga ita sai yara a wani gari ba, ba tare da aure ba dole ta koma gidansa. Wannan lamari ya sake dagula rayuwar Inno tana ji tana gani aka tafi da Daddy, ranar da suka tafi kwana ta yi tana kuka daga ƙarshe ta fauwala wa Allah lamuranta ta rungumi ƴarta Hasiya ta ci gaba da bata tarbiyya.
Rayuwar gidan Alhaji Ƙasim kusan rayuwar turawa suke yi, suna karatun boko sosai sai dai karatun addini ne basu bashi ƙarfi sosai ba. Ƴaƴan Alhaji Ƙasim suma a haka suka taso zuwan Daddy gidan ya sa shi ma ya ɗora daga in da suka tsaya, saboda da farkon zuwansa idan ya yi wani abin har dariya suke yi masa suna yi masa kallon ɗan ƙauye, sannu a hankali ya riƙa ɗaukan ɗabi'unsu har shi ma ya koma kamar yadda suke. Daddy sai da ya shekara biyar a Ingila (England) sannan suka zo ganin gida, Inno ba ƙaramin mamakin girman Daddy ta yi ba. Kamarsa da ta mahaifinsa ta sake fitowa sak, a lokacin Hasiya tana aji uku ƙaramar sakandire ta fara zama budurwa manema har sun fara fitowa, sai dai fir Hasiya ta ƙi basu fuska a cewarta ita ma so take ta zama babbar likita kamar yadda Mahaifinta ya zama. Da farko Inno ta ɗauka shafar aljanu ne ya hana Hasiya kula samari, don har ta fara yi mata ƴan jiƙe-jiƙe, amma da ta ji manufarta sai ta mara mata baya don duk wani abu da za a ce don a yi koyi da Alhaji babba ne, yana matuƙar faranta mata don tana alfahari da haka. Baffajo duk yadda ya so ya ga Inno ta yi aure haka ta ƙeƙashe ƙasa taƙi yarda don ta san muddin ta ce za ta yi aure ƴan uwan Mahaifin Hasiya ba za su bari ta yi agolanci a wani gidan ba. Ƴan uwan Mahaifin Daddy daidai gwargwado na zumunci suna taimakawa Inno da Hasiya don duk wata suke yi mata aike da kuɗi masu tsoka, wannan dalilin ya sa suka fita zakka ita da Hasiya a garin hatta mahaifinta ya huta babu yawon gonar da yake zuwa musamman da shekaru suka ƙara turawa. Lokacin da su Daddy suka zo sun kawo musu tsaraba kala-kala sai dai abu ɗaya ne bata ji daɗi ba ganin yadda yanayin tarbiyya da ɗabi'un Daddy suka sauya, hakan ya ɗaga mata hankali sai dai duk lokacin da ta yi sallah sai ta saka shi cikin addu'arta. Watansu ɗaya da zuwa suka koma a wannan karon Inno ta sawa zuciyarta dauriya, don ko hawaye bata yi amma ta fi sati tana jin kewar ɗanta a zuciyarta. A haka rayuwa ta ci gaba da shuɗawa har Daddy ya kammala karatunsa ya karanci Business Administration, Yaran Alhajin Ƙasim mazan tuni suka dawo Nigeria duka sun yi aure, Daddy na kammala karatunsa suka tarkato suka dawo gida Nigeria sakamakon yin ritaya da Alhaji Ƙasim ya yi, a lokacin tuni Hasiya ta yi aure ta auri wani lectural su da yake ta ci gaba da karatu zuwa matakin NCE a FCE Bichi amma ma zaunin garin kano ne. Alhaji Ƙasim ya ƙanƙare gidansa na gani na faɗa a cikin garin Katsina. Ya yin da Daddy ya koma wurin ɗayan ƙanin Mahifin nasa Alhaji Haruna da ke zaune a garin Kano, sakamakon wani babban kamfanin takalma da Alhaji Aƙasim ya buɗe masa. Sannu a hankali Daddy ya fara cin gashin kansa wannan dalilin ya sa ya sayi ƙaramin gidan a unguwar Sallari, Ya dawo da Mahaifiyarsa a cewarsa bai ga amfanin zamanta a ƙauyen ba tun da shi ma mahaifin nata ya rasu sai ƴan uwa da abokan arziƙi. Inno ba ƙaramin farinciki ta yi ba saboda ko ba komai ta dawo kusa da ƴaƴanta, tun da dama kullin hankalinta yana kansu. Shekararsa biyu da fara aiki ya haɗu da mommy a cikin garin albasu, lokacin ya je shi da Alhaji Haruna ganin wata ƙatuwar gona da za su siya a sake gida kamfanin shinkafa. Da haɗuwarsu ko shekara ba a rufa ba manya suka shiga magana, aka tsayar da ranar aure lokaci na cika aka ɗaura musu aure.
Mu Dawo Labari, amma fa ba shi kenan ba za mu sake tafiya a gaba don jin asalin Goggon ƴar garin Albasu.
Littafin Kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn ta wannan lambar 0706 206 2624
19
Ɗan jim Mahaifiyar Huzaifa ta yi ganin haka ya sa Malam Usman ya ce, "Idan baki da abin faɗa ki bani wuri na kammala abin da nake kai." Mahaifiyar Huzaifa ta numfasa sannan ta ce, "Malam ban jinkirta don gaza abin faɗa ba sai dai na rasa da bakin da zan yi maka magana, Ɗa ne ka haife shi baka haifi halinsa ba. Huzaifa tun yana ƙaraminsa baya ji ko kaɗan, ni mahaifiyarsa amma duk abin da zan gaya masa baya amfani da shi hasalima tuni ya yi hannun riga da mahallina, Malam ya gujewa addinina ya kama addinin kafirci wanda a kullin idan na tuna makomar kafiri na tuna addinin da Huzaifa yake bi zuciyata takanyi ƙuna, mahaifinsa ya cutar da ni ya ha'ince ni, domin shi ne silar duk abin da Huzaifa yake shukawa. Tabbas Huzaifa ya cutar musu da yarinya tun da jin kunnena na ji yana ambatar sama da shekara goma sha a jikinta, don Allah Malam ka yi masa afuwa saboda darajata, kada ka hallaka shi wallahi duk cikin ƴaƴana babu wanda Allah ya jarabce ni da tsananin ƙaunarsa sama da shi..." Tun bata rufe baki ba Malam ya katseta da cewar, "Akan soyayyar ɗanki sai na ƙyale shi ya dakusar da rayuwar yarinyar ƙarama, kina ganin adalci kenan." Murya na rawa Mahaifiyar Huzaifa ta ce, "Allah ya gafarta Malam ba manufata kenan ba, ina nufin ka jinkirta min zuwa wani lokaci zan tattauna da shi zan nemi ya fita daga jikinta amma don girman Allah karka ƙone shi." Shiru ne ya biyo baya Malam na shirin yin magana ya riski muryar Huzaifa yana faɗin, "Ba sai kin nemi wata alfarma a wurinsa ba, har kike zuwa kike kwaye min baya a gaban mutane. Sai me don kin gaya musu ni arne ne meye a ciki? Ni arne ne kuma mahaifina ma haka sannan ina alfari da kasancewata haka, amma ba ke ba kowa za a tara ba zan taɓa fita daga jikinta ba." A zafafe Malam Usman ya ce, "Kin ji abin da yake faɗa Malama Fatima ki ba ni wuri na babbake shi da ayar Allah." Mahaifiyar Huzaifa ta fashe da kuka sannan ta ce, "Ka dubi girman Allah Malam ka yi mini wannan alfarmar karka dubi baƙaƙen maganganun da yake faɗa, dukda dai na san Huzaifa ba lallai ya ji maganata ba domin nima rashin bibiya ga iyaye ne ya ɗora ni a wannan turbar. Tun Muna saurayi da budurwa ni da Mahaifinsa iyayena suka nuna basason alaƙata da Mahaifinsa Ibrahim, sakamakon sun ga take-taken tarbiyyarsa bata masu kirki bace duk da yana ƙoƙarin kwatantawa a zahiri amma a baɗini ba haka yake ba, amma zaƙin soyayya ya rufe min ido haka na watsawa iyayena ƙasa a ido har sai da aka aura min shi amma ba tare da yarjewar mahaifana ba. Ban taɓa sanin ƙasurgumin arne ba ne sai da zamanmu ya yi nisa da shi, mafi yawa daga cikin ɗabi'u da halaye bashi da su masu kyau. Ban taɓa sani ba ashe bakinsu ɗaya da wani hatsabibin aljani MARWAN, Wannan aljanin ko a cikin jinsinmu suna shakku da shayinsa saboda hatsabibancinsa. Sannu a hankali muka fara haihuwa sai muka samu yara uku Huzaifa ne babba, Hafsa ta biyu sai ƴar autata Nabila. Huzaifa tun yana ƙarami shi ne mai ɗauke da siffar mahaifinsu har halayya wannan dalilin ya sa tun yana ƙarami mahaifinsa ya tabbatar mini da tabbas Huzaifa tun da namiji ne addininsa zai bi. A lokacin hankalina ba ƙaramin tashi ya yi amma ganin bani da kowa sai Allah sai shi ya sa dole na amince da buƙatarsa, saboda iyayena suna aura min shi suka zame hannuwansu daga kaina. Haka na ci gaba da mummunar rayuwa a tare da shi, ban taɓa shiga tashin hankali ba sai lokacin da san waye mahaifin mijina wato kakan Huzaifa. A ranar da muka kai masa ziyara ina ɗauke da ciki amma yana tozali da ni nan take ya ce zai yi sihiri da abin ciki sakamakon jinin da wani bokan bil'adam ya zubar masa a kan wani babban aiki da zai yi wa ɗan siyasa. Amma babban abin da ya fi ɗaga min hankali gani yadda Ibrahim ya bashi goyon baya ɗari bisa ɗari, tun basu gama magana ba nan take na ji naƙuda ta kamani amma daga lokacin ban sake sanin wurin da kaina yake ba, sai farfaɗowa na yi na ganni a makwancina. Sannu a hankali na shafa cikina sai dai wayam na ji babu komai amma tsoro, firgici da tashin hankali suka hana ni furta ko da kalma ɗaya ne akan ɗan cikina. Tun daga lokacin duk cikin da zan samu baya zuwa ko'ina sai ya lalace, haka na ci gaba da rayuwar ƙunci har Ibrahim ya fara bijiro min akan dole na yanke alaƙa da addinin musulunci, a nan ne ni kuma na bijire masa muna tsaka da wannan turka-turkar Mahaifana suka rasu. Wannan lamarin ya sake ɗugunzuma mini hankali domin a wannan lokacin ne nake da niyyar zuwa neman yafiyar Mahaifana, amma kash sai rai ya yi halinsa. Haka muka ci gaba da cuɗawa da shi daga ƙarshe har muka rabu domin alwashi na ci akan ba zan taɓa barin addinina ba, da farko ya so ɗauke mini yara gabaɗaya amma na jajirce akan na bar masa Huzaifa domin tun yana ƙaramin ba ya jin maganata sai ta mahaifinsa, ƴan uwansa mata sun fi ƙaunata da tausaya min. Haka na rungumi ƴaƴana na ci gaba da basu tarbiyya, mahaifinsu shi da Huzaifa suka watsar da lamurammu ko waiwaiyarmu basa yi. Sai ni ce nake kaiwa Huzaifa ziyara idan kewa da begensa sun dame ni. Na san duk abin da ya faru da ni ta silar rashin biyayyar iyaye ne kuma na yi nadama har gobe ban daina neman gafara wurin ubangiji akan laifin da na yi wa iyayena ba. Amma duk wasu miyagun ɗabi'u da Huzaifa yake aikawa da sa hannun Mahaifinsa, shi ya gurɓata shi da miyagun ɗabi'unsa. Amma don Allah Malam ka ba ni dama domin na na yi tattaunarwar sirri da shi ko zai fahimci abin da nake nufi ya haƙura da yarinyar nan." Ilahirin jikin mutanen ɗakin ba ƙaramin sanyi ya yi, Mommy tuni ƙwalla ta ciko idonta Daddy jikinsa ya yi sanyi tausayin Mahaifiyar Huzaifa ya kama shi. Hatta shi kansa Malam Usman sai da ya ji wani iri a jikinsa amma hakan bai sa zai sararawa Huzufa ba. Ya kalli Raihan da ke zaune cikin yanayin tausayi sakamakon Mahaifiyar Huzaifa da ke kanta ya ce:
"Yaron da tun yana ƙarami bai ji maganarki ba bana jin yanzu zai tasirantu da abin da za ki faɗa masa, ki sani Huzaifa yana da kunnen ƙashi ba baki na yi miki amma babu yadda za a yi ya ji maganarki tun da bai ɗauke ki da muhimmanci ba, ya kamata ki cire ranki da kika ƙwallafa akansa domin ba shi kaɗai gare ki ba. Ki nunawa masu nuna miki kulawa domin sune za ki amfana ba wannan ba, Huzaifa yana ɗaya daga cikin JINNUL-ASHIQ kuma ba a wanyewa lafiya da su. Maganar iyayenki kuma kin matuƙar tafka kuskure sai dai kamar yadda kika faɗa ko ci gaba da yin addu'a komai ya yi tsanani maganinsa Allah, amma ki bar ɗauka ɗanki zai fita daga jikin yarinyar nan ta daɗin rai." Mahaifiyar Huzaifa na jin haka ta rushe da kuka, mommy ta sauke ajiyar zuciya don duk wata uwa sai ta fahimci abin da Mahaifiyar Huzaifa take ji. Tana tsaka da kuka ta kalli Malam Usman ta ce, "Na fahimci abin da kake nufi malama, shi kenan na gode matuƙa da shwararka a gare ni. Haka Huzaifa ya ga ya fiye masa don haka duk abin da ya faru da shi don kansa, ina mata fatan samun lafiya mai amfani na barku lafiya." Malam Usman na yin sallama ya yi bismillah ya ci gaba da yi wa Raihan Ruƙiyya, Huzaifa shiru ya yi don ya gama zuciya da abin da Mahaifiyarsa ta gama zayyanewa Malam Usman, sai da ya ji wuya ta yi wuya sannan ya gudu daga jikinta. Yaraf can gefe Raihan ta faɗi jiki a mace kamar mara numfashi, ban da ajiyar zuciya babu abin da take yi. A galabaice ta ɗago tana kallon mutanen ɗakin da yanayin mamaki, Malam Usman ya ƙarasa wurin Daddy ya ce, "Zo mu je falo ina son magana da kai." Daddy na jin haka ya bi bayan Malam, suna zuwa falo Malam Usman ya ci gaba da cewa:
"Huzaifa ya gudu daga jikinta amma fa ba tafiya ya yi gabaɗaya ba, mafi yawanci dama haka suke yi idan azaba ta ishe su. Ya kuke gani maganar gaskiya wannan aljanin yana da matuƙar hatsari domin a kowanne lokaci zai iya dawowa kuma a fusace yake komai zai iya faruwa." Da sauri Daddy ya zaro ido yana faɗin, "Malam babu wata mafita?" Yadda Daddy yake magana ne zai tabbatar maka da ya ji jiki iya jiki. Malam Usman ya yi murmushi ya ce, "Akwai mafita, mafitar kuwa ita ce muna da gadaje a ɗakuna da muke kwantar da masu wannan larura idan kuka ganin za a bata gado babu damuwa idan kuma a barta a nan ana zuwa dubata shi kenan..." Tun Malam bai gama magana ba Daddy ya yi karaf ya ce, "A tafi da ita salamun ƙaulan Malam don matuƙar Aljanin nan yana jikim yarinyar nan, wallahi za a wayi gari ta yi daga-daga da namanmu ta cinye." A wannan karan Malam Usman murmushi ya yi mai sauti ya ce, "Alhaji kuma kuna tsoronsu ne?" Daddy ya dubi hagu da dama sannan ya ce, "Allah ya gafarta malam wane mutum baka ga jikina ba." Nan Malam Usman ya ci gaba da gayawa Daddy irin abubuwan da za su yi wa Raihan idan aka kaita wurinsu.
Mommy na son ƙarasawa wurin Raihan amma tana shakkun abin da zai je ya zo, a hankali Raihan ta ɗago cikin galabaitarwa ta ce, "Mommy kaina." Hawaye ne ya ciko idon mommy a hankali ta taka gaban Raihan, tana zama Raihan ta faɗa jikinta Mommy idonta na zubda ƙwallah. Jikin Raihan zafi ya ɗauka zau ta janyo hannun mommy ta ɗora a kanta tana faɗin, "Mommy kaina ciwo." A hankali Mommy ta kama Raihan Malama Nafisa ta taimaka mata, mommy ta shiga banɗaki bakinta ɗauke da addu'a ta wankewa Raihan jiki. A kan katifa ta zaunar da ita tana kallon Malama Nafisa da kallon tuhuma, Malam Nafisa na shirin fita Malam Usman da Daddy suka shigo ɗakin, hankali a tashe Raihan da dubi Daddy ta ce, "Daddy me wannan? Wa ye ya ji maka ciwo a jikinka?" Daddy ya yi tsilli-tsilli da ido don bai san amsar da zai bawa Raihan ba. Malam Usman ya ƙarasa gaban gadon ya ce, "Malama Raihan ki kwanta ki huta kafin zuwa an jima." Raihan ƙurawa Malam Usman ido ta yi tana son gano inda ta san kammaninsa amma ta rasa takamaimai wurin da za ta shaida ta san shi, haka kawai ta ji mutumin ya kwanta mata ba za ta iya yi masa musu ba. Ba ta san ya aka yi ba amma kawai sai ta tsinci kanta cikin faɗuwar gaba, Malam Usman na niyyar fita ta ce, "Amma Abba don Allah me ya faru da Daddyna?" Daddy ya yi murmushin ƙarfin hali ya ce, "Ɗan accident na samu amma babu wani ciwo da na ji." Malama Nafisa ta dubi Mommy ta ce, "Hajiya ki sauya mata kaya ki haɗa kayan buƙatarku sabida tare za mu wuce."
Daddy tare da Malam Usman suka fita harabar gidan, su Inno na jin motsinsu da sauri suka fito, Goggo ta raɓe a bayan Inno kamar mai shirin fita da gudu. Inno ganin Daddy da yanayin da yake ciki ta rafka salati tana faɗin, "Audullai yanzu haka wannan hatsabibin ya yi maka, kai wallahi ba don zai iya ji na ba tuni na faki ido na kwashe masa albarka." Daddy ya fara takowa wurin yana faɗin, "Inno ai komai ya zo da sauki." Goggo ta matsa can gefe tana nuna Daddy da ɗan yatsa tana cewa, "Audullahi ka bar matso mu, don Allah ka tsaya Malam ya wanke aljanun da suka shafe ka. Allah ya sani idan ka ƙara tunkaro mu, taku ɗaya ba zan yi ba sai a Albasu, ina dalili Aljani ya shafi fatarka ka matso wurinmu." Inno ta fututtuke cikin ɓacin rai ta waiga wurin Goggo tana faɗin, "Wallahi a yau ba sai gobe ba Zinaru sai kin tafi Albasu, haka kawai ɗana da gidansa ki riƙa saka masa ido haka kawai gidan wani ko nasa? A gidan nan babu abin da Zainabu ta mallaka idan ba Raihanu ba, yoo kayan ɗakin da kika yo mata naga dududu da Tsahare dillahi ta siya ko dubu hamsin ba su