Showing 27001 words to 30000 words out of 157890 words

Chapter 10 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

137

amma a yanzu zan yi bakin ƙoƙarina na ga ta dawo daidai kafin wani lokaci. Amma idan ba shawo kan matsalar aka yi ba lamarin zai rinƙa yin gaba, tun da sannin kanmu ne a da ciwonta bai yi tsanani haka ba." Daddy kamar jira yake ya ce, "Hakan ma ya yi min daidai, abin da ya sa ma ban sake tunanin fita ba saboda ka san ba irin yawon da ba mu yi ba tun Raihan tana ƙarama."
Hamza yana shirin yin magana Inno ta turo ƙofa tana tafe Goggo na biye da ita, Inno cike da faɗa tana faɗi:

"Saboda Allah haka kawai ace duk wani tashin hankali bai faru ba sai a ranar da Ƴata Hasiya ta kwanta dama, ina dalili yarinya sai rikiɗa take kamar wahainiya. To Allah ya sani idan ban watsa mata albarka ba Mamman mai ƙawa'idi bai haife ni ba, ku bar ni yau ko ni ko Rihanu a gidan nan." Daddy ya waiga wurin Inno da niyyar zai yi magana, suna gano halin da Raihan take ciki da sauri su goggo suka yi baya cike da tashin hankali. Goggo ta dafe ƙirji jikinta sai tsuma yake yi kaɗan ya rage fitsari bai zubo mata ba, ta nuna wurin da Raihan take ta fara faɗin, "Laƙadi ja'akum yau na shiga uku. Allah ya sani duk garin Albasu babu mayya ko guda ya aka yi aka samu maita a zuri'ata, a'a wannan lamarin dole akwai ayar tambaya wallahi idan Raihanu bata shiga ƙungiyar asiri ba Na koma Albasu a ƙafa." Huzaifa ya waigo wurinsu yana faɗin, "Iya don Allah ku yi shiru ina kan Patient bana buƙatar hayaniya." Inno ta riƙe haɓa saboda takaici don gani take abin nasa kamar har da cin fuska, ƴarta ta mutu ba a yi zaman makoki yadda ya kamata ba kuma a kawo mata maganar Patient. A zuciye ta ƙarasa gaban Huzaifa sai da saita daidai fuskarsa ta wara hannunta a kai tana faɗin, "Ƙaniyarka ka ji, fitsararre kana fama da fuska kamar teba." Huzaifa ya kalli Inno a zuciyarsa yana ayyana idan da ya ga dama wurgi ɗaya zai yi da ita ta baje a ƙasa. Bai dawo daga tunani ba ya ji ta sake nuna shi da yatsa tana ci gaba da cewa, "Kai baƙin munafuki ka gaya min idan da ƴarka ce ta musu waɗannan masifun suke faruwa me za ka yi?" Daddy ya zagayo ta wurinta yana cewa, "Inno don Allah ki yi haƙuri shi fa wannan babu ruwansa a ciki." Goggo ta leƙa fuskar Huzaifa tana kwaɓe baki ta ce, "Akan wannan baƙin munafukin kake shiga gaban mahaifiyarka?" Ta waiga wurin Huzaifa ta ci gaba da cewa, "Wallahi ka fito ka gaya masa gaskiya ko na watsa maka albarka, ka san dai ciwon Yarinyar nan bana mai jan kunne ba ne." Huzaifa ya dubi Daddy kamar abin bai dame shi ba ya ce, "Alhaji a kawo min ruwa." Daddy na jin haka da sauri ya fita daga ɗakin, yana fita Huzaifa ya warto su Inno a hannu ya matse su wuri ɗaya. Kamar waɗanda aka naɗe su da igiya aka ɗaura haka su Goggo suka ji, suna shirin yin ihu bakinsu ya yi musu nauyi. Sai da ya yi hajijiya da su sannan ya watsa su can gefe kamar kayan wanki, zannuwa da ɗankwalen su Inno tuni suka maƙale a saman fanka.


Lokacin da Raihan ta faɗi a lokacin ne Abar bauta ta bada umarnin ga Raihan da ta kawo mata ziyara, nan take ruhinta ya fita daga jikinta zuwa tsibirin da ƙungiyar asirinsu take. Tana zuwa ta russuna ta yi gaisuwa ga Hatsabibiya, a take ta turɓune fuska ta dubi Raihan tana faɗin, "Mun aika kiran gaggawa ne don Abar bauta na buƙatar ku sha jinin mai naƙuda tare da ke, kuma yau ita ce ranar da za a yi miki wankan tsarki dole ke ce za ki kawo mana jinin da za mu sha daga jikinki, Muna buƙatar jinin mahaifiyarki daga yau zuwa gobe idan ba haka ba Abar bauta za ta iya yi wa danginki ɓarna." Ruhin Raihan wata irin zabura ya yi da jin wacce aka ce ya kawo daga cikin danginta, sai dai hakan bai hanata amincewa da buƙatarsu ba. Cikin girmamawa Raihan ta russuna tana faɗin, "Fansar Mahaifana yana gare ku na baku wuƙa da nama, mai naƙuda a ko'ina take zan kawo mana ita yanzun nan." Tana gama maganar ta bi ta iska ta fice daga tsibirin.
Ruhin Raihan na fita bai tsaya a ko'ina ba sai cikin wani babban asibiti, kai tsaye daƙunan majinyata ta fara shiga har za ta fice ta hango wata tsohuwa da alama tana jin jiki, a kan ruwan cikinta ta dira har ta kafa bakinta za ta tsotsi jini majinyaciyarta ta ƙaraso gabanta tana karanta mata ayatulkursiyyu tana tofa mata saboda tuni sun samu bacci ya ɗauketa, ta karanta mata addu'a saboda ita ma bacci take son yi. Da sauri Raihan ta tashi daga kanta ta matsa gefe tana sauke numfashi, daga can gadon ƙarshe ta hango wata mara lafiya bata jinkirta ba ta hau kanta tuni ta kafa bakinta a kanta ta fara zuƙar jini. Nan take jikin matar ya rikice ganin haka ya sa majinyaciyarta kiran nurses, sun kai mutum huɗu a kanta duk yadda suka kai ga bakin ƙoƙarinsu abin ya ci tura, nan take rai ya yi halinsa. Raihan na ganin haka miƙe ta fice daga ɗakin kai tsaye ta wuce can ɗakin haihuwa. Raihan na shiga ta hangi mata kusan uku masu naƙuda, a kan idonta ɗaya ta haihu ta cikin mutum biyun ta dira a gadon ta tsakiya. Tana niyyar kafa kanta a ƙirjinta daga bayanta ta ji an ce, "Jinin Matata ya fi ƙarfinki." A zabure ruhin Raihan ya waiga don ganin wanda ya dakatar da ita ga abin da take shirin aiwatarwa.



A MIN SHARE FISABILILLAH🌚

*ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*


© *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

FREE PAGE 9



Rangaji ta fara yi tamkar bishiyar dalbejiyar da take kaɗawa da iskar damuna, a hankali Kabiru ya ɗan fara ja baya don ko kaɗan hankalinsa bai kwanta da ita ba. Cikin wata irin murya mai jan hankali ta fara magana, "Ka amince min da buƙatata ƙwaya ɗaya ce tal na yi maka alƙawarin yaye maka wannan matsalar da take jikinka." Kabiru da yake jin wani abu yana yawo a zuciyarsa game da ita ya runtse idonsa sannan ya fara magana cikin wata irin kasalalliyar murya, "Ba na buƙatar ganinki cikin wannan yanayin." Tun bai rufe baki ba ta ƙarasa wurinsa ta sa hannu tana ƙoƙarin taɓa shi ta furta, "Laƙani aka bani domin cikar burina a kan Daularmu ta Daulatul jinnul-Turabiy. Idan har ka amince min za ka kusance ni kuma zan warkar da kai, idan ka yi min haka zan mallaki Daularmu da abin da yake cikinta, na zo a sirrance ne ta sanadi ƴar uwata wacce ta yi maka haka..." Tana tsaka da magana ya katse ta da furta, "A'uzubillahi minnasshaiɗanirrajim." Da sauri ta ja da baya tana hakki saboda yadda ta ji wani irin hucin zafi daga jikinsa. A hankali ya tattaro jarumta ya ci gaba da karanta ayoyin kariya da duk wata addu'a da ya san ya taba biyata. Nan take ta ɓace daga gabansa don yadda take ji tamkar zai halakar da rayuwarta, ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa saboda yadda hankalinsa ya sake tashi fiye dana da. A wannan lokacin ya yanke ƙauna don ji ya yi zama a gidan ya fice masa daga rai, gani yake zai iya haƙura da zaman gidan idan ya so duk wata sana'a da ya sani zai fita ya nema don ganin ya ci gaba da nemawa mahaifinsa lafiya. Yana gama nazarin ya miƙe ya ɗauki buhun kayansa, sai da ya leƙa ta window ganin hankulan mutane baya wurinsa ya sa ya yi zaraf ya fice daga ɗakin sannan ya zare sakatar gate ɗin ya fice daga gidan. Gudu-gudu sauri-sauri haka Kabiru ya fara tafiya, kasancewar unguwar shiru babu mutane ya sa bai haɗu da kowa a hanya ba, ta bayan wata doguwar katanga ya raɓa yana tafiya ba tare da ya san inda yake saka ƙafarsa. Yana tsaka da tafiya ya ji ya ci karo da mutum a gabansa, a hankali ya fara ja baya yana ƙoƙarin sake hanya ya ji mutumin da suka yi karo da juna yana faɗin, "Assalamu alaikum." Kabiru da ya fara tsorata a ɗan ja da baya sannan ya amsa masa sallamar, don gabaɗaya a rikice yake. Mutumin da har lokacin Kabiru bai tantance ko shi waye ba ya ci gaba da cewa, "Bawan Allah da wa ka dogara?" Kabiru ya fara sakin jikinsa don ya fahimci ɓoyayyan baƙonsa ne, murya can ƙasa ya ce, "Da Allah na dogara." Mutumin ya ƙara taku biyu zuwa gaban Kabiru ya ce, "Ka dogara da shi a ko'ina kake shi zai isar maka." Kabiru ya jinjina kai yana shirin yin magana, mutumin ya ci gaba da cewa: "Ina ƙaunarka fisabillahi don haka zan baka shawara karka ji tsoron kowa idan ba Allah ba." Kabiru na jin haka ya zaburo da sauri da niyyar kama hannun mutumin yana faɗin, "Don Allah wanene kai da kake yawan zuwa kana gaya min maganganu masu daɗi, da shawara akan al'amuran rayuwata?" Tun bai ƙarasa wurinsa ba mutumin ya ɓace, da sauri Kabiru ya hau waiwaye don neman wurin da zai ƙara ganin ɓullowarsa. Daga can bayansa ya ƙara jin muryarsa yana faɗin, "Karka damu da sanin wanene ni domin mai ƙaunarka na tare da kai a koyaushe, ni masoyinka ne ina mai ƙara tunasar da kai muhimmanci dogaro ga Allah." Yana gama maganar ya sake ɓace wa daga wurin. Jiki a sanyaye Kabiru ya jingina a jikin katangar, ban da kukan kwaɗi da ƙananan ƙwari babu abin da yake tashi a wurin. Lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa ta aminta da nasihar da bawan Allahn nan ya yi masa, nasihar da Mahaifinsa yake yi masa ta sake dawo masa, a fili ya fara furta Astagfirullah sannan ya koma ya nufi hanyar gidansu Raihan.



Inno kusan suma suka yi ban da juwa babu abin da suke ji, Huzaifa ya ƙarasa gabansu ya ya zaro musu ido. Suna haɗa ido suka ga ƙwayar idonsa na ci da wuta, kakin yawu ya yi ya tofar a kan tafin hannunsa nan take wuta ta tashi. Goggo tuni ta saki fitsarin da take matsewa ta sunne kai ƙasa cikin tashin hankali, Huzaifa ya buga musu tsawa yana faɗin, "Duk wacce ta sake gangancin shiga lamarin Raihan sai na banka mata wuta ta ƙone ƙurmus, kuma duk wacce ta sake ta furta wata magana a kaina da abin da ya faru sai na hallata shi cikin dare." Huzaifa ya ɗago ya damƙi wuyansu sannan ya ci gaba da cewa, "Kuma duk wacce ta ce za ta bar gidan nan tana fita zan ɗaye fatar jikinta." Inno da idonta yake runtse ta ce, "Babana mun gode, ko a ɗakin nan ka ce mu dauwama har ranar mutuwarmu mun bar sauka ƙasa." Huzaifa bai bi ta kansu ba ya ɗebe su ya watsa a saman fanka, sai ga su Inno a maƙale jikin fanka sai ciccila ƙafafuwa suke yi. Sai da suka jigata sannan ya miƙa hannunsa ya ɗauko su yana nuna musu zannuwansu dake can gefe ya ce, "Maza ku ɗaura zaninku ku fice daga ɗakin nan." Tun bai rufe baki ba Su Inno suka fara wawurar zannuwansu suna yi suna layi kamar waɗanda suka maku saboda juwar da take ɗibansu. Suna zuwa bakin ƙofa Daddy ya turo ya shigo mommy tana biye da shi Inno ta kusa tafiya luuuu za ta faɗi da sauri Daddy ya ruƙota yana faɗin, "Inno lafiya?" Inno ta fisge jikinta tana faɗin, "Sake ni ka ji Audullahi, jeka kan Raihanu Allah dai ya watsawa Likitanan albarka." Daddy ya yi murmushin jin daɗi don ya ga sauyi a wurin Tsofaffin saɓanin kafin fitarsa da ya tafi suna kwashe wa Likita albarka. Su Inno na fita suka zube a bakin ƙofa suna mayar da numfashi, Goggo ce ta fara rarrafawa tana sauka daga ƙafar bene, Inno ta leƙa tana faɗin: "Kai jama'a yanzu a daren nan za ki rarrafa Zinaru sai makarai sun makeki a hanya." Goggo da ta gama zuwa wuya a zuciye ta juyo ta ce, "Yooo shi wanda kika kuɓuto daga hannunsa Mutum ne? Ki yi ta kanki daga nan ni kam Albasu zan wuce don na tabbata ko ba aljani bane yana cikin ƙungiyar asiri, don wallahi mutum ba zai aikata abin da ya yi ba idan ba haka ba Malam mai allo bai haife ni ba." Nan take cikin Inno ya sake kaɗawa da sauri ta fara rarrafawa ta bi bayan Goggo suka sauka, suka wuce ɗakinsu.

Su Inno na fita Huzaifa ya koma kan Raihan tare da gayyato Jabin Raihan don ta maye masa gurbin Raihan ko ya samu ya sake dulmiyar da su Daddy ga zuwa ƙasar Indiya, saboda matuƙar suka je Indiya hakan zai taimaka masa wurin gano takamaimai abin da yake faruwa da ita. Kafin ƙiftawa ido sai ga Jabin Raihan ta fara motsawa tana sauke ajiyar zuciya, Sai dai babban abin da ya fi ɗaga masa hanakali da ya so ɗaukar gangar jikin Raihan zuwa Tsauninsa abin ya gagara, wannan ya sake tabbatar masa da akwai ɓoyayyan al'amari a dangane da ciwon Raihan, tashin farko Mugaza ce ta faɗo masa don ya san akan baƙin kishinta tana iya aikata komai don biyan buƙatarta. Daddy ne ya tsinke masa tunanin da yake yi yana faɗin, "My Raihan barka farkowa." Mommy da ke gefe ta ce, "Sannu Raihan." Da ido take bin su da kallo tana gyaɗa musu kai tamkar ƙadangaruwa. Mommy ce ta koma daga ɓangaren Raihan ta tsugunna ta fara karanta ayatulkursiyyu tana tofa mata, da sauri Huzaifa ya zabura ya matsa gefe cikin huci a gaggauce yana faɗin, "Shi kenan yanzu zan wuce Alhaji duk abin da ake ciki za ku ji ni saboda akwai wani patient da yake jirana." Daddy ya miƙa masa hannu suka gaisa cikin jin daɗi ya ce, "Ba damuwa na gode sosai Dr." Da sauri Huzaifa ya yi gaba har ya je bakin ƙofa Daddy ya ce, "Dr babu wani magani da za a ƙara mata akan na da ka san fa wancen ya ƙare." Huzaifa ya fara sosa kai sannan ya ce, "Babu damuwa zan turo maka text ta waya." Tun bai jira cewar Daddy ba ya fice daga ɗakin.

A hankali Mommy ta ɗago Jabun Raiha tana yi mata sannu, Daddy ya zauna a ɗaya ɓangaren sannan ya riƙo hannunta ya ce, "Allah ya baki lafiya My Raihan." Jabun Raihan ta ɗago tana gyaɗa kai. Mommy ta miƙe tana faɗin, "Mu je na raka ki, ki yi sallah kin ga Magriba ta wuce ga Isha'i ita ma tuni an yi ta." Ras gaban Jabun Raihan ya faɗi don ko kaɗan bata ƙaunar sallah ba abin da ta ƙi jini irin ta ji an ambace ta. Idan aka ce ta yi ma bata san ta inda za ta fara ba tun da ba addininta bane, tana cikin nazari ta riski muryar Daddy yana faɗin, "Haba Zainab yaushe yarinyar nan ta farfaɗo, don Allah ki bari ta huta ta ci abinci ta sha magani tukunna." Mommy ta ɓata fuska tana faɗin, "Daddy babu wani uzuri game da mara lafiya a kan sallah, hatta majiyacin da yake kwance baya iya tashi matuƙar yana cikin hayyacinsa dole a yi masa alwala ko yana daga kwance ya gabatar da sallah..." Daddy ya katse Mommy cikin ɓacin rai yana faɗin, "So kike ki kafirta mu ni da Ƴata kenan? Ce miki na yi ba za ta yi sallah ba? Ki fita idona Zainabu akan katsalandan ɗin nan da kike min yana neman wuce gona da iri." Mommy ta miƙe cikin fushi ta fice daga ɗakin don ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba.



A hargitse Raihan ta waiga don ganin wanda yake shirin dakatar da ita ga cika umarnin Abar bauta, tana waigawa ta hangi Alhaji Ƙarami abokin mahaifinta. A hankali ya fara takowa gabanta cikin izza yana faɗin, "Matata ce irin dana dasa don ya ci gaba da yaɗo domin samun farinciki da rayuwa mai morewa." Raihan cike da ƙarfin gwiwa ta juya wurinsa tana cewa, "Wa'adin yabanyarka ya zo ƙarshe don a yanzu ba sai gobe ba zan sallamawa abar bauta jininta, ko mahaifana basu isa su dakatar da ni ga aiwatar da wannan kudurin ba." A zabure Alhaji Ƙarami ya fisgo Raihan da niyyar illata ruhinta, da sauri ta kauce ya kaiwa ƙasa duka. Duk abin da yake faruwa babu wanda ya lura daga masu naƙudar dake cikin halin naƙuda har zuwa Nurses ɗin da suke taimaka musu. Raiha ta kalle shi a fusace ta nuna shi da yatsa tana faɗin, "Ka fita a ido tun ban hallaka ruhinka kai da matarka ba, ka barni na yi abin da ya kawo ni tun ban fusata na yi ɓarnar da za ta girgiza ruhinka ba." Ko ba a faɗa ba Alhaji Ƙarami ya san wacece Raihan a cikin Daular ƙungiyar asiri, dukda ba ƙungiyarsu ɗaya ba ya samu labarinta da jimawa a wurin Babban Dodo, tun da jimawa ya so ya ringajayi ruhinta zuwa ta su ƙungiyar amma Huzaifa ya yi kaka gida ya hana shi aiwatar da abin da ya yi niyya. Amma dukda ya san wannan ƙarfin iko nata ba zai hana shi tsayawa tsayin daka don ganin ya ƙwato rayuwar Matarsa ba don ita ce komai na shi a rayuwa. Ya kalleta cikin dakiya da ƙarfin zuciya ya ce, "Na salwantar da rayuwar Mahaifana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login