Showing 150001 words to 153000 words out of 157890 words
min mata wallahi sai na yi maka kisan da kare ma ba zai ci ba, don yadda na ƙone gidan gonarka da kamfaninka haka zan ƙoneka ƙurmus." Kashe wayar ke da wuya Alhaji Shatima ya wurgar da Raihan a gefe, lambar mai gadin Kamfanin shinkafarsa ce ta shigo yana ɗauka ya furta, "Haladu lafiya kake kirana da asubar fari?" A hargitse ya ji yana faɗin, "Alhaji wuta ta kama a kamfani yanzu haka da fara mamaye ko ina." Alhaji Shatima bai gama jin maganar Haladu ba ya fita da sauri, kai tsaye motarsa ya ɗauka ya fita da gudun gaske da niyyar ya nufi kamfaninsa. Yana tafe a hanya ya kira lambar Fire service yana ji an ɗauka ya kwatanta musu kamfaninsa da abin da yake faruwa. Gudu yake shararawa kamar zai tashi sama bisa tsautsayi kan motarsa ta ƙwace ta yi wani gidan mai da ke gefen titi, nan take wuta ta tashi gabaɗaya har motar Alhaji Shatima. Duk yadda ya yi ƙoƙarin fitowa ya kasa, kasancewar da sassafe ne ya sa babu mutane a hanyar mutane ba su lura ba sai da wutar ta ruru sosai sannan aka riƙa ɗiban ruwan kwata da ƙasa ana zubawa, daga ƙarshe sai da aka kira ƴan kwana-kwana sannan Allah ya taimaka wutar ta mutu bayan ta ƙone komai ƙurmus, don har ta fara taɓo ƙananan kantunan da ke maƙotaka da gidan man. Rayuka uku aka rasa a wurin daga Alhaji Shatima sai wasu ma'aikatan gidan man mace da namiji, sun ƙone ƙurmus haka aka riƙa ɗaukan hutunansu ana yaɗa wa a shafikan sada zumunta, daga ƙarshe aka samu da ƙyar aka ciro gawar Alhaji Shatima a mota aka haɗa da ta guda biyun aka wuce da su mutuware.
Tun bayan fitarsa Raihan ta kasa zaune ta kasa tsaye don bata san fitarsa me zai yi ba, tana nan zaune har gari ya waye sai dai ko ruwan tea ta kasa sha saboda tashin hankali da fargaba. Ta kira wayarsa ya fi a irga amma shiru ta ƙi shiga, tana nan zaune wajen ƙarfe tara na safe ta ji Mai gadi na ƙwanƙwasa mata ƙofa. Sai da ta yafa mayafi ta buɗe ta ji ya ce, "Ranki ya daɗe wani bawan Allah yana bakin gate ya ce Mahaifinki ne." Da mamaki Raihan ta ce, "Mahaifina kuma." Ya gyaɗa mata kai. Dakatar da shi ta yi ta je ta duba wayarta don ta kira wayar Daddy ta ji, sai a lokacin ta ga misscall ɗin Daddy da yawa, tana shirin kiransa ta ga wani kiran ya shigo wayarta, cikin girmamawa ta ɗauka tana faɗin, "Daddy ina kwana." Bai amsa mata ba ya furta, "Ina ƙofar gidanki ki fito yanzu za mu wuce gida." Rass! Raihan ta ji gabanta ya faɗi, tana shirin yin magana ta ji ya katse idonta ne ya ciko da ƙwallah. A hankali ta furta, "Na shiga uku me Alhaji ya ce wa Daddy ko shi ma sakina ya yi?" Hawaye na zuba ta zura takalminta ta fice, a bakin gate ta samu motar Daddy tana buɗe motar bayan ta dubi Daddy ta ce, "Daddy wallahi ban san komai ba sharri ne aka yi min." Kallonta ya yi ganin tana kuka ya sa ya yi tsammanin ko ta san abin da ya faru, amma daga yanayin maganrta ya fahimci ba abin da yake tsammanin ba ne. Cikin tausayawa Daddy ya ce, "Da aka yi me Raiha? Ki gaya min tsakaninki da Allah Raihan." Raihan bata ɓoye wa Daddy komai ba daga ƙarshe ta fashe masa da kuka tana faɗin, "Don Allah Daddy ka gaya masa ba na son ya sake ni ban san me mutane za su ce ba. Idan ya sake ni mutane za su ci gaba da surutu akaina kamar yadda suke yi a baya." Tausayin Raihan ne ya kama Daddy ya girgiza mata kai sannan ya ce, "Mu wuce gida tukunna." Daga haka Daddy ya tayar da motarsa suka wuce gida.
A hargitse Raihan ta ɗago tana jin maganar Daddy har sai da ta ji wani irin dum! A kunnenta kamar an buga mata guduma, hawaye ne bibbiyu yake bin fusakar Raihan ta ce, "Daddy ɗazun nan fa ya fita ka ce min ya mutu an ya kuwa ba wani mai kama da shi ba ne." Daddy cikin lallashin ya ce, "Raihan mutuwa ɗaya ce Alhaji Shatima ya tafi sai dai mu yi masa addu'ar Allah ya gafarta masa." Kuka Raihan take sosai zuciyarta na ƙuna jikinta har rawa yake, Mommy ce ta riƙa lallashinta tare da yi mata nasiha har ta daina kukan fili ya zamana sai hawaye da ke bin idanunta. A ranar Daddy da sauran Abokan Alhaji Shatima suka tsaya kai da fata aka bada gawarsa, bayan an sanarwa ƴaƴansa da ƴan uwansa aka yi masa sallah aka kai shi makwancinsa. Mutuwar Alhaji Shatima ba ƙaramin taɓa su Daddy ta yi ba, Raihan har bayan sadakar bakwai gani take kamar Alhaji Shatima zai dawo don har lokacin gani take kamar wani ne ya mutu ba shi ba, saboda a ƴan kwanakin da ta yi da shi ya nuna mata kulawa babu wata magana da za ta faɗa ta ɓatanci akansa, irin kulawar da ta samu ta ƴan awanni ko a gidan Al'amin ba ta same ta ba. Daga haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, Raihan ta ci gaba da zawarci a gidansu tana takaba. Wannan mutuwar ta Alhaji Shatima ita ta sake sarewa Raihan rai ta fidda maganar aure da soyayyarsa a zuciyarta, ta saka wa zuciyarta daga kansa ba za ta sake yin aure ba balle wani abu ya ƙara faruwa da ita ba. Malam da Al'amin da su aka gama zaman makokin Alhaji Shatima, sai dai Malam bai kawo komai ba dangane da zaman makokin da Al'amin yake zuwa a yi da shi sai a ranar da Raihan ta fita daga takaba sannan ya je ya samu Malam a gida. Bayan ya gama sauraronsa Malam ya furta, "A wannan karon ba zan jagoranci neman aurenka a wurin yarinyar nan ba domin a baya ka watsa min ƙasa a ido a wurin mutumin da nake ganin mutumcinsa yake ganin nawa. Ka je ka nemi soyayyar yarinya idan ta ga za ta saurareka shi kenan, idan bata yi da kai kuma Allah ya fito mata da wanda ya fika." Al'amin kamar zai yi kuka ya dubi Daddy ya ce, "Wallahi Daddy kunyarta nake ji." Malam ya riƙe baki sannan ya ce, "Amma dai baka da kunya Al'amin, wato ni ne ba na jin kunya da zan shige maka neman aurenta a kato na biyu ko? Fice ka ba ni wuri kafin ranka ya ɓaci." A sanyaye Al'amin ya miƙe ya fita, ya fi minti talatin a mota yana saƙa da warwara daga ƙarshe ya wuce gida. Tun da Sumayya ta ji rasuwar mijin Raihan hankalinta ya yi matsanancin tashi, don tana tsoron Al'amin ya ce zai dawo da ita ga shi har lokacin ba zaman daɗi suke yo ba balle ta nuna bata amince ba don a wannan lokacin ta san bata da wannan power.Tana zaune ya shiga tana yi masa sannu da zuwa da yauwa kawai ya amsa mata sannan ya wuce ɗaki, jiki a saluɓe Sumayya ta bishi don ya fito ya ci abinci amma ya ce mata baya ci. Duk yadda ta kai ga lallashinsa ya ƙi ƙarshe ma sai cewa ya yi ta fita ta bashi wuri baya son hayaniya, haka Sumayya ta fito fuska ɗauke da hawaye don ta lura yanzu ko kaɗan Al'amin baya gudun gaya mata magana ko ya ɓata mata rai.
Tsananin soyayyar Raihan ce ta hana shi sukuni har ya yanke shawarar zuwa gidansu don ya nemi soyayyarta, sai dai cike da ƙwarin gwiwa ya tafi saboda ya san a baya Raihan na mutuwar son sa. Lokacin da ya ce a yi sallama da ita fir ta ƙi fita don tuni ta daɗe da shafe shafin aure daga ranta. Al'amin babu yadda bai yi ba amma ta ƙi fitowa daga ƙarshe ma cewa Auwalu ta yi idan ya kuma zuwa wurinta sai ransa ya ɓaci, Al'amin haka ya juya ya tafi ba tare da ya samu abin da yake so ba. Lokaci ɗaya ya kaɗe ya lalace kamar ba shi ba, Malam na lura da yanyinsa duk da yana jin tausayin halin da yake ciki amma ya ji daɗin rashin haɗin kan da Raihan bata bashi ba, Ammi kuwa da har ta ce za ta je gidan su Raihan domin ta nemi alfarmarta akan a mayar da aurensu, Malam ya ce mata matuƙar ta fita ita ma sai ranta ya yi mummunan ɓaci. Wannan lamarin shi ya sake ɗaga hankalin Al'amin ga shi bai san wurin da zai sami lambarta ba, tun da ya yi zuwa ya fi biyar amma duk lokacin da ya je sai dai ace masa bata nan. Watarana Kabiru yana gidan da ya ji abin da Auwalu ya faɗa kishi ya turniƙe zuciyarsa, a fusace ya fito ya samu Al'amin ya gaya masa magananganu marasa daɗi. Al'amin ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ya dubi Kabiru ya ce, "Akan matata kake gaya min magana saboda baka da mutumci ko?" Kabiru ya yi dariyar rainin hankali sannan ya ce, "Amma dai kai baka da hankali, idan matarka ce me ya sa baka shiga ka ɗauki abarka ka tafi da ita ba. Indai Raihan ce ka rasata kenan har abada lusari mai ƙaramin tunani." A zafafe Al'amin ya yi kan Kabiru a daidai lokacin Daddy ya dawo daga masallaci, da sauri ya shiga tsakaninsu yana ƙoƙarin jin ba asi." Al'amin cikin ɓacin rai ya ce, "Daddy wai akan Raihan wannan banzan yake gaya min magana saboda na aika ayi sallama da ita." Kabiru ya karɓe maganar da cewa, "Daddy ana dole ne Raihan ta ce ba za ta fito ba, wai don na ce ya haƙura zai ce min matarsa ce a ina ta zama matarsa?" Daddy ya tura Kabiru cikin gida ya ce, "Wuce ciki bana son maganar." Sannan ya juya wurin Al'amin ya furta, "Don Allah ka yi haƙuri Al'amin." A kunyace Al'amin ya furta, "Ba komai Daddy ammm... Dama..." Sai kuma kunya ta kama shi ya kasa magana ya furta, "Shi kenan sai da safe Daddy."
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
52
🔚🔚🔚🔚🔚🔚
Al'amin na tafe a mota lokaci-lokaci yake sakin tsaki don ya fahimci wani abu a tattare da Kabiru, ya hango kishi ƙarara a ƙwayar idonsa. Babban tashin hankalinsa da ya rasa ta yaya zai samu lambar Raihan balle ya sake bata haƙuri ya nemi soyayyarta. Gashi ya yi juyin duniya akan Malam ya yi wa Daddy magana fir ya ƙi yadda, ya kawo ido ya zura masa don ya ce sai dai ya nemi soyayyarta.
Daddy na shiga cikin gida ya samu Raihan a falo tana lissafin wasu kaya da ta yi order su. Zama ya yi a kujera ta kalle shi da murmushi ta ce, "Daddy barka da shigowa." Daddy ya amsa cikin sakin fuska sannan ya ce, "Raihan ashe Al'amin ya zo." Nan take ta haɗe fuska ta ce, "Ya zo Daddy amma ban fita saboda a yanzu ba na son abin da zai sake dagula lissafin rayuwata." Daddy ya yi murmushin irin nasu na manya ya ce, "Amma da kin saurare shi ki ji abin da yake tafe da shi." Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Ai duk abin da yake tafe da shi na yafe masa ya riƙe kayansa Daddy." Dariya Daddy ya yi ya ce, "Shi kenan Raihan ɗin Daddy ba zan yi miki dole ba duk abin da kike so haka za a yi, amma fa kar ki manta aure sunnar Annabi ne." Raihan ta yi murmushi tana cewa, "Daddy ni fa ba komai nace ba amma gaskiya ni da aure kam sai nan da wasu shekaru." Daddy ya nufi hanyar part ɗin sa yana faɗin, "Shi kenan Allah ya nuna mana lokaci." Raihan ta amsa da Amin sannan ta ci gaba da abin da take yi.
Duk wata hanya da Al'amin zai bi ya samu Raihan ya kasa don haka wata dabara ta faɗo masa, searching ɗin sunanta ya yi ta shafin sada zumunta, nan take sunan da take kasuwanci da shi ya bayyana wato R-Raihan's Investiment. Farinciki ne ya mamaye zuciyarsa tamkar Raihan ɗin ya samu gabaɗaya, lambar da ya gani a jiki ya ɗauka don haka ya yi saving a wata sabuwar lambar wayarsa don ya tabbata idan ya yi mata magana da layinsa ta yuwu ta gano shi, don a sanin da ya yi mata na baya ta haddace lambarsa. Nan take ya yi mata magana ta Whatsapp. A lokacin bata online sai dai yana danna profile ɗin ta ya ga irin kayan da take oder da branches ɗinta, magana ya yi mata a zuwan zai sayi kaya. Ya yi mata maganar da minti goma ya ga ta duba ta yi masa replay wani irin farinciki ne ya kama shi, nan take ya buƙaci Acc number ta akan zai yi siyayya ta dubu ɗari biyar. Raihan ta ji daɗi sosai har sai da ta yi masa discount na 20k amma da ya tashi a madadin ya tura mata iya kuɗin da suka yi ciniki sai ya tura mata kusan ninkin haka. Ganin haka ya sa Raihan ta tambaye shi ko zai ƙara kaya ne amma ya ce a'a. Mai motar da yake kai mata kaya ta kira tare da bashi address ɗin wurin da za kai. A iya bakin titin Sharada Al'amin ya tsaya ya karɓi kayan ya tafi, da haka Al'amin ya samu mazauni a wurin Raihan domin tana girmama duk wani wanda ya sayi abu a wurinta. Don haka suke yawan gaisawa akai-akai da yake ya ci gaba da siyan kaya a wurinta. Ana cikin haka watarana Al'amin ya bijiro mata da maganar aure, ba ƙaramin dariya ya bata ba don a lokacin ta bashi amsa da cewar, "Yanzu kai ba mu taɓa haɗuwa ko waya ba mu taɓa yi ba sai ka ce kana so na." Al'amin ya yi mata replay, "Ai ba wani abu ba ne indai kin amince za ki aure ni a yanzu zan zo na same ki." Alamar dariya ta tura masa ta rubuta, "Ka yi haƙuri domin na riga da na rufe shafin aure a rayuwata." Duk yadda Al'amin ya so shawon kan Rainan fir ta ƙi amince masa daga ƙarshe ma sai ta daina yi masa replay koda ta ga abin da ya rubuto mata. Ganin wannan dabara bata kai shi ba ya sa ya yanke shawarar zuwa ya samu Daddy duk da yana tsanannin jin kunyarsa akan abin da ya yi wa Raihan. Ranar da ya je Office ɗin Daddy bai yi mamaki ba don tuni Malam ya gaya masa komai game da halin da Al'amin yake ciki, sai da Daddy ya gama sauraronsa sannan ya ce, "Insha Allah zan yi wa Raihan magana idan ta amince shi kenan saboda ka ga Raihan ba budurwa ba ce balle mu yi mata zaɓen miji da kanmu. Amma insha Allah za ta amince da buƙatarka, kar ka samu damuwa Allah ya shige mana gaba." Gwiwa a sanyaye Al'amin ya fita yana fita Daddy ya kira Malam bayan sun gaisa ya ce, "Gaskiya wannan abin da ake yi wa yarona ya yi yawa, a zo a mayar da auren nan ko ya samu kwanciyar hankali amma ka zuge yarinyar nan sai ja masa aji take. Wallahi kar na zuciya na nema masa wata tsaleliyar budurwar ya aura masa." Malam ya yi dariya sannan ya ce, "Ai ko ka nema masa ba zai so ta kamar Ƴata ba ka ga kuwa an yi aikin baban giwa." Daddy ya kwantar da murya ya ce, "Don Allah ya isa haka Malam zan je na samu yarinyar nan na yi mata magana." Malam ya ce, "Ai da ka bari an kwana biyu don ban so ya samu Raihan yanzu ba, na so ace sonta ya galabaitar da shi tukunna." Sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Daddy na zuwa gida ya samu Raihan da maganar Al'amin a zaton Raihan Daddy bai san yadda suka yi da Malam ba, sai da ya gaya mata ta yi ta mamaki sannan ya ce, "Ba tilasta ki na zo yi ba Raihan ki zaɓi zaɓin ranki, kin ga yau Alhaji Shatima kusan shekararsa guda da rasuwa. Kina da ƙuruciyarki don haka lokacin aure bai wuce miki ba. A baya Al'amin ya yi kuskure kuma ya gane kuskurensa don haka mai zai hana ba za ki yafe masa ki amshi tayinsa ba? Na san kin fuskanci ƙalubale da dama a rayuwarki ta fannin auratayya amma haka ba shi zai sa ki ce ba za ki sake yin aure a rayuwarki ba. Ban yi miki dole ba amma ke kanki kin san yadda Al'amin ya haukace a soyayyarki, na sani kin sani ke ma kina ƙaunarsa kin ga tun da ya gane kurensa ki ba shi dama ya gyara, mahaifinsa mutumin kirki ne ya yi mana komai a rayuwa ko don darajarsa ya isa ya sa ki amince masa tun da kina ga da kansa ya baki shawarar irin shan ƙamshin da za ki yi masa. Atoh ni dai babu ruwana don na gayawa Baban naki idan ajin na naku ya tsinke babu ruwana, babu abin da zai hana aura masa tsaleliyar budurwa kina kallo mu sha biki ya tare da abarsa." Murmushi Raihan ta yi a kunyace tana rufe fuska ta ce, "Shi kenan Daddy Allah ya tabbatar mana da alheri." Daddy ya furta Amin sannan ya wuce part ɗin Mommy, a ranar ya sanar da ita da su Inno, da farko su Inno faɗa suka fara yi sai da Daddy ya nusar da su karamcin Mahaifin Al'amin da abin da ya yi musu dangane da ciwon Rainan sannan suka sauko suka saka wa komen auren albarka.
Daddy da kansa ya kira Al'amin ya gaya masa a kowanne lokaci yana