Showing 69001 words to 72000 words out of 157890 words

Chapter 24 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

148

sake ta kai magriba a waje, juyawar da za ta ci suka yi gware nan take kayan da ke hannuwanta suka tarwatse a wurin, wayarta ta faɗi daidai ƙafarsa. Kusan tare suka miƙa hannu don ɗaukar wayar da sauri ta ɗago tana kallonsa, karaf suka haɗa ido da shi. Wani shu'umtaccen ƙamshi ne ya doki hannunsa ga wani irin kwarjini da ya yi mata. A hankali ta janye idonta sakamakon kasa jure kallon da yake yi mata, cikin inda-inda ta furta. "Am...Kawo...Bari na kwashe." Ta ƙarasa maganar tana miƙa hannunta za ta ƙarɓi wayar, janye hannunsa ya yi yana ci gaba da kallonta cikin wata sasaanyar murya ya furta, "Ni ne mai laifi don haka a bar ni na goge laifina." Ajiyar zuciya ta sauke don muryarsa ba ƙaramin kuwwa ta yi mata a dodon kunnen ba, a hankali ta ja gefe ya tsugunna ya fara tattare kayan sannan ya ce, "Kin gama ne?" Girgiza masa kai ta yi cikin kasalalliyar murya ta ce, "Zan je wurin turare." Gaba ya yi yana riƙe da kayan ta ƙarasa ta fara ɗaukan irin waɗanda take amfani da su, sai da ta gama ta miƙa hannu za ta karɓa tana faɗin, "Na gama bari na wuce gida." Hannu ya sa ya sake ɗebo mata waɗanda ya fa ta ɗiba da farko, Raihan ta fara bin sa da ido kamar za ta yi masa magana sai kuma ta ja bakinta ta rufe don ta ga iya gudun ruwansa. Yana gama ɗiba ya wuce wurin biyan kuɗi kafin Raihan ta zo har ya ciro ATM ɗin sa ya bayar. A hankali Raihan ta kalle shi ta ce, "Ka bari da kuɗi a wurina." Yamutsa fuska ya yi yana girgiza kai ya ce, "Gaskiya na wurinki sun yi kaɗan, na san ko 50k ba su kai ba." Waro ido Raihan ta yi da mamaki ta ce, "Kai ta ya ka sani." Dariya ce ta suɓuce masa ganin lokaci ɗaya ya yi mata dabara. Raihan na ganin haka ta gane wautar da yi lokaci ɗaya ta tura baki gaba ta ce, "Ai ATM ɗin biyu na taho da su idan wannan bai kai ba sai na ciro ɗayan." Murmushi ya yi mata ya miƙa hannu ya karɓi reciept sannan suka fito ya raka har wurin mota, hannu ta miƙa masa za ta karɓi kayan ya girgiza mata kai yana cewa, "Ba zan baki ba sai kin biya tukwici." Cikin rashin fahimta Raihan ta ce, "Tukwici kuma? Dama ai ba ni nace ka biya ba, ba na ce zan biya ba ka ce za ka biya?" Gyaɗa mata kai ya yi sannan ya buɗe murfin motarta saka kayan a ciki ya ce, "Eh! Lambarki za ki bani." Kunyace ta kama Raihan don ita bata taɓa kawo abin da zai karɓa ba kenan."

Tana cikin tunani ya miƙa mata waya a hankali Raihan ta karɓa ta saka masa lambarta, nan take ya yi kira lambarta. Daga nan suka yi sallama sannan Raihan ta shiga mota ta tafi, sai da ya ga tafiyarta sannan shi ma ya koma cikin Store ɗin don ya manta da tashi siyayyar. Raihan na zuwa gida ta zube a falo nan ta hau bawa Mommy labarin abin da ya faru tsakaninta da matashin saurayin, su Inno ban da murmushin farinciki babu abin da suke yi. Duk da bata ce musu saurayinta ba ne amma kana ganin yanayin yadfa Raihan take hirarsa za ka fahimci ya kwanta mata. Tana tsaka da basu labari sai ji ta yi wayarta ta yi ƙara, kallon Mommy ta yi ta ce, "Mommy wallahi shi ne ya kira." Ta ƙarasa maganar ta miƙewa za ta nufi ɗakinta, Mommy ta yi dariya tana cewa:

"Don Allah Raihan ki san yadda za a ki yi masa magana kar ki je ki yi ta sakarci a waya." Kafin Raihan ta yi magana Inno ta ce, "Ummhumm yoo ban da abin Raihanu bata fara ba ni wayar, shi saurayin nata ya gaishe ni. Ni fa na haifi ubanta Zainabu ko bata gaya masa tana da kakanni ba?" Mommy ta gimtse dariya da ke cinta ta ce, "Inno ina zan sani yanzu fa ta gama ba mu labari a gabanku." Goggo ta taɓe baki tana faɗin, "Mutum dai ya gama zagaye-zagayensa mu muka haifi uwa da ubansa idan muka gama mu ce saurayin bai yi mana ba dole a fasa auren." Inno ta yi karaf ta karɓe zancen da cewar, "Wallahi faɗi da ƙarfi Zinaru, wai yarinyar nan rana ɗaya za ta watsa mana katsa a ido. Saboda Allah idan bata ba mu ya bai gaida mu ba ta ya zai ga darajarta ya san ƴar babban gida?" Goggo ta taɓe baki ta ce, "Ga ne min hanya dai."

Raiha na jin su ta shige ɗaki sai da ta zauna ta ɗauka da sallam, amsa mata ya yi sannan ya ce: "Rowa kika yi min ni kuma na gagara haƙura." Kamar tana gabansa ta zaro ido ta ce, "Ni kuma?" Ya bata amsa da, "Eh baki gaya min sunanki ba." Raihan ta yi masa murmushi sannan ta gaya masa sunanta, ta riski muryarsa na cewa: "Sunana Salim Muktar." Bata san lokaci da ta furta, "Wow Nice name." Murmushi ya yi sannan ya ce, "Ya kai sunan saurayinki?" Raihan kanta tsaye ta ce, "Ni fa ba ni da saurayi." Daɗi ne ya ratsa zuciyar Salim don yadda yake ji akanta idan aka ce tana da saurayi bai san ya zai yi ba. Saboda lokaci ɗaya ya ji ta kwanta masa a rai, bai ɓata lokaci ba wurin zayyana wa Raihan abin da yake cikin ransa, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba sai dai lokaci ɗaya ta ji wata irin matsananciyar kunyarsa ta kama ta, bata iya bashi amsa ba sai katse wayar da ta yi. Duk kiran da Salim ya yi mata bata ɗauka ba sai text message da ta tura masa na amincewart, bakin Raihan ya ƙi rufuwa saboda farinciki. Haka kawai ta riski kanta cikin nishaɗi a ranar Daddy na dawowa sai da ta bashi labarin abin da ya faru, shi kansa ya ji daɗi sosai musamman da ya ga Raihan ta aminta da Salim.

Kafin wani lokaci tuni shaƙuwa da soyayya ta shiga tsakanin Raihan da Salim, Ranar da ya ce zai zo hira farinciki fal zuciyar Raihan. Kabiru na zaune ya ga shiru Raihan bata fito karatu ba har ya gama biya wa su Inno karatu suka koma, sai da Raihan ta fito Kabiru ya ce, "Fillo yau ba ɗaukan darasi." Da yake shi ma Kabiru Fillo yake kiran Raihan kamar yadda take gaya masa. Takawa ta yi har gabansa tana murmushi sannan ta ce, "Fillo yau a haƙura da karatun nan amma don Allah kar ka gaya wa Daddy." Hararar wasa Kabiru ya ce, "Hai kin san ba a aikin banza yanzu, ki ba ni cin hanci sai na yi shiru amma idan ba haka ba Daddy na zuwa an yi an gama." Da sauri Rainan ya buɗe baki tana ɗan ɓata fuska ta ce, "Wallahi Fillo ka lalace da son kuɗi, yanzu dai nawa zan baka?" Kabiru ya yi jim sannan ya ce, "Sai kin faɗi uzurinki don kowanne uzuri da yawan kuɗinsa." Raihan ta riƙe ƙugu tana yi masa fari da ido ta ce, "Saurayina ne zai zo kuma yanzu haka girki nake yi, don Allah ka rufa min asiri Fillo mu kashe mu binne." Kabiru ya sa dariya don ya gano lagonta ya ɗauke kai gefw ya ce, "A yanzu ma va zan karɓi kuɗinki ba sai Saurayin ya zo na ga kamun ludayinsa idan bai min ba, sai na zuga Daddy son raina." Raihan ta watsa masa harara tana juyawa cikin gida ta ce, "Kanka ake ji wallahi Saurayina ya fi nesa ba kusa ba." Tana gama maganar ta shige cikin gida.

Bayan sallar magriba Raihan ta gama shiryawa tsaf cikin doguwar rigar jar atamfa da mayafinta ja, ba ƙaramin kyau ta yi ba dukda ba wata kwallita ta yi ba. A ƙaramin falon su ta sauke shi sannan ta shiga kawo masa kayan ciye-ciye da shaye-shaye, Tun bai sha komai ba ya ce zai fara zuwa ya gaida su Mommy. A babban falo ya samu Mommy bayan ya same ta sun gaisa shi da Raihan suka koma ainihin falon da ta sauke shi, zuciyar Raihan fes da bata ci karo da su Inno ba don ta san da ta haɗu da su sai sun tsinkata a gaban Salima. Tana tsaka da tunani ta riski muryar Inno da Goggo sun tunkaro falon Inno ce a kan gaba tana faɗin, "Saboda Allah Zinaru ai kya bari na fara shiga tun da yarinyar nan dai ni ce na haifi Ubanta, duk yanda aka yi Raihan bata gaya wa yaron nan tana da kakanni ba da bai shigo ya ƙi zuwa gaida mu ba."


A YI HKR DA ERRORS BAN YI EDITING BA.

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn


26



Goggo ta karɓe zancen da cewar, "Ni dai sai na ga kamun ludayin yaron nan tukunna, saboda Allah ya sani ba zan bari Raihanu ta auro ɗan da bai fito daga gidan tarbiyya ba." Inno na bankaɗa labule ta rafka sallama har tsakiyar kan Salim, Raihan na ganin haka ta ɓata rai don ta san abin da zai hana su Inno su tsinkata a gaban Salim sai Allah. Inno na haɗa ido da Salim ta washe baki tana faɗin, "Wannan ne saurayin namu ashe?" Salim na ganin su Inno ya sauko ƙasa cikin girmamawa ya ce, "Baba Ina wuni?" Goggo da Inno suka amsa cikin haɗin baki, "Lafiya ƙalau samari ya tsofaffin?" A kunyace Salim ya amsa, "Duk suna lafiya suna agaishe ku." Inno na jin haka ta sake washe baki haɗe da zama akan kujera ta ce, "Allah sarki ashe har sun san da zamanmu? Kai wannan abu ya yi daɗi to ni dai da ka ganni ni ce na haifi Uban Raihanu, wannan kuma ita ce ta haifi uwarta Zainabu. Ka gansa nan Audullahi shi kaɗai ya rage min kamar tsoka ɗaya a miya, ita kuwa Zinaru tana da wata ƴar bayan Zainabu." Inno ta yi maganar tana nuna Goggo da tun shigowarta take ta sakin murmushi, Salim shi ma murmushi ya yi. Goggo ta kalli Salim ta ce, "Ashe shi ya sa Raihanu ta kasa tsaya wa a biya mata ayar Allah tana ta zumuɗin ganinka." Kunyar duniya ta kama Raihan da ido take yi wa su Inno sigina amma ko kallon wurin da take basu yi ba, Salim daɗi ya kama shi ya riski Inno tana faɗin: "Salmanu kake da suna ko Ɗan nan?" Raihan ta tura baki gaba kamar za ta yi kuka ta ce, "Inno sunansa Salim fa." Inno ta dubi Salim har tana leƙa fuskarsa ta ce, "Salim tashi ka hau kujera nan fa gidanku ne, ai na ɗauka Salmanu sunanka in ce sunan wani ɓarawon kaji kenan a Madaka." A kunyace Salim ya tashi ya hau kujera Goggo ta miƙe tsaye ta ce, "Yaro bari mu wuce don yanzu sai mu yi laifi a wurin Raihanu bayan tafiyarka ta zo ta riƙa yi mana faɗa ta ce mun tsinkata a gabanka." Inno ma ta miƙe tsaye suka yi wa Salim sallama har sun je bakin ƙofa Goggo ta ciro ledar goronta ta juya wurin Salim ta ce, "Yaro na ce tsofaffin suna cin goro ne? Ungo ka tafi musu da shi." Salim ya yi dariya don tsofaffin ba ƙaramin birge shi suka yi ba, lokaci ɗaya suka tuno masa da tsohuwar kakarsa da ta rasu ba da jimawa ba, fara'a ɗauke a fuskarsa ya ce. "Wallahi ba sa ci amma ni ina ci Goggo." Goggo daɗi ya kamata ta miƙa masa ta ce, "Allah ya yi maka albarka, ai kuwa duk ranar da na je albasu sai na taho maka da shi." Raihan ta yi zuru tana kallon su Goggo don tun da take da su ba su taɓa yi mata abin da ya ƙona mata rai ba irin na wannan ranar. Suna fita Salim ya kalleta da murmushi ya ce, "Baby zama da tsofaffi da daɗi amma sai ka yi haƙuri." Raihan ta ɗauke kai gefe ta ce, "To amma kawai kana zuwa sai su shigo ai sa bari ka ɗan zo da yawa." Salima ya yi dariya yana gutsurar goro ya ce, "Yanzu kenan kunya kika ji." Raihan ta ɗan zaro ido ganin ya zage yana cin goro ta ce, "Wai da gaske kana ci dama?" Kafaɗa ya ɗaga mata ya ce, "Wallahi a gurin Jadda na koya kin san ni fa goyon kaka ne." Dariya Raihan ta yi ta ce, "Ashe kaima da wuri za ka tsufa." Salim ya kwaikwayi muryarta yana faɗin, "Daɗin abin ma tare za mu tsufa kin ga tsoho mijin tsohuwa kenan." Raihan ta yi dariya don barkwancin Salim ba ƙaramim birgeta yake ba, kayan snack ɗin gabansa ya ɗauka ya fara ci haɗe da lumshe ido ya ce, "Haka kika iya girki Dear?" Kunya ta kama Raihan ta rufe ido tana dariya. Salim ya kalle ta ya sake cewa, "Wai da gaske yau saboda ni kika ƙi zuwa Islamiyya." Raihan ta rufe ido ta yi murmushi tana faɗin, "Ba fa islamiyya ba ce, Fillo ne yake koyawa min karatu a gida ni kuma yau ina aiki na ce ya bari sai gobe." Salim ya yi murmushi sannan ya ce, "To ashe ni ma za ki fara yi min ƙari kenan." Raihan ta saka dariya.

Sun jima suna hira sosai sannan Salim ya tashi ya yi wa Raihan sallama, sai da suka je harabar gidan ta gabatar masa da Kabiru har sai da suka gaisa. Salim na murmushi ya miƙa wa Kabiru hannu ya ce, "Malaminmu ina wuni?" Kabiru ya yi dariya ya ce, "Hai Samrayin Ɗaliba har ka fito." Kabiru ba karamin dariya ya basu ba, yana yi wa Kabiru sallama ta raka shi ƙofar gida a lokacin ya buɗe motarsa leda ce guda cike da alawoyi da chocolate ya miƙa mata. Da farko ƙin karɓa ta yi sai ta ga ya ɓata rai sannan ta karɓa ta yi masa godiya, tana shigowa ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Kabiru yana fito wa ta ɗaga ledar hannunta ta ce, "Ka ga irin abin kirkin da ake yi wa budurwa, ka koya don wataran idan za ka fara neman aure, na san ku fulani akwai maƙon tsiya." Kabiru ya girgiza kai ya ce, "Aradun Allah ina iya gaya wa Alhaji baki zauna karatu yau ba." Raihan ta taɓe baki ta ce, "Oho dai ko ka faɗa ai yanzo ya tafi." Ta ƙarasa maganar tana wuce wa cikin gida. Raihan na shiga sashensu su Inno suka fara washe baki, Raihan tana shirin yin magana Goggo ta ce: "Zainabu yaron nan na yaba da hankalinsa, ni sai yake min kama da wani yaro a albasu." Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Mommy wai yau kin ga irin abin da Tsofaffin nan suka min? Allah saura kaɗan na sa kuka saboda takaici." Mommy ta yi dariya saboda dama ta san za a rina tun lokacin da ta ji muryar su Inno a falon da ta kai Salim, cikin yanayin zolaya ta ce: "To meye don kakanni sun gaisa da saurayin jikarsu?" Raihan ta kwanta akan cinyar mommy tana faɗin, "Wallahi ni dai daga yau kar su ƙara zuwa idan ya dawo." Raihan na rufe baki Inno ta ɗago ledar ta ce, "Wallahi da ganin yaron nan zai iya riƙe gida, dubi ku ga abin kirkin da kawo mata." Nan su Inno suka fito da alawoyi suna dubawa. Zumbur Raihan ta miƙe ta kwashi wasu daga cikin alawar ta kaiwa Kabiru sannan ta dawo cikin gida.

Soyayya sosai suke yi tsakanin Raihan da Salim babban abin da yake ƙara birgeta da Salim riƙo da addininsa don duk bayan sallar isha'i zai kirata a waya su yi bitar karatu. Kuma duk karatun da Kabiru ya biya mata sai ta sake biya wa Salim, wannan dalilin ya sa suka samu kyakkyawar fahimta a tsakaninsu. Hatta su Mommy sun yaba hankali da sanin yakamatan Salim saboda nutsuwarsa da girmama na gaba.

Salim asalinsa ɗan garin Kano ne Mahaifinsa Alhaji Muniru babban likita ne a asibitin Malam Aminu kano. Mahaifiyarsa asalinta ƴar unguwar Gwale ce, suna zaune a unguwar Gyaɗi-gyaɗi. Salim shi ne babba a gidansu sai ƙannensa biyu duka mata Farida da Fatima, dukansu ƴan mata ne suna karatunsu a jami'ar Maitama Sule. Salim Yana da ilimin addini sosai da na boko, ya fi sha'awar kasuwanci don haka bayan ya gama karatu Mahaifinsa ya buɗe masa manyan shaguna a kasuwar kwari, shi yake safarar kaya daga ƙasashen waje yana kawowa cikin gida Nigeria. Yana da nutsuwa da tarbiyya sakamakon mahaifin bai da wasa a fannin addini, Salim ya taɓa budurwa ƴar aminiyar mahaifiyarsu, amma da ya fahimci ba me kamun kai ba ce tuni suka yi hannun riga.

Magana Raihan da Salim ta yi ƙarfi har manya sun shiga tsakani, bayan dogon bincike da Daddy ya yi akan Salim da Iyayensa Mahaifan Salim suka kawo kuɗin na gani ina so. Aka tsayar da ranar aure shekara ɗaya bayan Raihan ta kamallah karatunta, farinciki ba ƙaramin kama su Daddy ya yi ba haka suka shiga shirye-shiryen bikin Raihan. Raihan ta mayar da hankalinta sosai wurin karatu da ginin tubalin soyayyarta. Mahaifiyar Salim da ƙannensa ba ƙaramin ƙaunarta suke yi ba, takanas Salim ya ɗebo ƙannensa watarana suka kawo wa Raihan ziyara. Lokacin da za su tafi haka Raihan ta haɗa masu sha tara ta arziƙi ta basu suka tafi, sun ji daɗin ganin yadda Raihan ta karɓe su hannu bibbiyu. Lokacin da za su tafi Fatima ta dubi Raihan ta ce, "Matar Yaya don Allah zan dawo a koyana min Meatpie ɗin nan." Raihan za ta yi magana Salim ya karɓe zancen da cewar, "Princess ɗina ba kukunku ba ce, idan snacks za ku koya ku je Catering school." Fatima ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login