Showing 102001 words to 105000 words out of 157890 words

Chapter 35 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

177

wannan karon duk yadda ƴan jarida suka so jin ta bakin su Daddy abin ya ci tura, don haka suka dangana ga wurin ƴan sanda a nan suka samu bayanin da ba a rasa ba. Wannan tashin hankali da aka wayi gari ya sa ƴan bikin da suka ziyarci gidajen bukukuwan tuni kowanne ya kama gabansa zuciya a dagule, maganar ɓatan su Raihan ita ta kai har kunnen ƙungiyoyin lauyoyi ta ƙasa. Babu shiri suka tuntuɓi hukumar ƴan sanda haɗe da neman a haɗa su da iyayen Raihan don jin duk yadda abin ya kasance. Kamar yadda abin ya faru haka Daddy ya sanar da su iya abin da ya sani, daga ƙarshe ɓangarorin biyun suka ci alwashin binciko duk wurin da Raihan da Huzaifa suke. Tuni Hotunan su Raihan ya karaɗe kafofin sada zumunta lamarin da ya sake hautsina labarin kowa da abin da yake faɗa, wasu su ce aljanun Raihan kashe mazanta suke yi, wasu su ce su suka sace Raihan har ma su zargin tuni an gama da Huzaifa sai jiran bayyanar Raihan. Lokacin da Dr Hussain ya tabbatar da ɓatan Raihan ya shiga banɗaki ya fi a irga don ko a radio ya ji maganarta sai cikinsa ya karta ya faɗa banɗaki, daga ƙarshe Daddy ya bayar da umarnin a tafi da Dr Hussain shi ma. Har kawo wannan lokacin Iyayen Huzaifa na kulle ba a sake su ba, sai da aka kai ruwa rana sannan Daddy ya lamunce aka saki iyayen Huzaifa da sharaɗin a kowanne lokaci za a iya buƙatarsu don bayar da bayani.

BAYAN KWANA BIYAR.

Duk waɗannan kwanakin mutanen gidansu Huzaifa da Daddy sun yi su cikin rashin nutsuwa, fargaba da tashin hankali. Su Inno ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, ko abincin kirki ba sa iya ci. Kabiru tuni ya fige ya rame ya lalace don ko abinci bai fi ya yi cokali biyu ya ajiye shi ba, ba shi da aiki sai addu'a da sallar dare yana fatan Allah ya kuɓuto da Raihan cikin ƙoshin lafiya. Daddy tuni ya sanarwa da Malam halin fa ake ciki, ya bi makarantun islamiyyu da ta allo ya riƙa rarraba kuɗi yana neman a yi wa Raihan addu'a akan Allah ya bayyanata cikin alheri ko a mace ko a raye. Jikin Mommy yana sauki amma sai dai a kira shi da samun sauƙin mai haƙan rijiya, don kullin tana kwance ana bata kulawar da ta dace amma kullin ta farfaɗo maganarta ɗaya, "Ina Raihan?" Da ta kalli Daddy sai dai ta riƙa zubda ƙwalla. Ana cikin wannan yanayin Inna wuro ta kira Kabiru hankalina tashe tare da sanar da shi ciwon Baffajo ya tashi, wani sabon tashin hankalin ne ya dirarwa Kabiru don haka a ranar da Raihan ta kwana shida da ɓata, ya shirya da safe zuwa asibitin da Mommy take ya sanarwa da Daddy duk abin da yake faruwa, tare da faɗin zai je ya gano halin da yake ciki. Duk da Daddy na cikin damuwa bai hana ya gano tsananin damuwar da Kabiri yake ciki ba, kuɗi ya tura masa masu yawa ta Account ɗinsa. Kuka Kabiru ya gashe da shi har ƙasa ya tsugunna yana yi wa Daddy godiya. Daga asibitin gida Kabiru ya koma ya yi wa su Inno Sallama ya ɗauki ƙaramar jakarsa ya fita. Lokacin da ya fice daga gidan zuciyarsa ce ta karye game da lamarin Raihan, zuciyarsa ta fara tunane-tunane akanta don haka idanunsa suka ciko da ƙwalla ya sake waigawa ya kalli gidan sannan ya goge ƙwallar idonsa ya fara tafiya.

"Tabbas na sake lamincewa Huzaifa ya dawo da ƙarfinsa fiye da na baya, ina da yaƙinin ya samu taimako ne daga Kakansa Jabbul-ƙasi. Idan ba haka ba babu yadda za a yi ace Huzaifa shi kaɗai ya dagakatar da dukkan tsafi da sihirinmu. Ya auri Raihan ba tare da mun iya dakatar da shi ba, jikina ya gama ba ni ya fara fahimtar wani abu daga gare mu domin babu yadda za a yi Mugaza tana ji tana gani ta bari Huzaifa ya auri Raihan ba tare da wani abu ya gifta a tsakani ba. Ku shaida ne yau kusan watannin Mugaza huɗu kenan ba tare da ta halarci ƙungiya ba, kuma duk iya bincikenmu mun yi don ganin mun gano halin da take abin ya ci tura, shin me kuke tunani meye abin yi a wurinmu?" Abar bauta ta yi maganar a sanyaye saboda ta gama tsinke wa da lamarin Huzaifa. Hatsabibiya ta rungumo mijinta tamkar wani zai ƙwace shi tana shirin magana, ya miƙe zumbur ya fara sauya launi sai da ya rikiɗa zuwa kaloli kusan biyar sannan ya tsaya cikin kalar yello da baƙi. Kallon abar bauta ya yi ya numfasa sannan ya ce, "Yau kusan shekarata bakwai ban tofa muku komai a game da lamarin ƙungiya ba, ina buƙatar a bani damar na furta wani ba." Da yake Abar bauta mafita take nema don haka cikin sauri ta amsa masa, "Faɗi koma meye a bakinka." Mijin Hatsabibiya can gefenta ya koma ya maƙale matarsa sannan ya ce, "A wannan halin da ake ciki Huzaifa ya gawurta, tasirin tsafi da sihiri ba za taɓa aiki a kansa ba. Laƙanin Jabbul-ƙasi yana da matuƙar ƙarfi. A shawarce duk yadda ake ciki kar mu sake mu tunkari Huzaifa gaba da gaba. Kar ma mu jefa rayuwarmu cikin tashi domin matuƙar ya fahimci muna mu'amala da Raihan a cikin ƙungiya ta mu ta zo ƙarshe, don haka sai mun yi takatsantsan koda za mu cimma burinmu akansa. Sannan dole mu tabbatar da mun ceto Mugaza a kowanne yanayi take ciki idan ba haka a kowanne lokaci asirinmu zai iya tonuwa." Abar bauta ta jinjina kai cike da gamsuwa don bayaninsa ba ƙaramin ankarar da ita ya yi ba. Miƙe wa ta yi tana kai wa da kowo wa sannan ta dube shi ta ce, "Yanzu ta ina za mu fara?" Kai tsaye ta ji ya furta, "Dole mu ziyarci tsibirin Jabbul-ƙasi mu nemi agajinsa." A haukace duka suka kalle shi cikin hargitsattsiyar tsawa Abar bauta ta ce, "Kana hauka ne za ka ce mu ziyarci Kakan Huzaifa don mu nemo sa'a?" Murmushi ya yi sannan ya ce, "Na san waye Jabbul-ƙasi ba ruwansa da duba nasaba ko dangantaka. A yadda muka je da buƙata to buƙatar kawai zai kalla babu ruwansa da wanda za a aikatawa." Daɓass! Abar bauta ta zauna jiki a sanyaye zuciyarta na yi mata wasu-wasi akan ta amince da maganarsa ko ta yi watsi da ita. Tashi ta sake yi za ta shige raminta sannan ta waigo ta ce, "Ku dakace ni don na yi nazarin abin da ya kamata mu yi don gaskiya zuciyata na rawa akan wannan shawarar taka." Tana gama maganar ta shige ciki.

A cikin ƙasa da kwanaki bakwai Raihan duk ta lalace ta fita hayyacinta ta rame, idan ka ganta a yanayin da take ciki za ka yi tsammin ta yi wata doguwar jinyar. Ta koma tamkar mahaukaciya da yake gashin kanta ba a kitse yake ba ya sa duk ya hargitse, fuskarta duk ta jeme ga koyaushe cikin kwanan fargaba take babu wadataccen bacci idan ba ɗaukanta ya yi bata sani ba. Kullin cikin kuka take da addu'ar Allah ya kawo mata ɗauki take yi, sallah kuwa tun ranar da ta yi da dare kullin sai dai ta yi taimama ta yi, daga ƙarshe ma da ta tsorata sai wani ƙaramin dutse ta samu ta riƙa yin taimamar da shi. A kullin ta wayi gari sai Huzaifa ya ziyarce ta har yana nuna mata buƙatarsa a fili amma ƙarfin addu'a da Ayatulkursiyyun da Raihan take yi ya gagare shi ƙarasawa koda kusa da ita ne, sai dai ya tsaya daga nesa da ita. Hasalima sai ya riƙa tsoratata da waɗansu ƙananan halittu masu yanayin mutane amma ba sa kama da bil'adam ga su gajeru ko tsayin gwiwar Raihan ba sa kaiwa. Waɗannan Halittu su suka sake haukata Raihan don wani lokacin har ji take kamar suna yawo a jikinta, bata da aiki sai ihu da kiran sunan su Mommy. Abinci kuwa duk yadda Raihan ta kai ga tsoron cin abincin da take kawo mata dole ta zubar da makamanta ta fara karɓa tana ci, duk da ba kullin yake bata ba a cewarsa sai ta bashi haɗin ya yi mu'amala da ita. A ranar da Raihan ta cika kwana bakwai a wannan yanayin ta yanke shawarar bashi kanta don ta gaji da irin wahalalliyar rayuwar da take ciki, gara ta bashi kanta ko mutuwa za ta yi ta huta don ta lura a wannan wurin da take babu alamar fitarta, idan ta mutu ta sa mu sauƙin rayuwarta kowa ya huta. Tana nan zaune ta ji shigowarsa a wannan karon sanye yake waɗansu irin kayan saƙi tare da wuri sai waɗansu baƙaƙe da jajayan duwatsu, a wurin da ya saba tsaya wa ya tsaya yana kallonta ya ce, "Raihan na nuna miki ƙauna da kulawa amma ko kaɗan baki gani ba, a duk lokacin da na zo wurinki idan na koma sai na yi jinyar jikina saboda a kullin sai kin ƙona min ni, Raihah da ba na sonki ba zan juri haka ba." Durƙushe wa ya yi a wurin cikin rawar murya, nan take hawaye ya fara bin dakalin fuskarsa. Kuka yake sosai kamar ƙaramin yaro wannan ya sake raunana zuciyar Raihan, wata irin soyayyar Huzaifa da tausayinsa ta ji na ratsata. Kuka take sosai tana jin babu daɗi a zuciyarta, tana cikin haka ta riski muryarsa. "Duk duniya ba na ƙaunar wani abu kamar yadda nake ƙaunarki ba, na tabbata wannan yana daga cikin tsarin ƙaddarata. Raihan na haukace a kanki na yi nisa ba na jin kira ta yadda kunnuwa suka doɗe ban da harshenki babu abin da nake iya ji. Ni ba Mutum ba ne kamar yadda kike tsammani ni aljani ne, ina mata da ƴaƴana amma saboda ke duk na haƙura da su na haƙura da kowa nawa don Allah ki ƙaunace ni koda na rana ɗaya ne." Kuka ne ya ci ƙarfin Raihan don ko tsoron ma ya fita daga zuciyarta, cikin kuka ta dube shi ta ce: "Idan na ce ba na ƙaunarka na yaudari kaina ina sonka kamar yadda kake sona Huzaifa, amma zaman mu a inuwa ɗaya ba zai taɓa yuwa ba, saboda kai ba jinsina ba ne. Me ya sa ka hura wutar soyayyarka a zuciyata bayan kasan ba za ka iya kashe ta ba, ina ƙaunarka Huzaifa ina jin soyayyarka amma ka dubi girman Allah kar ka cutar da iyalinka a kaina, ka ci gaba da bawa iyalinka kulawa kamar yadda kake ba su a baya." Raihan ta goge hawayen idonta sannan ta haɗa hannuwanta wuri ɗaya alamun roƙo ta ce, "Ka dubi girman Allah ka mayar da ni wurin iyayena don na tabbata yanzu haka suna cikin wani hali." Cike da farinciki Huzaifa ya dubi Raihan ya furta, "Tabbas zan aiwatar kamar yadda kika buƙata zan ci gaba da bawa Iyalina kulawa, amma don Allah ki daina zancen na mayar da ke gida. Tun da har kin amince kina ƙaunata don Allah ki watsar da komai mu ci gaba da rayuwa, ni Huzaifa na yi miki alƙwari ba za ki taɓa hawaye ba. Zan baki kulawar da ba babu wani ɗan'adam da zai baki ita, wallahi ko kallon banza babu wani mahaluki mai numfashi da ya isa ya yi miki shi. Matuƙar baki amince min ba wallahi ba za ki taɓa fita daga wurin nan ba, balle wani namijin ya samu damar raɓarki har ya kai ga aurenki." Raihan na jin haka ta rushe da kuka don zuciyarta ta fara yi mata wasu-wasi akan ta amince da buƙatar Huzaifa.

Fuska ɗauke da damuwa Daddy ya dubi Malam ya ce, "Shi kenan Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alheri amma a wannan lokacin da muke ciki na fara sare wa da samun Raihan, shi kenan ya yi nasara a kanmu." Malam Usman ya girgiza kai haɗe da cewar, "Da ƙarfin addu'a da ikon Allah Huzaifa ba zai taɓa nasara akan mu ba. In sha Allah nan ba da jima wa ba Raihan za ta bayyana, mu ci gaba da addu'a kuma na gaya maka tuni akwai aljanun da na tura don su nemo min su a ko ina suke." Jikin dadi ya gama sanyi don haka murya na rawa ya amsa, "Shi kenan na gode Malam." Yana shirin fita Al'amin ya shiga har ƙasa ya russuna ya gaishe da Daddy tare da sake jajanta masa akan ɓatan Raihan, Daddy ya yi musu sallama ya koma asibiti. Mama Hafsa ita take jinyar Mommy akan dole aka bar wa su Inno Muhammad suke kula da shi, da yake ya saba da su ko rigima baya yi. Jikin Mommy yana sake samun sauƙi jininta ya sauke har tana iya miƙe wa ita kaɗai ta yi wasu abubuwan da kanta, nasihar da su Daddy suke yi mata ne ya sake ƙarfafa gwiwarta ta faula wa Allah lamuranta.

Lokacin da Kabiru ya ƙarasa gida ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba sakamakon ganin yadda jikin Baffajo ya rikice, ƴan uwa sun zagaye shi sai koke-koke ake yi. A daren ranar da ya koma ya sa aka ɗauki Baffajo aka wuce da shi babban asibitin garin Shanono, duk wanda ya ga yadda Baffajo yake jin jiki sai ya tausaya masa. Suna zaune a asibitin Kabiru ya dubi Inna wuro ya ce, "Inna ya kamata ki koma gida ni zan kulla da Baffa, kin ga an bar gida ba kowa ki wuce kawai." Gabanta ne ya faɗi a ɗan firgice ta ce, "Shi kenan wataƙila ya shiga gari." Da mamaki ya dube ta ya ce, "Waye Inna." Miƙe wa ta yi tana yafa mayafinta ta ce, "Ɗan tsintuwa ne Kabiru Allah sa dai bai shiga gari ba." Kabiru sam bai fahimci maganar Inna wuro ba don haka ya sake tambayarta. Inna wuro ta ƙarasa bakin gadon Baffajo sannan ta ce, "Wani yaro ne ƙaninka ya tsinto shi a kogin Iro mai garke, to da yake makarai sun taɓa shi ya rinƙa nema guje-guje kenan don haka muke kulle shi a ɗaki, amma duk da haka yara suna zuwa suna tura shi." Kabiru ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, "Allah ya bashi lafiya." Inna wuro ta amsa sannan ta yi musu sallama ta wuce gida.

Hasken rana da hayaniyar yara ne suka sata farkawa jiki a tsamame, wani mummunan wari ne ya doki hancinta da ƙarar ƙudaje da ta karaɗe kunnenta. A zabure ta miƙe tsaye tana dube-dube sakamakon tsintar kanta da ta yi a tsakiyar bola, tana shirin karkaɗe jikinta ta riski muryar yara suna faɗin: "Mahaukaciya ƴar macu kul..."


Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

39


Da matuƙar mamaki Raihan ta dube su a hankali ta riƙa takawa kai ba ɗankwali, ganin suna ci gaba da tsokanarta wasu har da masu jifanta da dutse ya sa Raihan ta fara tunkararsu tana faɗin, "Don Allah kuna ji na kuma kuna ganina." Dariya suka fara yi wasu daga cikin yaran suna jan rigarta ta baya suna faɗin, "Mahaukaciya ƴar macukule." Tafiya Raihan ta fara yi ba tare da ta san wurin da take jefa ƙafarta ba, sai da ta ji zafin wani ƙaton dutse da wani yaro ta jefeta a kanta, sanann ta tabbatar da ba mafarki take yi ba tabbas ita ce Allah ya kuɓuto da ita. Waiga wa ta yi tana ƙare wa mummunar bolar mai ɗauke da caɓalin kayan ƙazanta iri-iri, wani tunani ne ya dirar mata a zuciya. Ta ayyana kada Huzaifa ya sake sace ta, ƙafa ba takalmi kai ba ɗankwali Raihan ta zuba a guje don ta ci alwashin ko a ƙafa ne sai ta koma gidansu. Tana tafe tana gudu yara na biye da ita har ta ƙarasa bakin titi, duk Ɗan adaidaita sahun da ya zo da Raihan ta tsayar da shi idan ya dubi yanayinta da yaran da suke biye da ita sai ya ja mashin ɗin sa ya ƙara gaba. Yaran da suke biye da ita ne suka fara damunta don haka ta fara yi musu magana, daga ƙarshe da abin ya damu Raihan sai kawai ta fashe da kuka. Wani mutum ne da ya je wuce wa ya yi wa yaran tsawa amma suna ganin ya wuce suka ɗora daga in da suka tsaya. Ganin haka ya sa Raihan ta ci gaba da tafiya a ƙasa, nan take yaran suka fara ɗiban ƙasa suna watsa mata sai dai wannan karon bata kula su ba. Ganin abin nasu ya sake yawa suna ta jifanta da manyan duwatsu ya sa Raihan ta ɗiba da gudu za ta tsallaka titi bisa tsautsayi wani mai mota ya zo wuce wa ya make ta. Da sauri yaran suka yi carko-carko, Raihan ta faɗi a can gefe kanta ya fashe yana fara zubda jini. Ban da juyi cikin azaba babu abin da take yi, a rikice Al'amin ya fito daga motar yana sallallami, da taimakon wasu matasa aka saka Raihan a cikin mota wani ɗan sanda na daga gefe ya ƙaraso ya shiga gaban motar suka fara zuwa Police station aka rubuta report sannan suka wuce asibiti. Wani private hospital Al'amin ya kai Raihan da ke unguwar sharaɗa, nan take likitoci suka shiga bata kulawar da ta dace. Al'amin zaune ya yi ya haɗa kai da gwiwa a hankali ya fara ƙare wa Raihan kallo yana son sanin wurin da ya san fuskarta amma ya kasa tunawa, kasancewar yawancin hotunan Raihan da aka watsa duk na bikinta ne kuma da kwalliya a fuskarta shi ya sa farat ɗaya ba za ga ce ita ba ce. Wayar Malam Usman ce ta shiga da sauri Al'amin ya ɗauka bayan ya yi sallama Mahaifinsa ya ce, "Ka ƙarasa ne?" Jiki a sanyaye Al'amin ya gaya wa mahaifinsa abin da yake faruwa a rikice Malam Usman ya furta, "Hasbunallahu Wani'imalwakeel. Yanzu kuna wane asibitin?" Al'amin ya ce, "Health Care Clinic na kan titin mu." Malam Usman bai gama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login