Showing 48001 words to 51000 words out of 157890 words

Chapter 17 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

171

ya doka ƙofar banɗaki ya shige ciki yana sauke ajiyar zuciya. Sai dai gabaɗaya ya gama tsinkewa lamarin don yadda ya ji tana bugun ƙofar tamkar za ta ɓalleta, a haukace ta juyo wurin ƙofa don mommy na wurin tana ihun kiran Daddy tana ganin Raihan ta yo kanta da gudu ta yi gaba cikin tashin hankali, Su Inno da goggo da rarrafe suka fice daga falon ban da ɗankwalaye da zannuwansu babu abin da suka bari a wuri. Da ƙyar Mommy ta samu ta fice daga falon tana fita harabar gidan ta ja ƙofar ta rufe da ƙarfi amma dukda haka sai da Raihan ta yage bayan Mommy da faratanta.

Kabiru na kwance a ɗakinsa ya ji shigowarsu Inno ganin yanayin da suke ciki ya sa ya duburburci yana faɗin, "Hai Inno lafiya kuwa?" Goggo ta yi karaf ta ce, "Kai Kabiru buɗe mana ƙofa maza Albasu za ni." Kabiru ya dubi su Inno daga su sai ɗan fatarinsun zai yi magana ya ji ihun Mommy da sauri ya fito yana tambayarta, hankali a tashe mommy ta shiga nuna masa gidan tana faɗin, "Wallahi ciwon Raihan ne ya tashi Daddy na ciki ina tsoron kar ta yi masa illah." Cikin Kabiru ne ya kaɗa a tsorace ya ce, "Hajiya ya za mu yi ga Goggo ta ce Albasu za ta tafi." Mommy da hawaye ya gama jiƙe mata fuska ta ce, "Don Allah bar batun Albasun nan, wuce ka je Waraka a nan titin sharaɗa islamic chemist ɗin yake don Allah ka kira mana malamin." Kabiru ya yi jim ganin kamar ba gane abin da yake nufi ba, Mommy na hango hijabinta a kan igiya da aka yi wanki ta fisgo shi da sauri ta saka tana faɗin, "Kabiru ka kula da su Inno karka bari su fita." Tana gama maganar ta fice da gudu, Inno na shirin bin ta Kabiru ya sha gabanta ya datse ƙofar da ɗan mukulli ya cire ya koma ɗaki.



Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

16


Hankalin Daddy ba ƙaramin tashi ya sake yi ba ganin irin yadda Inno ta fara fita hayyacinta, a hargitse ya dubi mommy yana faɗin, "Zainabu me yake faruwa da Inno ne ko faɗuwa ta yi?" Mommy da ita ma ta fara fita hayyacinta ta nuna hanyar da Mar'usa ta bi tana faɗin, "Wallahi ba mutum bace." A daidai lokacin Goggo ta taho ta hanyar tana tafe tana faɗin, "Haka kawai kai ba arne ba kai ba baka haɗa iri da mai jan kunne ba ace gida kullin abu ɗaya, ina dalili ace koyaushe sai dai mu kalli ƙasashen turawa. Wallahi da sake, wannan tsohuwar ta bar ganin ita ta haifi Audullahi ni ma ina da iko da gidan tun da ai Ƴata yake aure, haka kawai wa ya sani ko zaginmu suke da yarensu ba mu sani ba. A'a raba ni da wannan lamarin ko a riƙa kunna min sangaya ko kuma na ɗauki ƙullin kayana na wuce Albasu, yoooo me gare su da babu a Albasu? Allah na tuba waccen tukunyar sanyin ce kaɗai ba ni da ita, tun kafin marigayi ya rasu ya ajiye mini talabijin na kalli sangaya na kalli Jan kunne. Ita ma tukunyar sanyaya ɗaki zan shiga adashin So dangi na haɗa da ƴan samiruna na bawa Zainbu ta cika ta saya min, zaman gidan siriki ko tashin hankali. Allah ya sani daga nan babu in da zan tsaya sai Albasu, abu ɗaya zan tsaya jira Audullahi ya haɗa min tsaraba na kaiwa su Rahila idan ba haka ba kullin suna liƙe da ni, su cika min ɗaki da tsamin kai da na hammata..." Bata kai ƙarshen maganarta ba ta ga Mommy na nuno wurin da take tana faɗin, "Da gaske ba mutum bace yaudararmu take yi aljana." Daddy na ɗaga kai ya yi tozali da Goggo, karaf maganganun mommy suka sauka a kunnen Goggo. Baki a sake ta ƙarasa wurin tana tafa hannuwa, Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Ni kam Zainabu kanki bai fara taɓuwa ba kuwa? Taimaka min mu kai Inno asibiti." Inno da take jin maganganun Daddy sama-sama nan take ta tuno irin jijjigawar da Huzaifa ya yi musu cikin siffar Likita nan take ta sake ruɗewa ta ce, "Ina Alhaji Babba?" Da mamaki Daddy ya ce, "Alhaji Babba kuma Inno." Alhaji Babba Mahaifin Daddy ne ya rasu kusan sama da shekara talatin baya. Inno bata san ma Daddy yana yi ba balle ta fahimci tambayarsa, ta sake wawuro hannun Mommy tana cewa, "Alhaji Babba ka riƙe hannuna ka shafa min ƙofar aljannah. Idan mun shiga karka bi da ni ta hanyar masu kofato a ƙafa." Daddy ya sake duban Mommy ya ce, "Wai me yake faruwa?" Mommy na shirin yin magana Goggo ta yi caraf ta karɓe maganar da cewa, "Yooo ka nemi ba'asi Audullah bayan matarka ta gama kwayewa uwarta baya, yanzu Zainabu ni kika maida sheɗaniya wacce ta fito daga jinsin aljanu?" Goggo na faɗin haka ta rushe da matsanancin kuka, ta sa gefen rigarta ta share hawaye sannan ta ɗora da cewa, "Don Allah Audullahi idan Allah ya tsine min za ta bi ni ko ba za ta bini ba?" Daddy da kansa ya ɗaure ya dafa kansa da hannuwa biyu ya ce, "Goggo me ya yi zafi haka?" Goggo ta nuna Mommy ta ce, "Ba ka ji irin tozarcin da matarka ta yi min ba? Na rantse da Allah idan wani ya taɓa maida ni jinsin Aljanu Allah ya watsa min albarka, amma tun da haka ne zan bar muku gidanku na ƙare rayuwata a Albasu ko mutuwa na yi idan ba a kai gawata can ba ban yafe ba." Mommy ta zauna zaman dirshan ta ce, "Goggo ni fa ba manufa ta kenan ba, wallahi uwani ba mutum bace aljana ce yanzu haka abin da muka gani kenan muka firgita ni da Inno..." Gabaɗaya Mommy ta zayyana musu abin da yake faruwa, daga wurin da Goggo take ta yi tsalle ta dira a gadon bayan Daddy cikin kiɗima ƙwaƙumeshi tana faɗin, "Wattaba'u matattulisshayaɗina Alamulki Sulaiman, don Allah Audullahi ka dubi girman Allah ka mayar da ni Albasu ko mayu bamu da su balle Aljanu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Zainabu!" Ɗagowa ta yi tana kallonsa, bai bi ta kanta ba ya ci gaba da cewa: "Yanzu saboda Allah haka kawai za ki riƙa razana kanki, ki dubi tsofaffin nan suma kin razana su." Mommy takaicin duniya da ashirin ya kamata, babban baƙin cikinta da komai ta faɗa Daddy baya amincewa da ita sai dai yace ta cika tsoro. A zafafe ta dube shi don wannan karon zuciyarta ta bushe ta ce, "Na ga ji da yadda idanunka suke rufe wa akan abubuwa da dama, ba tun yau ba nake zargin jinnu sun samu gurbin zama a jikin Raihan amma kullin cikin ƙaryata ni kake yi, me kake ɗauke ne? Kana tunanin duk duniya akwai wanda zai zo Raihan kamar irin soyayyar.da nake mata. Karka manta cikinta na ɗauka wata tara tun tana ƙwayar hallita har zama cikakkiyar mutum, ka san yadda laulayi yake kuwa? Ka san yadda nake son cin wannan ba na son wanna? Idan na ci na yi amai da ƙyar zan samu wani ya zauna. Lokacin da cikina ya tsufa ka san irin nauyin da Ɗa yake da shi a cikin mahaifa? Tun da cikina ya fara girma na daina kwanciyar rigingine sai gefe da gefe kasan irin wahalar da nake sha idan na zauna zan tashi. Tun lokacin da na fara naƙuda ka san irin raɗaɗi da zafin ciwon naƙuda kuwa? Ban raina abubuwan da kake yi min ba na kulawa duk macen da ta samu kamarka ta yi dace amma duk kulawar da kake ba ni; ni kaɗai na san irin abin da nake ji a jikina, shin ka san yadda ratsowar kan ɗa yake daga jikin Mahaifiya kuwa? Na shafe tsawon wata tara ina rainon cikinta, duk wani yanayi da nake ciki tana fuskata na farinciki ko baƙinciki, hatta sautin muryata ta tantance kalarta shin tana samun waɗannan abubuwan daga gare ka? Ka gaya min akwai shaƙuwar da za ta wuce tsakanin ta Ɗa da mahaifiya? Ka ga ya min akwai wanda zai nuna mata soyayya fiye da wacce zan nuna mata? Kana tunanih za ka fini ƙaunarta?"

Mommy ta ƙarasa yi wa Daddy tambaya tana tsare shi da ido babu alamar tsoro a tattare da ita. Shiru ya yi yana nazarin maganganunta, Mommy bata damu da haka ba ta ci gaba da cewa, "Duk wannan gatan da kake nuna mata sam ba soyayya ba ce, kuma ba zan taɓa alaƙanta Raihan da ciwon jinnu ba kawai don son raina ba. Uwani da muka shafe tsawon shekaru da ita ba mutum ba ce ƙaton aljani ne da ya shiga jikin Ƴarka Raihan, ɗazun nan muka fahimci haka ni da Inno idan kuma kana musu wataƙila idan ta gaya maka za ka ɗauki abin da muhimmanci, idan kana tantama ka duba cikin gidan nan kaf idan za ka sake ganinta." A wannan karon hankalin Daddy ya fi na koyaushe tashi, jikinsa har rawa yake ya dubi Inno da hargagin Mommy ya dawo da ita cikin nutsuwarta yana shirin yin magana Inno ta ce, "Audullahi!" Daddy ya amsa mata murya a sanyaye Inno ta ci gaba da cewa, "Idan baka haɗa ni da Zinaru ta kaini albasu ba Alhaji Babba ya dawo duniya. Ganin idona na ga Uwani da Kofato har tana gaya mana ita ba mutum ba ce yau mai hanani tafiya Albasu sai Allah." Goggo na maƙale a bayan Daddy ba tare da ta fahimci a wurin wa take ba, tana miƙa hannu ta shafo gemun Daddy a zabure ta leƙa fuskarsa tana faɗin, "Yau na shiga aljanna na kasa fitowa yau ni ce maƙale a bayan Audullahi, astagafirullah Allah ka yafe min me ya kaini bayan siriki ana zaune ƙalau?" Goggo ta ƙarasa maganar tana zazzage ɗankwali sai da ta ɗaura shi akanta ta ce, "Me zan zauna na ci gaba da yi a gidan nan ban da abin kunya, wannan Idan ƴan Albasu suka ji kashina ya bushe gara na tafi sawuna a likafa tun Audullahi bai yanke hukunci ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyi ya ce, "Zainabu meye mafita?" Mommy kamar dama jira take ta ce, "Mafita dole ka nemo malaman Islamic chemist ɗin da baka son a kira su zo su yi mata ruƙiyya." Inno ta hangame baki tana tafa hannuwa ta ce, "Kai ni dai wallahi Ƙasimu ya nakasa min rayuwa da ya ɗoraka a turbar rayuwar masu jajayen kunne. Kai dai Audullahi da kasan taimakon da malamai suka yi maka kana ƙarami da baka guje su ba, wallahi ko labarin ƙarzuwarka na baka ya isheka ishara, a bar batun fitsarin kwance da sannu Allah sannu Ma'aiki da yaya muka samu ka daina, ka san irin tashin hankalin da na shiga lokacin da na ji za ka yi aure, na ce na ga ta kaina yaro ya zo yana fitsarin kwance mace ta raina shi. A'a wannan lamarin ba na aikin likitoci ba ne, ko rashin haihuwar matarka Allah ya sani ina zargin sheɗanu sun murƙushe maka ƙwayoyin hallita, don kar na yi shisshigi shi ya sa na saka muku ido amma da tuni na kira Ɗan wanzam har gidan nan zai zo shi da Kawunsa Malam mai farin allo sun baku magani." Daddy tuni ya gama ƙosawa da maganar Inno, tun bai ƙarasa jin abin da take faɗa ba ya miƙe yana faɗin, "Yanzu bari na kira Alhaji Munniru na ji a ina zan samu wurin da za a karɓo mata magani..."

"Ba sai ka kira kowa ba, ga mu ga Waraka Islamic chemist a titin sharaɗa, kai tsaye ɗaukan yarinyar nan za mu yi mu wuce da ita, da zafi-zafi kan daki ƙarfe." Mommy ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Inno ta yi fiƙi-fiƙi da ido cike da firgice ta ce, "Billahillazi idan kun ga ba mu biku wurin nan ba Allah ya watsa mana albarka, haka kawai ku fice ku bar mu aljanu su dawo su casa hatsi a kanmu?" Mommy da yake neman mafita take bata jira cewarsu ba ta ce, "Shi kenan duk yadda kuka ce haka za a yi." Daddy da kansa ya tunkari ƙofar ɗakin Raihan sai dai lokaci ɗaya ya ji wani irin tsoro ya ɗarsu a zuciyarsa, yana daga tsaye ya fara jin wani irin gurnani kamar gurnanin zaki. Da sauri ya yi baya yana kallonsu Mommy a tsorace, Mommy na shirin yin magana ya ce, "Wallahi ji nake kamar ciwonta ya tashi gurnanin wani abin nake ji." Inno tuni cikinta ya kaɗa, ta maƙale a bayan Goggo tana leƙe. Mommy ita kanta hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, a hankali ta yi ta maza bakinta ɗauke da addu'a ta kalli Daddy ta ce, "Babu abin da ya gagari ubangiji, mu yi addua mu shiga ɗakin." Da sauri Daddy ya fara motsa baki yana biya ayatulkursiyyu yana tura ƙofar Raihan ta yi kuka kura ta faɗo kansu cikin wani irin gurnani mai tafe haushi kamar haushin kare. Idanunta a kakkafe suke kanta ya hargitse ga faratanta tuni suka fara sauya launi. Kafin su farga tuni ta fisgi hannun Daddy ta shige da shi ɗaki, ganin haka ya sa Daddy razana ya manta da addu'ar da yake yi ya fara ihu yana neman taimako. Yagarsa ta fara yi ta ko'ina da faratanta tana ƙoƙarin kai bakinta jikinsa Allah ya bashi sa'a ya hamɓareta ya doka ƙofar banɗaki ya shige ciki yana sauke ajiyar zuciya. Sai dai gabaɗaya ya gama tsinkewa lamarin don yadda ya ji tana bugun ƙofar tamkar za ta ɓalleta, a haukace ta juyo wurin ƙofa don mommy na wurin tana ihun kiran Daddy tana ganin Raihan ta yo kanta da gudu ta yi gaba cikin tashin hankali, Su Inno da goggo da rarrafe suka fice daga falon ban da ɗankwalaye da zannuwansu babu abin da suka bari a wuri. Da ƙyar Mommy ta samu ta fice daga falon tana fita harabar gidan ta ja ƙofar ta rufe da ƙarfi amma dukda haka sai da Raihan ta yage bayan Mommy da faratanta.

Kabiru na kwance a ɗakinsa ya ji shigowarsu Inno ganin yanayin da suke ciki ya sa ya duburburci yana faɗin, "Hai Inno lafiya kuwa?" Goggo ta yi karaf ta ce, "Kai Kabiru buɗe mana ƙofa maza Albasu za ni." Kabiru ya dubi su Inno daga su sai ɗan fatarinsun zai yi magana ya ji ihun Mommy da sauri ya fito yana tambayarta, hankali a tashe mommy ta shiga nuna masa gidan tana faɗin, "Wallahi ciwon Raihan ne ya tashi Daddy na ciki ina tsoron kar ta yi masa illah." Cikin Kabiru ne ya kaɗa a tsorace ya ce, "Hajiya ya za mu yi ga Goggo ta ce Albasu za ta tafi." Mommy da hawaye ya gama jiƙe mata fuska ta ce, "Don Allah bar batun Albasun nan, wuce ka je Waraka a nan titin sharaɗa islamic chemist ɗin yake don Allah ka kira mana malamin." Kabiru ya yi jim ganin kamar ba gane abin da yake nufi ba, Mommy na hango hijabinta a kan igiya da aka yi wanki ta fisgo shi da sauri ta saka tana faɗin, "Kabiru ka kula da su Inno karka bari su fita." Tana gama maganar ta fice da gudu, Inno na shirin bin ta Kabiru ya sha gabanta ya datse ƙofar da ɗan mukulli ya cire ya koma ɗaki.



Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

17


Inno sai da ta kalli hagu da dama ta ga babu kowa a harabar gidan daga ita sai Goggo sai kawai ta faɗa ɗakin Kabiru tana faɗin, "Kai yaro idan kana neman albarka ka buɗe mana gida mu fice." Kabiru ya kauda kansa gefe ya ce, "Inno ko ba a ce karna barku ku fita ba ai bana barku ku fita a haka ba, ku dubi kayan jikinku fa. Gaskiya bari na miƙo muku zannuwan Hajiya ku ɗaura, don zamanku haka bai kamata ba." Goggo ta ja dogon tsaki ta ce, "Kai muna maganar zuwa Albasu kai kana cewa a ba mu zani, shi aljani ina ruwansa da ɗaura zani." Inno da ta gama zuwa wuya ta ce, "Kai Kabiru kake ko wa? Yau da idanunan nawa na ga aljana ko tsirara ka gammu ba za ka yi mamaki ba." Da sauri Kabiru ya ƙunshe baki yana faɗin, "A'uzubillahi gara dai da kuke cikin sitira." Yana gama maganar ya miƙe ya fice ya ɗaukowa su Inno zannuwa suka ɗaura, suka yi jugun-jugun sai dai kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin tashin hankali.

Mommy ban da sauri babu abin da take yi kamar za ta tashi sama, duk wanda ya ga irin saurin da take yi sai tabbatar da tana cikin halin damuwa. Tana zuwa bakin titi ta fara taron adaidaita sahu don ko kaɗan bata yi tunanin ɗaukan mota ta fito da ita ba, sai da ta tsaida Adaidaita sahu sun fi uku babu wanda yake tsayawa saboda ganin irin yadda take yi musu magana a hargitse. Da ƙyar ta samu wani ya ɗauke ta tiryan-tiryan har Sharaɗa kwanar kasuwa a bakin Waraka Islamic chemist ya sauketa, ko waige mommy bata yi ba da ta sauka sai da ya ƙwalla mata kira tukunna ta waiga, da hannu ta nuna masa alamar ya jirata gata nan zuwa. Mommy tana shiga bakinta ɗauke da sallama ta dubi mutanen wurin tana tambayarsu, "Don Allah ina Malam yake?" Wata mata sanye da hijabi har ƙasa ta ce, "Hajiya lafiya?" Mommy ta ce Malam nake nema yarinyata ce babu lafiya." Matar mai hijabin ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin ce don masu kalar hijabinta kusan su biyar ne a wurin da alama shi ne uniform ɗin su. Kan kujera matar ta nunawa Mommy ta ce, "Ki zauna yanzu Dr ya shigo bari a yi masa magana." Matar na gama magana ta wuce ciki. Bata jima ba ta dawo tama faɗin, "Za ki iya shiga." Tun matar bata rufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login