Showing 57001 words to 60000 words out of 157890 words

Chapter 20 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

157

yi ba." Goggo ta gama zuwa wuya sai kawai ta nufi saitin windon Raihan ta fashe da kuka tana ƙwalawa Mommy kira, a hargitse mommy ta fita tana tambayar ba'asi. Goggo ta kalli Daddy ta ce, "Wallahi ka sakar min ƴata a yanzunan don yau duk dare a Albasu za mu kwana." Malam Usman da farko ya ɗauka wasa suke yi wa juna da sauri ya kalli Goggo yana faɗin, "Don Allah Mama ku yi haƙuri wannan ba girmanku ba ne." A zafafe Goggo ta dakatar da Malam Usman tana nuna shi da hannu tana cewa, "Dakata Malam wannan ba abin da ya shafi aljanu ba ne, ka bari idan muka zo fagen sai a neme ka, ka yi ruƙiyya yau zan nunawa wannan matar almatsutsan kaina sun fi nata. Zainabu dai nina haifi abata don haka yau ko a ƙafa sai mun tafi Albasu idan ya so duk abin da zai faru sa dai ya faru."




Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 idan
kina buƙata ki min magana 0706 206 2624


20



Ilahirin jikin Daddy ba ƙaramin sanyi ya yi ba, ya ƙarasa gaban Inno ya ce, "Don Allah Inno me kuke yi haka wannan abin da kuke yi ko Raihan ba za ta yi shi ba, ba fa mu kaɗai ba ne a gidan nan don Allah ko ma meye ku bari komai ya daidaita." Inno ta saki baki da hanci tana kallon Daddy sai da ya gama magana ta dubi Malam Usman ta ce, "Malam don Allah saboda wa nake haƙiƙance wa?" Malam Usman ya yi shiru don bai fahimci abin da Inno take nufi ba, Inno ganin haka ya sa ta dubi Daddy tana faɗin, "Audullahi saboda ina kare ka za ka ci zarafina?" Kafin Daddy ya yi magana Goggo ta dubi mommy ta ce, "Wai Zainabu duk maganar da nake yi ba ki ji abin da na faɗa ba ne? Na ga ko gezau baki yi ba." Mommy baƙinciki goma da ashirin ya cikata ta dubi Goggo tana faɗin, "Don Allah Goggo yanzu me kike so mu ce, kina gani yanzu haka kaya nake haɗawa za mu tafi nema wa Raihan lafiya, da wanne zan ji?" Goggo ta riƙe haɓa tana cewa, "Wai kina nufin yaron nan bai yi fata-fata da aljanin jikin Raihanu ba." Mommy ta jinjina kai fuska babu walwala ta ce, "Kin san ciwo shi yake shiga farat ɗaya sauƙi sai a hankali, balle irin wannan larurar ta Raihan sai an bi a sannu." Inno ta kalli Daddy rai a ɓace tana faɗin, "Amma dai Audullahi kun shammace ko in ce kun yaudare mu, yanzu a madadin ka gaya mana mu kame bakinmu sai ka bari mu yi ta sakin zance, Allah ya sani idan wani abu ya shafe mu kai da matarka kuna da kamasho a ciki don haƙƙinmu ba zai bar ku ba."Inno ta waiga wurin da Kabiru yake tsaye ta nuna shi da yatsa ta ci gaba da cewa, "Allah dai ya watsa maka albarka ka ji Kabiru, yaron nan bai bari mun furta ko tuf ba bayan ayar Allah, ban da hailala da istigifari babu abin da muke yi don kariya daga kaidin wancen hatsabibin." Malam Usman ya yi murmushi don rikicin tsofaffin ya fara bashi dariya, ya ƙarasa gabansu ya furta, "Mama babu abin da zai faru da ku in sha Allah. Ita ma Raihan za ta samu lafiya da yardar Allah." Cike da gamsuwa Goggo ta matsa gabansa sai da ta kalli hagu da dana cikin raɗa ta ce, "Ka dubi girman Allah malam ka yi min wani abu ɗaya kafin ka ƙone yaron nan." Lokaci ɗaya suka juyo wurinta, Goggo kuwa ko a jikinta ta sake kallon gabas da yamma tana faɗin, "Amma dai ba zai iya jinmu ba ko?" Inno ta ƙarasa wurin ta ce, "Shi wa?" Goggo ta yi mata alamu da hannu a kan ta yi maganar ƙasa-ƙasa sannan ta ce, "Wannan hatsabibin da ya yi rayuwa da a siffar uwani." Inno ta yi kasaƙe ba tare da furta komai ba don ita tsoron magana take akan Huzaifa, tana tsoron kar ya farmaketa a kowanne lokaci. Malam Usman ya gyaɗa kai yana cewa, "Eh ina jin ki Mama." Goggo ta zura hannu cikin kajarta (Siket ɗan ciki na tsofaffi mai aljihu a jiki.) Ƙullin goro ta ciro ta miƙa wa Inno ta ce, "Don Allah ci ki ji daushe ne ko namijin goro." Inno ta karɓa ta wurga a baki ji kake garas, Inno ta miƙa wa Malam Usman guntun wanda ta gutsira ta ce, "Ɗana ci ka ji kamar Daushe." Daddy ya kalli Malam Usman a kunyace ya ce, "Don Allah Malam ka yi haƙuri ka san lamari tsofaffi sai..." Malam Usman ya katse shi da cewar, "Babu komai Alhaji muma muna nan da su." Ya karɓa ya sa a baki yana fara tauna Goggo ta ce, "Don Allah ka taɓa jin goro mai daɗin wannan?" Malam Usman yana ci gaba da tauna yana girgiza kai, ganin haka ya sa Goggo ta washe baki tana faɗin: "Duk faɗin garin nan ban taɓa siyan goro a nan ba sai na niƙi gari na tafi Albasu duk ƙanƙantar wanda zan siya, amma hatsabibin can da ya yaudare mu da siffar Uwani kusan tare muke cinye wa da shi. Kai wallahi ina zargin har satar min yake ban sani ba, don idan na siyo na dubu biyar baya rufa wata biyu don Allah cin wannan goron ai daga ji ba na lafiya ba ne." Inno ta gyaɗa kai ta yi ƙasa da murya ta ce, "Ni nadamar da na yi da muka sakankance shegen nan yake ƙare wa tsirancinmu kallo. Allah ya sani da Alhaji babba zai dawo mai raba Huzaifa da shi sai Allah, don Allah Zinaru baki taɓa sauya kaya a gabansa ba? Ni tsorona Allah da Ma'aiki kar ya sake dawo mana, kuma wallahi da Alhaji babba zai dawo sai ya bi mini haƙƙina saboda Allah ya sani ban yafe ba." Goggo ta yi jim tana nazari sannan ta ci gaba da cewa, "Ki bari a fara sauraron shari'armu da shi tukunna." Malam Usman ya yi dariya mai sauti ya ce, "Mama wannan ai ba abin da damuwa ba ne tun da za a ƙone shi kin ga hukuncin ai ya yi har na cinye goron da ya yi miki." Goggo ta wara hannuwa tana washe baki ta ce, "Shi kenan ma! Amma don Allah ka ƙone shi da manyan ayoyi masu saurin babbake aljanu." Malam Usman ya amsawa Goggo; Inno na shirin magana ya ce, "Alhaji lokaci na tafiya ya kamata ya kintsa sai mu wuce ko?" Inno ta kalli Goggo murya a sanyaye ta ce, "Zinaru ni kam na roƙe ko gafara man." Goggo ta sunkuyar da kai ta ce, "Allah ya yi mana aikin gafara, amma ni kam baki taɓa yi min komai ba wanda ya faru ma sharrin shaiɗan ne." Inno ta karɓe zancen da cewa, "Allah na tuba Audullahi da Zainabu ko a lahira na ji za su raba gari ai sai in da ƙarfina ya ƙare, yoo ana zaune ƙalau mu ɗaukar wa kanmu zunubi. Kin san hukuncin wanda ya datse igiyar sunnar Annabi kuwa." Goggo ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, "Ai ko yau sai na kwana hailala da istigifari don tun a Albasu ban sake aikata irin wannan zunubin ba, ina ni ina raba auren Zainabu haka kawai na faɗa Sa'ira ko kuma Hawuya, a'a raba ni da wannan lamarin ai ko a Aljanna ma muna sahun masu shiga Firdausi." Mommy da Daddy suka yi murmushi saboda da farko hankalinsa ya tashi don tsofaffin ba ƙaramin rikici gare su ba.

Cikin gida Mommy ta koma ta ci gaba da taimaka wa Raihan ta shirya, sai da ta bata ruwan Tea ta sha sannan ta haɗa musu kayansu a jaka. Daddy ya jima a toilet yana gasa jikinsa sannan ya samu ya ɗan ji daɗin jikinsa dukda raunin da ta yi masa dole sai ya dangana da asibiti. Kafin wani lokaci tuni sun gama shiri tsaf. Inno da Goggo har lokacin ba su fahimci Mommy da Raihan za su koma Waraka da sunan sai Raihan ta samu lafiya za su dawo ba, sai da suka ga Mommy da kaya niƙi-niƙi sannan Inno ta wurga mata tambaya, "Zainabu ni kam wai baki huce ba ne Allah Albasun za ki tafi na ganki da kaya?" Mommy ta manta shaf da maganar tafiya Albasu don haka ta ce, "Inno Waraka za mu je fa, kin san suma Islamic chemist ɗin an ci gaba yanzu har gado ake bawa mara lafiya." A zabure Goggo ta ce, "Mu kuma mu zauna a ina?" Inno ta cafe da cewar, "Taya ni ji kin ji." Ajiyar zuciya Mommy ta sauke don ita hankalinta ya yi gaba ta manta cewar abin da ya faru ko me za a yi wa su Inno ba za su taɓa kwana a gidan ba. Cikin gida ta koma suka tattauna da Daddy sannan suka fita, yana fitowa ya ce ya kira waya za a kai su Albasu idan ya so bayan Raihan ta dawo sai a dawo da su. Wannan magana ba ƙaramin daɗi ta yi wa su Inno ba, basu ɗauki lokaci ba Direban Daddy ya kwashe su da kayansu, don kayan sawarsu ma sai Mommy ce ta kwaso musu sun ce ba za su taɓa shiga gidan ba. Daddy ya ɗebo kuɗi masu yawa ya basu haɗe da kayan abinci ya zuba musu a boot sannan suka wuce Albasu. Mommy lokacin da ta ce wa Raihan ta fito su tafi da farko ƙi ta yi sai da Malam Usman ya shiga gidan da kansa ta fito, tana tafe tana harare-harare. Ganin haka ya sa Daddy ya fara yin baya-baya da ita saboda dukan da ta yi masa bai gama wartsakewa ba. Kabiru ba karamin tausayin Raihan ya yi ba don lokaci ɗaya gabaɗaya ta fita hayyancinta duk ta yi wani iri ga wata rama da ta yi ta lokaci ɗaya.

Ilahirin waɗanda suke wurin daga jinsin mutane har zuwa jinsin aljanu sun yi jigun-jigun don da alama yanayin da suke ciki ba mai daɗi ba ne. Abar bauta ce ta miƙe cikin tsananin fusata ta fara zagaye su ɗaya bayan ɗaya tana jinjina kawunan jikinta, tana zuwa wurin wani dutse ta fara buga kanta da dutsen cikin ɓacin rai har sai da ta fara illata kanta. Hatsabibiya ta miƙe ta ƙarasa wurinta tana son taɓa ta don ta dakatar da ita amma tsoron abin da kaje ya zo ya sa ta tsaya daga baya tana faɗin, "Yake Abar bauta wannan ba ita ce mafita ba." A zabure Abar bauta ta juyo wannan karon bakinta har fidda amon wuta ya ce, cikin wata irin fusatacciyar murya ta ce, "Yana neman ruguza alƙaliman tsafinmu, cikin ƙasa da wuni guda ya yi mana mummunar asara. Na shafe dubannin shekaru ina burin cimma burina amma ya wargaza farincikina ya wargaza tasirina, me kuka ganin za mu yi me ye mafita a halin yanzu domin a halin da muke ciki Huzaifa ne ya kawai yake ba mu kariya, yana ba mu kariya ne saboda yana jikinta amma idan ba mu yi da gaske ba matuƙar ya fita daga jikinta ta mu ta ƙare gabaɗaya hallakar da mu za a yi. Don na lura wannan malamin da yake yaƙarmu da gaske yake ba da wasa ba, kuma yana da matsananciyar kariya da tuni mun dunfare shi mun gama da shi, sai dai na san ko karen hauka ya cije mu ba za mu yi gangancij yin haka ba don lokaci ɗaya zai gano mu kuma ya hallaka mu, tun da yanzu babu wanda ya san tana tare da mu hatta shi kansa Huzaifa." Mugaza da ke gefe ta yi shiru tana nazari don idan Huzaifa ya fita daga jikin Raihan tafi kowa farinciki, sai dai ita ma a halin da take ciki matuƙar ta ce ita kaɗai za ta gudanar da nata ɗaukan fansar za ta iya halaka, don yadda aka halakar da tsaunin abar bauta ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba. Ta ci alwashin ko ba komai sai ta shayar da Raihan azaba ta hanata kwanciyar hankali kamar yadda ita ma ta hanata nutsuwa. Daga wurin da take ta miƙe tsaye ta fara magana, "Matuƙar ina raye Huzaifa ba zai taɓa barin jikin Raihan ba." Lokaci ɗaya suka juyo wurinta cikin mamaki, ganin ta ja hankalinsu ya sa ta ci gaba da cewa, "Ƙwarai abin da na faɗa haka ne, Huzaifa ba zai bar jikin Raihan ba matuƙar ina raye domin daga nan zan je na sake tunzura shi akanta. Babu abin da ya tsana sama da na ce dole zai bar jikinta ko na furta kalma mara daɗi a kanta." Cikin jin daɗi Abar bauta ta matso ta rungumi Mugaza, abin da bata taɓa yi wa wani a cikin tsibirin ba. Mugaza ta yi shu'umim murmushi don ita kaɗai ta san manufarta ta gaya musu haka, a ganinta idan ta yi haka za ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Na farko za ta ƙara jefa soyayyarta da samun shiga a wurin abar bauta da ƙungiyar tsafinsu. Darajarta za ta ƙaru matsayinta zai ɗaukaka za ta zama ƴar gaban goshin abar bauta. Na biyu za ta ci gaba da hillatar Raihan har sai ta kai mizanin da take son aiwatar da mugun ƙudurinta a kanta. Nan take suka ci gaba da tattaunawa Intisar na ci gaba da yaudararsu da zantuka kala-kala don ta ga maganganunta ba ƙaramim shigar su ta yi ba.

"Duk wanda ya ce zai haɗiyi gatari sai a sakar masa ƙota, dama na gaya maka idan wani ya yi rawa an biya shi wani idan ya yi duka zai ci. Amma ba zan fasa gaya maka Raihan ta fi ƙarfinka, ka fita daga rayuwarta. Wai me za ta nuna min da kake neman salwantar da rayuwarka a kanta, idan ka mutu sun kashe banza sun kashe wofi fa. Ka ga an cuce ni da ƴaƴana akan wata sakarai." Mugaza ta yi maganar cikin zolaya da son harzuƙa zuciyar Huzaifa. Kallonta ya yi yana huci don ta kara wa Barno dawaki domin dama ransa a matuƙar ɓace yake kuma ta ƙara masa da wani. Gyambon jikinsa ya sa wani ruwan magani yana wankewa ta sake bushe wa da dariya a lokacin da idonta ya sauka a kan wata lafceciyar kuna a gefen kafaɗarsa, tana shirin magana ta riski muryarsa yana faɗin.

"Ki bar murna karenki ya kama kura, domin koda kura ta rame ta fi ƙarfin ƙosassun karnuka. Ba zan taɓa bari a raba ni da Raihan ba wannan alƙwari ne da na ɗaukar wa kaina, domin ita rabin jikina ce. Na yi sakankancewar da babu mahalukin da zai raba ni da ita, idan kuwa aka nemi halaka ni zan kashe ta kowa ya rasa don ko da na mutu gawata ba za ta iya jurar jin Raihan ta tare da wani namijin ba ni ba. Na yi rantsuwa da girma tsafi da hatsabibancin kakana idan na fito daga tsatson jinin hatsabibin kakana sai dai Raihan ta mutu babu aure, yanzu haka shiri zan sake yi na tunkari Malamin don sai ya fahimci a cikin jinsinmu ma rukuni-rukuni ne, domin wasu jinnun rako wasu suka yi duniyar ni da kike gani bil'adam bai isa ya ga bayana ba. " Daɗi ya ratsa zuciyar Mugaza don ko ta wannan fannin ta san ta yi galaba akansu, kafin ita ma ta fara dasa nata ɗaukar fansar.

Kafin fitarsu sai da Daddy ya jadaddawa Kabiru cewar duk wanda ya zo basa nan kar ya buɗe masa gida kuma ya ce masa kawai sun fita unguwa ne, Kabiru shi kansa ta maza yake yi don tun da ya ga an ɗaɗe an bar shi, shi kaɗai yake saƙa da warwara. Ganin tunanin banza na neman yi masa yawa ya sa ya ɗauro alwala fara tilawar Alƙur'ani. Su Mommy suna zuwa bakin ƙofar Waraka Islamic chemist Raihan ta coge, juyin duniya aka yi da ita ta fito ta ƙi. Kifa kanta ta yi a jikin kujerar mota ko ɗago wa ta kalle su bata yi ba balle su saka ran za ta kula su. Malam Usman bai yi mamaki ba don kusan masu irin matsalarta suna yin fiye da abin da ta aikata. Da kansa ya ƙarasa wurin motar ya tsaya, Raihan bata ɗago ba ta ci gaba da zama kamar yadda take. Malam Usman ya dafa jikin murfin motar yana faɗin, "Ka taso ka fito mu shiga ciki ta daɗi tun ban shigar da kai ta yanda ka ɓullo ba." Raihan ta ɗago da kanta ta kalli Malam da idanunta da suka rine kamar sabon barkono. Kamar ba za ta tanka masa ba sai kawai ta kalli wurin da Malam Usman yake tsaye ta tofar da yawu nan take wuta ta tashi a wurin. Baya Malam Usman ya yi yana jinjina kai don ya lura abin Huzaifa ƙara gaba yake ba baya ba. Ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin Mommy ya yi ba, tana daga gefe ban da hawaye babu abin da take yi. Malam Usman kira ya ƙwalawa ɗaya daga cikin yaransa ya basu umarni akan su kawo masa ruwan addu'a, suna kawo masa ya watswa wutar tare da Raihan ɗin gabaɗaya. A fusace Raihan ta kalli Malam tana cewa, "Malam karka bari na kai bango akan hukuncin da kake son yankewa a kaina. Meye haɗinka da yarinyar nan da kake son raba ni da ita ƙarfi da yaji? Na gaya mata matata ce ba zan fita ba ana dole ko so kake sai na illataka, tun da ban ji maganar Mahaifiyata ba kana tunanin kai da na haɗu da kai sama ta ka zan bi umarninka ne?" Malam Usman bai bashi ba amsa ba ya ci gaba da zuba masa ruwan addu'a yana nan tsaye ɗaya daga cikin yaransa suka kawo kasko da wuta aciki ya fara yi masa turare da habbatussauda.Cikin ƙaraji Huzaifa ya dubi Malam Ya ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login