Showing 72001 words to 75000 words out of 157890 words
ɓata fuska tana kallon Raihan ta ce, "Kin ji fa matar Yaya." Raihan ta yi murmushi sanna ta yi wa Fatima raɗa a kunne, lokaci ɗaya Fatima ta ƙwalla ƙara ta buga tsalle ta maƙale Raihan tana cewa, "Allah ya kaimu asha biki yasin gidanku zan dawo." Raihan ta yi dariya tana kallon Salima, Salim ya naɗe hannuwa a ƙirji ya ce, "Wato wariyar launin fata za a nuna min?" Yanda ya yi magana ba ƙaramin dariya ya basu ba, lokaci ɗaya suka saka dariya. Suna zuwa harabar gidan Kabiru ya fito ya ce, "Samrayin ɗaliba har ka hito?" Salim ya miƙa masa hannu suka gaisa ya ce, "Fillo mun fito za mu wuce sai jango." Farida ta zuba wa Kabiru ido lokaci ɗaya ta ji ya matuƙar birgeta, Kabiru na shiga ɗaki da sauri Farida ta matsa kusa da Raihan cikin raɗa ta ce, "Matar Yaya don Allah wannan waye? Ma sha Allah he looks so..." Raihan ta zaro ido waje ta ce, "So..." Fatima ta katse Raihan da cewar, "Bar ƴar rainin sence Farida fa bata da saiti." Dariya suka yi Raihan ta yi musu sallama amma har suka je gida Farida na tunanin Kabiru don ba ƙaramin burgeta ya yi ba.
BAYAN WANI LOKACI.
Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya abubuwa da dama suka shuɗe kwanaki na ƙarewa. A haka har lokacin bikin Salim da Raihan ya ƙarato, sai dai har lokacin idan Raihan ta tuna babu aminyarta Intisar za a yi aurenta tana jin babu daɗi a ranta. Daga ɓangaren su Mommy shirye-shirye sun yi nisa su Inno sai jiƙe-jiƙe suke yi wa Raihan a cewarsu sune ya kamata su yi Raihan gyaran da duk yakata a yi wa Amarya. Saura sati biyu biki aka kawo lefen aure daga gidansu Salim, lefe ne ɗan ubansu na kece raini dukda akwatuna shida Salim ya yi mata amma an zuba mata kaya masu tsada tare da ƙunshin kuɗi masu yawa. A ranar da aka kawo kayan lefen saboda farinciki Mommy kasa bacci ta yi, lokaci-lokaci take tuna wai Raihan ɗinta ce za ta yi aure. Ita kanta Raihan ba ƙaramin farinciki ta yi ba saboda murna har da ƙwallarta, daga ƙarshe ta tashi cikin dare ta yi sallar nafila tare da gode wa Allah bisa wannan ni'ima da ya yi mata.
"Ya ke abar bauta wannan shirin da muka yi gani nake kamar ya yi yawa, kina ganin Raihan gadan-gadan aure ta yi yanzu haka za mu saka ido nasarorin ƙungiya suna dakushe wa." Hatsabibiya ta yi maganar hankali a matuƙar ɓace. Abar bauta ta saki wata shu'umar dariyar sannan ta ce, "Auren Raihan ba zai hana mu gudanar da abin da muka yi niyya ba, ba na ganin auren Raihan zai kawo mana cikas domin yin aurenta shi zai ba mu damar aiwatar da duk abin da muke so, saboda idan ta yi aure duk wanu zarge-zarge da ake yi mata na jinnu zai kau za mu biyar da ita yadda muke so." Hatsabibiya ta lalubo hannun Mijinta ta saƙale shi sai da suka je bakin wata baƙar rijiya sannan ta ce, "Tabbas abar bauta ke ya cancanci ki amsa sunan Hatsabibiya saboda kin wuce tunanin mai tunani. Wai Abar bauta Mugaza har yanzu babu amo baby labari ne?" Abar bauta ta wage ɗaya daga cikin bakunan jikinta ta hau ɓaɓɓaka dariya sannan ta ce, "Mugaza tana can tana jinyar Huzaifa saboda kaɗan ya rage bai mutu ba, kin ga ta yuwu lokaci da za mu mallaki gangar jiki da ruhin Raihan har lokacin Huzaifa bai maro daga jinyar da yake ciki ba." Hatsabibiya ta sake bushewa da dariya sannan ta suka faɗa cikin taohuwar rijayar nan take ta shafe daga kamar ba a taɓa ƙirƙirar rami a wurin ba.
Wata ƙawar Mommy Hajiya Safiya ita take zuwa har gida tana yi wa Raihan gyaran jiki, sana'arta ce har wasu garuruwan take zuwa gyaran amare. Hajiya Safiya gyara take yi wa Raihan ciki da waje don har magungunan gyaren jiki take haɗawa, Daddy ban da shige da ficen shirin biki babu abin da yake yi. Bikin Raihan saura sati guda tuni Daddy ya gama tanadar komai na hidimar biki, an sanarwa da ƴan uwa da abokan arziƙi tuni shirye-shirye ya yi nisa daga gidansu Raihan zuwa gidansu Salim lokacin biki kawai suk jira. Ƙawayen Raihan ba ƙaramin mamakin jin bikin Raihan suka yi ba, haka suka yi ta tsegungumi kowa yana son sanin waye mijin da ya yi shahada zai auri Raihan, saboda Daddy bai ɓoyewa Salim da iyayensa komai ba game da ciwon Raihan, duk da ƙawayenta sun san warkewarta amma mafi yawan ƙawayenta ba su yarda ba.
MUN KUSA SHAN AMARCI🤸🏻♀️ ALLAH YA SA DAI KAR SALIM YA HAƊU DA AMAYAR KAZA😂
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn ta wannan number 0706 206 2624
27
Raihan ba ƙaramin kyau ta yi ba fatar jikinta ban da sheƙi babu abin da take yi, ta yi wani irin fresh kallo ɗaya za ka yi mata ka ji kamar ka sace ta. Tun ranar Laraba aka fara bikin Raihan, a ranar ne ta yi bridal shower da ita da wasu tsirarin ƙawayenta. Doguwar riga baƙa ta saka mai ratsin fararen duwatsu, kasancewarta mai hasken fata ba ƙaramin kyau kayan suka yi mata ba. Ƙawayenta su Shida suka yi ankon Ash ɗin material, a cikin gidansu Raihan aka yi komai. Suka kira masu decorations suka tsara musu komai gwanin birgewa. Ranar alhamis aka yi kamun amarya da ango, a ranar Raihan ta saka blue ɗin atamfa shi kuma Salim ya saka blue ɗin shadda. Ba ƙaramin burge mutane suka yi ba, kasancewar Salim mai matuƙar barkwanci ya sa ban da fara'a babu abin da yake yi. Abokansa ba ƙaramin ƙoƙari suka yi ba don sun yi masa kara matuƙa, da su aka yi komai aka watse daga taro. Ranar juma'a aka ɗaura aure da kimanin ƙarfe biyu na rana lokacin an sauko daga sallar juma'a, an ɗaura auren Salim da Raihan a masallacin Marigayi Sheik Jafar da ke unguwar ɗorayi.
Ƙarfe goman dare aka fara dinner su Raihan a Lailan Event center, wani rantsattsen leshi Raihan ta saka wanda Daddy ya siyo mata daga Dubai. Su Inno an kame a kan kujeru sai kallon mutane suke ɗaiɗai bakin nan ya ƙi rufuwa. A yadda aka tsara Dinner babu mutane da yawa amma su Inno suka kafe kai da fata akan duk mutanen da suka zo daga Albasu da waɗanda suka zo daga Daura sai an shiga da su. Sai da Mommy ta yi musu dabara sannan ta samu suka bar maganar. Farar Shadda Salim ya sa daga shi har Raihan sai dai mutum ya ce sam barka, sai mai hassada shi zai kushe irin kwalliyar da suka yi. Anci an sha taro ba ƙaramin kyau ya yi ba mommy sai hada-hada take yi da mutane, ita kanta ba ƙaramin kyau ta yi ba. Kimanin ƙarfe sha biyun dare aka tashi daga dinner, Salim da Raihan a motar abokinsa Muhsin suka zo. Da za su koma gida ma motarsa suka shiga, Salim riƙo hannun Raihan ya yi lokaci ɗaya gabanta ya faɗi sakamakon haka bata taɓa kasancewa tsakaninta da shi ba. Ɗagowa ta yi suna haɗa ido ta sunkuyar da kai ƙasa saboda wata irin kunyarsa da ta ji. Janyota ya yi jikinsa a lokacin Muhsin ya buɗe ƙofar zai shiga, yana ganin haka ya koma da baya. Raihan ta zaro ido waje ta ce, "Habibi Muhsin fa ya ganmu." Salim ya sumbaci gefen wuyanta cikin kasalalliyar murya ya ce, "Shi ma yana komawa gida wurin matarsa za shi, laifi ne don na zo wurin tawa matar?" Kunya ta kama Raihan ta yi shiru tana murza ƴan yatsunta, Salim ya sake kwantar da murya ya ce, "Ni dai gaskiya ki cewa su Daddy a kai ki yau Allah gobe fa ta yi nisa." Raihan ta buɗe baki tana zaro ido ta ce, "A'a wallahi rufa min asiri inmutu maza su kaini." Muhsin ne ya kira shi a waya yana ɗauka Salim ya fita daga motar zai yi magana Muhsin ya ce, "Kai fa ɗan iska ne ai ka bari idan Allah ya kaimu gobe ka fara ɗana amarcin." Salim ya yi dariya ce, "Ɗan sa ido me ye naka a ciki." Dariya suka yi gabaɗaya sannan suka shiga motar suka wuce gida.
Washegari.
Bayan sallar Magriba aka shirya Raihan cikin wata tsadaddiyar alkyabba, ba ƙaramin kyau ta yi ba sai dai tun da gari ya waye ban da kuka babu abin da Rainan take yi. Lokacin da za a tafi kaita su Inno ne suka yi mata nasiha sosai da sauran tsofaffin da suke wurin, ana cewa Raihan ta fito ta rungume Mommy ta sa kuka. Ita kanta Mommy tun tana dakewa har ta gagara ta fashe da kuka, da ƙyar aka cireta daga jikin Mommy kai tsaye ta falon Daddy aka wuce da ita tana ganin Daddy ta rungume shi ta fashe da wani irin kuka. Murmushi Daddy ya yi don jin kukanta yake har cikin ransa. Nasiha ya yi mata mai ratsa jiki daga nan aka wuce da ita ɗaya daga cikin motar da Salim ya aiko don ɗaukan amarya.
Tsayawa tsara gidan Raihan ɓata lokaci ne saboda Daddy ba ƙaramin kuɗi ya kashe mata ba, kai tsaye gidansu Salim aka fara kai Raihan Mahaifiyarsa ta yi mata nasiha sannan ta ɗauko turarrika da kuɗi ta bawa Hafsa ƙanwar mommy da take riƙe da ita daga nan suka wuce da ita katafaran gidanta da ke Tudun yola.
Katafaran gida ne mai ɗauke da ɗakuna kala-kala an ƙayace shi da kayan alatu na more rayuwa, ƴan uwa da abokan arziki ban da santin gidan babu abin da suke yi, lokacin da su Inno suka shiga gidan sakin baki da hanci suka yi ban da kalle-kalle babu abin da suke yi. Suna shiga kitchen Goggo ta dubi Inno hannu riƙe a haɓa ta ce, "Ni kam Audullahi ya san zafin dukiya kuwa?" Inno ta wara hannuwa ta ce, "Taya ni duba wa Zinaru wai nan fa madafa ce. Ki duba ki ga yadda wasu gilasai suke sheƙi sai kace shagon ɗan kasuwa." Inno na ƙarasa maganar ta miƙa hannu kan wasu fulasai tana shafawa, gabaɗaya ɗakunan babu inda ba su shiga ba. Da sun keɓe za su fara mitar Daddy ya narkar da dukiya, don gidan Raihan sai mahassadi shi zai kushe shi. Kafin wani lokaci tuni kowa ya watse an bar Raihan daga ita sai su Safna ƴaƴan Mama Hafsa ƙanwar Mommy. Raihan na zaune Salim ya kirata a waya, a hankali ta zame mayafinta ta ɗauke muryarta har ta dashe saboda kuka. Haka kawai ta ji gabanta ya faɗi har sai da ta sauke ajiyar zuciya, tattaro jarumta ta yi a hankali ta furta, "Hello!" Daga can ɓangaren Salim ya amsa mata cikin fara'a tare da faɗin, "Habibity ina ta tunaninki." Murmushi Raihan ta yi ta ce, "Amma zan yi missing ɗin su mommy da rigimammun tsofaffin nan." Salim ya kwaikwayi muryarta yana faɗin, "Ni ma missing ɗin ki nake tun ɗazu da safe, kuma ni hanyar nisa take min na ƙagu na ƙaraso wurin Cutie." Kunya ce ta kama Raihan har sai da ta saci kallon su Safna ta ga suna ta danne-dannen waya ta bashi amsa, "I really miss you My Zauji." Dariya sosai Salim yake don shi mutum ne mai barkwanci da fara'a, Raihan ta yi murmushi tana shirin magana ya ce, "Kin san me nake tunani?" Raihan ta ce, "A'a sai ka faɗa." Salim ya yi jim sannan ya ce, "Gaskiya na musamman ne idan na ƙaraso sai na fi jin daɗin sanar miki." Raihan gabanta ya sake faɗuwa don haka kawai take jin faɗuwar gaba tun da aka taho da ita hanyar gidanta. Ta yi ƙarfin halin cewar, "Allah ya kawo min kai lafiya." Salim ya yi ƙasa da murya kamar mai raɗa sannan ya ce, "I so much love you Cutie." Raihan ta yi ƙasa da murya don kar su Safna su ji ta ce, "I Love you too Zauji." Daga haka suka yi sallama sannan suka ci gaba da hira.
Kimanin ƙarfe goma na dare Safna ta kalli Raihan ta ce, "Raihan ni fa na gaji wallahi bacci nake ji, ki kira mijinki su yi su ƙaraso don kar bacci ya ɗauke ni." Raihan ita kanta ta ji shirun ya yi yawa sai dai tana kunyar kar ta kira shi ta ce shiru bai ƙaraso ba, tana cikin nazari suka ji ƙarar tsayawar mota a ƙofar gidan. Tsayuwar motar ya yi daidai da faɗuwar gaban Raihan, ta dubi Safna ta ce: "To ga shi nan ma sun zo da har kina niyyar yi min tijara." Safna ta miƙe tsaye tana gyara ɗankwalinta ta ce, "Babu wata tijara wannan Angon ai ya fiye jinkiri har kusan goma bai ƙaraso ba." Tana rufe baki suka fara jin bugun gida, Safna ce ta fita ta buɗe ƙofar. Da mamaki take bin ta da kallo tare da faɗin, "Mami lafiya ke ce da daren nan?" Mama Hafsa bata kula Safna ba ta ƙarasa ɗakin wurin Raihan a daidai lokacin saƙo ya faɗo wayarta, da sauri ta duba don a tunaninta Salim ne sai dai baƙuwar lamba ta gani, tana shiga saƙon ta riske shi kamar haka:
" _Amarya! Amarya!! Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida, ina taya ki murnar amarcewa tare da yi miki jimamin babban rashin da kika yi. Daga mai ƙaunarki ba dare ba rana_." Tun bata ƙarasa karantawa ba jikinta ya fara rawa gabanta na ci gaba da tsananta faɗuwa, muryar Mama Hafsa ce ta risketa tana faɗin, "Raihan ta so mu wuce gida." Bugun zuciyarta ne ya tsananta ta riƙo hannun Mama Hafsat ta ce, "Mama Hafsa gida kuma? Me yake faruwa? Ina Salim yake?" Mama Hafsat ta fakaici idon Raihan ta ce, "Salim yana can gida wurin Daddy wani uzuri ya kawo shi ya sa Daddy zai haɗa ku ya yi muku magana." Raihan za ta yi magana ta ji wayarta ta fara ringing ganin wannan baƙuwar lambar ya sa ta saurin ɗauka jikinta na ci gaba da karkarwa. Murya na rawa ta furta, "Waye?"
Tun bata rufe bakinta ba ta ji an ce, "Mijinki ne, ku hanzarta ɗauke wancen mushen da ke cikin mota shi da abokansa kafin su ƙone su zama toka, na faɗa musu ni kaɗai ne mijinki ni kaɗai zan mallake ki har abada. Duk wanda ya sake yin gangancin aurenki sai na yi masa abin da ya fi wannan muni." A haukace Raihan ta furta, "Waye kai? Ina Salim yake?" Ƙit ta ji an kashe wayar. A furgice ta dubi Mama Hafsa ta ce, "Wani abu ya faru da Salim wallahi ni na sani, tun ɗazu Salim ya ce min ya kusa ƙarasowa amma har yanzu shiru don Allah karki ɓoye min Mami me ya faru da Salim." Raihan ta ƙarasa maganar kuka na cin ƙarfinta. Mama Hafsa hawaye ne ya fara zuba a fuskarta ta dafa kafaɗar Raihan ta ce, "Mu je gida Raihan." Mama Hafsa na rufe baki Wani kiran ya sake shigowa wayar Raihan, number Farida ta gani. Jikinta har rawa yake ta ɗauka sai dai kukan da ta ji Farida na yi ne ya sake karya mata zuciya, tana shirin yin magana Farida ta ce.
"Matar.Yaya yanzu shi kenan Yaya Salim ya rasu ɗazun nan fa muka rabu ina tsokarta wai shi ne ya..." Raihan bata ƙarasa jin abin da Farida take faɗa ba wayar ta zame daga hannunta luuuu ta faɗi sumammiya.
Hankali a tashe Mama Hafsa ta kama Raihan, Safna na ganin haka ta ɗauko ruwa aka fara yayyafawa Raihan amma ko motsi bata yi ba. Hankali a tashe Mama Hafsa da yaranta suka kama Raihan suka fitar da ita kai tsaye suka saka ta a mota, ban da ruwan hawaye babu abin da Mama Hafsa take yi. Kulle gidan suka sannan suka wuce gidan su Mommy hankali a tashe, saboda irin gudun da take sharawa ya sa ba su jima ba suka ƙarasa gidan. Tun kafin su ƙarasa hankalin Mommy a tashe yake don babban tashin hankalinta bata san halin da Raihan za ta shiga ba matuƙar ta ji rasuwar Salim, Daddy ban da zarya a falo babu abin da yake yi gabaɗaya mutane kowa ya yi carko-carko. Inno na daga kan kujera ban da sharɓar hawaye babu abin da take yi, Goggo ta dubi Inno ta ce, "Kaico mutuwa duniya zancen banza.Ɗazu yaron nan ya gama zolayata wai yanzu shi ne ya yi hatsari motarsu ta ƙone ƙurmus, Allah ka jiƙan Salmanu ka gafarta masa." Inno ta sharce hawaye da gefen zaninta ita ma ta ce, "Ki duba irin budurin da aka yi ni babban tunanina halin da Raihanu za ta shiga, Allah ya sani Salmanu yaron arziƙi ne halinsa na gari ya bishi." Suna cikin wannan halin Mama Hafsa ta shiga ta sanar musu halin da Raihan take ciki, da sauri Daddy ya fita hankali a matuƙar tashe. Ganin halin da Raihan take ciki ya sa Daddy bai yi wata-wata ba ya wuce da Raihan asibiti, da matsanancin gudu ya bar cikin unguwar wanda ya yi daidai da fitowar Mommy cikin kiɗima don ganin halin da Raihan take ciki. Zuciyarta ba ƙaramin karyewa ta yi ba nan take da fara hawaye sai ƙanwarta Hafsat ce ta kama ta suka wuce gida.
Daddy na zuwa asibiti da sauri likitoci suka shiga bawa Raihan taimakon gaggawa, sun jima a kanta sannan suka samu numfashinta ya daidaita, suka yi mata allurar bacci don ta samu hutu. Daddy ban da zarya babu abin da yake yi hankalinsa gabaɗaya baya jikinsa, wayarsa ce ta fara ƙara don tun yana tuƙi wayar tashi take ringing bai samu sukunin ɗauka ba. Jiki a matuƙar sanyaye ya ɗauki wayar ya kara a kunne ba tare da ya furta komai ba,