Showing 117001 words to 120000 words out of 157890 words
miƙa masa ya ce, "Yanzu miƙewar da ka ga na yi shi zan siyo ina son na yi wa Raihan tofi, riƙe kuɗinka Malam zan taho maka da shi." Malam ya ce, "Ah haba ina ba za a yi haka ba ni ma tofin nake son yi mata saboda wannan yanayin nata ya ba ni tsoro." Kabiru ya ɗora masa kuɗin akan cinyarsa ya fice, bai jima da fita ba ya dawo da ruwan gora guda huɗu tare da man zaitun ya ɗauki biyu ya miƙa wa Malam biyu. Bakinta ya buɗe ya ɗan kurɓi kaɗan sannan ya fara karanto ayoyon alƙur'ani yana tofawa. Daga ɓangaren Malam ma tofin ya fara yi mata don tun da ya ji an ce jini har ta gabanta yake zuba daga jikinta, Huzaifa ya faɗo masa duk da ya san ciwon zuciya babu abin da baya saka wa amma zuciyarsa ta ƙi aminta da ciwon zuciya ne ya haifarta mata zubar jini ta gabanta. Saboda ya san sheɗanu na iya shiga jikin mara lafiya musamman idan sun shafe shi su ƙara tunzura ciwonsa, idan har abin yanzo da ƙarar kwana sai a rasa. Idan kuma da yuwuwar a tashi sai a sha matuƙar wahala.
Duk yadda Likitoci suka kai ga ƙoƙarinsu abin ya ci tura, suna nan kan Raihan Mommy da Daddy na daga gefe suna yi mata tofi cikin ikon Allah aka samu jijiya aka saka mata jini, haka aman da yake fita ta hancinta shi ma ya tsagaita. Malam da kansa ya ƙarasa bakin gadon ya yi bismillah ya fara karanta addu'o'i yana tofa mata, sai da ya jima akanta sannan ya miƙa wa Mommy jarkar hannunsa ya ce ta yi bismillah ta shafa mata a jiki kuma ta samu ko yaya ne ta ɗiga mata a bakinta. Kabiru yana daga gefe bayan ya kammala tofin ya ciro wata ƙaramar kwalbar man zaitun da habbatussauda ya tsiyaya a ciki sannan ya ƙarasa bakin gadon Raihan, ganin haka ya sa likitocin suka fara faɗa don a cewarsu ana ɓata musu aiki tun da sun fara kamo bakin zaren. Kabiru bai bi ta kansu ba sai da ya gama yi mata addu'a sannan shi ma ya miƙa wa Mommy ya ce ta shafa mata a hafin ƙafarta da tafin hannunta sai fuskarta, a zuba ɗan kaɗan a tsiyaya a kunnenta da tsakiyar kanta. Da ƙyar likitoci suka bari Mommy ta shafawa Raihan waɗannan tofin, tana gama shafa mata jikinta ya fara fitar da gumi sai kuma ta fara rawar ɗari kamar mai jin sanyi. A hankali ta buɗe idanunta da suka shanye tana bin mutanen wurin da kallon, A fili su Mommy suka furta Alhamdulillah Kabiru ya ɗaga hannu sama yana gode wa Allah. Da taimakon Allah da taimakon litocin suka samu Raihan ta dawo hayyacinta, nan take suka yi mata allurar bacci Nurses ɗin da suke da duty a lokacin suka zo suka fara gyara wurin. Tun daga ranar wani abu bai sake faruwa da Raihan ba saboda kullin akwai tofin da Malam yake yi mata ana bata, haka shi ma Kabiru duk dare sai ya biyo daga Kamfani ya yi mata tofi da addu'o'i sannan ya wuce gida. Malam da Al'amin kusan kullin sai sun je asibiti duba Raihan saboda har lokacin Malam bai sanar masa da komai ba, haka Mai ɗakin Malam ita ma zuwanta uku daga haka suka yi sabo da Mommy sosai saboda Mahaifiyar Al'amin macece mai kirkin gaske, idan za ta zo har girki take yi wa su Mommy wannan karamcin ya ƙara wa Malam da iyalansa matsayi a wurin su Mommy. Raihan ta warke sosai tana cin abincinta kuma duk wani abu da yake damunta ya yi sauƙi, don haka likitoci suka sallame su. A ranar da aka sallami su Raihan da dare Kabiru bayan ya gabatar da sallar Isha'i yana shirin kwanciya ya ji kamar ana bubbuga ƙofar ɗakinsa, mamaki ne ya kama shi don bai taɓa samun haka daga masu gidan ba saboda ko abu Daddy zai saka shi sai asuba yake yi masa maganar idan ya fito sallar asuba. A hankali ya ƙarasa ya buɗe ƙofar amma babu kowa a wurin, komawa ya yi ya kwanta har bacci ya fara ɗaukansa. Ta jikin windonsa ya ji haushin kare ya ƙi ci ya ƙi cinye wa. Haska fitila ya yi a hankali yana kallon windon daga kwance, guntun tsaki ya yi ya koma ya kwanta yana nan kwance yana saƙa da warwara bacci ya yi awon gaba da shi. Cikin baccinsa yake jiyo kukan mage kamar a saitin kansa, firgigit ya motsa saboda ko kaɗan baya ƙaunar mage. A guje ya ga ta ɗare kan windon ɗakinsa tana zaro masa idanu, baƙa ce wuluk sai hasken idanunta da yake gani. Rigarsa da ya cire ya ɗauka yana korarsa don ya lura Muzuru ne amma ko gezau, kamar almara ya ji ya furta: "Saƙo na kawo maka kafin na cika aiki." Wata farar takarda ce ta faɗo, sai kuma ya nemi magen ya rasa. Wata zuciyar har ta hana shi ɗauka sai kuma ya yi bismillah ya ɗauka ya fara karanta rubutun da aka yi da ajami kamar haka: "Ina ƙara jan kunnenka akan ka fita hanyar Raihan ka ƙi, ka tsaya matsayinka amma sai cusa kanka kake wallahi sai na nuna maka iyakarka, idan har Raihan kake so sai na damalmala rayuwarka ta yadda ko wata macen ka gani ba za ka yi sha'awar kallonta ba balle ka ji ɗigon santa a zuciyarka. Ba dai matarka ciki gare ta ba, wallahi ka saurari saƙona yana tafe nan ba da jimawa ba. Mai HUZAIFA mijin Raihan har abada." Kabiru na gama karanta wa ya fahimci wanda ya aiko da saƙon, ƙirjinsa ne ya buga musamman da ya ji ya ambato Maryama da ke ɗauke da tsohon ciki don yana tsoron kar ya cutar masa da ita, hannunsa har rawa yake ya lalubo wayarsa ya kira lambarta amma yana kira ya ji a kashe take. A hankali ya miƙe ya faɗa banɗaki ya ɗauro alwala ya shiga gabatar da sallah yana kai wa Allah kukansa akan ya shiga tsakaninsu da sharrin Huzaifa da dukkan wani abin ƙi, baccin da bai koma kenan ba a ɓangare ɗaya kuma ya shiga tunanin wanda Raihan take yi wa tsananin soyayyar da har ciwon zuciya yake barzanar kamata. Tausayin kansa ne ya kama shi don ya san zuciyarsa bata yi masa hallaci ba da ta faɗa ƙaunar Raihan, don ya san dama ba tsararsa ba ce domin ya kwana da sanin hanyar jirgi daban da ta mota. Ba shi ya koma bacci ba sai gabanin asuba har so ya yi ya makara, don ma ranar babu aiki kasancewar juma'a ce. Kuma tun daga juma'a Daddy yake bada hutun ƙarshen mako har zuwa ranar Lahadi.
A razane Al'amin ya ɗago ya dubi Mahaifinsa baki na rawa ya ce, "Daddy ban fahimci abin da kake nufi ba fa." Malam ya sake ɗaure fuska ya ce, "Abin da ka ji na faɗa da farko shi za ka sake tarayo wa ka saurara, yarinyar nan saboda kai har tana neman salwantar da rayuwarta. Yanzu Aminu aibu ne don an ɗaura maka aure da mata biyu a rana ɗaya, na ga kowacce da halinta za ta zauna kuma kowaccensu tana ƙaunarka. A da na ce sai bayan aurenka da sati guda amma ina ganin babu fa'idar ɗagawa gara a ɗaura rana ɗaya, idan ya so ko bayan sati ɗaya da bikin ne sai ita Raihan ta tare tun nasan ba lalle sun gama shiri ba." Al'amin ya ɓata fuska kamar zai yi kuka murya na rawa ya ce, "Kuma yanzu yaro da ji a riƙa cewa matana biyu, wannan wanne irin abu ne Daddy." Mama na daga gefe ta karɓe zancen da cewar, "Al'amin wanda ya ce ya sonka ya fi wanda baya sonka, menene aibun yarinyar nan ba sai ka gaya wa Sumayya halin da ake ciki ba ka yi mata bayani." Al'amin ya miƙe murya a ciki ya ce, "Shi kenan ba komai." Daɗi ne ya kama su Malam suka shiga saka masa albarka, saboda dama sun san Al'amin ba zai ƙi Aurenta ya bujire musu ba. Yana shiga ɗaki ya fara zarya don bai san ta inda zai fara gaya wa Sumayya ba saboda ya san kishinta, yana cikin wannan tunanin ya ji muryar Daddy yana waya da Mahaifinta. Kamar wanda ruwa ya cinye haka Al'amin ya yi sak jikinsa tamkar an zare masa lasa, kasa motsa wa ya yi yana jin abin kamar a mafarki, a hankali ya ja ƙafarsa ya hau kan katifarsa daga haka bai sake fahimtar abin da Daddy yake faɗa ba ya zurfafa cikin tunani. Mahaifin Sumayya bai ji komai ba hasalima shi da kansa ya ce zai sanar wa da Summaya halin da ake ciki don ta yi wa Al'amin kyakkyawar fahimta. Malam ya ji daɗi ƙwarai da fahimtarsa da Mahaifin Sumayya ya yi, hira suka taɓa dangane da harkar bikin sannan suka yi sallama.
Lokacin da Mahaifiyar Sumayya ta samu labarin tsalle ta yi ta dire ta ce sam bata lamun ce ba, sai da Mahaifin Sumayya ya yi mata ba daɗi sannan ta sauko. Ita kuwa Sumayya yana gaya mata ta fashe da kuka haɗe da shiga ɗaki da gudu, tana zuwa wayarta ta ɗauka ta kira lambar Al'amin sai da ta katse tana shirin kira ta ga ya kirata. Cikin kuka ta furta, "Hubby da gaske ne abin da Daddy ya gaya min wai mu biyu za ka aura? Shi kenan ka daina sona ko?" Al'amin shuru ya yi yana jin kukanta har cikin zuciyarsa, tattaro jarumta ya yi ya ce, "Don Allah ki fahimce ni Dear kin san ina ƙaunarki kuma na tabbata za ki yi min adalci, idan kika ce na daina son ki kamar ba ki yi min adalci ba. Ina son ki ina ƙaunar ki kuma ba zan taɓa haɗa ƙaunarki da kowa ba, don Allah ki kwantar da hankalinki kin san komai muƙƙaddari ne daga Ubangiji." Hawaye ta goge sannan ta furta, "Amma me ya sa ba za ta nemi mijinta ba sai mijina, Hubby har yanzu zuciyata rawa take yi akan yarinyar nan gani nake kamar kana ƙaunarta, idan ba haka ba ya za a yi maganar aure lokaci ɗaya ta kankama kai da ita." Al'amin dafe kansa ya yi don duk yadda ya so nusar da Sumayya sam taƙi fahimtarsa idonta ya riga ya rufe, daga ƙarshe ma katse wayar ta yi tana kuka ya yi kiran duniya ta ƙi ɗauka. Sai dai ko kaɗan bai ji haushinta ba saboda ya san zafin kishi irin na Sumayya kuma kowacce macce aka yi wa haka abin da za ta yi kenan, lokaci ɗaya ya ji haushin Raihan ya kama shi don ita yake ganin ta zame masa linzamin da ta ja dokin rayuwarsu faɗa wa cikin matsala tsamo-tsamo.
Tarihinsu Al'amin.
Usman Ahmad Kafin Hausa shi ne aihinin cikakkan sunan Malam, asalinsa ɗan garin Jigawa ne a wani gari Kafin Hausa. Su biyu ne a wurin iyayensu daga shi sai Yayansa Alhaji Mu'azzam amma akwai tazara mai yawa tsakaninsu ta kusan shekara goma, Mahaifinsa manomi ne don kafin rasuwarsa har sai da aka bashi sarautar sarkin noman yankinsu. Mahaifiyarsu ta rasu tun suna ƙanana daga nan Mahaifinsu ya auri wata mata mai suna Hajjo amma ba yarinya bace, don ko da ya aureta bata haihu da shi ba. Lokacin da Malam ya fara tasowa yaro ne mai ƙwazo da son ilimi ganin haka ya sa Mahifinsu ya yanke shawarar kai shi almajiranci, da yake yayan matarsa a garin Maiduguri yake yana da tsangaya sai Mahaifinsu Malam ya ɗauke shi tare da ɗan'uwansa ya kai su can neman ilimin Muhammadiyya. Yayansa ba a son ransa ya je ba sai don babu yadda zai yi, saɓanin Malam da yake farinciki don kullin burinsa bai wuce ya zama malami kamar limamin garinsu ba. Shi kuma yayansa burinsa ya gaji mahaifinsa ya zama babban manomi, don haka koda aka kaisu Malma ya fi mayar da hankali wurin karatu fiye da ɗan'uwansa. Daga ƙarshe ma sai Yayansa ya riƙa bin kasuwanni yana ƴar buga-bugarsa da haka ya samu ya tsinci abin da ya tsinta saɓanin Malam da ya mayar da hankalinsa kacokan kan harkar neman ilimi. Ba ƙaramar kulawa suke samu ba kasancewar Mahaifinsu na yawan kai musu ziyara akai-akai, kuma duk lokacin da za shi sai ya tafi musu da kayan abinci niƙi-niƙi. A haka suka yi saukar Alƙur'ani suka dawo gida, suna dawo wa yayansa ya faɗa harkar kasuwanci da Noma kamar yadda yake buri. Shi kuma Malam ya sake komawa garin Maiduguri a nan Malaminsu ya saka shi makarantar boko tare da ƴaƴansa sannan ya fara ɗora su akan harkar kasuwancinsa saboda ya fahimci Malam mutum ne Mai amana. Ana cikin haka Malam suka daidaita da Amina Mahaifiyar Al'amin wacce ta kasance cikakkiyar babarbariya. Amina Umar Babagana shi ne ainihin cikakken sunan Mahaifiyar Al'amin, asalinta babarbariya ce ɓangaren uwa da uba duk haifaffin ƴan Maiduguri ne. Ƴar aminin Malamin su Malam ce kusan komai a gidan su Malam take yi, tun suna soyayayarsu a ɓoye har aka fara fahimtarsu. Alokacin da ta kammala firamare (Primary) Malamin Malam ya yi wa iyayensa maganar halin da ake ciki, ba a ɗauki lokaci ba aka saka musu rana lokaci na yi aka ɗaura aure a lokacin tuni Malam ya gama sakandire. Kasuwancin da suke yi Allah ya saka masa albarka don har garuruwa sun fara zuwa suna sarin kaya suna kawo wa Maiduri, kwatsam aka wayi gari da mummunan labarin hatsarin da ya ritsa da Malaminsu. Wannan mutuwa ta ratsa shi bayan kwana arba'in aka yi wa iyalansa rabon gado, akan dole Malam ya koma Kafin hausa tare da iyalinsa da zama. Daga haka ya fara buga-buga yana haɗa wa da aikin noma har ya fara tunanin buɗe ƙaramar tiredar sayar da mayukan habbatussauda da sauran magungunan musulunci, kasancewar yana da ilimi a wannan fannin domin Malaminsa ya koya masa iliminsu tun zamansa a Maiduguri da yake yana da babban shagonsa da yake taimakawa marasa lafiya da masu matsalar aljanu. Da wannan shawarar ya amicewa zuciyarsa har ya yi tunanin buɗe tiredar a jikin shagon Yayansa da ke cikin garin kano, da ƙaramar tireda ya fara sannu a hankali har Allah ya sa masa albarka ya dawo da iyalinsa sakamakon yana zaune a gidan Yayansa. Dawowarsa keda wuya Mahaifinsa Allah ya yi masa rasuwa, wannan rashi ya taɓa su sosai bayan wani lokaci kowanensu ci gaba da neman kuɗinsa, sai dai Malam ya ci gaba da neman kuɗinsa haɗe da neman ilimi sannu a hankali Allah ya riƙa buɗa musu.
Al'amin su biyar ne a wurin iyayensu shi ne ɗan su na uku domin sun haifi yara biyu mace da namiji duk sun rasu, daga Al'amin sai ƙannensa mata huɗu, Aisha, Shamsiyya, Hauwa sai Zarah. An yi wa mata aure Aisha da Hauwa aure ya yin da Zarah da Shamsiyya suke karatunsu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Al'amin ya yi karatunsa tun daga na boko har na islama a cikin garin kamo, ya karanci ɓanagaren Islamic a jami'ar Bayero yana da matuƙar ƙoƙari da hazaƙa don haka wasu suke kiransa da Babban ƙwaro. Bayan ya kammala Degree ɗin sa Malam ya tura shi jami'ar Madina ƙaro karatu, bayan ya kammala karatunsa suka riƙe shi saboda yaba wa da ƙwazonsa da ƙoƙarinsa da suka yi. Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yi wa Malam ba amma sam Al'amin bai so haka ba saboda ya fi son zama kusa da iyayensa, sai da ya shafe sama da shekara biyu sannan ya zo ya ga iyayensa Amma kafin zuwansa lokaci-lokaci suna kai masa ziyara. Ya shafe kusan shekara biyar yana koyarwa sannan ya nemi dawowa ƙasarsa don ya ci gaba da tallafawa ƙasarsa, yana dawo wa Jami'ar Bayero suka bashi gurbin zama domin dama ba baƙo ba ne a wurinsu, a lokacin da Raihan ta haɗu da shi bai dawo ƙasa Najeriya da zama ba ya dawo ganin gida ne ya shiga saboda akwai wata takarda za a yi masa signing a jiki.
Mu dawo Labari.
Shirye-shirye ya kankama daga gidaje uku na ƙaratowar bikin, daga ɓangaren Amarya Sumayya babu wani shiri da take yi hasalima bikin duk ya fice mata daga rai. Fushi ta ɗauka sosai da Al'amin sai da kyar ya lallasheta ta sauko, sanann suka shiga tsara yadda bikin zai kasance. Duk wata lalura ta Raihan sai da Malam ya sanar wa Al'amin don gudun samun matsala, kuma ya tilasta masa zuwa wurin Raihan don ya tambayeta abin da take buƙata game da biki kuma su fahimci juna kafin auren. Wannan karon ta gan shi ba yabo babu fallasa sai dai babu wata doguwar hira da suka yi, bai jima ba ya yi mata sallama ya tafi saboda ya tambayeta abin da take buƙata na biki ta ce masa bata buƙatar komai don babu wani abu da za ta yi. Idanun Kabiri akan Al'amin har ya zo ya tafi, haka kawai ya ji baya ƙaunar Raihan da Al'amin don ya lura babu soyayyarta a tare shi. Haka ya ci gaba da lallashin zuciyarsa amma kullin ji yake kamar sake rura watar ƙaunarta ake a ransa. Ana saura kwana biyar biki Malam ya kammala haɗa lefen Raihan a daren Ranar shi da wasu abokansa da Yayansa suka kai gidansu Raihan. Ranar juma'ar da ta zagayo cikin satin aka ɗaura auren Raihan, Sumayya da Al'amin. Babu wani shiri da Raihan ta yi don ko event ɗaya babu wanda aka kama aka yi biki a ciki, ƴan uwa ne kawai suka taru aka yi yinin biki. Su Inno sai murna suke don har cewa suka yi irin wannan auren zazzafan rabo ne yake sa a yi shi cikin gaggawa, Kabiru yana ji yana gani aka sake ɗaura wa Raihan aure babu yadda ya iya. Da daddare bayan an yi wa Raihan Nasiha Malam da kansa ya zo ya ɗauki Raihan ya wuce ya ɗauki Summaya dama