Showing 114001 words to 117000 words out of 157890 words

Chapter 39 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

145

zai yi miki zaɓin alkairi. " Kuka ne ya ci ƙarfin Raihan ta gyaɗa masa kai ba tare da ta iya furta masa komai ba, da ido ya raka ta yana jin zuciyarsa babu daɗi. Kamar kazar da aka tsamo daga ruwa haka Kabiru ya wuce ɗakinsa ya zaune haɗe da faɗawa duniyar tunani.

Daddy yana tafiya hanyar office wayar Malam ta shigo masa, sai da suka gaisa sannan Malam ya ce idan ya samu lokaci yana son ganinsa. Jin haka ya sa Daddy ya fasa zuwa office ɗin ya wuce wurin Malam don jin maganar da yake son yi masa, bayan ya ƙarasa cikin girmama juna suka gaisa sannan Malam ya ce, "Alhaji dama na kira ka ne game da maganar hatsabibin Aljanin nan." Daddy ya tattara hankalinsa wurin Malam yana jinjina kai. Malam ya ci gaba da cewa, "Wannan Aljanin na jima ban haɗu da hatsabibin junnu kamar shi ba, ka san ya ci alwashin gujewa kusanci da mu don buƙatar kansa. To na tura wasu aljanu su kawo min shi amma ya yi musu ƙafar rago ya rufta su ciki, intaƙaice maka dai waɗannan aljanun ya yi garkuwa da su. Domin sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, saboda Huzaifa ya samu ɗaurin matsayi a wurin Kakansa Jabbul-ƙasi don haka sai na tashi sosai na yi shiri kafin na sake tunkararsu. Na san waye Jabbul-ƙasi ina da tarihinsa sama da shekara talatin baya." Zaro ido Daddy ya yi ya ce, "Dama suna garkuwa da junansu?" Malam ya yi murmushi sannan ya ce, "Ai Alhaji duk yadda kasan muna mu'amala suma haka suke gudanar da mu'amala a tsakaninsu, na kira ka ne don na sanar da kai ba don ka tada hankalinka ba sai don a ƙara tsayawa tsayin daka dangane da yarinyar nan Raihan. Saboda suna da matuƙar wayo fiye da tunanin mai tunani, sun san hanyar da za su bi su yaudari mutum." Daddy ya jinjina kai cike da gamsuwa sannan ya ce, "Allah ya ƙara tsare mu bakiɗaya." Magunguna kala-kala Malam ya sake haɗa wa Raihan don wannan karon ya ci alwashin sai ya ga bayan Huzaifa ta kowanne hali. Bayaninsu ya yi wa Daddy da yadda za ta yi amfani da shi, godiya Daddy ya yi wa Malam sannan ya tura masa kuɗi masu yawa suka yi sallama ya koma gida. Yana zuwa gida ya yi wa Mommy bayanin abin da yake faruwa tare da yi mata bayanin yadda Raihan za ta gudanar da magungunan. Cikin damuwa Mommy ta sake yi masa zancen halin da Raihan take ciki, shi kansa yana lura da yanayin yarinya, ji ya yi babu daɗi amma babu wani abu da yake ganin zai iya yi saboda da kunya ya tunkari Malam da wannan maganar. Ɗakin Raihan ya shiga a lokacin tana zaune ta tasa laptop a gabanta tana hawaye, sakamakon kallon hoton Al'amin da ta yi a shafinsa na fuskar littafi, (Facebook). Tana ganin shigowar Daddy da sauri ta rufe laptop ɗin tana goge hawaye. Daddy zama ya yi akan kujera ya kalle ta duk sai ya ji ba daɗi saboda lokaci ɗaya ta rame ta lalace, da wata irin murya ya kira sunanta jiki a sanyaye ta amsa sannan Daddy ya ce, "Raihan yanzu wannan rayuwar kika ɗaukarwa kanki, dubi yadda kika rame kika lalace. Raihan me ya sa kike son saka rayuwarki a cikin wani hali, me ya sa ba za ki miƙa wa Allah lamuranki ba ki cire yaron nan daga zuciyarki? Ki yi addu'a Allah ya kawo miki mafi alheri ina ganin haka ya fi da ki saka wa ranki damuwa har wani ciwo ya kama ki." Raihan ta faɗa jikin Daddy tana fashe wa da kuka, sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta ɗago ta ce, "Daddy wallahi na kasa cire shi a rana amma kullin ƙaunarsa nake ji a zuciyata, don Allah ka yi wani abu Daddy." Raihan ta ƙarasa magana tana haɗe hannuwanta wuri ɗaya alamun roƙo, hawaye bibbiyu yana zuba. Jikinta ya ji zafi zaau da zazzafi tausayinta ba ƙaramin kama shi ya yi ba, hannuwanta biyu ya kama ya ce, "Ki yi Addu'a Raihan domin babu abin da ya fi ƙarfin addu'a, kuma insha Allah zan san yadda za a yi Allah ya shiga lamuranmu." Cikin kuka Raihan ta amsa da Amin. Sai da Daddy ya jima a wurin yana lallashinta sannan ya fice daga ɗakin, yana fita ya sa Mommy ya haɗa mata ruwan tea ta shiga ɗakin da ƙyar ta matsa mata ta iya sha sannan ta sha maganin ta kwanta. Wannan ciwo na Raihan ba ƙaramin damun su Mommy ya yi ba, ba su kaɗai ba hatta su Inno lamarin Raihan damunsu yake don mommy bata sanar da su takamaimai abin da yake damunta ba, don tana gudun mitar su Inno kuma duk wanda suka haɗu da shi ta san sarai sai sun sanar masa da abin da ake ciki ita kuma tana gudun surutun mutane.

"Na tara ku ne domin na sanar da ku game da hukuncin da na yanke, sanin kanku ne mun ɗauki dogon hutu mai tsayi saboda halin da ƙungiya take ciki. A bisa shawarar da aka ba mu wancen karon za mu kai wa Jabbul-ƙasi ziyara akan buƙatarmu domin matuƙar mu ka ce za mu ɗore a haka tabbas kwaɓarmu za ta yi ruwa kuma ba za mu kai labari ba. Ni da Hatsabibiya da mijinta, sai zaratan Aljanu goma daga jinsin Bil'adam goma za mu shirya mu tafi, dole mu shirya da shirinmu domin tafiya wurin Jabbul-ƙasi ba wasan yara ba ne. Za mu haɗu da ƙalubale a hanyar tafiya domin duk wannan tsawon lokacin na yi bincike negame da yanayin hanyar tsibirin Jabbul-ƙasi. Kuma na tura Aljani Ɓurƙum domin ya karɓo mana izinin zuwa wurinsa, saboda idan ka cire zuri'arsa wato waɗanda suka fito daga tsatsonsa haramun ne ka kai ziyara wurinsa ba tare da ka nemi izini ba. Wannan magana da nake yi muku ba za mu kai labari duka ba, domin ya faɗa wa Aljani Ɓarƙum cewa gabaɗayanmu mu rai goma ne zai tsira domin sauran duka za su halaka. Abin da bai sanar da mu ba su waye za su mutu su waye za su rayu, amma ni na yanke wani hukunci duk wanda aka kashe za mu ɗora zuri'arsa a gurbinsa." Abar bauta ta ƙarasa maganar cike da ƙarfafa musu ƙwarin gwiwa. Da farko jikkunansu ya yi sanyi da jin bayanin Abar bauta amma da suka ji yadda ta ƙarfafa gwiwarsu sai suka saki jikinsu, amsa mata suka yi cike da ladabi sannan ta ɗora da cewa, "Za mu zaɓi waɗanda za mu yi tafiyar da su sannan za mu bar waɗanda za su yi gadin ƙungiya saboda ba zai yuwu mu bar wurin haka sasakai babu kowa ba, sannan abin da zan ja hankulanku da shi wannan sunan na Abar bauta da kuke kirana da shi dole ku daina daga yanzu domin ya bi bakinku, kuma ya zama wajibi ku daina bauta min domin babban zunubin da zai iya kaimu ga hallaka shi ne a yi min bauta a hanyar mu ta zuwa tsibirin Jabbul-ƙasi. Ba wai sai kaɗai hanya ba Jabbul-ƙasi bai amince da wata bautar ba don haka ko da kuskure kar ku sake ku bauta min idan ba haka ba gabaɗaya mun zama halakakku." Cike da gamsuwa suka amsa sannnan Abar bauta ta ci gaba da yi musu bayanin yadda tafiyar su za ta kasance, ta tabbatar musu da cewar za su yi tafiyar cikin kwana Talatin masu zuwa.

Lokacin da Mommy ta ji bayanin Daddy game da Kabiru da ƴan uwansa ta yi farinciki sosai, saboda ita kanta Kabiru na matuƙar birge ta saboda kyawawan ɗabi'unsa. Bayan kwana biyu da faruwar haka Kabiru ya samu Daddy da magana akan yana son sai mai ɗakinsa ta sauka idan ya so sai su dawo gabaɗaya, Daddy ya ji daɗin haka domin shi yake nuna ya san mutumcin mace kuma yana tausayawa matarsa tun da ya yi tunanin haka. Amma sai ya nunawa Daddy ƙaninsa zai zo a cikin satin domin ya kama na shi aikin idan ya so shi kuma ya fara aiki a kamfanin da Daddy ya ce, Daddy da kansa ya bawa Kabiru kuɗi don ya turawa ɗan'uwansa na mota ya taho, cikin jindaɗi Kabiru ya karɓa yana yi wa Daddy godiya. Wata ranar laraba da dare Daddy ya samu Kabiru ya yi masa magana akan ya shirya saboda a washegari zai fara aiki kamar yadda ya gaya masa, ranar Kabiru kusan kwana ya yi bai yi baccin kirki ba saboda murna, gari na waye wa ya shirya yana jiran Daddy bayan wani lokaci ya fito suka tafi. Duk wainar da ake toyawa Raihan bata sani ba sai lokacin da Kabiru ya kusa sati biyu da fara aiki a kamfanin Daddy tukunna, tana daga ɗaki ta ji Daddy na yabon ƙwazo da aikin Kabiru. Raihan ba ƙaramin haushi ta ji ba don gani take a yadda ta ɗauki Kabiru bai kamata ya ɓoye mata wannan ci gaban da ya samu ba, da ta so zuwa ta same shi a ta yi masa tas amma sai wata zuciyar ta hana ta ita ma ta ce ba za ta kula shi da maganar ba. Sannu-sannu ciwo ya fara saka Raihan a gaba tun tana jinyar kanta ita kaɗai har Mommy ta fara fuskantar ciwon Raihan ya fara tsanani. A ranar wata Litinin ne suka wayi gari da tashin hankali sakamakon tashi da suka yi Raihan na wani irin amai mai haɗe da sirkin jini a jiki, kafin suyi wani yunƙuri tuni numfashinta ya ɗauke ta suma a wurin. Hankali a tashe Mommy ta kira Daddy take sanar da shi, da ƙyar ta iya kama Raihan ta saka ta a mota ta wuce da ita asibiti. Tana zuwa asibiti likitoci suka rufu a kanta sai dai har lokacin da Daddy ya ƙarasa ba su shawo kan matsalar ba, sai da suka shafe kusan awa guda da mintuna sannan suka samu damar daidaita numfashinta. Amma lokaci-lokaci wani irin jini na fita daga bakinta, wannan lamarin ba ƙaramin ɗaga hankulansu ya yi ba. Mommy ban da kuka babu abin da take yi, Kaburi yana harabar Asibitin ya haɗa kai da gwiwa ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Bayan Likitoci sun samu komai ya lafa suka samu Daddy Dr Muhammad ya fara yi masa bayani, "Alhaji gaskiya yarinyar nan tana cikin matsananciyar damuwa, wanann damuwar ita ce take barazanar tarwatsa rayuwarta. Kuna ina haka ya faru why? Yarinya ƙarama ta samu irin wannan condition ɗin? Yanzu haka zuciyarta na barazanar fashe wa sai dai wani ikon Allah amma gaskiya akwai gaggarumar matsala." Jiki a sanyaye Daddy ya ce, "Wallahi likita babu abin da yarinyar nan ta nema ta rasa, jarabar soyayyar wani yaro ta ƙwallafawa ranta alhalin shi yaronma bai san tana yi ba." Dr Muhammad ya mayar da glass ɗin idonsa sannan ya ce, "To gaskiya ku tsaya ku duba lamarin nan domin komai zai iya faruwa Allah ya kiyaye." Damuwa goma da ashirin ce ta yi wa su Daddy yawa. Don sai da Raihan ta kwana uku a asibiti ba tare da ta san wanda yake kanta ba, a rana ta huɗu ta fara gane mommy amma bayan ita babu wanda take gane wa kowa sai dai ta bi shi da ido. Ranar da su Inno suka zo duk iya zaman da suka yi bata tanka musu ba, sun yi kuka sosai saboda duk wanda ya ga halin da Raihan take ciki sai ya tausaya mata. A wannan lokacin Daddy ne ya yanke hukuncin sanar wa Malam ainihin abin da yake faruwa don ko kaɗan baya son ya rasa Raihan, lokacin da Malam ya ji wannan batu ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba saboda gani yake ba komai ba ne don Daddy ya yi magana an haɗa Raihan da Al'amin, kuma a wannan lokacin ya tabbatarwa da Daddy Al'amin zai auri Raihan bayan aurensa da sati guda. Wannan magana ba ƙaramim daɗi ta yi wa Daddy ba, sai dai har lokacin ba a sanarwa Al'amin takamaiman abin da yake faruwa ba. Ranar da Raihan ta cika kwana biyar a asibiti Malam ne ya je dubata bayan magariba kamar yadda ya saba. Kabiru na zaune akan kujera ya haɗa mata tea ya bata tana sha, Daddy da Malam ne suka shiga ya dubata. A kunyace Raihan ta amsa sannan Malam ya ce, "Ƴata duk na ji abin da yake faruwa don haka na zo da kaina na yi miki albishir don Allah ki kwantar da hankalinki indai Al'amin ne nan da sati biyu za a ɗaura miki aure da shi. Ni da na san haka ne ai da tuntuni an yi an gama, amma yanzun ma bata ɓaci ba tun da dai saura sati ɗaya bikinsa bayan auransa da sati guda sai a ɗaura naki." Wani irin farinciki ne ya kama ta don duk yanda ta so ɓoye wa sai da ta murmusa, Kabiru miƙe wa ya yi hankali a tashe jiki na rawa saboda ɓacin rai ko gabansa baya gani ya fice daga ɗakin. Daga Daddy har Malam babu wanda ya kawo komai dangane da fitar Kabiru, Daddy ya miƙa wa Malam Hannu suka sake gaisawa yana yi masa godiya. Daga bayan gatangar asibitin Huzaifa da ke laɓe ya furzar da iska mai zafi rai a matuƙar ɓace ya furta, "Tabbas na so ki kuma na ƙaunace ki amma dole zan haƙura da ke, zan yi miki abin da ban taɓa yi ba domin ba zan juri ganin wani ya same ki bayan ni na rasa ki ba." Rufe bakinsa ke da wuya Raihan da ke shan shayi ta ƙware nan take ta fara tari tun suna ganin kamar ƙwarewa ce har ta fara kyalawa wani irin aman jini ta baki da hanci.



Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624


43



Hankali a tashe Daddy ya fita yana ƙwala wa Likitoci kira, Kabiru har ya suka fita ya ji muryar Daddy yana juyawa ya ga Likitoci sun nufi ɗakin Raihan. A guje ya juyawa jiki na rawa don ya ji lokacin da Daddy yake gayawa Dr Bashir halin da Raihan take ciki, yana niyyar shiga ɗakin Dr Muhammad ya dakatar da su shi da Daddy suna nan tsaye Malam ya fito cikin tashin hankali, don tun da yake bai taɓa ganin matsanancin abin da ya faɗar masa da gaba kamar wannan ba. Mommy ce ta ƙaraso fuskarta ɗauke da fara'a da yake a lokacin ta fita raka wata ƙawarta da ta zo dubiya, ganin yanayin da suke ciki ya sa ta sha jinin jikinta don haka jiki a sanyaye ta dubi Daddy ta furta, "Daddyn Raihan lafiya kuwa?" Jinjina kai ya yi ya ce jikin Raihan ne ya tashi." Tun bai rufe baki ba Mommy ta nufi ƙofar za ta shiga Daddy ya sha gabanta da sauri yana cewa, "Ina za ki shiga Zainab? Baki gan mu a waje ba Likitoci ne suke aikinsu don Allah ki bari su gama." Hawaye ne ya taru a idon Mommy ta ce, "Daddyn Raihan ina son ganin halin da take ciki ne." Girgiza mata kai ya yi don ya tabbata da tana nan Raihan ta fara aman jini babu ko tantama ita ma sai an tallafi tata rayuwar, cikin dakiya ya ce mata: "Na ce ba za ki shiga ba, idan ki shiga kina da abin da za ki yi mata ne?" Gefe mommy ta matsa tana hawaye don a wannan lokacin jikinta ya gama sanyi da lamarim ciwon Raihan, sun jima a nan wurin Dr Bashir ya fito fuska babu walwala jiki a sanyaye ya furta, "Alhaji gaskiya yuwar canja wa yarinyar nan asbiti domin lamarin ciwonta yana neman gagararmu, mun yi mata allurar tsayar da aman nan abin ya ci tura babban tashin hankalinmu yanda jini ya ɓalle daga gabanta. Yanzu haka bata cikin hayyacinta so za mu taimaka da Amblance aka kaita babban asibiti, da gudu Daddy ya faɗa ɗakin ba tare da ya tsaya jin ƙarashen zancen Dr ba. Yana zuwa kusan mutuwan tsaye ya yi ganin yadda Raihan take kace-kace cikin jini, jiri ne ya ji ya fara ɗaukansa a hankali ya dafa bango sannan ya riƙo gefen rigar Dr Bashir ya ce, "Dr don Allah kar ku yaudare ni, idan har kun san yarinyar nan ta rasu kada ku ɓoye min domin dukkan mai rai mammaci ne." Dr Bashir ya kalli Daddy ganin yana hawaye ya sake sanyaya gwiwarsa domin shi kansa baida tabbacin Raihan za ta tashi ko ba za ta tashi ba, don kar ya sake karya gwiwar Daddy ya girgiza kai ya ce, "Alhaji idan mutuwa ta yi ba za mu ɓoye muku ba domin ba ma ɓoye wa mutane mutuwar patient ɗin su. Raihan tana da rai sai dai tana cikin wani irin yanayi da take buƙatar agajin gaggawa. Mun yi bakin ƙoƙarinmu amma mun kasa sai dai aka kaita babban asibiti domin suna da manyan injinan da ba mu da su." A gaggauce aka ɗauki Raihan aka saka ta a mota ba tare da ta san waye a kanta ba. A wannan karon Mommy kasa kukan ta yi saboda yadda zuciyarta ta bushe, Malam da Kabiru a mota ɗaya suka tafi Daddy da Mommy a motar asibitin da aka saka raihan. Kai tsaye daga nan asibitin AKTH aka wuce da ita ɓangaren Emergancy, da sauri suka karɓe ta suka shiga bata agajin gaggawa. Allurai suka yi mata suka shiga ƙoƙarin neman jijiya domin saka mata ledar jini saboda na jikinta sai zuba yake, amma suka nemi jijiya sama da ƙasa suka rasa. Likitoci kusan bakwai ne akanta amma tana sharɓe tamkar gawa ko motsi bata yi. Daga mommy har Daddy babu wanda bai fidda rai da Raihan ba, saboda duk wanda ya ganta ba zai ce tana numfashi ba. Malam da Kabiru suna zaune duk sun yi jigum-jigum, kuɗi ya zaro ya miƙa wa Kabiru ya furta, "Siyo min ruwan gora guda biyu." Kabiru ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login