Showing 84001 words to 87000 words out of 157890 words
haɗe da bayanta ta ce, "Uwar ɗakina kin guje ni yanzu ke bakya kewata?" Raihan ta janye jikinta haɗe da tashi zaune ta ce, "Mama Uwani na gaya miki ba na buƙatar ki riƙa taɓa min jiki." Mama Uwani ta miƙe a fusace ta ce, "Ai dama na daɗe da sanin an yi mana farraƙu a tsakani kuma da ni kike zancen." A fusace Raihan ta miƙe ta ce, "Mama Uwani ni kike gaya wa haka? Tsaki Mama Uwani ta yi ta fice daga ɗakin, da sauri Raihan ta bita amma ga mamakinta sai ta ganta a wani ƙaton fili. Waige-waige ta fara yi don kanta ba ƙaramin juyewa ya yi ba, ganin bata da mafita ya sa ta fara tafiya har ta isa bakin wani ƙaton kogi. Wani ƙaton baƙin sa ta hango yana tunkarota yana tafe yana jijjiga kansa, ganin girma da munin san ba ƙaramin razana Raihan ya yi ba. Hankali tashe ta fara gudu don ta lura kanta yake san ya yi gadan-gadan, tana tafe yana biye da ita har ta yi masa nisa sai dai tana shan wata kwana ta ci karo da shi. Da sauri ta ja da baya ƙirjinta yana bugawa da ƙarfin gaske bata yi aune ba ta ji ya fisgi hannunta ya yi gaba da ita, cikin matsanancin tashin hankali ta ƙwalla wata gigitacciyar ƙara haɗe ta zabura wanda ya farkar da ita daga nannauyan baccin da ya yi awon gaba da ita. Ajiyar zuciya ta riƙa sauke wa jikinta na rawa a daidai lokacin Mommy ta turo ƙofar ɗakin tana faɗin, "Raihan lafiyarki kuwa kike yi mana ihu a gida?" Ganin yanayin da Raihan take ciki ya sa Mommy ƙarasawa bakin gadon ta ce, "Raihan! Me yake damunki?" Raihan ta ruƙo hannun Mommy har lokacin jikinta na rawa ta ce, "Wallahi wani mafarki na yi mommy daga kwanciya bacci." Mommy ta kalle ta sosai ta sake maimaitawa, "Mafarki? Mafarki wane iri?" Nan take Raihan ta zayyane wa Mommy duk abin da yake faruwa sannan ta ɗora da cewa, "Wallahi na yi kewar Mama Uwani ko tana wace duniyar yanzu oho?" Hankalin Mommy ba ƙaramin tashi ya yi ba, da sauri ta riƙo hamnunta ya ce, "Mu je ɗakina ki huta a can." Ba musu Raihan ta bi bayan Mommy suna zuwa Mommy ta kunna karatun Alƙur'ani, Raihan ta kwanta akan gadon Mommy ita kuma ta zauna a gefenta tana shafa kanta. Tunani kala-kala ne ya riƙa zarya a birnin zuciyarta tana Allah-Allah Daddy ya dawo don ta sanar masa abin da yake faruwa, don ko da wasa ba ta fatan Raihan ta riƙa ire-iren mafarkin nan saboda ba alheri ba ne. Baccin da Raihan bata koma ba kenan, ita kanta ta jima tana maimaita yanayin mafarkin da ta yi a zuciyarta, amma tunaninta ɗaya Mama Uwani ko tana wace duniyar don ba ƙaramin sabo suka yi da ita ba, dukda ta ji Mommy ta ce wani dalili ya dakatar da ita da yi musu aiki gabaɗaya. Mommy na jin shigowar Daddy ta miƙe ta fice daga ɗakin, a falo ta same shi ya kunna television yana kallon labarai. Murmushi ya yi mata yana miƙa mata hannu, martanin murmushi ta sakar masa cikin yaƙe ta zauna a gefensa ya tallafota da hannu ya ce, "Ni kam matar nan ban gane wa yanayinki ba. Tun a Dubai nake zarginki don wallahi duk kin sauya kamar ba ke ba." Kallonsa ta yi don bata fahimci in da maganar Daddy ta dosa ba ta ce, "Daddyn Raihan ni fa ban gane zagaye-zagayen nan naka ba, me kake nufi kana nufin ƙasar wasu tafi karɓa ta kenan?" Daddy ya yi dariya sannan ya ce, "Zainab ga ki dai shekarun sun fara yawa amma wani abin idan kika faɗa kamar Raihan." Hannunsa ya kai kan cikinta ya ce, "Jikina yana ba ni akwai ajiyata a nan." Mommy zaro ido waje ta yi ta kalli Daddy ta ce, "Don Allah ka daina faɗin wannan maganar Daddyn Raihan, tsofai-tsofai da ni wace irin haihuwa kuma? Yanzu da Raihan na tare da Salim ɗan/'yarta da sun doshi shekara har da wani abu." Daddy ya jinjina kai ya ce, "Nawa kike Zainab kawai don Raihan ta yi tsawon ƙafa ni kin rufa talatin kuwa?" Hararar wasa Mommy ta yi masa ta ce, "A'a ka manta ashirin zan yi." Ta sauya murya cikin shagwaɓa ta ce, "Wai don Allah Daddyn Raihan me ka mayar da ni?" Daddy ya yi dariya ya ce, "Yarinya mana." Mommy ta jingina da kujera ta ce, "To ka sauke don wallahi ni ma girma ya zo." Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Serious Habibty ina zargin ciki gare ki don tun kafin mu tafi Dubai na fara zargin haka." Mommy ta yi sak jiki a sanyaye ta ce, "Ni wallahi ba ciku gare ni ba, don Allah yanzu na samu ciki na cewa mutane me? Kawai sai Raihan da su Inno su wayi gari ina tura ciki gaba?" Daddy ya yi dariya har da riƙe ciki ya ce, "Su Inno da Raihan ba sun san kina da mijina, yanzu dai yaushe rabonki da baƙon wata?" Mommy shiru ta yi ta faɗa duniyar tunani nan take gabanta ya yanke ya faɗi.
Tunawa ta yi sam bai zo mata ba saboda tun kafin tafiyarsu Dubai take sa ran ganinsa amma har suka tafi bai zo ba, zuwan su Dubai sai ta manta da komai sai yanzu da Daddy ya tuna mata. Idonta ne ya ciko da ƙwalla ta ce, "Wallahi tun kafin mu tafi Dubai nake sa ran ganinsa bai zo ba." Daddy ya wara hanninsa haɗe da cewa, "Shi kenan kin ga na ci gari." Mommy ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba amma don kar ga nuna wa Daddy ya sa ta kawar da zancen da cewar, "Daddyn Raihan da matsala fa." Ya kalleta cikin nutsuwa ya ce, "Matsala kuma? Wacce iri?" Nan take mommy ta zayyane masa irin mafarkin da Raihan ta yi, kai kawo Daddy ya fara yi cikin damuwa ya furta, "Huzaifa-Huzaifa. Huzaifa ba zai bar min yarinya ta sarara ba ne wannan waccen irin rayuwa ce. Ni ina zargin ba shi ya cire wa yarinyar nam son kula samari ba kuwa? Kina ga kowa ya nuna yana son Raihan za ta fara maganar tsohon mijinta, yanzu haka rayuwar yarinyar nan za ta ƙare?" Mommya ta ƙarasa wurim Daddy ta riƙo hannunsa sai da suka zauna ta ɗauki sauran ruwan da ya sha ta miƙa masa, ajiyar zuciya ya yi sannan ya karɓa sha. Mommy ta dube shi cikin ƙarfafa gwiwa ta ce, "Idan aka san ciwon abin da yake damun mutum kamar an ci rabin magani ne, sannin Raihan na tare da wannan shaiɗanin ba ƙaramar rahama ba ne a wurinmu. Mafita kawai mu ci gaba da yi mata addu'a muna nema mata magani dukkan tsanani yana tare da sauƙi, kuma wannan abin yana daga cikin shafin ƙaddararta. Fatanmu akanta Allah ya bata lafiya ya tsare dukkan musulmi bakiɗaya." Daddy ya amsa da amin sannan ya fara tunanin zuwa don karɓo wa Raihan magani. Sun jima suna tattauna wa akan matsalolin da suke damun Raihan sannan mommy ta ƙarasa ɗakin su Inno don tun dawowarsu da suka shige ɗaki bata ƙara jin motsinsu ba.
Mommy na shiga ɗakin ta same su sun baje kaya ɗaiɗai da yake dama jakunkunansu daban mommy ta yi musu, Mommy na shiga Inno ta ɗago wani leshi da Daddy ya sawa musu ita da Goggo ta ce, "Zinaru wannan leshin a ƙasan akwati zan saka shi, idan Allah ya kaimu Allah ya sauki Zainabu lafiya ranar suna zan rangaɗa kayana." Goggo ta ware wasu kaya kala uku a gefe ta ce, "Ai ba zan ɗinka kala ɗaya ba, saboda ko a Albasu ba na fitar suna da kala ɗaya. Kai amma yarinyar nan ta shammace mu, a lokacin da muke saka rai da ciki babu sai yanzu da Allah ya nufa." Inno ta yi wani murmushin jin daɗi ta ce, "Ni kam na ɗauka Audullahi ya yi bankwana da haihuwa ashe Allah ya ɓoye ajiyarsa mu muke abin mu." Mommy ta ɗan yi gyaran murya haɗe da sallama don ta ji duk hirar da suke yi, gabanta ne ya faɗi take ayyana ashe suma kallon ciki suke yi mata ita take abinta. Su Inno suna ganin Mommy suka washe baki Inno ta ce, "Zainabu an shigo?" Mommy ta zauna a gefen gadon Goggo ta ce, "Inno yanzu tun baku huta ba kun hau kwance kaya, don Allah ku kwanta ku huta man." Goggo ta sake janyo wani ƙunshin kaya da wuƙa a gefe tana kiciniyar yankawa ta ce, "Zainabu kenan a bari ya huce shi yake kawo da rabon wani, kin taɓa ganin na bar kaya sun kwana ko Albasu na je?" Mommy ta girgiza kai haɗe da miƙe wa ta ce, "To bari na baku wuri don na gaji bacci nake ji." Inno ta ce, "Ai dama gara ki huta don gaskiya kina buƙatar hutu." Mommy ta juya ta fita tana daga bakin ƙofa Goggo ta yi ƙasa da murya ta ce, "An ya yarinyar bata ji hirar mu ba?" Inno ta waiga ta kalli ƙofa ta ce, "Da ta ji za ta yi mana magana, idan ta ji ai na ga ta kaina ina uwar miji guda ai sai ta ce na saka mata ido. Don ma Zainabu dai yarinyar kirki ce ni uwa ta ɗauke ni ba sirika ba, amma wallahi matsalata ɗaya da ita da bata son yi mana tuwo saboda Allah ina laifi a ce duk dare mu ci tuwo a gidan nan." Goggo ta wara hannuwa ta ce gane min hanya amma wallahi Audullahi ya fi ta laifi don Allah shi ba zai tsawatar mata akan abin da muke so ba?" Inno ta yi guntun tsaki ta ce, "Bar batun Audullahi baƙin Bayahude ne har gara Zainabu tana yi mana tuwo sau uku a sati amma kin taɓa jin Audullahi ya ce ta yi tuwo?" Goggo ta girgiza kai. Inno ta ci gaba da fito da kaya ta ce, "Ki bar su ƙarƙari idan muka gaji mu kama gabanmu ina dalili gida kullin ka ci shinkafa, ko kunu sai na yi sati biyu ban sha ba." Goggo ta ce, "Ba don ina jiran haihuwar Zainabu ba ai wallahi daga Iyafot (Airport) Albasu zan wuce." Mommy ban da dariya babu abin da take yi don tsofaffin ba ƙaramin dariya suka bata ba. Daga nan kai tsaye ɗakinta ta wuce don ba ƙaramin zafi idonta suke yi mata ba, tana kwanciya babu jima wa bacci ya yi awon gaba da su.
A ranar da Mommy ta sanar da shi mafarkin Raihan a ranar ya je Waraka Islamic chemist, da yake duk yaran Malam Usman sun san Daddy da irin magungunan da ake haɗa wa Raihan ya sa suka haɗa masa magunguna tare da yi masa bayanin yadda za ta yi amfani da su. Kuma tun daga ranar Raihan bata sake irin mafarkin nan ba, su Mommy sun dage sosai wurin nema mata magani kuma babu wani abu da ya sake faruwa da ita. Raihan suna yawan gaisawa da Intisar wani lokacin har video call suke yi, musamman yaran Intisar da Raihan take jin su har cikin ranta. Daddy tsaraba ta musammam ya yi wa Kabiru kasancewar ya shiga ransa sosai saboda Kabiru yana da hankali da nutsuwa. Mommy tun tana ganim kamar duk zancen ne maganar da Daddy ya yi mata na ciki har ta fara zargin kanta sakamakon irin sauye-sauyen da take samu, daga ƙarshe watarana ta shirya ta je asibiti a ranar likita ya tabbatar mata da ciki, sakamakon gwaje-gwajen da aka yi mata. Raihan kasuwancin da take yi ba ƙaramin karɓarta ya yi ba, ganin haka ya sa Daddy ya yi tunanin buɗe mata Boutiqe. Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yi wa Raihan ba, haka ta ci gaba da rayuwarta haɗe da kasuwancinta gwanin birgewa. Sai dai a fagen samari duk yadda suka kai ga ganin sun saye zuciyar Raihan abin ya ci tura. Tun bata kula su daga ƙarshe ma suka daina zuwa gabaɗaya, da farko abin ko kaɗan bai damu Raihan ba saboda a ganinta ba za ta ƙara samun masoyi kamar Salim ba, shi kuma wanda take bege har tsawon wannan lokacin bata sake cin karo da shi ba. Don haka rashin zuwan samarin da basa yi ya fara damun Raihan har take ganin kamar rashin saurar da ba ta yi musu ne ya sa suka ja da baya. Abin da Raihan bata sani ba tuni wasu daga cikin mutane suka yanka mata ayar tambaya don tuni mutane suka ɗora zargin mutuwar Salim akan rashin lafiyar Raihan ta baya, saboda zancen duniya ko kaɗan baya ɓuya. A haka suka ci gaba da gudanar da rayuwa har cikin Mommy ya kai wata takwasa da sati biyu, a wannan lokacin aka yi wa Mommy Cs don tun a lokacin awon cikinta Likita ya ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda shekarunta sun ɗan ja, idan aka ce a bari ta haihu da kanta za ta sha wahala. An yi aiki lafiya aka ciro mata jaririnta Namiji lafiyayye gwanin birge wa, murna wurin Raihan abin ba a magana. A gaggace take tafiya don ganin ta ƙarasa wurin da ta yi parking ɗin motarta, za ta koma gida don karɓo wa Mommy ruwan shayin da su Inno suka dafa. A jikin motarsa ta same shi a tsaye da waya a hannu yana dannawa, a gaggauce ta buɗe murfin motar ta kalle shi tana faɗin, "Don Allah Malam zan ɗauki mota sauri nake yi." Bai ɗago ya kalle ta ba kuma ko kaɗan bai motsa ba balle ta saka ran zai tanka mata, haushi ne ya fara kama Raihan don a yanayin mutumin da ta gani bai yi kama da wata ɗan ƙabilar ba balle ace baya jin hausa. Haushi ya kama ta a ɗan zafafe ta ce, "Wai Malam baka jin abin da nake faɗa ne?" Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta sai dai bai tanka mata ba ya ci gaba da latsa wayarsa. Ƙugu Raihan ta riƙe ta dawo ta gabansa tana nuna shi da yatsa ta ce, "Malam ba na son wulaƙanci ka matsa min daga jikin mota." Raihan na rufe baki ya ɗago sai da ya kalleta na ƴan daƙiƙu ya ce, "Ki fara koyo sallama kafin ki furta wa ɗan'adam koda kalma ɗaya ce."
Littafin Kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624.
32
Shiru Raihan ta yi saboda ba ƙaramin kunya ta ji ba, amma don kar ta nuna masa yanayinta sai ta ɗauke kai gefe ta ce, "Tun da kai ka iya ya wadatar ba sai na koyo ba don Allah ka matsa ka ba ni wuri." Kafin ya bata amsa daga bayanta ta ji an furta, "Barista Huzaifa! A sanyaye ya ɗago ya kalli mai kiran nasa don suna haɗa ido ya faɗaɗa fara'arsa da cewar, "Likita bokan turai." Mamaki ne ya kama Raihan don yanayin fuskar wanda aka kira da Barista Huzaifa bata taɓa nuna mata alamar ya taɓa dariya ba. Dr Hussain ne ya ƙarasa ya bashi hannu suka gaisa sannan ya kalli Raihan ya ce, "Raihan kar dai kuna da relation Barista?" Ya yi tambayar cikin fara'a don duk wanda ya ga irin tsayuwar da su Raihan suka yi zai ɗauka suna da wata alaƙa. Dr Hussain na gama magana Raihan ta taɓe baki ta ce, "Dr wallahi bansan shi ba, don Allah ka ce ya matsa min zan je gida na kawowa mommy ruwan zafi." Jikin Barista Huzaifa ne ya yi sanyi don yadda Raihan ta yi maganar ya nuna masa a ƙagauce take, don alamu sun nuna Mahaifiyarta ce babu lafiya. Dr Hussain ya yi murmushi ya ce, "Barista abokina ne." Ya juya ya kalli Barista Huzaifa ya ce, "Barista kun yi shiru kamar bakwa duniyar, saboda kun danne manya kaya sai ku yi wa talaka nisa." Barista Huzaifa ya matsa daga jikin motar Raihan ya ce, "Wallahi ba haka ba ne, ka san yanayin aikinmu sai a slow. Yanzu haka na shigo gari wani abokina ne aka kwantar da shi da babu lafiya." Dr Hussain ya ce, "Subhanallah ya sunan patient ɗin?" Barista ya waiga yana kallon motar Raihan da ta fice daga harabar asibitin, sannan ya juyo ya ce, " Sunansa Barista Sani ƙofar nasarawa. Amma mun fi kirsansa da ƙofar nasarawa." Da yanayin mamaki Dr Hussain ya ce, "Kar dai shi ne mai matsalar ciwon siga?" Barista Huzaifa ya jinjina kai yana faɗin, "Exertly, and yana jin jiki sai dai mu yi fatan Allah ya bashi lafiya." Gabaɗaya suka amsa da amin. A hankali suka fara takawa Dr Hussain ya ce, "Yanzu za ka wuce ne Barista?" Barista Huzaifa ya kalli agogon hannunsa ya ce, "Gaskiya wuce wa zan yi dama akwai wani abokina da nake jira but ina da uzuri a waje saboda akwai case ɗin wata yarinya da aka yi rapping ɗinta da nake bincike akai." Dr Hussain cikin jimami ya ce, "Ai dama kuna ganin cases kala-kala Allah ya sa mu dace." Suka amsa da amin har sun je wurin motar Barista za su yi sallama Barista Huzaifa ya ce, "Dr wannan yarinyar da ta wuce fa?" Dr Hussain irin mutannan masu surutu yana jin haka ya washe baki ya ce, "Wai Raihan?" Barista Huzaifa ya gyaɗa masa kai. Nan take Dr Hussain ya zayyane masa komai akan Raihan na haihuwar Mommy, da yake shi ne likitan da ya yi mata Cs. Cikin gamsuwa Barista ya jinjina kai ya ce, "Tsiwarta ta birge ni." Dr Hussain ya yi dariya ya ce, "Mutumina ka rufta dai kawai. Yanzu sai wacce shekarar za mu sake haɗuwa?" Barista ya yi murmushi mai sauti haɗe da faɗin, "Zan ɗan kwana biyu a Kano insha Allah saboda mun samu hutu, zan iya kai kwana huɗu kafin na wuce Kaduna." Sun jima suna tattaunawa daga ƙarshe suka yi sallam Barista ya shiga motarsa ya wuce, Dr Hussain ya koma