Showing 75001 words to 78000 words out of 157890 words
Mommy na jin an ɗauka ta fara magana cikin kuka. "Daddyn Raihan kuna wane asibitin don Allah me yake faruwa da ita? Ina Raihan..." Tattaro jarumta ya yi irin ta Namiji ya daidaita muryarsa tare da katse ta da cewar, "Zainab!" Ya kirata da wata irin murya, Mommy na jin haka kuka ya sake kwace mata jikinta har rawa yake ta ce, "Don Allah Daddyn Raihan..." Sake katse ta ya yi da cewar, "Zainab ki ba ni hankali ba na son shiririta." Shiru mommy ta yi hawaye na zarya a kan dakalin fuskarta. "Raihan ta samu bacci a halin yanzu, ba na son ki sawa kanki damuwa saboda duk abin da kika ga ya faru da bawa rubutacce ne a wurin Ubangiji. Idan Allah ya rubuta Raihan ɗin za mu rasa muna da ikon hanawa ne?" Daddy ya yi maganar zuciya a dake. Kamar Mommy tana gabansa ta girgiza masa kai sannan ta ɗora da cewa, "Ina fargabar halin da Raihan za ta shiga, ban san ya abin zai zo mata ba. Yanzu kuna wane asibitin zan ƙaraso." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke sannan ya ce, "Idan har kuka za ki zo kina yi tun wuri ki haƙura da zuwa, yaron nan Salim ya samu kyakkyawar shaida tun daga wurin mutanen gari. Shin ita Raihan ba musulma bace da ba za ta karɓi jarrabawar da Allah ya yi mata ba, idan kina faɗan irin haka ta yaya za ki bata ƙwarin gwiwa har ta cire komai a ranta?" Jiki a sanyaye Mommy ta ce, "Haka ne na fahimce ka, gaya min sunan asibitin yanzu na ƙaraso. Allah ya gafarta masa halinsa na gari ya bishi." Kwatanta mata asibitin ya yi sannan suka yi sallama. Mommy ita da Mama Hafsa ne suka tafi suna zuwa Daddy ya wuce gidansu Salim.
Su Mommy suna zaune jigum-jigum Raihan ta buɗe idonta, kallonsu ta fara yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta runtse idonta ta sake buɗewa. Da sauri ta zabura za ta tashi zaune Mommy ta riƙe za ta yi magana Raihan ta riƙo hannunta tana hawaye ta ce, "Mommy da gaske Salim ya mutu, Mommy ɗazu fa muka yi waya yace zai gaya min wata magana don Allah ki gaya min gaskiya ko wasa ake yi min?" Mommy ta fakaici idon Raihan ta goge hawayen idonta ta ce, "Raihan!" Raihan ta sake fashewa da kuka ta ci gaba da cewa, "Mommy don Allah kar ki ce min Salim ya mutu!" Mommy ta sauke ajiyar ta ce, "Raihan muna da ikon dakatar da mutuwa ne? Ke fa musulma ce me ya sa ba za ki rungumi ƙaddararki hannu bibbiyu ba? Allah shi ya halicci Salim kuma ya karɓe shi babbar soyayyar da za ki nuna masa ki yi masa addu'a." Raihan ban da hawaye babu abin da yake zarya a fuskarta. Kamar wacce ake yi wa raɗa haka ta ji maganganunsa na dawo mata a lokacin da suke waya, a zabure ta miƙe tsaye jikinta har rawa yake ta ce, "Ina wayata don Allah ba ni wayata na kira lambarsa na ji." Mommy na ganin haka hawaye ya ci gaba da zubo mata don ta san duk abin da Raihan take yi tana yin sa ne cikin ruɗewa da tashin hankali.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn0706 206 2624
28
Lokacin da Daddu ya ƙarasa ƙofar gidansu Salim cike yake da mutane sun yi jigum-jugum, yana tsaye motar asibiti ta ƙaraso ƙofar gidan tana zabga jiniya. Mahaifin Salim ne ya fito daga motsarsa babu jimawa aka fara kiciniyar fito da gawar Salim daga Amblance, matsawa mutane suka fara yi don a bayar da hanya su shigar da gawar. Lokaci-lokaci Mahaifin Salim yake share ƙwallah da take zuba daga idonsa, ana shiga da gawar Salim Mahaifiyarsa da ƙannensa suka fashe da matsanancin kuka. Mahaifin Salim na ƙofar gida mutane suka fara yi masa gaisuwa, jiki asanyaye Daddy ya ƙarasa wurinsa ya ce, "Alhaji ya muka ji da haƙuri?" Mahaifin Salim ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, "Alhamdulillah da godiya duk abin da Allah ya yi mai kyau ne." Daddy ya jinjina kai ya ce, "Haka Allah ya jiƙansa halinsa na gari ya bishi." Mahaifin Salim ya ce, "Amin ya rabbi, amma ya ya matarsa ina fatan babu wani abu da yake same ta?" Daddy ya ɗan yi jim sannan ya ce, "Ka san sha'anin ƙuruciya yanzu haka dai tana asibiti ta farfaɗo amma jikinta da sauki." Mahaifin Salim ya furta, "Allah ya bata lafiya." Gabaɗay suka amsa da amin, sun ɗan jima suna tattauna yadda jana'izar Salim za ta kasance sannan suka yi sallam. Jikin Daddy duk ya yi sanyi ko da bai ga gawar Salim ba amma yadda ya ji ana maganar irin ƙonewar da suka yi abin ya ɗaga hankalinsa.
A lokacin da Salim ya gama waya da Raihan kallon Nadabo abokinsa ya yi ya ce, "Mutumin ni fa na yi muku nisa sai kun biyo sawu." Nadabo da yake driving ya yi murmushi ya ce, "Allah na tuba da me kwaɗo ya fi gaya, amma duk cika bakinka ai yanzu dai ɗaya muke da kai tun da yanzu muke kan hanyar zuwa kaika. Ni Allah sa ya sa ma karka ba mu kunya duk kurin nan ka kasa cika aiki." Salim ya saka dariya yana saka wayarsa a aljihu ya ce, "Allah ya kiyaye kai fa shegen kaya ne, an gaya maka abin da zan je yi kenan." Nadabo ya yi masa hararar wasa ya ce, "Ɗan iska irinku ne idan kuka rufe ƙofa tun safe sai bayan isha'i." Lokaci ɗaya suka saka dariya don Salim mutum ne mai shiga rai, mu'amala ta rana ɗaya za ku yi ya shiga ranka. A daidai Zayyan suya spot suka yi parking, Salim da Nado suka fito kowanne sanye da babbar riga. Sauran motocin abokan Salim ne suka yi parking kasancewar suna bayan motar su Salim. Kaji huɗu Nadabo ya sa mai Naman ya saka a leda, mai naman da murmushi ya dubi Nadabo yana murmushi ya ce, "Abokina da alama kai ne angon don na lura ban da ƙyalli babu abin da goshinka yake yi." Nadabo ya sake buɗa babbar riga yana dariya ƙasa-ƙasa ya ce, "Ga angon nan amma yadda kasan ni aka ɗaurawa don ko sheƙin angoncin baya yi." Salim ya yi dariya ya dubi mai nama ya ce, "Wallahi za ka ja na bar maka kazarka don sai mu koma wani wurin haka kawai Allah ya ba ni girma ka sauke min." Mai naman ya yi dariya yana miƙa musu manyan ledoji, Nadabo ya karbi ledar yana taɓe baki ya ce, "To ya na iya dole na biya kuɗin kaza kuma na yi dakonta, idah da rai da lafiya nima baɗi war haka ja rako ni ɗakin matata." Nadabo ya yu maganar yana miƙawa mai nama kuɗinsa. Mota suka buɗe suka shiga juyawar da Nadabo ya yi zai sa ledar kazar a mazaunin baya ya ci karo da wani baƙin kare mai jan ido, ƙirjinsa ne ya buga ya runtse ido ya buɗe amma sai bai ga komai ba. Jiki a sanyaye ya waiga ya ce, "Salim don Allah baka ga komai a bayan motar ba." Salim ya waiga babu komai a wurin ya ce masa, "Kamar ya fa? Ba abin da na gani." Shiru Nadabo ya yi ya kunna motar suka fara tafiya. Ba su yi nisa ba sai jin wani irin haushin kare wanda ya ratsa har tsakiyar kansu, a firgice duk suka juya don ganin abin da yake faruwa. Kafin su kaiga ganin kammanin kare ya yi kukan kura ya faɗa kan Salim tare da kai bakinsa kan daidai maƙogaronsa, Nadabo ba ƙaramin razana ya yi ba nan take motarsu ta fara tangal-tangal akan titi ƙarshe ta faɗa cikin wata babbar kwalbati, motar abokansa da ke biye da su ita ma ta i bayansu sai ta ukun ce Allah ya kare. Nan take wuta ta tashi a wurin mutanen da ke bakin titin suka fara kawo ɗauki ta hanyar zuba ƙasa da ruwan kwata, amma wutar tamkar ƙwara mata fetur suke, sai da ta ci don kanta sannan ta lafa a daidai lokacin ƴan kwana-kwana suka ƙaraso wurin tare da motar asibiti. Sai da suka ƙarasa kashe wutar sannan aka ɗebi gawargwarin su Salim aka wuce asibiti da su.
Kafaɗar Raihan mommy ta dafa ciki dakakkiyar murya ta furta, "Raihan!" Raihan bata amsa ba sai hawaye da yake zarya a fuskarta, ta kafe mommy ta ido amma ilahirin jikinta rawa yake. Zuciyar mommy babu daɗi amma duk da haka ta kauda kanta gefe ta ci gaba da cewa, "Ke muslma ce! Don haka ki rungumi abin da Allah ya jarabce ki da shi. Salim ya mutu kuma lokacinsa ne ya yi idan ke ni ko ke Ubangiji ya so ɗauke wa ye yake da ikon hanawa?" Raihan ta kasa furta komai ban da hawayen da ke zuba a fuskarta. Mama Hafsa ita kanta hawaye take don duk wanda ya ga halin da Raihan take ciki sai ya matuƙar tausaya mata. Mommy ta riƙo hannun Raihan ta ce, "Ta so mu je ki ɗauro alwala ki yi sallah raka'a biyu ki yi wa mijinki Addu'a." Raihan na miƙe wa daga kan gado ta faɗa jikin Mommy ta fashe da matsanancin kuka. Bayanta ta fara bubbugawa sai dai ta kasa bata haƙuri, a hankali ta ɗago Raihan daga jikinta ta raka ta banɗaki ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah raka'a biyu tana yi tana zubda ƙwallah. Lokacin da Daddy ya ƙarasa asibitin dare ya tsala sosai, don lokacin kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Yan zuwa asibitim ya samu su Mommy a zaune jigun-jigun, Raihan na zaune a kan dadduma ta kifa kanta da cikin ƙafafuwanta. Daddy na zuwa Raihan ta ɗago tana kallonsa sai kawai ta fashe da kuka ta ce, "Daddy kaima ka ji Salim ya mutu? Wallahi ɗazu muka gama waya da shi Daddy don Allah me ya sa..." Daddy ya ƙarasa gaban Raihan ya sa hannunsa ya rufe mata shi yana cewar, "Raihan ba na san ki riƙa surutu haka." Yana daga tsugunne ya kalli mommy ya ce, "Yi wa nurses ɗin nan magana su yi mata allura ko za ta samu relief." Mommy ta jingina kanta da bango ta ce, "Tun ɗazu suka zo wallahi fir taƙi yarda." Daddy ya jima yana yi wa Raihan nasiha ta yi shiru tana sauraronsa tana hawaye. A haka suka ƙarasa ganin daren ba tare da kowa ya iya runtsawa ba.
Mahaifin Salim sai da ya tsawatar wa Mahaifiyar Salim da ƴan uwansa sannan suka yi shiru amma kana kallon Mahaifiyarsa za ka fahimci irin tashin hankalin da take ciki. A daren aka suturta Saim sai dai ko wanka ba a yi masa ba sakamakon mummunar ƙunan da jikinsa ya yi. Su Salim su Biyar ne suka rasu sai dai gabaɗaya a cikinsu da ƙyar mahaifansu suka gane su saboda sun ƙone ƙurmus sun yi baƙiƙƙirin musamman Salim da gawarsa ta fi ta kowa munana saboda irin kisan gillar da mummunan karen nan ya yi masa. Wannan mummunan labarin na rasuwar su Salim lokaci ɗaya ya yaɗa ko'ina musamman da ƴan jarida suka taimaka da masu manyan wayoyi suka riƙa watsa labarin, duk wanda aka cewa Ango ya rasu da abokan a hanyar zuwa raka ango gidansa ba ƙaramin jimantawa suke ba, musamman da hotunan bikin su Raihan ya ratsa kafofin sada zumunta sai kuma katsam aka samu wannan labarin. Mutane waɗanda suka sansu da waɗanda basu san su ba haka suka riƙa ɗora hotunan Salim da Raihan na ranar Dinner da Kamu suka saka alamar kuka tare da yi masa addu'ar Allah ya kyauta makwanci.
Wani irin baƙin hayaƙi ne yake fitowa daga ko'ina na sassa jikinta, ya yin da bakinta yake fitar da harshen wuta ƙasanta na fesar da wani irin tafasasshen ruwan mai yauƙi. Ɗaukan bil'adam ta riƙa yi ɗaya bayan ɗaya tana wurgawa cikin bakinta dukda kasancewarsu halattatun ƴan ƙungiya, ganin haka ya sa suka fara nema ceton ransu suna tserewa da ƙafafuwansu. Ƙanananun aljanun da suke wurin a tunaninsu sun tsira sai dai ba su yi aune ba suka riski Abar bauta ta faɗa ɗaukan wasu daga cikinsu tana haɗiyewa. Lokaci ɗaya wurin ya kacame da iface-iface da kururuwa don abin da ba su taɓa gani ba ne, Hatsabibiya gefe ta zauna ta zurawa Abar bauta ido sai da ta gama duk abin da take yi sannan ta furta, "Ko ba komai kin rage mana ƴan ƙungiya sai dai hakan ba yana nuna ƙungiyarmu ta ci baya ba, amma kina ganin wannan ɓacin ran naki zai kai mu ga cin abin da muke buƙata? Aikin gama ya gama tun da Huzaifa ya riga da gama ɓata mana shiri tun da ya kashe mata miji, na ci burin ɗora duk wani shirinmu akan ta bayan aurenta domin shi zai kaimu ga cimma burinmu." Wani irin huci Abar bauta ta yi sannan ta ce, "Laifin Mugaza ne kuma dole za mu ɗauki mummunan mataki a kanta. Ita idanunmu ce kuma kunnuwanmu ce mun sakakankance akan za ta ba mu jawabin halin da ake ciki amma wannan karon tana neman ba mu kunya, na fara zargin tana sane da komai akan a duk hukuncin da Huzaifa ya ɗauka." Hatsabibiya na shirin yin magana suka ji an furta, "Babu sa hannu ko kaɗan akan abin da Huzaifa ya aikata hakazalika ni kaina yaudarata ya yi domin bai taɓa nuna min ya samu lafiya ba. Kullin cikin kwanciya yake amma jiya kawai na neme shi na rasa, ina ganin Huzaifa buɗe mana hanya ya yi don mu ƙara miƙe wa tsaye don mu san ta yadda za mu shawo kan matsalar. Huzaifa ya fargar da mu baccin da muka fara domin na lura da sabon shiri ya dawo na tabbata ko ni ce na kawo masa wargi akan Raihan zai iya kawar da ni." Mugaza ta yi dogon sharhin tana ƙarasawa cikin tsibirin.
Asubar fari bayan sun idar da sallah Daddy yake sanarwa da Mommy cewar ƙarfi takwas na safe za a yi jana'izar Salim a ƙofar gidansu, hakan ne ya sa suka nemi sallama a lokacin don tun farkowar Raihan taƙi yarda su yi mata wata allurar baccin. Kai tsaye daga asibitin gida suka wuce suka kintsa sannan suka yi mota uku suka wuce gidansu Salim, tun da aka doshi hanyar gaban Raihah yake tsananta faɗuwa nan take jikinta ya fara karkarwa. Suna zuwa mommy ta riƙe hannunta suka shiga cikin gidan, su Farida na hango Raihan suka tafi da sauri suka rungume ta suna kuka. Da ido mutane suka riƙa bin su da kallo gwanin ban tausayi, sainda Mahaifiyar Salim ta ƙarasa ta riƙota tare da mommu suka wuce ɗakinta. Mahaifiyar Raihan sosai ta yi wa Rainan nasiha sannan ta ja zuwa ɗakin da aka shirya gawar Salim don ta yi masa addu'a kafin a tafi da shi. Tana tafe gabanta na faɗuwa haka suka ƙarasa ƙofar ɗakin, tana shiga ya same shi a kwance an gama haɗa shi. Jikin Raihan nan take ya fara karkarwa a hankali ta zube a wurin tana fara yi wa Salim addu'a, lokaci ɗaya kuka ya kwace mata ta jingina kanta a jikin Kan Salim ta ci gaba da rera kuka mai tsuma zuciya. A hankali Mommy ta riƙo hannunta tana shirin fito da ita sai gani ta yi numfashinta yana sama, kafin Mommy ta yi wani yunƙuri Raihan ta faɗi a wurin.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min magana 0706 206 2624
29
Hankali a tashe Mommy ta yi kanta da sauri Mahaifiyar Salim ta ɗauko ruwa aka fara yayyafa wa Raihan, a hankali take sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe idanunta tana kallon su Mommy. A daidai lokaci Mahaifinsu Salim da sauran ƴan uwansa suka shigo ɗakin suna faɗin, "Za mu ɗauke shi mu yi masa sallah mutane sun gama taruwa." Hawaye ne ya ciko idon Mahaifiyar Salim, Raihan na jin haka ta fara bin su da kallo a zuciyarta take ayyana shi kenan ita da Salim sun yi bankwana. Tana raɓe a gefe suka ɗauke shi suka fice da shi lokacin ƙafafuwanta suka fara karkarwa. Tsugunnawa ta yi a wurin don yadda take ji ƙafafuwanta ba za su iya ɗaukanta ba. Zoben hannunta ta zurawa ido tana tuna ranar Dinner su da Salim ya saka mata shi a hannu, murza ɗan yatsanta ta fara yi a hankali kamar almara sai jin irin muryar Salim ta yi an ce, "Ki ba ni zobena na tafi da shi." Zaburar da ta yi ne ya fargar da Mommy da sauri ta riƙe ta tana faɗin, "Ke Raihan ina za ki?" Raihan ta nuna bakin ƙofar fita ta ce, "Wallahi Salim magana yake min, don Allah ku duba bai mutu ba." Ganin yadda Raihan ta firgice musu lokaci ɗaya ya sa Mahaifiyar Salim ta dubi Mommy ta ce, "Hajiya mai zai hana ku wuce da Raihan gida ina ganin kamar zai fi." Mommy ta yi jim sannan ta ce, "Shi kenan Hajiya Allah ya gafarta masa, za mu wuce insha Allah zuwa anjima zan dawo." Maman Salim ta yi murmushin ƙarfin hali ta furta, "Karki damu Hajiya ki kula da ita don tana cikin wani irin hali ko baki dawo ba anjima babu komai, Salim addu'a kawai yake buƙata amma yana da kyau ita ma a ji da ita." Daga haka Mommy ta riƙe hannun Raihan gam suka fito duk in da suka gifta mutane kallonsu ake yi. Lokacin da su Mommy suka fito a lokacin aka gama sallarta Salim har an saka gawarsa a mota za a wuce da shi, wasu daga cikin masu rakiyarsa na cikin mota wasu na kan mashina wasu ma da ƙafa suke takawa. Ganin haka ya sa Mommy ta ja hannun Raihan suka koma da baya, sai da suka jima a tsaye mommy ta fahimci masu rakiyar gawar sun yi nisa sannan suka fito suka shiga mota suka wuce gida. Suna zuwa gida Raihan ta