Showing 108001 words to 111000 words out of 157890 words

Chapter 37 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

152

ka taɓa gagarata ba balle ka gagari ayar Allah. A wannan karon ba zan saurara maka ko na baki dama ba domin na lura kai zuma ne sai da wuta, zan ƙoneka idan ya so kowa sai ya huta." Huzaifa ya fara takawa a hankali sai kuma ya huyo ya sake kecewa da dariya sannan ya ce, "A wannan karon ba zan baka haƙuri ba ka yi duk abin da za ka yi Malam, amma na tabbata ba za ka taɓa hallaka ni ba. Na yi gawurtar da sai na futune ka kai da iyalinka, a da ban yi niyyar taɓa wani naka ba amma a yanzu ni da kai ɗan Halak ka fasa. Zan ganye daga jikin Huzaifa domin wanda ya kawo mana aikin bai cika mana alƙwarinmu ba, zai binne jariri sabuwar haihuwa da ransa ya aiwatar amma bai yanka mana farar jaka ba. Zan bar jikin takwarana amma ka sani ba wai na bar jikinsa kenan ba lokaci-lokaci zan riƙa kawo masa ziyara. Ita kuwa Raihan har abada ina tare da ita, ba za ta taɓe gujewa halwata ba domin ni ne mijinta na har abada." Huzaifa na gama maganar sai Malam Usman gani ya yi ya yanke jiki faɗi yana wani irin numfarfashi, da sauri Malam ya kira sauran yaransa da suke kula da marasa lafiya. Zuwan su keda wuya suka riski Huzaifa yana ta zabga atishawa, turaren habbatussauda aka yi masa sannan Malam ya shafa masa wasu magunguna. Sun jima a kan Huzaifa sannan ya dawo hayyacinsa, a hankali ya riƙa bin mutanen wurin da kallo, miƙe wa ya yi yana tangaɗi sannan da mamaki ya furta, "Su waye ku? Don Allah ku yi haƙuri kar ku cutar da ni wallahi na daina bin kowacce mace, kema da muka haɗu da ke tsautsayi ne." Malam ne ya ƙarasa wurin Huzaifanya ruƙo hannunsa sai da ya kai shi kan gado ya zaunar da shi sannan ya ce, "Huzaifa!" Malam ya kira shi da dakakkiyar murya, kallonsa Huzaifa ya yi yana waige-waige sai kuma ya sa hannu bibbiyyu ya dafe kansa haɗe fa faɗin, "Wash kaina." Da sauri Malam ya sa aka ɗauko wani turare aka turara masa sannan aka shaƙa masa wani a hanci tare da shafe masa jikinta da wani ruwan tofi. Lokaci ɗaya jikinsa ya saki ya faɗi yaraf can gefe yana sauke ajiyae zuciya da sauri, Malam ne ya sa aka kunna masa fanja saboda gumin da Huzaifa yake sharɓawa. Huzaifa ya jima a haka sannan ya ɗago yana sake ƙare wa mutanen wurin kallo, a hankali ya buɗe baki yana faɗin, "Su waye ku? Don Allah nan a ina nake?" Malam ya ƙarasa gabansa ya ce, "Huzaifa!" Da kallo Huzaifa ya dubi Malam yana shirin yin magana ya riski muryara Malam ya ci gaba da cewa, "Ko za ka iya fahimtar a ina kake yanzu." Kallon wurin Huzaifa ya sake yi ya ce, "Don Allah ka yi min rai kar ka halaka ni, wallahi duniya da lahira ba zan sake neman mata ba har abada wannan ma sharrin Shaiɗan ne." Kafaɗarsa Malam ya dafa ya ce, "Dube ni da kyau Huzaifa ka nutsu ka ji." Shiru Huzaifa ya yi yana bin Malam da kallo, kai tsaye ƙofa ya buɗewa su Baba suka shigo Huzaifa na ganinsu da gudu ya maƙale shi yana faɗin, "Don Allah ku zo mu gudu wallahi a taiku za ta jefa ni." Nan take Huzaifa ya sake rikice musu sai da Malam ya yi da gaske sannan ya samu ya koma kan fado ya zauna. Jan Mahaifin Huzaifa ya yi suka fita waje sannan ya dube shi yana faɗin, "Alhamdulillah na san duk abin da yake faruwa kuna ji sheɗanin nan ya fita daga jikinsa, amma duk da haka yana buƙatar kulawarmu domin bai gama dawo wa daidai ba. Za a bar shi ya zauna a nan na tsawon mako guda mu ga yanayin yadda jikin za yi, shi kuma wannan karon ba zai taɓa tsallake wa ba domin na lura taƙadari ne don haka duk in da ya shiga zan saka a kamo shi kuma duk inda ya shiga zai an nemo shi na ƙone shi ƙurnus." Baba gyaɗa kai ya yi cikin farinciki don tuni ya sanarwa da Mahaifiyarsa halin da ake ciki suma sai murna suke yi, Daddy ne ya ƙaraso wurin a kunyace ya dubi Baba ya furta, "Don Allah ka yi haƙuri ku gafarce ni akan abin da ya faru. Wallahi na shiga ɗimuwa akan wannan lamarin don haka nake ganin kamar Huzaifa ne ya tafi mini da ƴa ashe ba haka ba ne." Baba ya dubi Daddy ya ce, "Ka yi abin da kowanne uba zai iya aiwatarwa don haka ja daina ba mu haƙuri, Allah ya kiyaye gaba ya katange mu daga kaidi da hatsabibancin shaiɗanun nan." Lokaci ɗaya suka amsa da Amin.

Kafin wani lokaci tuni labarin dawowar Huzaifa ta watsu a cikin danginsu, ƴan uwa da abokan arziƙi sai zuwa duba shi suke yi suna yin Allah sanya alheri. Abin ba iya nan ya tsaya ba har zuwa kafafen watsa labarai haka ka yi ta maganar cikin ta'ajibi don har sai da ƴan jarida suka ji ta bakin Daddy da Baba suka watsa wa duniya. Daga ƙarshe wasu mutanen har ganu suke kamar ƙarne wannan sharhin abin da ta faru, har sai da Ƴan jaridu sula sake hira da Malam Junaid Malunfashi ƙwararran masani ne kan abin da ya shafi harkar aljanu, bayani ya yi sosai na kusan minti ashirin dangane abin da ya shafi jinnu da al'amuransu. Daga ƙarshe ya shawarci al'ummma da su riƙe azkar na safe da yamma, su yi riƙo da addu'a domin takobin muminu ce. Haka Huzaifa ya ci gana da samun kulawar da ta kamata har ya shafe tsawon waɗannan kwanakin, kuma cikin ikon Allah jikinsa ya warware hatta surutan da yake yi ya daina. A ranar da Huzaifa ya ƙarasa warware a ranar ne abokinsa Abubakar ya wayi gari da hausa tuburan don shi har yagar nama jikinsa yake yi yana cewa zai ci, tun abokansa na bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sun taimaka masa har suka gaji daga ƙarshe suka tattara shi suka kai shi garinsu, da yake iyayensa tsofaffine kuma ba su da ƙarfi ya sa suka gagara kula da shi ƙarshe ya ɓige da yawo akan bola. Ranar da Huzaifa ya cika kwana takwasa a wurin Malam ne aka sallame shi sakamakon ya warke garau babu wani abu da yake damunsa.

Raihan ta warware raunukan jikinta duk sun warke, kuma tun da Kabiru ya samu labarin dawowar Raihan kusan kullin sai ya kira wayar mommy ya ce a bawa Raihan zai dubata. Mommy har mamakin wannan kulawar da Kabiru yake bawa Raihan yake yi amma da ta tuna irim ɗawainiyar da Daddy yake yi masa sai take ganin kamar saka alheri da alheri ne Kabiru yake yi kuma hakan ba ƙaramin faranta ransu yake yi ba. Su Baba faɗa suka yi wa Huzafa sosai game da abubuwam da yake aikawata, ya yi nadama sosai don haka ya ji aikinma gabaɗaya ya fice masa da kai. Sai da Abokan aikinsa suka ƙarfafi gwiwarsa sannan ya koma bakin aiki, kuma kafin tafiyarsa sai da aka ɗaura masa aure wara cousine sister ɗinsa da sakamakon dama ya jima yana son ya yi mata magana tun a lokacin gaya, amma sai a wannan lokacin Allah ya yi don haka ba a ɗauki lokaci ba dudu wata uku aka tsayar lokaci na cika aka ɗaura musu aure ya tafi da matarsa. A wannan lokacin tuni Kabiru ya dawo garin Kano sai dai a lokacin da zai baro garinsu Matarsa na ɗauke da cikin wata biyar don har ya fara fitowa, a da baya jin komai game da Maryama amma ɗan zaman da ya yi lokacin rasuwar Mahaifinsa ya ƙara musu shaƙuwa tsakaninsa da ita, sosai ya riƙa jin kewar matarsa lokacin da zai taho sannan ga wani irin ƙaunarta da yake ji ita da abin da yake cikinta. Tun bayan da komawar Raihan gida Daddy ya samu Malamai game da auren Raihan da aka ɗaura, nan take suka nusar da shi auren Raihan babu shi domin an yi shi ne a cikin rashin sani hasalima ba shi ne ainihin mai wannan siffar ba kuma ba jinsinta ba ne. Don haka babu wurin da aka halatta aure tsakanin jinsin mutum da aljani, da farko iyayen Huzaifa sun so a tambayi Raihan ko za ta amince ta auri wannan Huzaifan idan ya so sai a ɗaura musu aure. Daddy ne ya dakatar da maganar a take don cewa ya yi ko Raihan ɗin ba zai gaya mata ba, saboda ba za ta iya rayuwa da Huzaifa saboda a kodayaushe ta gan shi zai riƙa tuna mata da wancen. Tun da ko daga baya ita kaɗai idan ta dubi hotunan bikinsu sai ta riƙa ganin suna yi mata gizo, har ta kai ga hotunan kamar sun fara tsorata. Ba shiri ta ware rana ɗaya ta ƙone su gabaɗaya, waɗanda suke cikin wayarta da na Mommy suma duka aka gone. Rahan haka ta ci gana da kasuwancinta gwanin birgewa saboda da farko ne ta saka wa ranta damuwa amma daga baya duk ta watsar ta fauwala wa Allah lamuranta. Sai dai babbaj abin da ya fi nuƙurƙusar zuciyarta bai wuce tunanin Al'amin da take kwana take tashi da shi ba, tun tana iya danne wa har ta samu Mommy da maganar don a lokacin ba ta da aiki sai na mafarkinsa da tunanin suna gudanar da rayuwa cikin farinciki da annushuwa. Wannan tunane-tunane ne ya sake rura wutar da ke cikin zuciyar Raihan, ba a ɗauki lokaci ba ta zabge ta rame ita kaɗai ta rasa abin da yake damunta. Ga shi tana fargabar tarar Mommy ta gaya mata don bata san yadda za ta ɗauki maganar ba, watarana tana zaune da tunanin Al'amin ya addabi rayuwarta miƙe wa ta yi ta ɗauki key ɗin motarta. Tun bayan bikinta da Huzaifa ba ta sake fita ira kaɗai ba sai ranar, Inno na ganinta da mukullin mota ta ƙanƙance ido tana sannan ta ce, "Raihanu ni kam wannan makullin gidan abinci ne?" Raihan ta ɗago shi ta nuna wa Inno sannan ta ce, "Mukullin motata ce fita zan yi." Da sauri Inno ta zaro ido waje ta furta, "Fita ina ban gane ba." Tura baki gaba Raihan ta yi, ta yi ƙasa da murya ta ce, "Idan na je na dawo kya gane." Da sauri Inno ta ta shi ta tare bakin ƙofar tana kiran Mommy, nan take ta ƙaraso tana tambayar ko wani abu ne ya faru. Inno ta nuna Raihan ta ce, "Gata nan wai fita za ta yi, wallahi ki shaida Zainabu idan waccen hatsabibin ya sake ɗauke ta ko ƙyallin hawaye ba za ki gani a idona ba." Mommy na shirin yin magana Goggo ta ce, "Wallahi balle bikin ƴar gidan Safare gare ni ko ƙarƙashin kukar Bulukiya ya kai ki babu abin da zai hana ni tafiya Albasu biki." Mommy ta dubi Raihan ta ce, "Ina za ki je?" Idanun Raihan suka ciko da ƙwallah kafin mommy ta yi aune sai ga hawaye na zuba." Baki suka riƙe gabaɗaya suna kallonta, Goggo ta tafa hannuwa cike da takaici ta ce, "Raihane kin ji kunya gwandamemiya kamar ke kina wannan sakarcin daga tambaya." Raihan kukan da take yi fargabarta kar ta hana ta fita don haka ta tattaro jarumanta ta goge hawayen ta ce, "Mommy shop zani fa komai na maka up ɗina ya ƙare." Mommy jim ta yi sannan ta ce, "Ba na son ki riƙa fita ke ɗaya Raihan gaskiya ki kira Daddy idan ya ce ki fita shi kenan." A nan take Raihan ta kira Daddy ta sanar da shi da farko bai amince ba sai daga baya. Raiham kamar za ta yi tsalle ta tashi sama saboda sauri, don lokacin da ta fita mommy har kallonta ta yi tana mamakin saurin da take yi. Amma da yake ba fita take ba, sai ta yi tunanin ko ɗokin fita ne take yi.

Sai da ta fara zuwa store ta siyo kaya shafe-shafe sannan ta ɗauko hanyar Waraka Islamic store, tana parking ƙirjinta ya buga sakamakon hango shi da ta yi a barandar asibitin. Ajiyar ta sauke a hankali ta furta, "Allah ka cika mij burina wanda yake alkairi a gare ni." Cikin shauƙin so ta nufi wurin da yake zaune a kan kujera, tana ƙarasawa ta ɗan yi gyaran murya sannan ta yi sallama sakamakon ta same shi yana yin waya. Sai da ya ɗago ya kalleta sannan ya gyaɗa mata kai ya furta, "Ok Ur hightness i wll call you later..." Daga can ɓangaren aka katse shi da cewar, "Baby ba dai wata beb ɗin ka yi ba?" Lumshe ido ya yi sannan ya furta, "No wara patient ce da Daddy bawa magani." Amsa ta bashi sannan ya furta, "Na yi kewarki dear yaushe za ku kawo ne, gaskiya zan biyo ki garin Dutsen nan."


Afwan ban tace shi i ba.


Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 0706 206 2624
41


Tamkar wacce aka watsa wa ruwan zafi haka Raihan ta ji kalaman Al'amin a cikin zuciyarta, ƙwallah ce ta ciko idonta zuciyarta na tururi. Tana cikin wannan yanayin riski muryar Al'amin yana faɗin, "Take care Hayaty" Sai da ya saka wayar a aljihunsa sannan ya kalli Raihan ya furta, "Wa'alaikis salam." Murmushin yaƙe Raihan ta yi ta ce, "Abba fa?" Ɗan jim ya yi sannan ya ce, "Daddy bai shigo ba sai an jima." Raihan duk ji ta yi zuciyarta babu daɗi saboda yadda Al'amin ya tarbe ta tamkar bai taɓa saninta ba, duk da sun jima ba su haɗu ba amma a ganinta ba zai ce bai gane ta. Tana nan tsaye Jamila ɗaya daga cikin ma'aikanta Malam ta ƙaraso ganin Raihan ya sa ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin, "Raihan yau ke ce da kanki." Raihan ta sakar mata murmushi sannan ta ce, "Wallahi na zo karɓar turare wurin Abba ashe baya nan." Kasancewar ma'aikanta wurin duka sun san Raihan ya sa Jamila ta furta, "Ai kuwa bai ƙaraso ba sai zuwa anjima bari na baki kujera ko za ki shigo ciki?" Murmushi Raihan ta yi ta ce, "A'a Aunty Jamila nan ma ya isa." Kujera Jamila ta kawo wa Raihan ta zauna, sai da suka shafe wasu mintuna a zaune ta riski muryar Al'amin yana faɗin, "Ya jiki?" Sai da ta kalli hagu da dama ta juya bayanta don neman da wanda yake maganar amma bata ga kowa, saboda a ƙalla sun shafe kusan minti goma sha biyar ba tare da ya furta mata komai ba, kuma a yananyin yadda ya yi maganar sai ka rantse ba da ita yake ba. Murya a sanyaye Raihan ta furta, "Da sauƙi na gode." Bai tanka mata ba kuma bai sake ɗago wa ya kalleta ba, sai dai tun zaman Raihan gabanta yake faɗuwa har ta gagara saita kanta ban da kallonsa babu abin da take yi tana jin zuciyarta na yi mata zillo a kansa. Babban abin da ya fi ɓata mata rai jin yadda yake gaya wa wata macen kalamai masu daɗi, saɓanin ita da kallon arziƙi bata samu a wurinsa ba. Tana cikin wannan nazarin ta riski motar Daddy ta ƙaraso harabar wurin, miƙe wa ta ga Al'amin ya yi ya ƙarasa wurin Motar Malam sannan ya karɓo jakar hannunsa, tun daga wurin motarsa ya hango Raihan a zaune tana ganin sun nufo wurinta ta miƙe tana yi wa Malam murmushi, yana ƙaraso wa ya faɗaɗa fara'arsa yana faɗin, "Ƴar gidan Abba ba dai tun ɗazu kike nan a zaune ba." Sai da ta russuna har ƙasa ta gaida Malam sannan ta amsa masa, "Eh to zan kai minti Arba'in zuwa hamsin Abba." Kallon Al'amin ya yi ya ce , "Amma dai ka fiye sakarci Aminu a madadin ka tambayeta maganin da ta zo karɓa amma sai kawai ka barta a zaune, da ban ƙaraso da wuri ba fa?" Al'amin ya sosa kai sannan ya ce, "Daddy ai bata ce min magani ta zo karɓa ba na ji dai tana gayawa Jamila." Takaici ne ya kama Malam don haka ya yi tsaki yana faɗin, "Allah ya kyauta Raihan mu je ciki kin ji." Ba musu Raihan ta bi bayan Malam suka shiga ciki, wayar Malam ta fara ringing sai da ta zauna sannan ya ɗauka bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa aka yi; Raihan ta ji Malam ya ci gaba da cewa, "Insha Allah a gobe ne Yaya da kimanin ƙarfe biyun rana, a'a gidansu yarinyar a unguwar Karkasara yake. Ai idan mun je bai fi a tsayar da ranar auren nasu wata huɗu zuwa biyar ba, sai dai gobe insha Allah ma ƙarasa maganar." Gaban Raihan ne ya ci gaba da lugude jikinta har rawa yake don ita kanta ba ta san abin da yake damunta ba. Ji take kamar ta tambayi Malam auren wa za a saka amma ko kaɗan ba za ta iya ba, yawun bakinta ne ya yi mata ɗaci ga wani irin sarawa da kanta yake yi. Ba ta yi aune ba ta riski muryar Malam na yi mata magana, "Ƴar gidan Abba me kika zo karɓa maganin sha ne ko turare, sai da ta mayar da ƙwallar idonta kai a ƙasa ta furta, "Abba turare da garin habbatussaauda ne babu." A jikin wani ƙaramin kati ya rubuta mata da yake Raihan ba baƙuwa ba ce a wurinsa ya sa ya rubuta suna da shekarunta ba tare da ya tambayeta ba, miƙa mata ya yi ta yi masa godiya har ta miƙe ya kira sunanta. Cak ta tsaya wuri ɗaya jiki ba ƙwari ta juya tare da amsawa, kujera ya nuna masa ya ce: "Zauna!" Ba musu Raihan ta zauna tana sake sauke kanta ƙasa don bata son ya fahimci halin da take ciki, sunanta ya sake kira sannan ya ci gaba da cewa, "Me yake damunki? Ko akwai wata matsalar ne Raihan?" Kamar mai jira sai kawai Raihan ta fashe da kuka, shiru ya yi sai da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login