Showing 141001 words to 144000 words out of 157890 words
da saki uku ka yi, kuma duk mai son aurenta da kai sai dai ya yi haƙuri. Cikin fa ya zube Hubby yanzu wannan ma mun yi asararsa?" Sumayya ta fashe da kuka. Tausayinta ne ya kama shi ya kwantar da murya ya fara lallashinta, kuka Sumayya ta saka sai da ƙyar ta yi shiru. Mahaifiyarta na dawowa ya ce su tafi shi zai kwana da ita a asibitin, yadda ya ga rana haka Al'amin ya ga dare don tunanin Raihan ne ya riƙa yi masa kai-kawo a zuciya, tuno waccen rashin lafiyar ta Sumayya ya yi da irin ɗawainiyar da Raihan ta riƙa yi, haka ya riƙa saƙa da warwara har gari ya waye.
Washegari da safe bayan su Daddy sun shirya kai tsaye Waraka Islamic Chemist suka tafi, suna yin parking ɗin motarsu ta Malam na shigowa. Sai da ya yi parking ɗin motarsa sannan ya fito suka gaisa suka wuce ciki, ma'aikatan wurin ne suka riƙa gaishe su cikin girmamawa su Daddy suna amsawa cikin sakin fuska. Duk wani abin buƙata da gari ya waye an yi wa Kabiru, Malam ne kan gaba ya tura ƙofar ɗakin ya shiga baƙinsa ɗauke da sallana. Ga mamaki sai ji suka yi ya amsawa Malam, Baffa ya saki baki cike da mamaki sannan ya yi masa daƙuwa yana cewa, "Hai amma dai Kabiru ka cika shakiyyin bawa, saboda Allah tuni Ibrahim ya wuce ka ke wahalar da mu?" Malam ya yi murmushi yana kallon Kabiru ya ce, "Kabiru yana nan sai dai za ku ɗan ba mu wuri ina son tattaunawa da shi." Babu musu su Daddy suka ja da baya suka koma kan kujerun da ke reception amma duk abin da Malam yake faɗa suna jin sa. Zaman su babu daɗe wa Al'amin ya ƙarasa sai dai ganin Daddy ba ƙaramin nauyi ya yi masa ba, har ƙasa ya gaishe da su a kunyace sannan ya wuce ɗakin da Kabiru yake don zuwansa gida kenan Ammi ta ce Malam ya bar sallahu ya same shi a office. Yana shiga Malam ya nuna masa kujera a gefen gadon Kabiru, Al'amin ya zauna sai dai yana son tambayar Malam dalilin kiransa ganin babu wasa a fuskarsa ya sa ya ja bakinsa ya tsuke, sai kallon Kabiru yake yi yana jinjina hatsabibanci irin na jinnu, don babu abin da ya bambamta Kabiru da mutumin da ya ga ya fito daga ɗakin Raihan. Malam ne ya kalli Kabiru ya ce, "Assalamu alaikum. Bawan Allah da wa nake magana?" Kabiru ya amsa masa sallama sannan ya ce, "Kana magana da Ibrahim Alƙasim Bn Muhammad Mustafa." Malam ya jinjina kai yana faɗin, "Malam Ibrahim me ya sa ka shiga tsakanin bawan Allahn nan da iyalansa har na tsawon wasu kwanaki kuma ba tare da ka furta koda kalma ɗaya ba." Kai tsaye Ibrahim ya furta, "Saboda ba na son buɗe baki a gaban Mahaifiyarsa don na san matuƙar na yi magana za ta roƙe ni akan na bar abin da na furta zan aikata, ni kuma ina ganin girmanta ba zan iya yi mata musu ba." Malam ya ce, "Amma ba ka gani kamar akwai shiga haƙƙi?" Ibrahim ya furta, "Ba wani shiga haƙƙi domin abin da aka yi masa ne ban ji daɗi ba kuma alƙwari na ɗauka ba zai tashi a banza ba." Nan take Ibrahim ya zayyanewa Malam dangantakarsa da dalilin da ya sa ya ce sai ya hukunta Huzaifa, sai da ya gama jawabinsa sannan Malam ya yi murmushi ya ce, "Masha Allah, Ibrahim ba Kakanka ba ne Mustafa shi ne ya riƙe Limanci a yankinku tsawon shekarun baya da suka wuce." Da mamaki Ibrahim ya gyaɗa kai ya ce, "Tabbas haka ne don tun ba a haife ni ba haka Mahaifina ya ba ni labari." Malam yana shirin yin magana Ibrahim ya ci gaba da cewa, "Don Allah Malam karka dakatar da ni domin abin da Huzaifa ya aikata rashin imani ne, na yi maka alƙwari ba zan sake hana shi magana ko jinkiri a jikinsa ba kuma kana nan sai na kawo maka Huzaifa da yardar Allah." Malam ya ce, "Amma wani hanzari ba gudu ba, akwai wasu da suka tafi nemo min shi..." Malam bai ƙarasa magana ba Ibrahim ya katse shi da cewar, "Babu damuwa sai na taimaka musu saboda Huzaifa hatsabibin gaske ne, kuma dama akwai tsohuwar rigima tsakanin Kakana da Kakana ka ga kenan akwai ƴar tsama." Malam ya yi jim sannan ya ce, "To shi kenan Allah ya sa mu ji alheri." Ibrahim ya amsa da Amin. Malam na yin sallama da Ibrahim sai Kabiru ya faɗi gefe jikinsa na karkwarwa kamar mai jin sanyi, a hankali ya yunƙura ya tashi zaune yana ƙarewa wurin kallo. Malam ne ya ƙwallawa su Daddy kira suka shiga, Kabiru na ganin Daddy ya ce, "Alhaji yaushe na zo nan Ina su Inno wuro." Baffa na shirin yi masa magana don kar ya fahinci lalurar da ta same shi, Malam ya yi masa bayanin duk abin da yake faruwa da abin da Ibrahim ya faɗa dangane da neman Huzaifa. Jikin Kabiru ne ya yi sanyi haka kawai ya ji yana kewar abokinsa kuma ɗan'uwansa Ibrahim, ga wani irin farinciki da ya ji musamman da aka ce ga rawar da zai taka dangane da Huzaifa wanda yake son za me musu ciwon ido. Al'amin yana zaune yana kallon ikon Allah, Malam ya dube shi cikin takaici ya ce, "Tashi ka ba ni wuri dama abin da na kirawoka kenan kuma an yi an gama." Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka Al'amin ya fice daga ɗakin, haka kawai ya ji yana jin haushin kansa da kansa.
Kwanan Kabiru ɗaya Malam ya sallame shi suka wuce gida, shi kuma Baffa a washegarin ranar da aka sallami Kabiru ya wuce garin Shanono. Jikin Sumayya ya yi sauƙi sosai har an bata sallama don haka cikin dabara Al'amin ya ce mata zai yi tafiya don haka tun da gidan ita kaɗai ce ta wuce gida kafin ya dawo, ba don ta so ba haka Sumayya ta bi su Mami suka wuce can gidansu. Kamar yadda Malam ya bashi umarni haka Al'amin ya koma kwana a gida shi kaɗai Sumayya na gidansu, tunanin duniya ya fara cika masa ƙwalƙwala kuliin sai dai su yi waya shi da ita.
Raihan ta miƙawa Allah lamuranta don ba ƙaramar nasiha Mommy ta yi mata ba, haka ya sa ta fara ƙoƙarin fitar da duk wata damuwa daga zuciyarta, don ta fahimci duk irin nasihohin da take yi mata kuma sai a lokacin ta gane ba ƙaramar wauwata ta yi ba, domin a tunaninta idan ta auri Al'amin shi zai wanke mata duk wata damuwa da take ciki. Ɗakin saukar baƙi aka gyarawa Kabiru yake zaune a ciki saboda Malam ya ce a bari ya kwana biyu a nan tukunna. Wannan Dalilin ya sa Daddy ya turawa su Inno wuro da kuɗin mota kamar yadda ya yi alƙwari a baya zai dawo da su ya sa suka taho garin Kano. Tun kafin su ƙaraso Daddy ya sa aka gyara musu sauran ɗakunan saukar baƙin da suke kusa da na Kabiru, lokacin da su Inno wuri suka ga wurin da Daddy ya ba su har da kukanta saboda Farinciki. Shi kansa Kabiru har da ƙwallarsa yana yi wa Daddy godiya, don ma Daddy ya tsawatar masa akan baya son yawan godiyar da yake yi masa. Tun dawowarsa gidan yake ganin Raihan sai dai ya lura tana cikin matsananciyar damuwa, ya yi mamakin yawan kwanakin da ta ɗauka a gidan yana son sanin dalili amma yana tsoro, don tun da ta yi aure yake yin baya-baya da duk wata alaƙa da za ta shiga tsakaninsu. Su Mommy hannu bibbiyu suka rungumi su Inno wuro sai Maryama da jaririnta, lokacin da Raihan ta ga jaririn hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba. Tana son ta samu Kabiru da maganar tana ganin kuma kamar bai dace ba, don haka ta bar abin a cikin zuciyarta. Satin su Inno biyu da dawowa gidan Daddy Malam ya kira Daddy ya haɗa shi da wani yayan maƙocinsa Sarkin ruwa na garin wudul, Daddy ne ya sake yi masa bayanin yanayin Jaririn Maryama nan take ya buƙaci da su je gidan ya gan shi. Lokacin da suka je a harabar gidan suka tsaya Maryama ta fito da Sadiq a hannunta, Sarkin ruwa na ganinsa ya jinjina kai ya furta, "Yarinya wannan ba ɗanki ba ne." Hawaye ne ya ciko idonta don ita kanta ta san kowaye ya ga yanayinsa ya san ba jininsu ba ne. Gudun kar a saka mata wasu-wasi ya sa Sarkin ruwa ya ce ta kira har Mahaifiyar Kabiru don zai je bakin ruwa za su ga abin da zai yi masa. Babu musu ta fito suka shiga motar Malam za su ɗauki hanya tun ba su fita daga layin su Daddy ba jaririn ya riƙa mimmiƙewa sai gani suka yi yana kakari jikinsa ya yi laƙwas numfashinsa ya ɗauke. Sarkin ruwa na ganin haka ya yi murmushi ya ce, " Ina ruwan Lurzu, Ya san ba zai ji da daɗi ba kun ga ya karaya har ya fice daga jikinsa, yanzu abin da za a yi ku binne shi ke kuma yarinya Allah ya baki wani mai albarka." Maryama ta saka kuka saboda ko ba komai sun ɗan shaƙu da shi, Malam da Sarkin ruwa ne suka wuce su kuma Daddy ya yi gida da su. Kamar yadda Sarkin ruwa ya faɗa Kabiru da kansa ya je ya binne shi sai yake jin sa sakayau kamar an cire masa ƙaya.
Sumayya tun tana yi wa Al'amin kawaice har ta same shi da maganar komawarta, don ta gaji da zaman gidansu. Shi kuma tun yana yi mata hanya-hanya har ta fahumci akwai abin da yake ɓoye mata don haka wata ranar Alhamis da suna hira ya fito ya gaya mata irin hukuncin da Malam ya yanke, don shi kansa lamarin ba ƙaramin damunsa yake ba tun da har sun doshi wata basa tare ga wata irin kewarta da yake ji. A ɓangare ɗaya kuma har lokacin ya kasa cire tunanin Raihan a zuciyarsa har lokacin ji yake kamar ya zalinci rayuwarta. Shi kuma Malam har lokacin ya ƙi bada fuska don ko gaishe shi ya yi daga ita ba sa doguwar hira balle ya saka ran zai sakar masa fuska, ranar da Ammi ta yi masa maganar fata-fata ya yi mata don sai da ita ma ranta ya ɓaci. Lokacin da Sumayya ta gama jin Al'amin surutai ta riƙa yi kala-kala har tana cewa gara ya saketa ko ta huta da yawo da aurensa akanta. Wannan lamarin ya sake dagula lissafin Al'amin don ko abincin kirki baya ci, duk ya fige ya lalace ya rame.
Watan Kabiru guda da dawowa gidan Daddy Ibrahim ya dawo jikinsa, yanayinsa da maganganunsa ya sa Maryama ta fahimci haka don haka ta sanarwa da Inna wuro, ita kuma Inna wuro ta sanar da Mommy. Nan take Mommy ta kira Daddy ta gaya masa don tuni ya fita aiki, da yake har lokacin Kabiru bai koma bakin aiki ba. Daddy na kiran Malam ya sa motar office ɗin su ta zo har gida, wasu daga cikin ma'aikatansa suka tafi da shi har office ɗin Malam. Kusan tare suka ƙarasa da Motar Daddy don yana gama waya da Malam shi ma ya ɗauko hanya, a galabaice Ibrahim ya fara magana."Alhamdulillah Malam mun yi nasara, sai dai ba mu samu damar kama Huzaifa ba don tun kafin zuwanmu Kakansa ya sa shi ya tsere. Amma mun kamo Kakansa kuma mun baje tsibirinsa mun hukunta na hukuntawa mun kashe na kashewa, sai tsiraru da suka karɓi kalmar shahada." Cike da farinciki Malam ya furta, "Alhamdulillah." Ibrahim ya ci gaba da cewa, "Yanzu haka muna tare da Kakansa da wata mace wacce ta roƙi alfarmar mu kawota za ta roƙi gafarar Raihan."Malam ya ce, "Ikon Allah muna ji." Murya na rawa Mugaza ta ce, "Ni dai sunana Mugaza amma Raihan da iyayenta sun fi sanina da Intisar..." Nan take Mugaza ta zayyane musu duk wata alaƙarta da Raihan da yaudararta da yi har zuwa lokacin da Huzaifa ya gano sannan ta ɗora da cewa, "Na kai Raihan Ƙungiyar tsafinmu ne don na bayar da jininta saboda mijina na mutuwar sonta ni kuma kishi ya rufe min ido, saboda matan bil'adam sun fi mu kyau da kyawun siffa nesa ba kusa ba. Da na kaita ashe sa'a ce tare da ita kuma da yake da sauran kwananta a gaba sai su Abar bauta suka gano tana da muhimmanci a cikin ƙungiya. Yanzu haka Huzaifa ya kashe mini ƴaƴana duka saboda na gano maɓoyar ɗan da Raihan ta haifa masa na kashe shi, kuma ya kashe su abar bauta ni ma yana ƙoƙarin kashe ni muka ji alamun zuwan baƙin nan, to da yake dama Jabbul-ƙasi ya san da labarin zuwansa kuma ya ba shi ɓoyayyayun sirrika sai ya ɓace daga wurin mu." Gaɓoɓin jikin Daddy ba ƙaramin sanyi suka yi ba, kusan mutuwar zaune ya yi yana mamakin maganganun da Intisar ta faɗa. Jabbul-Ƙasi ne ya fara magana shi ma cikin gadara duk da a wahale yake ya furta, "Jikana ba zai taɓa kamuwa ba a wurinku don haka na bada kaina koma meye ku yi min domin kuwa dama tsufa ya cimmi ni mutuwata ta kusa." Takaici ya saka Malam ya sa aka yi turare Habbatussauda sannan ya fara yi musu ruƙiyya, ganin sun galabaita ya sa Malam ya tambayi ta ko za ta musulunta amma dukkansu suka ƙeƙashe ƙasa suka nuna matuƙar suka karɓi addinin musulunci sun zubda ƙimarsu. Ita kuma Mugaza ta ɗora da faɗin gara ma Malam ya ƙoneta don ta tsani musulunci kuma gara kisan da Malam zai yi mata akan na Huzaifa. Malam bai saurara musu ba ya ci gaba da karatu duk yadda suka kai ga taurin kai sai da suka galabaita suka fara roƙon Malam cikin ɗimuwa. Bai saurara musu ba ya ci gaba da yi har sai da ya ƙone su ƙurmus. Cike da farinciki Malam ya furta, "Alhamdulillahi." Sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin. Su Daddy ba ƙaramin farinciki suka yi da jin an ƙone su Mugaza don haka suka ci gaba fatan shi ma Huzaifa Allah ya ba su sa'ar kamo shi a ƙone shi kowa ya huta.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
50
Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya Kabiru ya warke garau ya koma bakin aikinsa, a hankali ya fahimci duk abin da yake faruwa don a wannan lokacin ya gano auren Raihan ne ya mutu har ta dawo gida da zama. Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗe wa Al'amin don ji ya yi duniyar ta yi masa zafi ga takurar da Sumayya take masa don daga ƙarshe ma Mahaifinta ne ya kira Al'amin ya ce masa matuƙar yana son ci gaba da zama da Sumayya ya bashi sati guda ya je ya tafi da ita, idan ba haka ba sai dai ya sakar masa saboda ba za ta ci gaba da zama ba tare da ta san matsayinta ba. Tashin hankalin da ya sake zugar da shi har yake tunanin hanyar da zai samu Mahaifinsa da maganar, a ɓangare ɗaya kuma ga tunanin Raihan ya damalmala zuciyarsa har ji yake zuciyarsa na ingiza shi akan ya je ya nemi yafiyarta wataƙila idan ta ce ta yafe masa zai daina jin damuwar da ya yi da ita a zuciyarsa. Da wata safiyar Juma'a ya je gidansu ya samu Mahaifiyarsa ya sanar mata duk abin da yake faruwa dangane da maganar mahaifin Sumayya, Ammi ba ƙaramin tausayinsa ta ji ba sai dai ita kanta tana fargabar samun Malam ta yi masa magana don wancen karon bata ji da daɗi. Kallonsa ta yi ta furta, "Shi kenan ka je Al'amin zan samu Mahaifinka da maganar." Miƙe wa Al'amin ya yi har ya fara tafiya ya juyo ya ce, "Amm dama Ammi na ce..." Kallonsa ta yi ta ce, "Akwai wani abu ne?" Sunne kai ƙasa ya yi ya ce, "Wallahi Ammi na zalinci Raihan, gani nake kamar na je neman yafiyarta..." Da sauri Ammi ta katse shi da cewar, "Kai da bakinka kake faɗin ka zalinci Raihan Al'amin? Tabbas Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Shi ya sa ba a wulaƙanta ɗan'adam a rayuwa duk ƙasƙancinsa domin baka san baiwa da martabar da Allah ya yi masa ba. Yarinyar nan ta nuna maka soyayya a duniyar nan amma ka yi amfani da wannan damar ka riƙa cusguna mata, ai shi kenan sai ka je idan ka samu ta saurareka to, idan baka samu wannan damar ba shi kenan. Ka ga wannan sai ya zama izina a gare ka domin ɗan'adam duk yadda yake yana da daraja." A hankali Al'amin ya fara tafiya yana zuwa bakin ƙofa suka haɗu da Malam, gaisawa kawai suka yi Malam ya fahimci yana cikin matsananciyar damuwa. Yana shiga cikin dabara Ammi ta sanar masa abin da yake faruwa da Al'amin, murmushi ya yi ya furta, "Yaro man kaza. Shi kenan Allah ya kaimu ranar Litinin sai ya je ya tafi da ita. Ita kuwa Raihan yanzu ai baida iko da ita ruwanta ne ta saurare shi ko akasin haka. Wallahi ni na san dama haƙƙin yarinyar nan ba zai bar shi ba, Allah ya sa dai ta saurare shi." Ammi ta jinjina kai don ta fahimci kamar Al'amin ya faɗa tarkon son Raihan sai dai bata gaya wa Malam ba don ta san ba ƙaramin faɗa zai yi ba. Da daddare Al'amin ya fi minti talatin a ƙofar gidansu Raihan sai ya yi kamar ya ƙwanƙwasa ƙofa sai ya wata zuciyar ta hana shi daga ƙarshe ya yi ta maza ya ƙwanƙwasa. Yana bugawa Auwalu ya leƙa yana tambayarsa, Al'amin ya aro jarumta ya furta, "Am na ce don Allah Raihan za ka kira min." Da mamaki Auwalu ya ce, "Malam Raihan fa?" Al'amin ya ce,