Showing 60001 words to 63000 words out of 157890 words

Chapter 21 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

167

"Ya isa haka Malam mu je zan shiga." Matsa wa Malam ya yi sannan Raihan ta fito jiki ba ƙwari don Malam ya gama sagar da duk wani kuzarinsa. Kallon titi Raihan ta yi ta hango wata babbar motar da alama cike take da fetir, kukan kura Huzaifa ya yi ya faɗa kan tsakiyar titin. Don yanda ya ayyana wa ransa da ya bar jikin Raihan gara ya yi sanadin da za ta mutu, idan ya so kowa ya rasa.


Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn ta wannan lambar.0706 206 2624

21


Malam Usman da Daddy kusan a tare suka yi dirar mikiya a gaban Raihan, da sauri Daddy ya riƙe ta a gigice yana faɗin: "Raihan titi ne fa." Da wata irin murya mai ban tsoro Raihan ta dube shi idanunta suka ƙara firfitowa ta ce, "Ni ba ƴarka Raihan ba ce." Malam Usman ya kama hannun Raihan a fusace ya fisgota gefe, duk yadda Raihan ta so fisge wa ya gagara don haka Malam Usman ya ja hannunta har cikin ɗakin da suke kwantar da marasa lafiya. Kowanne ɗaki mutum biyu ne sai dai akwai ɗakin mutum ɗaya idan kana da buƙata, sai dai kowanne da tsarin yadda kuɗinsa yake. A ɗakin mutum ɗaya aka kwantar da Raihan, Malam Usman ne ya buƙaci a kulle ta a ɗakin ba tare da kowa ya shiga ba saboda gabatowar sallar magriba. Mommy gabaɗaya kuzarinta ya ƙare saboda lamarin ciwon Raihan kullin gaba yake yi, don haka ta jima tana addu'a bayan ta idar da sallar Magriba. Malam Usman bai buɗe ɗakin da Raiha take ciki sai da ya haɗa kayan magungunansa wuri ɗaya tare da ruwan addu'ar da yake ƙone jinnu. Shi da ma'aikatan wurin mata suka shiga wurinta tana zauna a ƙasa ta ɗaga kanta sama Tana ganin Malam Usman ta miƙe tsaye tana wurga masa mugun kallo, Malam Usman turare ya fara yi mata sannan ya ɗauko turaren miski tare da wani garin magani ya sake shaƙa mata sannan ya yi bismillah ya fara yi mata ruƙiyya. Wannan karan Huzaifa ya daɗe bai yi magana ba har sai da Malama Zainab ta ce, "Malam ina ga kamar baya jikinta fa." Malam Usman ya yi murmushi ya ce, "Malama Zainab kenan ya yi lamfa ne don ya shammaci hankulanmu, amma har yanzu yana jikinta. Kin san waye Jinnul-ashiq kuwa? Kin san me ake nufi da Zaijatu Jinnul-ashiq? Kina tunanin matar aljani daidai take da sauran mata? Sam ki sake hankalta domin matuƙar namijin aljanin soyayya ya auri macen bil'adama akwai aiki ja kafin a samu a rabata da shi. Duk wannan abin da yake yi iya taku ne, kuma ba zai yaudare ni ba don na kara da waɗanda suka fi shi saboda haka mu ci gaba da abin da yake gabanmu." Nan take suka ci gaba yi wa Raihan ruƙƙiya sai da suka kusa shafe awa ɗaya da rabi sannan Huzaifa ya fara magana cikin tsananin azaba. "Ya isa haka Malam zan fita daga jikinta wannan karon ba da wasa nake yi maka ba." Malam Usman ya ce, "Huzaifa ka yi mana wasa ka gani ai ga fili ga mai doki, yanzu tun wuri ka fice daga jikinta kafin na ƙarasa babbake ruhinka." Huzaifa ya sauke ajiyar zuciya a wahale ya ce, "Amma matuƙar ka raba ni da ita wallahi ba a yi mini adalci ba domin ba ƙaramar bauta na yi mata ba, yanzu kana nufin ta tashi a banza kenan." Malam Usman ya bashi amsa, "Dama garin banza ai a farau-faraun wofi yake ƙare wa, me ya sa baka zauna ka yi wa matarka wahalar ba? Raihan jinsinka ce da za ka bauta mata da aikin wahala?" Wannan magana ta Malam ba ƙaramin tunzura Huzaifa ta yi ba, a hassale ya dubu malam yana cewa: "Duk duniya babu macen da nake tsananin kishi kamar Raihan don haka ba zan taɓa bari wani ya raɓe ta ba, mahaifinta ma kulawar da yake bata wani lokacin ɓata min rai take don dai kawai na san babu aure a tsakaninsu ya sa ban taka masa burki ba." Daddy da yake ta waje ya ji abin da Huzaifa ya faɗa nan take ya hau raba idanu don ba ƙaramin tsorata ya yi da lamarinsa ba.

Ganin yana ɓata wa Malam lokaci ya sa ya ci gaba da ƙone shi da ayara Allah, faɗuwa Raihan ta yi a can gefe tana sauke ajiyar zuciya. Malam ya ji sautin wani tsoho ya fara magana, "Saboda me za ka riƙa azabtar min da jika babu gaira babu dalili? Da farko na yi kawaici don na san Huzaifa baya jin magana amma azabtarwar ta yi yawa ai. Kana ta iƙirari Huzaifa ya auri bil'adam ko me ya faru ba ku kuke ja ba? Idan matanku sun killace kansu za mu gansu mu yi sha'awa ne? Ko kuwa haka kawai sai mu auri macen da bata burge mu ba? Idan haka ne ai da gabaɗaya mun aure matan bil'adam. Ni na san waye Huzaifa farin sani, kuma ni na haifi mahaifinsa. Ni hatsabibin Aljanine har bil'adam ina basu kariya, amma tun da na ga Huzaifa ya dage akwai dalilinsa na shiga jikinta." Malam Usman ya mayar masa da martani, "Kenan kana ɗaure masa kar ya fita daga jikinta ko?" Kakan Huzaifa ya amsa da cewa, "Ban ɗaure masa komai ba amma ka yi nazari ka duba irin abubuwan da ƴaƴanku na bil'adam suke yi, kai ko a cikinku na san da babu hukunci maza da yawa sai sun riƙa afkawa mata a titina. Ba zan ɓata lokacina a nan ba domin ina da aikin yi yau zan kashe wani babban mutum a duniyarku, amma ka sani matuƙar aka kashe mini jika akwai mummunan mataki da zan ɗauka." Malam Usman na shirin yin magana Kakan Huzaifa ya matsa daga wurin. Malam bai saurara masa ba ya ci gaba da ƙone Huzaifa, cikin galabaita Huzaifa ya furta: "Dakata Malam na yi maka alƙawari matuƙar ka bar ni zan fita daga jikinta amma don Allah ka barni na sanar da kai abin da ya kaini jikinta." Malam Usman banza ya yi da Huzaifa sai da ya ga ya galabaita sannan ya rabu da shi ya ce, "Ina jin ka, a ina ka haɗu da ita?" Huzaifa ya sauke ajiyar zuciya a galabaice sannan ya ce, "Wata rana..."

TARIHIN SU MOMMY.

Malam Bala Shu'aibu shi ne ainihin cikakken sunan Mahaifin Mommy amma mutane da dama sun fi saninsa da Malam Bala Magini. Asalinsa ɗan garin Albasu ɗaya daga cikin ƙananan ƙauyukan da suke cikin garin Kano, ya taso su bakwai a gidansu amma shi kaɗai ne namiji a cikin ƴan uwansa duk mata ne. Mahaifinsu Malam Shu'aibu malamin makarantar tsangaya ne yana da almajira da yake koyar da su, wannan dalilin ya sa Mahaifin Mommy ya taso cikin da ilimin addini mai zurfi. Sai dai abu ɗaya mahaifinsu ya gindaya musu karatun boko, don ko kaɗan bai amince da karatun boko ba shi ya sa ƴaƴansa mata suna fara zama ƴan mata yake aurar da su. Malam Bala ya so karatun boko a lokacin da Mai garin Albasu ya kawo musu wannan ci gaban sakamakon gwamnatin jaha da ta gina musu ƙananan makarantun boko a cikin gari, mutane da dama ba su karɓi abin ba amma da Mai gari ya wayar musu da kai sai wasu daga ciki suka amince wasu kuma suka juya wa abin baya aciki har da Mahaifinsu Malam Bala Magini. Dole ƙanwar na ƙi ta sa ya haƙura da karatun ya kama na addini hannu bibbiyu, da ya fara zama saurayi sai ƙanin Mahaifiyarsa yake tafiya da shi wurin aikin leburanci. Tun bai iya ba har ya ƙware ya iya gine-gine kala-kala, a lokacin iya cikin garin Albasu kawai suke yin aiki amma daga baya sai Allah ya sa masa nasibi yake samun aiki har cikin garin kano.

Zinaru Sama'ila Mai kaba shi ne ainihin sunan Goggo ita ma ƴar garin Albasu ce, ita kaɗai ta taso a wurin Mahaifiyarta. Amma a wurin Mahaifinsu su goma ne da yake matan aurensa Uku, Mahaifiyar Goggo ita ce amarya ta yiyyi ɓari kafin cikin Goggo ya zauna sai daga baya Allah ya zaunar mata da cikin Goggo aka haifeta. Mahaifin su Goggo sana'ar Kaba yake a garin Albasu duk garin babu wanda bai san shi ba, ko daga tasha ka tambayi gidansu kai tsaye za a kaika cen. Ta yi karatun addini daidai gwarwado macece mai barkwanci, amma bata da san raini. Mahaifin Mommy ya haɗu da Goggo ne a makarantar mahaifinsa, sakamakon nan ne makarantar allon da Goggo take zuwa ita da sauran ƴan uwanta. Tun suna soyayyarsu a ɓoye har manya suka shiga magana daga ƙarshe aka tsayar da rana aka sha shagalin aurensu. Malam Bala Magini yana matuƙar nuna kulawarsa ga Goggo, haka suka ci gaba da zamansu cikin kwanciyar hankali, Goggo sai da ta shekara biyu sannan ta samu ciki tana cikin ta uku Allah ya sauke ta lafiya ta haifo Ɗanta namiji. Ba ƙaramin farinciki suka yi ba ranar suna aka saka masa suna Abubakar, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Abubakar na da shekara huɗu Goggo ta haifi ƴarta mai suna Hafsa, sai dai kafin suna Allah ya yi mata rasuwa. Rasuwa Hafsa babu wuya Goggo ta sake samun wani cikin bayan wata tara ta sake haifo ƴa mace aka saka mata suna Zainabu (Mommy) Daga kanta sai da Mommy ta shekara biyar sannan Goggo ta sake haihuwar ƴa mace aka mayar mata da suna Hafsa. Daga kan wannan hafsar Goggo bata sake haihuwa ba, haka suka ci gaba da kula da ƴaƴansu cikin rufin asiri duk da su ba masu kuɗi ba ne.

Bayan Wasu Shekaru.

Abubuwa da dama sun faru ciki har da mutuwar iyayen waɗannan bayin Allah, wato Goggo da Malam Bala Magini. Abubakar ya fara bin wani yayan Goggo suna tafiya Lagas suna sayar da kayan gwari, a lokacin Mommy ta zama budurwa tana da shekara goma sha shida a duniya. A wannan lokacin tana aji biyu na babbar sakandire sakamakon Mahaifinta bai bi sunnar Mahaifinsa ba, don ya ci burin yadda bai yi karatun boko ba ƴaƴansa ba za su taso haka ba. Dukda ya tsaya musu tsayin daka akan karatun addini, Abubakar sai da ya yi diploma sannan ya fara tafiya neman kuɗi. Ita kuwa mommy a lokacin da take aji biyu na sakandire ne wata rana ta fita ɗiban ruwa ta haɗu da Daddy sun shigo garin Albasu don siyan wata gona su mayar da ita kamfani, Haɗuwar Mommy da Daddy babu jimawa Allah ya yi wa Malam Bala Magini rasuwa, bayan wani lokaci da rasuwarsa Daddy ya tura ƴan uwan Mahaifinsa don a nema masa aure. Da farko Goggo ta so dakatar da maganar a cewarta bai kamata a katse wa Mommy karatu ba alhalin ta kusa candy, amma da Daddy ya nuna ba zai hanata karatu ba ya sa Goggo ta amince. Sai dai a ɗaɗɗare take da su Daddy musamman ta da ga irin galla-gallan motocin da suke shigo wa da su cikin garin albasu.

Bayan auren Daddy da mommy ko shekara biyu ba su yi ba ya ɗauko Goggo ya dawo da ita gidan da ya sayawa Inno, saboda tun bayan bikin Mommy zaman garin ya gaza yi mata daɗi. Ga Abubakar yana nesa ga ba miji ita ma Mommy da suke kashewa su binne an yi mata aure, ga ƴan uwan Goggo da suke Uba ɗaya sun saka ta a gaba wai ta ga kuɗi ta sayar da ƴarta saboda zalama. Ɗaukan da Daddy ya yi wa Goggo ba ƙaramin daɗi ya yi wa mommy ba a lokacin Hafsa ita ma ta fara zama budurwa, daga ci da sha har karatun Hafsa Daddy ne yake ɗaukar nauyi. Daga baya da ya kammala gidansa wanda ya fi wanda suke ciki girma, sai ya kwashe su gabaɗaya ya mayar da su kusa da shi. Mommy da Daddy sai da suka shafe shekara sama da goma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, sun yi wayon asibitoci gari-gari ƙasa-ƙasa amma duk wurin da suka je sai dai ace lafiyarsu ƙalau. Da yake Daddy sam bai yarda da maganin gargajiya ba shi ya sa ko na hausa bai yarda sun nema ba, tun suna damuwa har suka fauwalawa Allah lamuransu. Inno ta so Daddy ya ƙara aure amma da yake ta lura bashi da ra'ayi sai ta kawo ido ta saka masa, kuma da yake Mommy na matuƙar basu kulawa tana haƙuri da su ya sa take jin daɗin zama da ita. Don shi kansa Daddy wani lokacin idan suna rikici abin ɓata masa rai yake, sai a sannu da Mommy take nusar da shi wani abin da suke yi har da yanayin tsufa sai Daddy yake zura musu ido.

Bayan sun fitar da rai da samun haihuwa kwatsam wata rana mommy ta wayi gari da matsanancin zazzaɓi da ciwon ƙirji, da yake tana da olsa ko da ta je asibiti abin da ta cewa likita kenan. Suna bata tasa-tasai ciki ya bayyana, nan fa suka shiga murna da farinciki su Inno baki ya ƙi rufuwa. Daddy da kansa ya shige musu gaba suka fita ƙasashen waje don siyayyyar kayan jarirai. Bayan wata tara mommy ta haifo kyakkyawar ƴarta mace, tun a ranar Daddy ya saka mata suna Raihan. Haka ya ƙwallafa rai a kanta ko ƙuda baya son taɓa ta, soyayyar duniya ya ɗora mata duk abin da zai saka ta kuka baya so don wani lokacin har faɗa suke yi da Mommy akanta. Haka suka ci gaba da rayuwa da har Raihan ta fara girma kyau da wayonta ya sake fito.

Lokacin da Raihan tana da shekara biyar a duniya, kwatsam watarana sun fita shan Ice-cream suna hanyar dawowa ta hango wata agwagwa a bakin wani kanti da Daddy ya yi parking zai sayi kayan provision, murfin ƙofar ta buɗe da sauri tana fita ta tunkari agwagwar ta ruƙota da hannu biyu, a daidai lokacin Daddy ya fito daga shagon. Murmushi ya yi don ya yi tsammanin agwagwar birge Raihan ta yi, daga wurin da yake ya furta: "My love kina son na saya miki ne..." Tun bai rufe baki ba Raihan ta ɗago agwagwar ta damƙe fuka-fukanya ta da hannu sosai sannan ta talata da ƙarfi lokaci ɗaya fuka-fukan agwagwar suka fita daga jikinta, suka tsintsinke gabaɗaya. A haukace ta juyo wurin Daddy cikin ƙaraji tana faɗin, "Ita ta cin ye min Ɗana shi ya sa nima ba kasheta." Ilahirin mutanen da ke wurin sakin baki suka yi a tsorace suna kallon ikon Allah, don wannan abin da Raihan ta yi ba su taɓa ganin irinsa ba. Nan take wasu suka dasa mata ayar tambaya suna ganin kamar mayyace maitarta ce ta fito fili.


Littafin kuɗi ne Idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624

22


Daddy kusan suman tsaye ya yi jikinsa har rawa yake yi, ya ƙarasa wurin Raihan yana fisgo hannunta ya ce, "Ke Raihan me kike yi haka?" Idanunta jajawur ta ɗago tana kallonsa cikin wata irin ta ce, "Duk wanda ya hallaka min ɗana sai na yi masa abin da ya fi haka." Da sauri Daddy ya waiga yana kallon mutanen da ke zagaye da su, ya yi ƙasa da murya a daidai kan Raihan ya ce, "To zo mu je gida duk abin da kike so ta zauna." Yana rufe bakinsa ya kai hannu zai riƙota ta fisge, ba tare da ta kula shi ba ta wuce ta buɗe murfin mota ta shiga. Cike da kunya Daddy ya kalli mai kanti yana faɗin, "Don Allah wa kuka sani mai agwagwar nan?" Mai kanta ya yi jim sannan ya ce, "Gaskiya Alhaji ba na ce ga mai ita ba tun da muma a inda ka ganta mu ma a nan muke ganinta." Daddy ya zaro kuɗi masu yawa ya miƙa musu ya ce, "Gashi nan sadakar kuɗin agwagwar ne." A ɗaɗɗare mutanen wurin suka karɓa don ganin abin da Raihan ta yi ya dasa musu shakku a zuciya. Lokacin da Daddy ya shiga mota Raihan na zaune ta kifa kanta a tsakankanin cinyoyinta, kai tsaye daga nan wurin asibiti ya wuce da ita. Bayan ya gama yi wa Likita bayani allurar bacci suka samu suka yi mata da ƙyar don fisge-fisge da bige-bige take yi har sai da ta kai wa Daddy cizo a hannu fatar wurin ta kwaile. Mommy na gida lokacin Daddy ya sanar da ita abin da yake faruwa, hankali a tashe ta tafi asibitin ba tare da ta sanar wa su Inno takamaiman abin da ya faru ba. Bayan ta farka daga bacci garau ta yi kamar ba ita ba, ba a ɗauki lokaci ba likita ya sallame su. Haka suka ci gaba da rayuwa tun Raihan na yin abin sama-sama har ya fara bin jikinta, tun da ta haɗu da wannan larurar babu damar Daddy ya siyo kifi cikin gidan ko wuce wa suka je ta wurin da ake suyar kifi take haukace musu ta yi ta neme-neme tana cewa wani ya sace mata ɗanta zai hallaka shi. Idan kuwa ɗanyan kifi ta ci karo da shi babu wanda ya isa ya ƙwace daga hannunta. Rungume shi take yi ta ƙwaƙume shi tana sunbatarsa haɗe da yi mata wasa kamar yadda babar mace take yi wa ɗanta ko ƴarta.

Duk wanda ya tunkareta a lokacin da take riƙe da wannan kifin cikin biyu za a yi ɗaya, inma ta illata shi da yaƙushi ko kuma ta kafa masa haƙora har sai an kwace shi da kyar. Wannan lamari ba ƙaramin saka su Mommy ya yi a uku ba, duk farincikin da suke ciki ya dakushe kullin cikin fargabar wannan ciwon nata suke yi, kuma idan ciwon nata bai tashi ba sai ta yi ta sabgoginta kamar yadda sauran yara suke yi.Wannan dalilin ya su Inno suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login