Showing 36001 words to 39000 words out of 157890 words

Chapter 13 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

153

Tana gama Haɗiyarsa wani irin tari ya turniƙeta idanunta suka yi jawur, kanta ya fara sara mata ga wani irin gumi da yake tsattsafo mata. Ana cikin haka jikinta ya fara wata irin karkarwa kamar mai jin sanyi, tun tana daga tsaye har ta fara ƙoƙarin durƙushewa, cikin bada ƙarfin gwiwa Abar bauta ta fara magana da ƙarfi, "Kin kasance jaruma karki bari wani ruhin ya rinjaye ki, kin kasance mai nasara kuma har abada za ki kasance mai nasara." Ruhin Raihan ya sake yunƙura da ƙyar yana layi sannan ta samu ta miƙe tsaye daram, tashinta tsaye ya sa kogon wurin ya fara girgiza haɗe da hasken walƙiya. Lokaci ɗaya Hatsabibiya da abar bauta suka ƙyaƙyace da wata irin mahaukaciyar dariya cikin haɗin baki suka furta, "Barka da shiga sabuwar rayuwa yake shugaba." Raihan bata kulasu ba ta wuce ɗakin Kujera ta haye kan wata karagar kujera mai ɗauke da ƙoƙon kawunan bil'adam a saƙale a jiki. Sai da ƙare musu kallo cikin izza, isa da nuna tsantsar mulki ta ce, "Barka dai, a wannan lokacin bana buƙatar hayaniya hutu ya wajaba a gare ni." Tun bata rufe baki ba suka dare daga gabanta kowanne ya kama gabansa.

Kafin wani lokaci Tuni Mama Uwani ta shirya tsaf cikin atamfa, sai da ta yi sallama da su Inno har ta zo bakin ƙofa Inno ta ce, "Saboda Allah Uwani idan muka bari kika tafi dubiyar nan ke kaɗai ba mu yi rashin kara ba?" Mama Uwani ta yi musu murmushi ta ce, "Babu komai Inno ni ma ai gobe zan dawo." Goggo ta yi karaf ta ce, "Ita fa ziyarar mara lafiya lada gare ta, ina ni ina barin lada a wurin Allah? Uwani bari na ɗauko mayafina mu tafi saboda Allah mahafiyarki ai kamar tamu ce gabaɗaya."

(Har na gano idon Goggo a duniyar aljanu)

Mama Uwani ta sake murmushi ta ce, "Ai na ga kuna amsar baƙi ƴan gaisuwa shi ya sa da kin yi zamanki Goggo." Goggo ta yi jim sannan ta ce, "Ke Uwani yi tafiyarki kin ji, ina ni ina zuwa ƙauyenku bansan kalarsu ba haka kawai su lashe min kurwa. A'a raba ni da wannan tafiyar daga nan gidan sai albasu, Albasu babu mai kambun baka balle maita je ki sai kin dawo ki duba mai jiki." Huzaifa ya yi dariya don har zuciyarsa Diramar su Inno bashi dariya take, sannan ya fice daga ɗakin. Kuɗi masu yawa Mommy ta ɗiba ta bawa Mama Uwani tare da kayan abinci sannan suka yi sallama.

Huzaifa na fita daga gidan nan take ya ɓace ya fara lulawa cikin iskar sararin samaniya, bai tsaya a ko'ina ba sai Dajin Bolgal-Kissam a cikin ƙarƙashin ƙasa cikin wara tsohuwar ƙorama. Yana zuwa wasu dakarun aljanu suka dakatar da shi, waɗanda suke zagaye da wani tsohon aljani tukuf. A fusace Huzaifa ya fara fisgewa yana shirin yin magana Dattijon aljanin da ke zaune a tsakiyarsu ya furta, "Tabbas lamarinka ya munana Huzaifa, a kullin ina gaya maka kowa ya bar gida; gida ya bar shi."


TO ME KUKE HARSASHE SHIN HUZAIFA ZAI SAMU BIYA BUƘATARSA KO ƘAƘA😂 INA LABARIN SHUGABA RAIHAN? 😂 INA MUKU FATAN ALHERI🥰


Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min magana ta wannan number 0706 206 2624

12



Huzaifa ya furzar da iska mai zafi cikin ƙunan rai ya dubi sauran sakarun aljanun da suka riƙe su, yana shirin fusgewa ya ruski muryar Dattijon na ci gaba da cewa, "Da ace wannan alƙaryar tana magana tabbas da ita da kaina za ta shaide ni akanka, idan baka manta ba shekaru ɗari huɗu da suka wuce ka yi bankwana da ni da alƙaryata. Kamar yadda nake zaune a wurin nan ranar da za ka tafi sai da na tabbatar maka ko ba daɗe ko ba jima za ka dawo gare ni, kuma sai da na jaddada maka za ka dawo gare ni kana mai neman buƙata a wurin shin akwai abin da na ƙaga na faɗa sabanin abubuwan da suka gabata?" Huzaifa ya murtuke fuska rai a ɓace ya dubi kakansa yana faɗin, "Ka zartar da umarni a sake ni domin wannan ƙasƙanci ne a wurina a ce ina jininka hadima su dakatar da ni."Jabbul-ƙasi ya yi murmushi mai ɗauke da ma'anoni sannan ya ce, "Kowa ya ƙona rumbunsa ya san a inda toka take kuɗi, Huzaifa ka ɓarar da damarka a lokacin da kake tsaka da iko da ita, karka ji haushin kowa ko ka ƙullaci kowa domin duk abin da ya fi kaine sanadi." Jabbul-ƙasi ya tsahirta da zancensa yana kallon Dakarun da ke riƙe da huzaifa ya ce, "Ku sake shi ya ku masu biyayya." Tun bai rufe baki ba suka saki Huzaifa, Huzaifa ya kalle su cikin jin haushi sannan ya fara takawa zuwa mazaunin kakansa. Tsugunne ya yi a gaban Jabbul-ƙasi sannan ya fara da cewa, "Na zo ne domin wata buƙata amma sai ka sallami waɗancan." Huzaifa ya yi maganar cikin isa da ƙasaita. Jabbul-ƙasi ya bushe da wata irin dariya, nan take jaririn aljanu suka firgice domin basu taɓa jin irin wannan dariyar ta sa ba, ƙananan dabbobin da ke kusa da tsibirin suka faɗi matattu wasu daga cikinsu suka bazama, hatta dakarun da ke tsaron tsibirin sai da wani irin matsanancin tsoro ya kama su. Huzaifa yana zaune ƙyam ko motsi bai yi ba, saboda ƙarfin zuciya irin tashi. Jabbul-ƙasi ya jinjina kai yana kallon Huzaifa ya ce, "Idan za mu ninka shekarun da muka yi a baya sau ɗari tabbas halinka ba zai taɓa sauyawa ba Huzaifa, ko ɓata ka yi a cikin dubbanin jinnu wannan ƙarfin izzar taka ita za ta sa na gane kai ɗin jinina ne. Ka aikata min babban laifi sama da shekara ɗari biyu ban sa ka a idona ba, amma yau ka zo da buƙatarka wurina sai dai maganganunka suna nuna min tamkar umarni kake bani." Huzaifa ya ɗago yana yi masa wani irin kallo ba tare da ya furta komai ba, Jabbul-ƙasi ya zurawa Jikan nasa ido yana jiran cewarsa. Sun jima a haka ba tare da Huzaifa ya ce uffan ba sannan Jabbul-ƙasi ya fahimci abin da ya sa Huzaifa ba yi magana ba, ɗaga ido ya yi ya kalli dakarun dake wurin tun bai yi magana ba suka ɓace daga wurin kamar yadda Huzaifa ya buƙata.

Jabbul-ƙasi ya dube shi don jin abin da Huzaifa zai faɗa ba don ba shi da masaniya dangane da abin da yake tafe da shi ba. Huzaifa ya sake ɗaure fuska tamau ya ce, "Matata ce take cikin wani yanayi, duk bincikena na rasa gane inda ta dosa." Jabbul-ƙasi ya yi murmushin dattijantaka sannan ya ce, "Zaujinka wacce kana nufin Mugaza? Domin idan ita ko wata biyar da suka gabata ta kawo mana ziyara ba mu ga wani saɓanin lamari a tattare da ita ba." Huzaifa ya kauda kansa gefe cikin takaici sannan ya ce, "Matata Raihan nake nufi, na aureta tsawon shekarun baya. A da babu abin da yake mini shamaki da ita, ina kusantarta a duk lokacin da na yi niyya. Ta haifa mini ƴaƴa takwas amma duka Mugaza ta salwantar mini da su sai na ƙarshen nan ne ya tsaya. Yanzu haka ita nake zargi akan rikicewar al'amuranta don haka nake son ka yi mini wani abun a kai." Jabbul-ƙasi ya sauke ajiyar zuciya bayan ya gama sauraron Huzaifa ya ce, "Ka riga da ka yi sake ɗan zaki ya girma." Huzaifa ya dube shi cikin rashin fahimta ya yana shirin tambayarsa Jabbul-ƙasi ya ci gaba da cewa, "Raihan matarka ce amma kana tafe da gingimemen ƙalubale a gabanka, ta yi maka nisa mai tazarar gaske don yanzu baka da ikon da za ka sarrafata a ƙarƙashin ikonka." A firgice Huzaifa ya ɗago a firgice don jin abin da Jabbul-ƙasi ya faɗa, hankali a tashe ya furta, "Ka yi mini bayanin da zai gamsar da gangar jiki da ruhina."Jabbul-ƙasi ya kishingiɗa daga wurin da yake ya ci gaba da cewa, "Raihan har gobe matarka ce matuƙar za ka jajirce tsayin daka akan soyayyar da kake mata. Amma batun ka sarrafa ko ka kaita duk wurin da kake buƙa bai taso ba, baka da ikon sarrafata domin tana tare da ruhin Gurzuzu jinnu-nariy.

A firgice Huzaifa ya miƙe tsaye jikinsa na karkarwa ya furta, "Ya aka yi ruhin Gurzuzu ya kai ga Raihan? Waye ya haɗa ta da shi wanene ya tari aradu da ka?" Jabbul-ƙasi ya tashi zaune ya ƙurawa Huzaifa ido yana kallo, kamar ba zai tanka masa ba sai daga baya ya ce, "Ni kaina bansan waɗannan amsoshin ba domin Gurzuzu ya wuce tunanin mai tunani balle ruhinsa. Matsawar tana tare da ruhin Gurzuzu duk wani bincike da zan yi aikin banza ne, a dul faɗin duniya babu wanda zai iya karya alƙadarin ruhin Gurzuzu mutum ɗaya ce tal, kuma a halin da ke ciki ba ni da yaƙinin har yanzu tana doro ƙasa domin tun ina ina goyon mahaifiyarka rabona da ita..." Cikin sauri Huzaifa ya katse Jabbul-ƙasi da cewar, "Wacece ita? A ina take? Wacce alaƙa gare ta da Gurzuzu da har za ta iya karya alƙadarinsa? Ya za a yi na ganta?" Jabbul-ƙasi ya yi murmushi mai sauti yana shirin magana wasu baƙaƙen aljanu suka shiga wurinsa suna sauke ajiyar zuciya, na farkonsu ya fara cewa: "Boka Iliyasu ya sadaukar maka da baƙaƙen raguna biyu tare da zakaru jajaye uku sakamakon aikin matar nan da aka kashe uwar mijinta wacce ka tallafa masa." Jabbul-ƙasi ya jinjina yana murmushi, na biyu ya ce: "Boka Harisu na saman tsauni ya baka kyauta mushen jaki da maguna biyar akan aikin mijin matar nan da ka taimaka masa wacce ta rufe bakin mijinta a kan dukiyarsa." A wannan karonma Jabbul-ƙasi ya sake yin murmushi, suna shirin tashi daga wurin ya dakatar da su da cewa: Yanzu aiki huɗu ne a gabanmu. Na ɗaya akan ɗan Kasuwan nan da za a haukatar da shi kai Bilgilu kaine zaka zartar da wannan aikin. Aiki na biyu akan ma'aikacin kwanstom ne wanda za mu cire masa ƙaunar aiki domin mataimakinsa ya samu nasarar ɗarewa kujerara, kai Billu kai ne da wannan aiki. Sai sauran ayyukan biyun da suka rage na macen nan da zamu sakawa warin jaɓa ne da saurayin nan da zamu kashe shi a kan budurwar nan. Cikin girnamawa suka jinjina kai, Jabbul-ƙasi ya ci gaba da cewa: "Za mu fara aiki daga gobe." Suna amsa masa suka ɓace daga wurin.

Huzaifa da yake cike da ƙaguwa da jin amsar tambayoyinsa ya kalli kakansa yana cewa, "Ina ƙaugauce da jin amsar tambayata." Jabbul-ƙasi ya kalli Huzaifa yana faɗin, "Duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu, Huzaifa daɗina da kai gaggawa shi ya sa saurari lamuranka suke chaɓewa. Burtultika ita ce macen da za ta iya sarrafa ruhin Gurzuzu, a ƙalla ta bani shekari dubu ɗaya da ɗari biyu. Tana rayuwa ne a dajin KALULLUƁU da ke ƙarƙashin Tsauni Zukkin. Daga wannan tsaunin nawa tafiya ce ta shekara ɗaya da rabi, idan har ka same ta da rai za ka yi zaman watannin biyar a fadarta kafin ka samu ganawa da ita. Idan ka sadu da ita tamkar buƙatarka ta biya, ita ɗin tsohuwar budurwar Gurzuzu ce. Labari ya same ni cewar Gurzuzu ya mutu ne saboda tsananin kishinta, ko uwarsa baya jin maganarta kamar yadda yake jin maganar Burtiltika." Jabbul-ƙasi ya kalli Huzaifa cikin rashin damuwa ya ce, "Dabara ta ragewa mai shiga rijiya zaɓi ya rage naka, idan za ka juri wannan tafiyar zan iya taimaka maka da dakarun aljanu masu yi maka rakiya. Idan kuma ba za ka iya ba shi kenan ka ƙyale yarinyar mutane ta ci gaba da rayuwa, kaima ka ci gaba da rayuwarka da Mugaza.


"Koda nisan tafiyar ta yi nisan zai ƙare numfashina zan hallici wurin domin zan iya sadaukar fa komai don ganin jindaɗi, walwalar Raihan sun dawo. Taimako ɗaya na ce ka yi min domin neman hanyar mafita, amma ba na buƙatar agajin dakarunka. Raihan tawa ce ni kaɗai don haka wannan yaƙim nawa ba na neman sa hannun kowa, zan koma gida domin na ɗaura ɗamarar zuwa ga dajin KALULLUƁU." Zumbur Huzaifa ya miƙe yana shirin tafiya Jabbul-ƙasi ya katse shi da cewar, "Ina alfahari da samun nagartacen jika tamkar ka, amma ka sani akwai ƙura a tatattare da yarinyar nan bincike na yana nuna wata baƙar ƙura na bibiye da inuwa yarinyar. Zan yi maka fatan nasara domin duk lalacewa kai ɗim jinina ne, dukda kai mai bijirewa umarnina ne zan fi son ka yi nasara ko ba komai za ka shiga kundun tarihi na wanda suka ziyarci Burtultika." Huzaifa har ya je bakin ƙofa ua waiga ya ce, "Ka riƙe fatan nasararka domin ni dama can ɓai nasara ne." Yana gama maganar ya fice daga tsaunin, Jabbul-ƙasi ya yi murmushi mai ɗauke da ma'anoni a fili ya furta, "Yaro kenan man kaza."


Lokacin da Mommy koma ɗakin Daddy tuni ya yi sallah ya koma ya kwanta, a gefensa ta zaune murya a sanyaye ta fara yi wa Daddy magana. "Daddyn Raihan!" Janye blanket ɗin fuskarsa ya yi bai amsa mata ba ya zuba mata ido tare da sakar mata murmushi, ganin yanayinta kaɗai ya tabbatar masa da tana cikin matsananciyar damuwa. Nan take ya ji ta bashi tausayi don shi kansa ya san macece mai juriya da ƙarfin hali, tana shirin yin magana ya rigata da cewar: "Zainab!" A hankali ta ɗago idanunta tana kallonsa ya ci gaba da cewa, "Me yake damunki." A madadin ta bashi amsa sai kawai ta faɗa jikinsa ta fashe da wani irin matsanancin kuka, hannu Daddy ya sa a bayanta yana bubbugawa a hankali yana faɗin, "Shiiiii ba kuka na ce ki yi min ba." Mommy sai ta yi mai isarta sannan ta ɗago tana faɗin, "Daddyn Raihan gidan nan sam bashi da kyau, don Allah ka sauya mana domin jiya tsorata ni aka yi Allah ne kaɗai ya sa ina da yawancin kwana." Ido ya zura mata yana kallo sai kawai ya ji ta bashi tausayi, ya samu kansa da cewa: "Ina kike son mu koma? Kar ki manta kwananmu ɗaya yau da tarewa." Mommy ta yi jim sannan ta ce, "Haka ne amma gaskiya ina jin tsoro." Duk abin da ya faru da ita sai da Mommy ta sanar masa shi kansa Daddy jikinsa ya yi sanyi don haka ya amsa mata da cewar: "Kin ga muna shirye-shiryen tafiya India mai zai hana mu fara nemawa Raihan lafiya idan za mu dawo sai mu sauya gida, ina ga kamar haka zai fi." Mommy har ta fara aminta da maganar Daddy ta ce, "To idan mu za mu tafi India ya za mu yi da su Inno? Ina jin tsoron kar a tsorata su kasan ga jikin girma." Cikin gamsuwa Daddy ya gyaɗa kai yana cewa, "Tabbas kin yi tunani mai kyau a yau insha Allah zan san abin yi ina jin na sa a gyara gidana na Rijiyar zaki." Ba ƙaramin daɗi mommy ta ji sannan ta ce, "Ya kamata a yi saukar Alƙur'ani kafin a shiga gidan saboda shaiɗanu." Daddy ya yi dariya yana faɗin, "Oh Zainabu ko da mai rauhanai zan sa miki? Kullin baki da magana sai ta shaiɗanu, to ai shi kenan yadda kika ce haka za a yi uwargida sarautar mata tun da kin maidani mijin hajiya." Mommy ta kashe masa ido ɗaya tana faɗin, "To ai dama ba a canzawa tuwo suna." Daddy ya birkitota jikinsa yana cewa, "Wai yaushe za ki nemar mini ƴar budurwa na aura ne, ko a ƙawayen Raihan ki duba min mai hankali man." Mommy ta yi masa harar wasa tana faɗin, "Na ga ka fini manyan idanu ka duba wacce ta fi maka, ba don ina kishi ba da sai na ce ka auri Intisar don ta fi sauran nutsuwa." Daddy ya sa dariya ya ce, "Wai Allah don Allah daina faɗa gemai-gemai da ni ai sai girma ya faɗi, kedai kawai kin binne min kan angulu don kar na ƙanƙaro amarya." Gabaɗaya suka saka dariya.


A ranar Daddy ya bada umarnin a gyara gidansa da ke Rijiyar zaki, mommy ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Bayan tafiyar Mama Uwani ta ƙara saka karatun kur'ani ta sake kwanciya don bata sami wadataccen bacci ba. Daddy na hanyar komawarsa gida ya kira lambar Dr sai da suka gaisa Daddy ya ce, "Dr ya ake ciki da maganar tafiyarmu, bizarmu fa ta fito duk abin da ake buƙata ya kammala na ji baka sake yi min maganar ba, ga shi har yau ba mu sake yin waya ba." Dr ya yi jam sannan ya ce, "Wacce irin tafiya Alhaji? Wallahi jiya na so na kira na baka haƙuri a kan rashin zuwan da na yi, sakamakon wani yanayi da na ji amma sai na ga dare ya yi..." Daddy ya katse Dr da cewar, "Ban gane abin da kake nufi ba." Dr ya yi gyaran murya ya ce, "Alhaji jiya ba ka kira ni akan rashin lafiyar Raihan ba?" Daddy cikin sauri ya amsa da, "Eh haka ne." Dr ya ci gaba da cewa, "Na taso zan zo dubata kaina ya sara ban kuma sanin wurin da nake ba sai goma saura, to na so na kira ka kuma dare ya yi." Daddy jikinsa ba ƙaramin sanyi ya yi ba, a hanzarce ya ce, "Dr ni fa kaina ya kulle jiya ba kai ka zo ka dubata har ka yi min maganar zuwa India ba?" Dr cikin mamaki ya ce, "Kai an ya kuwa Alhaji ko dai baka gidan ne Alhaji." A gaggauce Daddy ya ce, "Kana ina yanzu zan zo na same ka."Kai tsaye Dr ya kwatanta masa wurin da yake, Daddy ya bawa motarsa wuta yana gabda ƙarasawa ya ci karo da mata matashiyar budurwa tsugunne a kan titi ta kifa kanta cikin cinyoyinta da alama kuka take yi.

Yau kunsha kura-kurai ban yi Editing ba a yi sorry🥱


LIttafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min magana ta wannan lambar. 0706 206 2624


13



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login