Showing 33001 words to 36000 words out of 157890 words

Chapter 12 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

129

kaɗan bai san ana yi ba, sai dai har lokacin bakinta yana ci gaba da karanta ayoyin Ubangiji, da abar bauta ta zo kawo mata cafka sai ta ga mommy ta zille mata kamar tarwaɗa. Kabiru na shiga ɗaki ya koma ya kwanta sai dai fir idanunsa sun bushe bacci ya ƙaurace masa, tashi ya ƙara yi ya fito a ƙofar ɗakinsa ya ɗaura alwala yana shirin shiga ɗaki ya ji ƙusur-ƙusur ɗin ya yi yawa. A hankali ya fara takawa yana haske-haske da ƙaramar fitilarsa, daga can bayan ɗakinsa ya hango Mommy a kwance sai shure-shure take yi tana motsa baki da alama magana take yi. Tsoro ne ya kama shi don ko a mafarki bai taɓa ɗauka mommy bace a wurin, a tsorace ya fara faɗin, "Hajiya lahiya kuwa?" Mommy hannu ta fara miƙa masa tana kiran sunansa, ganin haka ya sa Kabiru ya fara ƙoƙarin miƙa hannu don ya taimaka mata amma tunowa da abubuwan da suka faru da shi ya sa ya ja da baya yana karanto aytulkursiyyu ya fara tofa mata tare da falaƙi da nasi. Kamar wanda aka yi wa wankin kunne raɗau ya ji maganar Mommy a kunnensa saɓanin da; da baya jin abin da take faɗa, tsugunnawa ya yi a wurin yana faɗin, "Hajiya me ya fito da dake a tsakar daren nan?" Mommy da ta ji jikinta ya fara sarara mata ta ce, "Kabiru taimaka min ka kaini ciki kar su halaka ni." Kabiru ya zaro ido yana dube-dube yana shirin magana mommy ta dafo hannunsa da sauri ya yi baya yana kurma ihu don ya gama tsorata gabaɗaya. Abar bauta da take laɓe ta fara Allah-Allah akan Kabiru ya basu wuri don ta dawo ta ci gaba da abin da take niyyar aiwatarwa, donma ita kanta Mommy ba ƙaramar wahala suka sha akanta ba amma so take ko ta wanne hali ta samu ta lakuci jinin jikinta idan ya so ko da sihiri ne in sun kaiwa ɗakin arziƙi jininta magana ta ƙare. Kabiru har zai shige ɗaki da gudu sai wata zuciyar ta ayyana masa ta yuwu ita ma shaiɗanu sun yi mata abin da suka yi masa ne har suka tsorata ta fito. Bakinsa ɗauke da addu'a ya sake tunkararta Mommy ta dafa kafaɗarsa ta miƙe tsaye tana layi, da ƙyar ta iya tsayawa a kan ƙafarta ta fara takawa da ƙyar kanta na ci gaba da sara mata. Kabiru na raka ta bakin ƙofa zai juya fir mommy ta ƙi yarda don har sa da ta saka Kabiru ya rakata har ƙofar ɗakin Daddy sannan ya koma ɗakinsa, tana shiga ta zube a bakin ƙofa tana ci gana da karanta duk ayar da ta zo bakinta. A lokacin da ta koma ɗakin tuni Daddy ya yi bacci, da rarrafe ta fara rarrafawa zuwa bakin gadon tana kiran sunansa. Sai dai babban abin da ya sake firgitata yadda ta ji yana sauke wani irin munshari mai ban tsoro, ga ƙwan ɗakin da fara ɗaukewa yana kawowa.


Raihan da abar bauta kusan tare suka koma kogon dutsen ƙungiya kowannensu fuska babu walwala, abar bauta ta dubi Raihan rai a ɓace ta ce: "Mahaifiyarki za ta bamu matsala domin tana da riƙo da addini. Sannan wannan Bafulatanin yana ƙoƙarin wargaza shirinmu tabbas za mu ɗau mummunan mataki a kansa, amma fa duk da haka Mahaifiyarki bata sha ba domin za mu ɓullo mata ta sigar da ba za ta taɓa tsammani ba. A yau saura kwana biyar ta fara al'ada don haka zan yi amfani da wannan lokacin, domin alƙawarinta na yi ga ɗakin arziƙi." Raihan ta jinjina kai cikin girmamawa, abar bauta ta nuna wata ƙaramar ƙorama ta ce,: "Ki ɗebi ruwan wanke zunubi ki yi wanka domin kin karya ƙa'idoji da dokar ƙungiya." Raihan na yin wanka kamar yadda Abar bauta ta umarceta ta fice daga kogon dutsen.

Intisar ce ta ɓullo daga ƙarƙashin ƙasa ta yi gaisuwa ga abar bauta, kusan cikin haɗin baki suka furta, "Huzaifa zai aika da Raihan ƙasar India don bincike na musamman akan Raihan." Abar bauta ta yi murmushin takaici ta ce, "Na san da haka shi ya sa na nemo ki yanzu. Zai kaita India ne wurin Kakansa Jibbul-Ƙasi don ya yi mata bincike a kanta, ya ɗora zarge-zarge akanta ciki kuwa har da ke." Intisar ta jinjina kai sannan ta ce, "Tabbas na san za a yi haka domin na san wanenen Huzaifa da bin didiginsa." Abar bauta ta miƙe tsaye sai da ta yi zagaye wurin sau uku sannan ta ce, "Ba zai yi nasara a kanmu ba, domin za mu mallakawa Raihan duk wani ƙarfin iko, idan a da bata san wacece ita ba ya zama dole mu sanar da ita ta hanyar sakata a ɗakin arziƙi." Hankali a tashe Mugaza ta ɗago tana faɗin, "Kina nufin tun yanzu za ta mallaki shuɗaɗɗan ruhi ba sai nan gaba ba ya Abar bauta." Abar bauta ta ci gaba da tafiya tana jinjina kawunan jikinta ta ce, "Alƙawarin ƙungiya baya tashi, matsawar Huzaifa ya kaita wurin kakansa tabbas sai ya gane shirinmu kuma sai Kakansa ya wargatsa ƙungiyar nan. Idan kuwa muka saka mata shuɗaɗɗan ruhi dole zai zama garkuwa a gare ta, za ta gagari Jabbul-Ƙasi da dukkan wani shirinsa.

WASAN YA FARA ƊAUKAN ZAFI🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ RAIHAN TA KUSA ZAMA SHUGABA LIKAFA TA CI GABA😂😂 MENENE ALAƘAR SHUƊAƊƊAN RUHI DA RAIHAN, SHIN DAMA RAIHAN NA DA WANI A ƘUNGIYAR ASIRI NE DA HAR RUHINSA ZAI MAYE GURBINTA KO YAYA? WACCE ALAƘA CE TSAKANIN SHUƊAƊƊAN RUHI DA KAKAN HUZAIFA JUBBUL-ƘASI? CAKWAKIYAR ƘARA GABA TAKE🥵 MAZA HANZARTA KI BIYA DON JIN YADDA ZA TA KASANCE GARA KI BIYA 300 KI KARANTA AMMA IDAN NA KAMMALASHI SAI KIN SAKA 500 ZA KI SAME SHI🥱🥱🥱 WANNAN SHI NE SHAFIN ƘARSHE WATO SHAFIN ƘAUTA😎 MU JE ZUWA ƳAN GROUP ƊIN *ZAUJATU PAID* A CI GABA DA GASH SUYA SAI RANAR BIKIN NAƊIN 👸🏻 RAIHAN A ƘOGON DUTSEN ƘUNGIYA🤸🏻‍♀️💃🏼

SHARE HILIS🌚

11



"Amma ya kamata ku kwana da sanin Jabbul-ƙasi hatsabibin aljani ne hatta cikin jinsin Aljanu suna matuƙar shakkar shiga gonarsa, ya wuce tunanin mai tunani ya wuce duk inda muke tsammani. Ina tsoron a samu matsala don na tabbata muddin aka samu matsala gabaɗayanmu ba za mu kuɓuta daga hannunsa ba." Hatsabibiya ta yi maganar tana ƙarasowa wurin hannunta sarƙe da na mijinta. Abar bauta ce ta kalleta tana jinjina kai sannan ta ce, "Na san wanene Jibbul-ƙasi don haka ba zan bar wani giɓi da zai sa kwaɓarmu ta yi ruwa ba, amma dole sai mun yi iya bakin ƙoƙarinmu don kar a samu matsala. Mugaza da har lokacin take cikin matsanancin tashin hankali, ta ƙarasa gaban Abar bauta tana cewa: "Abar bauta na shafe sama da shekara ɗari uku a cikin ƙungiyar nan, na yi muku biyayya tun bansan daɗin zaman ƙungiya ba. Ban taɓa bijirewa umarninku domin ku ɗin masu biyan buƙata ne." Abar bauta ta jinjina kai tana murmushin jin daɗi da irin kambabawar da Intisar ta yi mata, Mugaza ta sake marairace murya sannan ta ci gaba da cewa, "Haƙiƙa duk duniya babu wacce na fi tsana sama da Raihan, na kawo ta ƙungiya ne domin a hallakar da ita bisa karan tsaye da ta yi a zuciyar mijina. Amma sai ga shi a lokaci ƙanƙani tana shirin yi min fintinkau cikin ƙungiyar nan, Shin abar bauta kina tunanin idan ta maye gurbin shuɗaɗɗan ruhi alaƙata da ita za ta ci gaba da rufuwa kamar a baya. Karku manta a baya na je mata a zuwan Intisar wato aminiyarta da suke karatu a University ɗaya, babu wanda bai san abotarmu da Raihan ba kuma duk na yi ne don biyan buƙatar kaina. Ina tsoron kar ta samu nasarar maye gurbin shuɗaɗɗan ruhi asirina ya tonu a wurinta domin har abada ba zan yafe mata irin baƙincikin da ta jefa ni a ciki ba koda zan rasa raina. Ta gadar mini da ɓacin ran da har yau na gagar wanke shi, ta farraƙa tsakanina da miji tare da ƴaƴana gabaɗaya. Alƙwari na ɗaukarwa kaina duk daren daɗewa sai na hallakata da kisa mai tsanani ko dan na samu damar fanshe abin da ta yi min. Amma dole zan jinkirta har sai wa'adin zamanta a ɗakin arziƙi ya zo domin zamanta a ƙungiya ni kaina babbar nasara ce." Abar bauta ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya mai nakasa kunnuwan mai sauraro sakamakon kasancewar duk kawunan da ke jikin abar bauta ne suke ɓaɓɓaka dariya. Abar bauta na yin shiru Gawunge da ke gefe mijin Hatsabibiya ya sa hannuwa biyu ya fisge kansa da ke haɗe da gangar jikinsa sannan ya ƙurawa Intisar idanu lokaci ɗaya ya fashe da kuka mai haɗe da dariya. Sai da ya yi mai isarsa sannan bakinsa ya fara magana da yake jikin dungulmin kan da cewar, "Aikin abar bauta baya ɓaci domin ita shakundum ce, bata aiki kara-zube don komai nata a lissafe yake. Shekarata Ɗari da ashirin ina cikin daskararriyar rayuwa, tun kafin kasancewar haka Abar bauta ta min alƙwarin dawowa cikin rayuwata ta baya, don haka ki daina wasu-wasi akan duk abin da abar bauta za ta faɗa." Mugaza har lokacin fuskarta babu walwala sai dai ta ɗan samu ƙwarin gwiwa, Abar bauta ta fara wani irin zagaye lokaci ɗaya ta yi gammo tamkar wawakekiyar rijiya nan take ƙura ta garwaye wajen, daga cikin ƙurar wani ƙasurgumin maciji ya bayyana. Da ace mutum zai yi tozali da wannan macijin zai yi tsammanin wata shirgegegiyar bishiya ce don jikin macijin tauri gare shi tamkar jikin katuwar bishiyar kuka, tsayin macijin bashi da iyaka illlah ƙaton kanta da yake nannaɗe a tsakiyarta. Da ace Macijin zai kwanta zai iya rufe ƙaton gida da abin da yake cikinsa. Baki macijiyar ta buɗe sai ga amon wuta na fitowa daga ciki, ganin haka ya sa Intisar ta yi sujjada cikin neman afuwa tana faɗin, "Tuba nake abar bauta, a gafarce ni na aikata zunubi amma wannan shi ne na farko na ƙarshe." Wasu ƙananan hallitu masu kama da jaririn jakuna suka ƙaraso wurim Mugaza suna tayata nema mata afuwa. Wani ruwa ne ya fara fita daga bakin macijiyar nan take wutar ta mutu sannan ta fara magana cikin wani irin gurnani mai firgitarwa, tana jima tana gurnanin sannan ta fara magana cikin wani irin yare mai rikitarwa.

🥵 Bari mu ɗana yarensu🥱

( Waskibatin kintasur minbaskila, haisartan kalbiskutu lakastu baksitu warkidasu baigalliasu fatafursu kininar.... Mu bar shi haka😂)

"Mun yi miki rangwame domin aikata zunubi ba aikinki bane, amma ki sani ni abar bauta na gagari kowa a duniya saboda ina iya sarrafa komai yadda nake so. Asirinki ba zai taɓa tomuwa a wurin Raihan ba, za ki ci gaba da yaudararta kuma Huzaifa dole mu katange ki da shi domin ya saka miki ido yana bin diddigin ke wacece, duk da mun sakaya ruhinki a wurinsa. Sanin kanki ne ɗakin arziki kamar gadon mulki ne duk wanda ya hau shi sai ya sauka, za mu ɗora Raihan karaga mulkine don cimma burrin ranmu, da zarar aikinta ya kammala a wurinmu za mu shafe babinta. Amma ki sani ya zama miki wajibi ki kula da kwalbar sihiri domin muddin ta sha iska tamkar ruhin Raihan ne ya ke shaƙar isar ƴanci. Duk wannan abin da take yi tana yin sa ne ba a cikin hayyacinta ba, karku manta mun yi galaba a kanta a ranar da take Chartting a banɗaki lokacin da ta zagaya bayan gida tana tsugunno tana chartting ta nan muka yi amfani da wannan damar don ganin mun gayyaci ruhinta, ba zan ja ki da nisa ba amma zan jaddada miki adana kwalbar sihiri har lokacin da buƙatarmu za ta biya.

A hankali mommy ta fara ja da baya bakinta na ci gaba da furta addu'o'in kariya, sai dai har lokacin a tsorace take. Ido ta sake zurawa Daddy lokaci ɗaya ta daina jin wannan gurnanin da yake yi mai abin tsoro, tana shirin yi masa magana daga can wajen ƙofa ta fara jin wata irin ƙara mai haɗe da kuka, ihun Raihan take ji sosai har da shassheƙa lokaci ɗaya zuciyarta ta sake tsinkewa sai dai wannan karon bata jin za ta iya zuwa, duba da irin firgicin da ta shiga. Daga kan Mudubi ta hango wayarta da sauri ta rarrafa ta janyota, cikin hanzari ta fara lalubar ɓangaren da Audio yake tana shiga ta ci karo da suratul baƙara, hannunta har rawa yake yi ta danna nan take karatun ya karaɗe cikin ɗakin. Kamar an yi ruwa an ɗauke haka ta ji komai ya ɗauke mata, wata nutsuwa ta sake saukar mata. Ta yunƙura ta ƙyar ta haye gado kusa da Daddy ta kwanta a jikinsa tana sauke wata irin ajiyar zuwa, ta jima a kwance tana saƙa da warwara dangane da abin da ya faru da ita sai daga baya bacci ya yi gaba da ita.

WASHEGARI.

Kasancewar bacci bai ɗauki mommy da wuri ba sai wurin asuba ya sa ta makara, ba ita ta farka ba sa wajen ƙarfe bakwai saura, da sauri ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala tana fitowa ta fara bubbuga filon da Daddy yake kai tana faɗin, "Daddyn Raihan ka tashi mun makara." Cikin magagin bacci Daddy ya yi miƙa yana faɗin, "Asuba ta yi ne?" Haushi ne ya kama Mommy don tana burin ta ga mijinta na da tsayayyir ibada amma hatta sallar asuba sai ta tashe shi, idan kuwa ita ta makara to sai dai su yi sallah da safiyar Allah. Kan dadduma ta hau tana saka hijabinta ta ce, "Don Allah ka tashi bakwai saura fa dubi rana har ta fito." Daddy ya yi juyi yana mutsuka idanu, Mommy tana gama magana ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta jima a kan sallaya tana addu'o' sannan ta shafa ta koma kan Daddy ta sake tashinsa. Bayan ya shiga toilet hijabinta ta ajiye ta nufi hanyar fita don ta tashi Raihan saboda ta tabbatar bata tashi daga bacci ba. Tana tafe gabanta na faɗuwa don abin da ya faru a daren ranar ne yake sake faɗo mata, cikin dakiya ta ci gaba da takawa tana tafe tana karanta Amanarrasulu. Lokacin da ta zo bakin windon da ta ga Raihan na zaune ta jima a wurin tana kallo sannan ta wuce sashen Raihan ta tura ƙofa, tana shiga ta same ta daga ita sai wata yaloluwar riga iya cibiya tare da gajeren wando da kaɗan ya fi pants. Bubbuga fulonta Mommy ta fara yi tana kiran sunanta, Raihan har ta ɗago ta kafe Mommy da ido sai kuma ta sake tafiya luuuu bacci ya sake yin gaba da ita. Mommy ta sake ɗago da Raihan tana faɗin, "Ke Raihan me yake damunki ne tashi ki yi sallah." A hankali Raihan ta buɗe idonta sannan ta yunƙura ta tashi zaune cikin magagin bacci ta ce, "Mommy lokaci ya yi ne?" Mommy ta watsa mata harara tana faɗin, "A'a ke ake jira, yarinya kullin sai antashe ki sallah amma kullin abin ki ƙara gaba yake." Raihan ta tashi tana tura baki gaba ta ce, "Ai ke dama kullin mommy a cikin masifa kike shi ya sa nafi son Daddy wallahi." Kanta ba ɗan kwali ta nufi banɗaki da sauri Mommy ta buga mata tsawa tana miƙa mata hularta da ke kan katifa. Ba don ta so ba ta amsa ta faɗa ba tare da ta furta kalma ɗaya ta addu'a ba. Mommy na tsaye Raihan ta fito ta fara duba drower kayanta tana lalubar hijabinta. Ganin haka ya sa Mommy ta fice ta bata wuri, kai tsaye ta wuce sashensu Inno. Tura ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama tana faɗin, "Inno barkanku da safiya." Bacci ta same su suna yi ganin haka ya sa ta fice daga ɗakin, ɗakin baƙi ta leƙa ta samu Safara'u wasu ƴan uwan Inno da suka rage basu fi mutum biyar ba, sai da suka gaisa sannan ta fito. Tana shirin hawa sama ta riski muryar Mama Uwani na gaisheta sai dai yanda ta lura kamar Mama Uwani na cikin damuwa. Bayan sun gaisa har mommy za ta haye sama da juyo ta ce, "Uwani lafiya kuwa?" Idanun Mama uwani suka ciko da ƙwalla ta ce, "Hajiya ina cikin damuwa, yanzu haka yau da farar safiya aka yi min waya ciwon Mahafiyata ya tashi." Fuska ɗauke da damuwa Mommy ta ce, "Ciwon Inna ne ya sake tashi." Mama Uwani ta gyaɗa kai tana sharce hawaye, Mommy ta yi ƙasa da muryar cikin tausayawa ta ce, "Allah ya bata lafiya amma gaskiya ya kamata ki je ki dubo ta yau don Mahaifi ba wasa ba." Mama uwani ta goge ƙwallar idonta tana faɗin, "Allah ya saka da alheri Hajiya." Mommy ta ɗan bata fuska ta ce, "Na ce ki daina yawan yi min wannan godiyar mama uwani mun riga mun zama ɗaya. Ki shirya yanzu idan kin gama ki yi min magana, kafin ki tafi ki shiga store ki tafi musu da kayan abinci." Mama Uwani ta tsugunna har ƙasa tana godiya bisa tsautsayi kofaton ƙafar Mama uwani ya bigi ƙafar mommy har sai da mommy ta ɗan yatsuna fuska saboda zafin da ta ji, amma sai bata kawo komai ba ta ɗago Mama Uwani tana faɗin, "Haba Uwani tashi don Allah. Mama Uwani ta tashi sannan mommy ta wuce wurin Daddy.

Raihan na ɗago hijabi ta ji wani irin jiri na ɗaukanta, da ƙyar ta iya dafa bango ta ƙarasa bakin gadonta, ƙarasawarta keda wuya ta yanke jiki ta faɗi. Abar bauta na ganin ruhin Raihan ya fita daga jikinta ta yi murmushin samun nasara, Raihan ce tsaye a bakin ɗakin arziƙi wani irin farin hayaƙi mai ɗauke da surar wata irin hallita ya fara zagaye Raihan, sannu a hankali Abar bauta ta zagaya gaban Raihan ta ce, "Kasancewarki a nan yana nufin zamtowarki Shugaba, buɗe bakinki domin mallakar shuɗaɗɗan ruhi." Ba musu Raihan ta hangame bakinta nan take wannan farin hayaƙin ya fara shiga ta cikin bakinta, ya jima yana tafiya sannan ta haɗiye shi gabaɗaya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login